Showing 18001 words to 21000 words out of 103785 words

Chapter 7 - IDAN AN CIZA..! Part 1 Complete by Janafty.txt

Janafty   

20 Dec 2024

4792

TURA SHAIDAR BIYA TA WAƊANNAN LAMBOBIN.*
*09069067488*
*80032773332*
*Ƴan kasuwa masu bukatar a tallata musu hajojinsu cikin farashi mai sauƙi, ku yi min magana ta wannan lambar*
*09069067488*
*NA GODE.*












*Janafty*
*IDAN AN CIZA..!*


*Wattpad:Jamilaumar315*
*Arewabooks:Jamilaumarjanafty*
*Mallakar:Janafty*


*SADAUKARWA GA HAJIYA AISHA AHMAD IYA*


MMN MUJAHID KAYAN MATA AND SUPPLEMENT


SHIN KINA DA LABARIN MACCE MAI GYARA DABAN TAKE GA ZUCIYA MIJIN TA, MUNA DA KAYAN MATA MASU ZAFI NA BUGAWA GA JARIDA
HAJIYA TA KUDI DA KUDI AKE NEMAN SU


INA MASU FAMA DA MATSALA RAMA BA GABA BA BAYA KINA ZAUNE ANA KWATANCI DAKE KINA CI BAKI KOSHI MUNA DA MAGUNGUNA DA ZUMA 3 IN 1 KIBA BRST HIPS TA CIKO MIKI KU INA KIYI FRESH MUNA DA KWAYOYI MUNA DA GARI DUK MASU CIKO JIKI NE KIYI DUM


INA MASU FAMA DA MATSALA BRST KU TSUHU YAFI SON YAGA NONO A TSAYE DUK MAI MAGANIN DA TACCE MIKI ZATA BAKI MAGANIN NONO KAI TSAYE YAYI MIKI KARYA CE MAGANIN BRST SAI KIN SHA ADADIN WANDA ZAI MIKI SBD DUK CIKIN GYARAN JIKI NA BRST YAFI WAHALA YI


INA MASU FAMA DA MATSALA SANYI MUNA DA MAGANIN SANYI ORIGINAL
MUNA ADASHEN GATA SBD YANA YIN DA MUKE CIKI 500 DUK SATI IN KIN KAMALLA ABAKI DUK ABINDA KK SO


INA MASU ZAMAN BANZA BABU SANA'A KINA KONE DATA KI GA BANZA WURIN TSEGUMIN KALLON STATUS DIN WASU GA DAMA TAZU MUNA HAR GIDA GA WAYAR HANNUN KI KI MALLAKE MOTA MILLION 8 HAR FIYE GA ALBASHI GA RIBA GA KYAUTA KAYA IRIN SU WAYA
BLENDER
WASHING MACHINE


08066726866


MMN MUJAHID KAYAN MATA AND SUPPLEMENT Y'AR MUTAN SAKWATO


*Page 4*


*ABUJA GWARIMPA, N0:770*
*Saturday 18, Feb. 2022*
11:44am.


Gidan retire Major Kabir Sulaiman Dabo tun yana cin zamaninsa gida ne da ya amsa sunansa gida, yana cikin garin Abuja sannan a cikin wannan kyakyawar anguwan nan ta samu kusa a gwanmati wato Gwarimpa. Gidan nyana nan da kyansa kamar baya, ko da megidan ke kwance ba shi da lafiya Dr. Sulaiman da Daddy Hamza ba su bari gidan ya bukaci wani abu ba.


Akwai tarin ma'aikata acikin gidan tun daga megadi zuwa masu kula da haraban gidan, ciki kuma masu aikin bangaren share share da girki saboda Barr. ba mazauniya ba ce tana fita kotu in tana da shari'a.
Ammh kafin ta fita sai ta gyara mijinta tsab ta masa duk abin da yake so sannan take fita, in ta na gida ita da kanta ta ke shiga kitchen ta girka masa irin abincin da yake ci saboda yanayin jikinsa.
Major Kabir ba shi da wani aiki daga kwanciya sai ko in ya gaji ta kama shi ta ɗora shi saman Wheelchair da taimakon wani Musa mai kula da fulayoyin gidan tunda ita kaɗaai ba zata iya ba. Duk da kuma tana ma iya bakin ƙokarinta.
ƴayansu suna nesa da su amma suna zuwa ganinsu lokaci bayan lokaci musamman ma Dr. Sulaiman da duk wata shi da iyalansa suna zuwa Mimi kuma sai ta yi wattani uku bata zo ba suna dai magana ta waya.


