Showing 6001 words to 9000 words out of 103785 words
na Inna Merin
sauran sasan kuma da ya gyara gidan sai ya fitar musu da kofar su ta can, shashen iyayen sa kuma ya fitar musu da tasu kofar daga kudu.
Yana kokarin kafe mashin ɗin sa ya ji muryan Mariya ta na faɗin"Yayanmu sannu da zuwa."
Ta faɗa cikin muryanta mai sanyi, sai da ya kafe mashin ɗin sannan ya dago yana kallonta tana tsaye tana ta yi masa mirmishi.
Akwai wutar nepa hasken farin kwan lantarkin dake waje ya haske masa ƴar farar fuskarta. Cikin rashin sakewa ya ce"Yauwa."
Daga haka ya wuceta dai dai lokacin da magajiya ta fito daga makewayi da buta a hannunta. Sai ya shigeta zai shige koridon Maman Mu'azzam shi ya sa bashi da mafita sai sun haɗu.
Bai tsaya ba yana gota ta sai ta ji yana faɗin"Barka da dare Magajiya."
Ta juya ta na kallonsa cikin harzuka da ɗaga murya ta ce"Ji min wulakamci da reni, in ba za ka iya kirana da suna Mama ko Umma ba sai ka sakaya sunana ka ce Maman Auwalu ko maman Mariya ammh ba ka rika kirana da sunana Magajiya gantsal ba, wannan dai sam ba tarbiyan ba ne."
Ta gama faɗa ta na faman hararan bayanshi, shi dai bai ko juyo ba mamaki ya cikasa to me take son ya kirata?
Ya ga dai ko ƴa'yanta da ta haifa ma tun yana ƙarami ya ji suna gatsa sunanta Magajiya kuma bata damu ba sai shi don yau ya kirata da magajiya sai ta ce ba tarbiya ba ne?
Yana wannan tunanin yaji ta na fadin"Har kina wani fita kina gaishe shi don ubanki to ni nan uwarki ban ci darajan ya ganni ya ce min ina kwana ba, na kara ganin kin gan sa yazo kin fito kina yi masa dariya ki gani in ban falla miki mari ba."
Bai juyo ba ammh ya san baki Mariya ta tura kafin ta ce"Kai magajiya Baba fa ya ce yayanmu ne."
Daga murya tayi kafin ta ce"Karya ne wlh, Agola ne ba ɗan gida bane, ba ku haɗa komai da shi ba."
Ya ji sanda ta furta kalmar agola, adai dai lokacin ya yi sallama ƙofar ɗakin Maman Mu'azzam. Inna Meri uwar Mansoor Innar Mu'azzam.
*Janafty*
*1rd, March 2023*
*Post on 04 August 2024*
Follow this link to join my WhatsApp group: https://chat.whatsapp.com/FpA4NvQPg3XIRUQOgytNh5
*IDAN AN CIZA..!*
*Wattpad:Jamilaumar315*
*Arewabooks:Jamilaumarjanafty*
*Mallakar:Janafty*
*SADAUKARWA GA HAJIYA AISHA AHMAD IYA.*
*MADALLAH DA SURAYYA DEE, ALLAH YA CIKA MIKI DUKA BURIKAN KI NA ALHERI YA BA KI SANYIN IDANIYA AMIN.*
*FATAN ALHERI GA AMINIYATA AISHA MUHAMMAD ALTO(SISINAH), ITA ƊIN TA DABAM CE A WAJENA. NA GAISHE KI*
*NA GAISHE DA IYAYEN ƊAKINA*
*ZAINAB INUWA(AUNTYSIS)*
*HAJIYA LUBABATU MUSA*
*KHADIJA SALISU YUSUF(UMMINA)*
*HAJIYA HABIBA ABUBAKAR IMAM*
*ANTY ZAINAB ABDULWAHAB*
*HAJIYA HALIMA ƊALHA SHEHU.*
*ANTY HADIZA MAHE MUHAMMAD*
*ANTY SALAMATU ABUJA.*
*ANTY FADILA KABIR*
*ANTY FIDDAUSI KABIR*
*FATAN ALHERI NAGODE*
*INA GAIDA MARUBUTA, KARAMCINKU ABUN YAƁO NE. ALLAH YA ƘARA BASIRA ƳAƳAN BAIWA AMIN.*
*Page 2*
A tsakiyar falon ya ci karo da Inna Meri tana tsaye ita da Walida, ya yi sallama suka amsa gabaɗayansu. Tun kafin ya buɗe baki ya fara gaishe da Inna Walida ta yi zaraf ta ce"Yayanmu barka da dare"
Saboda sanin halinsa yanzu tana cewa ina yini sai yace bai ga yinin ba, sai dai ta ce masa barka da dare. Cikin mamakin ganinsu a tsaye ya ce"Barkan mu lafiya na gan ku a tsaye, Innanmu lafiya kuwa?
