Showing 108001 words to 111000 words out of 131263 words
sauri ganin yadda Musbahu ya sauka Daga kan gayen dake kwance malale akan gado tamkar ruwa Don ya kasa katabus gara Musbahun ya samu courage din mikewa.
Gaba daya Khulthum ta manta ta rufe kofar hakan yasa ta dinga jijjiga kofar tamkar zata balla kofar amma ko gezau kofar baiyi ba a haka Musbahu ya iske ta, hannunshi ya daura akan kafadar ta, tamkar garwashi haka taji ga wani masifar tsoro da ya kara turnuke ta, juyo da ita yayi Fuskarshi tamkar ta zaki wanda ya shekara bai ci ba gashi kuma ya hadu da abincin shi, babu ko imani digo a Fuskarshi ya fuzge Hijabin dake jikinta, take jikinta ya bayyana cikin wata riga wadda Baki daya net ne fari tas wanda in har Namijin da yake lafiyayye ne to tabbas sai hankalinshi ya tashi amma ko a jikinshi se wani mugun kallo da yake bin ta da shi na bakida Abinda zaki birgeni dashi.
Tsugunnawa yayi don tun sakkowarshi daga gado yaga key din bedroom din, kofar ya bude, Khulthum dake gefe ta taho cikin wani azababben sauri zata fita ya rike hannunta tamau yadda duk wannan tirjiyar da take ta gagara kwace hannunta, juyawa yayi Yana duban wannan gayen da tuni ya Mike ya maida kayanshi jikinshi ya fito ya wuce ba tareda yace uffan ba, yana fita Musbahu ya maida kofar ya rufe tareda zare key din daga kofar ya cigaba da jan hannun Khulthum wadda ilahirin jikinta rawa yake, tasan tayi iskanci a waje amma ko sau daya a Rayuwarta bata taba tunanin haka daga Musbahu ba, Gay! Neman Maza yake! Hannunta ta kara kokarin kwacewa amma ya mata rikon tsauri, ganin tana neman wahalar da shi yasa ya hankada ta kan gadon, kafin tayi wani yunkurin kubcewa har ya hayo gadon, idanunta ta Kara budewa tareda bude bakinta tana fadin
"Dan Allah...... "
Muryarshi ya bude wanda Tunda take bata taba jin Irin wannan Amon ba, shikanshi ya isa firgitata
"Ba hakkinki kika zo karba ba? Fine"
Wajen Mintina ashirin babu Abinda yake tashi cikin part din na Musbahu banda ihu da kururuwar Khulthum tamkar wadda ake zare mata ranta, Tana kwance babu komai jikinta se rizgar kuka take tamkar an bata sakon mutuwa, a hankali kofar da nake tunanin Itace ta toilet ta bude, the Charming Musbahu ya bayyana cikin wata farar bathrobe, kanshi ruwa Yana ta diga, kamar kullum fuskarnan babu digon annuri akai, daidai inda take ya tsaya Yana Kare mata kallo tareda jin ihunta na kokarin tarwatsa mishi kwakwalwar kanshi bawai don tausayinta ba a'a se Don naturally baya son hayaniya.
"Kinzo ki karbi hakkinki sanann kinzo kiga me nake aikatawa, ban so kika ga hakan ba saboda kada zuciyarki ta buga, Amma duk Abinda na fada miki kada ki cika bincike amma kika saka kafa kikai fatali da hakan. Ina fatan you're satisfied, idan kina bukatar Kari zan baki saboda ban taba kawowa Anal sex haka take da dadi ba se yau"
Yana gama fadar haka ya wuce cikin walk in closet dinsa ko Mintina ashirin bai kara ba ya fito ya shirya cikin sweat pants black da Top maroon , kallon ta ya kuma Yi har lokancin Bata motsa Daga gurin ba amma kukan ya dauke sakamaakon dusashewar da muryar ta yayi saboda yadda ta bude murya da makogaro tana kwarara ihu.
"Tashi ki fitar min a daki"
Ya fada cikin kakkausar murya, jikinta na rawa ta Mike tare da daukar Hijabin da ta zo dashi tayi waje a million, sosae hakan ya bashi dariya, ya dauke kanshi babu ko dar na tsoro cikin zuciyarshi, ta hutar dashi da tazo ta ganewa idanunta komai, ba se yayi bayani ba.