Wannan watan ba ta kai karshe ba suka haɗu gabaɗayansu a Abuja Saboda jikin Abi da ya motsa, da ya ke akwai likitan na musamman ne daga babban Asibitin Abuja yake zuwa ya na dubashi ko da aka san laluran bata warkewa ba ne, amma zama waje ɗaya dole akwai bukatar tallafawan likitoci da sharwarwari.
Bayan Dr. Sulaiman da iyalansa har da Khadija(Khadi) ta zo itama sai Mimi da Hajiya wacce ta na jin Mimi zabta je ta ce ita ma ba za ta zauna ba, dole Mimi ta yi musu bucking din jirgi suka taho ranar jumma'a da yammah. gidan sai ya yi albarka Sosai Madiha ce kaɗai bata samu zuwa ba ta ce sai karshen wata za ta shigo tayi hutun ta, daga nan har Gombe za ta shiga ta ga dangi kafin ta koma.


Jiya kwana suka yi hira Abi yaji daɗi sai dai yana kwance yana ta faman mirmishi kamar yau ɗin ma da gabaɗayansu suke cikin Bedroom ɗinsu shi da Mommy tunda yace a barshi a kwance yafi jin daɗin kwanciyar. Gabaɗayansu suna ɗakin ƴayan Dr Sulaiman su biyu kacal duka kuma mata da mai sunan Mommy Murjanatu suna kiranta Ummita sai mai sunan Hajiyar Shagamu suna kiranta Momi.
Sune ke tare da Abi suna ta nuna masa abu acikin Kananun tab ɗin su na yara da yake hannunsu. Hajiya na gefen kafafun Abi ta na mgana da Mommy.


Dr.Sulaiman na daga gefe tsaye ya harɗe hannayensa a saman kirjinsa dogon farin Bafullatani mai cike da fara'a da zati.
Matarsa kuma mai suna Jawahir ta na gefen Mimi, ita tana zaune a saman kujerun Dreesing mirro, Mimi kuma tana daga saman madubi sai dai waya ce a hannunta tana ta faman latswa rabi da rabi hankalinta ke wajen Hajiya tana jin hiran da take yi ma Mommy, jefi jefi kuma Big bro na saka musu baki Sisto kuma ta fita ta je za ta yi wanka.


Duk Lokacin da Mimi ta ɗago kanta sai ta ga Abi na kallonta sai ta yi masa mirmishi kawai shima sai ya mai da masa martanin mirmishinsa Allahu Akbar rayuwa kenan Abi na bata tausayi in ta kallesa shi ya sa ka bi rayuwa a sannu in kasan mafarin ka, ba ka san karshen ka ba. Ba za ta manta Rayuwar da suka gudanar a wannan gidan ba shi ya sa har gobe bata kaunar duk wani aiki na kaki saboda gani ta ke yi kamar yadda Abi ya rika tafiyar da rayuwarsa a baya saboda kakin da ke jikinsa ne. Abi ya yi zamanin da duk abin da ya ce ba wanda ya isa ya ta da shi, hatta Hajiya da ta haifesa kuwa, Mommy kuwa da suka yi auran soyayya ba ta isa ya nemi shawaranta ba ra'ayinsa ya ke bi da abunda ya yi masa dai dai shi ya ke aiwatarwa. A zamanin baya mutum ne mai murɗewa da ka'ida mai tsauri, amma sai ga shi rayuwa ta sauya komai yanzu ya yi sanyi Abi ya koma rayuwar kwanciya cikin ibadar Jinyar ta Ubangiji sai ta ga ya yi sanyi rayuwar ma kamar tsoro ta koma ba shi. Duk sanda zata zo ta koma tsakaninsu sai ban hakuri ya rika cewa Ki yi hakuri kin ji ko Mimi?
Sai ta ce bakomai Abi zan cigaba da yi maka biyayya har karshen numfashi na.


Yana so ya yi mata mgana amma kuma har gobe ya kasa iya furta wani abu.
Ko mganar ta ƙi sauraran kowa ake yi a gabansa sai ya ce a kyaleta a daina takura mata, in kuma yan'uwansa suka zo suka fara mganar Mimi taki aure har yanzu kuma shekarunta na tafiya sai ya ce kar da wani a cikinsu ya ce zai takura mata a kyaleta ta yi aure a lokacin da take so da kuma wanda ta ga ya dace da ita. Kowa yasan dalilinsa na cewa a kyale Mimi to bakin alƙalami ya riga da ya bushe abin da ya faru a baya ba wanda ya isa ya iya sauya shi.


"Habibi ko Dr zai ɗaura ka saman Kujeran nan ne, na ga tun jiya fa kake ta kwanciyar nan?


Mommy ta faɗa Lokaci ɗaya tana mikewa Hajiya ta ka da baki ta ce"Gaskiya kwanciya da zama waje ɗaya ba daɗi. Kabiru Allah yasa kaffara ne amma ana ta Ibada Allah ya bamu sa'a kawai." aka amsa mata da Amin Shi kuma Abi sai ya yi mirmishi kafin ya ce" Honey kyaleni kawai nafi jin daɗin kwanciya in na zauna sai kuguna ya rika min zafi zafi wani lokacin.'
Sulaiman ya kariso yana faɗin "Abi to ai saboda kana jimawa a kwance ne, yawan zaman zai rage lanƙwashewar da jikin ka ya yi a waje ɗaya"
Kwallah suka cika kwarmin Idanuwan Abi ya yi saurin shanyewa yana faɗin"Ku kyaleni kawai, na fi jin daɗin kwanciyar fiye da zama."


Yadda ya yi mganar ne ya sa sai jikin Kowa ya yi sanyi, Hajiya ta yi tagumi kafin kuma ta fara sharan ƙwallah tana faɗin "Lafiya lau kabiru ya bar wajena ina saka masa albarka, sai ganin Hamza nayi yazo cikin ɗimuwa ya na faɗa min Kabiru sun samu hatsari a hanyarsu ta komawa Habuja, Allah ya jiƙan Mallan Sale ina ganin fuskarsa a cikin Idanuwana har yau wlh."
Sai ɗakin ya dauki shuru aka koma Jimami, Abi kuma hawaye suke ziraro mai ta gefen kunnuwansa duka biyu Mommy ke saka tissue tana share masa, Mimi ta sauke wayar hannunta ta na sauke numfashi hankalinta duk ya tashi, in ta kalli Abi sai ta ji ta kara tsoron rayuwa gabaɗaya ba Abin da ta sani a baya ba ne jajirtacce namiji wannan Abin a kwance yake yana kokuwa da kaddaran Ubangijinsa.
Sai da Hajiya ta dai na kukan sannan Abi shima ya dai na. Shigowar Sisto Khadi ya sa sai a ka shiga wata hirar na dabam, Jawahir kuma taja ƴayant azuwa Kitchen suna kukan yunwa suke ji, ita kuma Mimi sai ta koma kan wayarta tana karanta sakon Baby Rukayya.


"Don Allah ko sunan shi ki faɗa min Mimi ta"


Charting suke yi tana ta mata magiyan sai ta faɗa mata sunan wanda ta ji yaddiko da Hajiya na mgana ita kuma ta ce mata wannan wani abu ne da ya shuɗe bukatar taso da mganar da ba ta da amfani.
A wajen aiki ma haka Rukky ta rika yi mata magiyan wai sai ta ba ta labarin shi ko wannan mutumin waye shi da Mimi ta kasa mantawa da shi. Ita kuma Mimi ta ce ta bar damunta da wannan mganar, abu ya riga ya wuce ba amfanin ta da maganar yanzu.


"Sunan shi Hayatu.."


Sai ta fara yar dariya saboda yadda Rukky ta turo mata emojin kuka da damuwa, saboda Hayatu sunan saurayin Rukayya ne da suka rabu shi ya sa ta mata shakiyanci.
Tana cikin Mirmishi taji Hajiya na faɗin"Hamza fa ya matsa kan mganar Jaheed da Binta, yaddiko ma ta yi min ƙorafin tunda shi Jaheed ɗin na sonta mai zai hana ayi yar gida?
Mimi ta tsaya cak da abin da take yi tana kallon Hajiya cikin mamaki. Har sau nawa za ta faɗa mata bata son Jaheed amma Hajiya ba za ta fahimci yaren ba kenan


"Mimin ta amimce da shi ne yanzu Hajiya?