Khulthum Seda ta taka kafarta cikin part din sannan ta ji wani Irin azababben radadi ta gurin Bayan gidanta, kafafunta sunyi mummunan sagewa ga tarin gajiya da tayi mata rubdugu, da kyar tana Jan kafa ta isa dakinta ko gado kasa hawa tayi haka ta kwanta kan carpet idanunta na zubar da hawaye.
A hankali ta samu damar tuno Irin mugun ganin da tayiwa Mijinta, hade da wani katon namiji ba ma mace ba, babban laifun da Allah ya hallaka mutanen Annabi Lut AS Amma ita mijinta kenan, ga wani haramci da ya tafka wato Anal sex, saduwa ta dubura wadda Allah da manzonshi sukai Hani akan hakan, Kaddara ta kenan! Auren GAY!!!
Karfe daya na ranar litinin motar da ta taso Daga Kano zuwa kaduna ta sauke passengers dinta a Tashar DIT dake alheri radio. A hankali Subay'a ta sakko daga motar janye da trolley, hannunta da handbag yar karama, tana Kallon mutane yadda suke ta kai kawo, Bata kalla kowa ba duk yadda 'yan union suke tambayarta inda zataje amma bata kula kowa ba, hankalinta yana ga Irin tarbar da zata samu daga inda zataje. Napep ta tare tare dayi bashi address din gidan, ya yanko kudi daidai suturar jikinta ya fada mata ta shiga suka wuce zuwa gidan da ta manta rabon da kafafunta su taka.
Kofar gidan Rtd Gen. Lukman Birnin kudu Subay'a ta tsaya tana tunanin ta inda zata Fara, ta jima a tsaye ba tareda sanin inda ta kama ba, ga kuma Anxiety.... The fear of Unknown, ta isa bakin kofar dan fara kwankwasawa taga an bude tangamemen Gate dinsu. Jawad ne ciki wanda ke kokarin fita zuwa Aiken Mami, kamar yasan tana tsaye ya juyo idanunsa gurin karaf suka hade. Fitowa yayi tare da nufo inda take tsaye kanta a kasa saboda tsabar kunya, ta tuna lokutan da Jawad ke zuwa gidan ta tayi mishi banza.
"Maman Ahmad Yaushe kika zo? "
Kanta ta dago tace
"Yanzun. Mami na ciki? "
Kanshi ya gyada yace
"Tana ciki Ki shiga"
Kanta ta gyada ya koma mota itakuma ta shiga, dake sojojin dake gate din sun Santa, hakan yasa suka gaida ta, Smith har kokarin karbar trolley din hannunta yayi amma ta mishi godiya ta wuce ciki. Tunda ta zura kafarta tasan akwai wani muhimmin abu da zai faru a gidan saboda yadda gidan ya hargitse bawai datti ba a'a very neat and tidy ga kamshin turaren wuta da nasu fresheners na lavender flavor da ya cika gurin, Amma duka masu aikin se kai kawo suke ko Lura da ita basui ba Seda Imratu ta sakko hannunta cikin na Muhammad wanda ya sha wanka an shirya shi cikin kaya masu kyau. Kallon kallo sukayi da Imratu kafin Imratun ta dan saki fuskarta tare da karasowa inda take tsaye, Muhammad bai lura da Subay'a ba wasanshi kawai yake har Seda suka zo gaf da juna kafin yace
"Mimi"
Lumshe idonta tayi don wata kwalla ce ta cika mata idonta, tsugunnawa tayi ta rungume shi Tsam cikin kirjinta tana sakin ajiyar zuciya, kanshi ta dinga shafawa tana jin abubuwa da dama suna taba mata zuciya, a hankali ta furta
"I missed you son"
Kwace jikinshi yayi yana fadin
"Mimi kizo kiga yadda Mami ta gyara komai yau da Daddy da Ammiey zasu dawo! "
Dam taji kirjinta ya buga, a hankali ta Mike tsaye Daga tsugunnon da tayi ta saki Muhammad, shi kuwa bai lura da ita ba ya ruga sama se Imratu ce ta karba trolley dinta tace
"Muje ko"
Hawayen dake kokarin sakko mata ta shanye tareda sniffing hancinta ta bi bayan Imratu zuwa sama, tamkar ta juya haka taji inda tasan Abinda zata tarar kenan da babu yadda zaayi ta dawo gidan. Suna zuwa parlon ta tarar Mami na Zaune gefen ta Ahmad yana danne danne a system din Mamin. Mamaki sosae Mami tayi ganin Subay'a a wannan lokacin Kuma Harda trolley, ganin yadda tayi kasa da kanta Mami tace
"A'a Subay'a sannu da zuwa, Ahmad bakaga Mimi ba? "
Zama Subay'a tayi yayinda Ahmad ya taso da murmushi a Fuskarshi ya rungume ta sanann ya cigaba da Abinda yake, kafin wani Lokaci an cika mata gabanta da lemuka da abinci, lemo kadai ta iya sha sannan tace da Mami
"Mami zanyi sallah"
Kallon Imratu Mami tayi tace
"Kuje Imratu "
Tare suka nufi dakin da Imratu ke zama idan tazo anan aka sauki Subay'a seda ta nuna mata inda komai yake kafin ta fice ta barta akan sallaya. Seda ta Idar da sallah sannan ta hada kanta da gwiwarta ta saki kukan bakin ciki hade wani masifaffen kishi da ya turnuke ta Lokaci daya, Da gasken kenan da kishiya zata zauna, da gaske Sulaim ta zama kishiyarta ta kwace mata mijinta, kuka sosae ta dinga yi har Bata san lokacin da ta dauka a haka ba, amma tasan tafi karfin awa daya Don har fuskarta seda tayi jawur ga babu Wanda ya kara ko nemanta a gidan.
Ganin haka yasa ta Mike ta cire kayanta ta fada toilet tai wanka ta dauro Alwala nadama fal cikin Zuciyata babu Abinda take banda inama ace Nayi kaza! Inama ace banyi kaza ba!! Amma ina Lokaci ya kure tuni sede a tari wani lokacin. Bubu ta wani cotton lace ta saka ta yafa mayafin kayan sannan ta samu guri gefen gado ta zauna, tamkar jiran zamanta ake taji ihun Ahmad yana fadin
"Daddy! Ammiey!! Oyoyo!!! "
Idanunta ta runtse da karfi, tareda dafe kirjinta hawaye suka Balle mata duk kuwa da yadda take kokarin ganin ta Hana su zubar Amma it is natural dole hakan ya kasance.
A parlor Junaid na gaba ya Saba Ahmad a kafadarshi Fuskarshi murmushi ne kwance akai me nuni da tsananin kwanciyar hankali da cikar buri, a bayanshi Dove ce hannunta rike da na Muhammad da yake rigimar se Sulaim ta daukeshi amma taki, tana ganin Mami ta nufe ta da gudu ta rungume ta wanda hakan ya kusa kada su baki daya, take parlon ya cika da murnar dawowar Love birds, a tsakiya suka saka Mami kowa na bata labari, farin cikin da take ciki yasa ta manta da wata Subay'a. Da kyar ta samu suka tafi wanka kafin su dawo itada Imratu sun gyara gurin sannan sun shimfida dining mat an Jere warmers din abinci. Junaid ne ya fara hawowa shida Jabir suna dariya, Junaid ya kara kyau se kyalli fatar jikinshi take, kana kallonshi kasan bashida wata matsala. Gefe guda suka zauna se sannan Sulaim ta fito tayi kyau cikin gown ta atamfa ABC wax, tayi kiba ba wai cancan ba amma ta murje ta murmure, yaranta sun saka ta a tsakiya suna tambayar ta tsarabarsu. Bata zauna ba Mami ta cigaba da tayawa aiki duk yadda Mamin taki amma se kyaleta yayi, Duk inda tayi idanun Junaid na binta Yana jin tamkar ranar farko da ya Fara ganinta kenan, tsabar kallon da yake mata Seda Jabir ya zungureshi yace
"Haba mana"
Dariya Junaid yayi yace
"Bazaka gane ba "
Dariyar Jabir ya sake yi tare fadin
"Really?"