Mommy ta katse Hajiya da wannan tambayar Sulaiman ma ya ce"Matsalan har shi Jaheed din ba ka gane in da ya dosa ne."
Mommy ta ce"To nima shi na gani mai so ai shi ya ke nema ko Hajiya?
Khadija da ta fi kama da Mommy ta gyara zama tana faɗin "Mommy ni ko sai na ga Jaheed ba laifi, Mimi ce matsalan kusan halinta kowa sai ta ce ba ta so kuma in aka biye mata sai dai kila ta mutu ba ta yi aure ba a take taken ta wlh."
Khadija ta faɗaa lokaci ɗaya ta juya tana mai kallon Mimi ta ke ta hararanta.
Sulaiman ya kalleta ya na yar dariya kafin ya ce"Sisto taho nan naji me ya sa baki son Jaheed din? Mimi ta tura baki kafin ta mike sanye ta ke da doguwar riga mai santsi ta na da buɗewa ta kasanta sannan ba ta kama Jiki sosai ba.
Har gabansa ta zo ta tsaya ya kama hannunta yana faɗin"Me ya sa ba ki ba ma Jaheed dama ba Mimi?
Mimi ta yi shuru ba ta yi mgana ba kuka ke son taso mata sai dai ta danne amma taki mgana.


Khadija ta ce"Ba ta da wani dalili fa, Saboda tasan ba shi da makusa, haka abokin Dee ya ce yana sonta nan ta wulakantashi ni nasan abin da take yi ma ƙulafuci wannan yaro shi ke cikin ranta har yau ta kasa cire shi."
An so so mata in da ke mata ƙaiƙayi kawai sai ta fashe da kuka har da jiniya, Abi na kwance faɗi yake yi" Dr. Kyaleta ku kyaleta Mimin Abi taho nan taho nan wajena."
Sa gudu ta haura gadon ta faɗa gefensa ta na kuka shi kuma ya saka hannunsa guda ɗaya yana shafa kanta cikin lallashi yake fadin"Ki daina kuka, ki kwantar da hankalinki tunda baki son shi ba wanda zai ce dole sai kin aure shi Ok?
Sai ta gyaɗa kai kafin cikin kuka ta ce"
Abi ba na son shi, ni wlh ba na son Jaheed"
Ta karishe faɗaa ta na gunjin kuka kamar wacce aka daketa. Mommy da Hajiya suka kalli juna ba su yi magana ba.
Abi ya ɗago idanuwansa ya na kallonsu kafin ya ce"Kar a ƙara takura ma Mimi da mganar kowa tunda ta ce ba ta so a kyaleta, shima Hamzan zan kira shi a bar wannan mganar tunda Mimi ba ta so period."


Khadija ta buɗe baki ta ce" Amma Abi..'"


"Na ce tunda Mimi bata so a bar mganar nan, abin da Mimi take so ko bayan raina shi za ku yi mata wanda kuma ta ce ba ta so kar ku ce za ku matsa mata don Allah.."


Abi ya katse Khadija, ya na mgana kamar zai saka kuka da sauri Sulaiman ya ce"Abi ba wanda zai takura mata kan abin da ba ta so tunda tace ba ta ra'ayi nima ina goyon bayan a bar mganar."
Hajiya ta ce" Ni kaina ba zan ce a yi ma Binta fole ba Kabiru, Yaddiko ce da Hamzan suka matsa da zamanta haka ba aure shekaru talatin ai ba kwana talatin ba ne."
Mommy ta yi shuru ba ta yi mgana ba wani abu da ya faru a shekarun baya suna dawo mata, duk abin da ke faruwa da rayuwar Mimi ba kowa ya ɓata komai ba sai shi.
Ba'a maida hannun agogo baya tasan da ana maidawa da tuni Major Kabir ya maida lokacin ya gyara kuskuren da ya tafka a zamanin baya da ya ke ji da duniyar a saman kansa.


Mimi jin a bar mganar Jaheed sai ta daina kuka ta tashi ta fice daga 'ɗakin ta koma Bedroom ɗinta na gidan kwanciyarta ta yi ta na sharan kwallah, Jaheed ɗin fa da gaske ba shi da makusambSai dai ita kawai ba ta son shi ne, sannan shagwaɓaɓɓe ne ko ita mace albarka ta zauna tana wannan shagwaɓan Mama boy ne. Jaheed babban yaron Daddy Hamza ne yana Lagoa can ya ke aiki a wani babban kamfanin sarrafa Karafuna.