Shareshi yayi ya cigaba da binta da kallo, Yana ganin lokacinda tayi pouting lips dinta alamar kallon ya isheta hakan. Gaba daya suka zazzauna aka Fara cin abinci Cikeda nutsuwa da nishadi hadi da soyayya, Mami ce ta aje spoon tareda kallon Imratu wadda ta tattara dukkan hankalinta Kan chicken Salad din da take ci,
"Imratu kirawo ta taci abinci"
Mikewa Imratu tayi a ranta tana tunanin yadda abubuwa zasu kasance, itakam Mami tausayin Sulaim take ji yadda ta saki jikinta sosae tana tunanin ta manta Junaid na da wata matar. Da kyar Imratu ta samu Subay'a ta biyo bayanta don tasan ranta ne kawai zai baci don yadda ta dinga jiyo muryoyinsu yasa jikinta ya kuma yin La'asar Don tasan suna cikin farin ciki.
Sulaim ke facing dakin don haka idanunta akan Sulaim din ya fara sauka, haka itama Sulaim din ita ta Fara ganin Subay'a, idanunta ta dan zaro saboda yadda taji kirjinta ya buga kusan tare da Subay'a din, gaba daya ji tayi taste din abincin ya bace, taji gaba daya zaman ya gundure ta, a hankali ta cigaba da taunar abincin tareda sunkuyar da kanta Tana ambaton Allah saboda wani Irin abu ne ya tokare mata makoshi, Mami na kallonta amma bata ko kula ta ba ta dubi Subay'a tace
"Kizo ki zauna mu ci abinci mana"
A lokacin Junaid ya dago idanunshi wanda suka sauka tar cikin idanun Subay'a wadda ta dauke Nata cikin saurin gaske, se ta samu kanta da kasa yiwa Mami musu ta zauna a gefen Ahmad Wanda suna ta tsakurar abincinsu ba Lallae idan sun San tazo gurin ba, Aje spoon din hannunshi Junaid yayi ya Mike don barin gurin, Mami ta dubeshi tace
"Har ka gama? "
Kanshi ya gyada ya tafi abinshi ba tareda ya ko kalli kowa ba, bai taba tunanin Subay'a batada kunya ba se yau, kenan ta bullo mishi ta bayan gida inda bai isa ya ja ba, kwanciya yayi Yana jin tamkar an rugurguza mishi wani plan ne. A parlor kam tunda Subay'a ta fito gurin yayi shiru se karar spoon dake tashi, a hankali daya Bayan daya suke tashi ya rage daga ita se Mami se Sulaim wadda ta kasa tashi har Seda Mami tace
"Auta kwashe kayan nan kije ki Kira min Yayanki"
Da sauri ta Mike ta fara tattare kayan jikinta kamar an mata duka, babu wani kuzari haka ta nufi kitchen ta kai kayan sannan ta nufi dakin Junaid, A kwance ta same shi yayi zurfi a tunani Amma sassanyan turarenta yasa shi saurin dagowa don bai kawo ita din ba ce amma se ya ganta a tsaye kana kallon fuskarta kaga me cike da damuwa, mikewa yayi Yana jin abubuwa suna kara kunce mishi a kanshi, Yana Zuwa inda take ta fada jikinshi Lokaci daya ta saki kuka Wanda ita kanta bata san me yasa take kukan ba, tasan dai zuciyar ta bata mata dadi tana jin wani zafi a kirjinta. Janye tayi daga jikinshi ya shiga share mata hawayen a hankali cikin kunnuwanta ya ce
"Everything will be OK, kinji? "
Kanta ta gyada mishi don ya fahimci kishi ke damunta, ba tun yau yake ayyana zuwan wannan ranar ba gashi ta zo a lokacinda shi kanshi bai shirya ba, hannunta ya ja suka fito Yana ta fada mata kallamai wanda yasan suna saka ta farin ciki, a haka har suka isa parlon Mami da Subay'a na nan inda ta barsu. Kusan tare Mami da Subay'a suka dubi hannayen Sulaim da Junaid, gaba daya Mami kunyar Subay'a ta kama ta hakan yasa ta watsawa Junaid harara, Dan chuckling yayi ya saki hannun nata ita kuwa straight ta nufi dakin Mami gabanta na kara faduwa. Zama yayi Fuskarshi a murtuke tamkar bashi bane wanda ya gama dariya yanzun ba, kallon Mami yayi wadda ta hade rai itama don da gaske Junaid so yake ya bata kunya.
"Junaid me nasha fada maka akan rayuwa? "
Kanshi ya girgixa Cikeda kosawa ga kukan Subay'a na taba zuciyarshi tareda karya mishi zuciya Amma dukda haka abinda yayi niyya bazai fasa ba
"Hakuri of course Mami!"
A hankali Subay'a ta dago idonta Wanda yayi jawur hatta fuskarta tayi ja, kallon Mami tayi sannan ta dubi Junaid da ya kara hade rai, Mami tace
"A yau ba'a matsayin mahaifiyarka nake maka magana ba, ina maka magana a matsayin wannan babbar kawar ta ka....."
Da sauri ya katse ta, ta hanyar dawowa gefenta Daga kasa tareda rike hannunta yace
"Mami don't please.... Mami please!"
Da sauri Subay'a ta Mike har tana tripping foot dinta, tsoron abinda kunnuwanta zasu iya jiye mata suke takeyi, tasan abu na karshe saki ne su zama zawarawa itada uwarta. Ajiyar zuciya Junaid ya sauke tare da fadin
"Mami ranar da zan tafi Malta, kin tambayeni me zan yiwa Subay'a idan ta dawo? Nace sakinta zanyi ko? "
Kai Mami ta gyada don ta rasa bakin magana saboda yadda aka daure ta da jijiyoyin jikinta.
"Kika roka mata hakuri da sassauci, nayi hakuri saboda darajarki amma Wallahi tallahi, billahil azim se Subay'a taje gida ta koyi Menene aure! Se ta gane ni Allah yace na shugabance ta! Nine leader ni nake aurenta ba ita ba! Inason ta nutsu ta gane kuskurenta. Mami kada ki hanani, hakan is an opportunity Allah ya bani na daidai ta gidana... I'm sorry"
Ya karashe maganar Yana daura kanshi akan cinyar Mamin, yau an tuna da kenan. Itama Mamin tausayinshi ne ya cika mata zuciya ta shiga shafa kanshi tare da fadin
"Hakan yayi, kayi hakan is ok amma ina son duk Abinda zai faru ka kalli Ahmad da Muhammad, taci darajar haihuwarsu, ko a alkiyama filin hisabi wani yana cin albarkacin wani. OK? "
Kanshi ya gyada yana jin sanyi Yana ratsa shi, Mami ce ta Fara mikewa tayi dakinta don kuwa hankalinta duka yana kan Sulaim wadda ta shige daki, tana shiga ta sameta as expected ta hada kanta da gwiwarta tana ta kuka me cin rai, gefenta ta zauna ta janyo ta jikinta tana patting bayanta alamun rarrashi haka tana jin babu dadi cikin ranta, wannan shi ne Abinda ta gudar wa Sulaim din tun farko, Auren mijin wata, to ya zasui kaddarar ta ce!
"Me kike ji auta?"
Cikin kuka da yarinta Tace
"Mami ina jin abu ya tokare min wuyana, zuciyata zafi take min, kirjina yayi min nauyi, Mami bana son Yaya!"
Da sauri Mami ta toshe mata Baki tareda fadin
"Kar na kuma jin kin fadi haka, kishi yake damunki kuma it's normal kaji kishi akan abinda kake so, kishi halal ne, Nana A'isha Harda Nana Khadija wadda bata taba gani ba tayi kishi da ita, Tasha barar da abinci idan an kawowa manzon Allah SWA Daga dakin Nana Safiyya kasancewar ta great cook. Kinga ba laifi kikai ba amma ina son daga yau kada ki kara kuka Dan kinga Subay'a, inason Kiyi amfani da kishinki me da ilimi ki kwaci mijinki, mace ce kamar ki, Baki fita ba bata fiki ba, me biyayya da wanda ya iya zama da miji shi zai kwace miji, shi zaiyi winning Sulaim.
Inason ki maida hankalinki ki manta Yana da mata, ki Kafa kanki a gurinshi, kiarki Bari wata ta kwace shi kinji? "
Kanta ta gyada har lokancin kukan bai tsaya ba amma ta rage, kuma radadin ya ragu sosae
"Uwargidan mutum ita ta kafa shi, ita ce foundation dinshi, Duk yadda ta zubar da darajar ta Tanan matsayin uwargida wadda ta sanshi. Ko zaku shekara talatin tare bazaki taba sanin shi kamar yadda tayi ba, haka duk lalacewar uwargida idan miji ya rabu da ita, duniya se