Sannan kuma a America ya yi karatunsa na Engeniaring har na tswon shekara biyar, yana da wayewa har ta yi masa yawa kuma ita a tunaninta ba sonta yake yi ba kawai yana sonta ne saboda tana aikin gidan Tv asan fuskarta a duniya sannan tana da kyau domin ya sha faɗa mata shi bazai iya auran macen da bata da kyau ba, shi komai nashi ya na son harka da abu mai kyau
Yaddiko ta matsu ta yi aure kamar a saman kanta take zaune shi kuma Daddy saboda Jaheed ne shi ya ke matsa masa tunda ta ki ba shi dama kuma yasan har yanzu bai samu karɓuwa. Ba ko da yaushe take ɗaukan wayansa ba sai ta ga dama, a chart kuma sai ya yi mgana da wajen sati sannan ta ke dubawa. Ita fa Namiji kwara ɗaya ta taɓa so kuma har abada shi kaɗai take so.
Tunda Abi ya ce a bar mganar tasan mganar ta mutu. Saboda a baya ne Abi ke girmama ra'ayinsa saman na kowa, amma yanzu zai iya girmama nata ra'ayin sama da na kowa ba na shi ba ma. Saboda yana tuhumar kanshi da komai ya faru da rayuwar Mami shi ne silar hakan.


Tana jin shigowar Khadija ɗaakin sai ta yi kamar ta yi barci tana jinta ta kira Anty Madiha a waya tana faɗa mata duk abin da ya faru da yadda Abi yace a bar mganar.
Abu ɗaya ya fi bata haushi irin in da Khadijan ta ce"Ni fa nasan me ya sa Mimi ta kin sauraran kowa, wannan yaron ta kwallafara rai akansa wanda ba ta san isalinsa ba, tuni ya yi auransa ma ya manta da ita, itama ai ya kamata ta manta da abin da ya faru a baya ta gina wata sabuwar rayuwar."


Tana da tabbacin khadija ba ta san menene SO..! Da ace ta taɓa ɗanɗana shi ta ji ya ya raɗaɗinsa yake da ba ta yi wannan mganar ba. Da ace tasan ya ya zafin dafin so ya ke da ta yi mata uzuri, ammh itama ta yi ma lta uzuri saboda wanda take so ba ta sha wahala a kansa ba ta same shi. Shi ya sa ba za ta san zafin dafin ka rasa wanda zuciyarka ta aminta da shi ba, ba ta san ya ya zafi da raɗaɗin raba ka da wanda kake so ba. Duk ba ta san wannan zafin da raɗaɗin ba so khadija tana bukatar a yi mata uziri ko da uzurin ya kai kimanin sau saba'in ne. Saboda wannan dalilin ya sa har suka koma Gombe ita da Hajiya ba ta kara walwala a gidan ba. Haushi Khadija take ji, itama Khadijan haushinta ta ke ji Sulaiman kuma ranar oahadi suka bi jirgi zuwa Kano shi da matarsa da ƴayansa. Mimi kuma sai washegarin litini suka bi jirgi ita da Hajiya zuwa Gombe nan suka bar Khadija tunda ita sai mijinta ya so za su koma tare.


Ko bayan dawowarsu Hajiya ma ba ta kara ta da mganar ba, sai dai kwana uku tsakani ta dawo daga wajen aiki ta iske Yaddiko a gidan ta na ganinta sai da gabanta ya faɗi domin tasan akwai mgana.ilai kuwa kan mganar jaheed ne tana ta ma Mimi faɗan da ta ki ɗan uwanta so take yi ta zauna ta cigaba da fita aiki tana nuna fuskarta a duniya bata da niyar aure.
Daga karshe ta gatsa ma Mimi mgana da cewa" In ma wannan yaron kike ta jira to kin yi a banza, a gabanki a gaban mu mahaifinki ya ce ko bayan ransa kika auri wannan yaron bai yafe miki ba."
Mimi ta fashe da kuka wiwi Hajiya ta fara yi ma Yaddikon faɗan me ya sa take haka ne? Ita kuma ta ce ai gaskiya gwara ma ta rufa ma kanta asiri ta karɓi ɗan uwanta yadda ma tun

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login