Inna Meri wata bakar dattijuwa kallon farko za ka yi mata ka fahimci ta fito daga shiyar sokkoto ne, sannan ta haɗa jini da Arawa, saboda gefen bakinta dama da hagu ga zanenta na Arawa nan ɓaro ɓaro ya bayyana duk da ko ta na baƙa na iya ganinsa. Sannan sai alokacin na fahimci in da Mansoor ya ɗauko tsawon sa, Inna Meri doguwa ce sosai mai kaurin jiki kuma.
A shekarunta iyakarta 56 zuwa da bakwai a duniya ba ammh yanayin jikinta bai nuna wahala ba sosai tana sanye da hijabi ne a jikinta hannunta kuma casbaha ne, daga gani ta idar da sallar mangariba ne tana lazimi. Cikin yanayin maganarta ta ce"Tun da naji Kwakwazon Magajiya na ce to Baban Inna ya shigo gidan" Mirmishi ya yi ba tare da ya yi mgana ba, Walida tayi saurin shimfiɗa masa darduma sanin halinsa bai son zaman kujera duk ko da irin tuma tuman kujerun alfarman dake mamaye da falon na inna Meri ko wata amarya albarka. Cikin natsuwarsa ya zauna itama Inna Meri sai ta samu daga gefensa ta zauna saman cafet mai taushi dake malale a cikin ɗakinta.
Cikin yalwataccen fara'an da ba a raba fuskarta da shi ta ce" Tun fa ɗazu muke ta duban hanyan ka ni da Babanku muka ji ka shuru." Daman yasan tuni labarin dawowarsa ya zo musu tunda Mu'azzam ya ji labari. Kansa na kasa ya ce"Innarmu kun yi mgana da Mu'azzam ne?
Cikin jimami ta ce"Ya kirani kamar ya yi kuka Baban Inna ba ka kyauta ma ɗan Innna ba gaskiya, me ya sa ba ka je ka duba ɗan uwanka ba?
Kai tsaye Ya ce"Inna wasa muka je bugawa kamar kuma wani mace sai a ganni daga zuwa wasa ina faman biye biye
Inna Meri ta ce"To menene? ba wajen ɗan uwanka za ka je ba? ya ce matarsa ta kasa zama waje ɗaya saboda zuwanka maganar gaskiya Baban Inna ba ka kyauta ba."
Ba ya son jan mganar ya sa Ya ce"Shike nan ki yi hakuri Innarmu, Ina Baba ko a masallaci ban gan sa ba?
Inna Meri tace"Tun ɗazu abokinsa Mallam Hashimu ya kirasa kan dai zaman da ake yi akan auran ƴarsa maigado shi ne ina ga har yanzu ba su kai ga matsaya ba."
Cikin mamaki Ya ce"Auran ya mutu ne?
Tana gyara zama ta ce"To abin dai nasu sanin gaskiya sai Allah ita ta ce ya saketa shi kuma ya yi rantsuwan bai furta mata saki ba sun dai yi sa'insa har ya dake ta"
Mansoor ya yi shuru bai yi mgana ba, yana ji Inna Meri ta cigaba da ba sa labarin yadda akayi jin ta kawai ya ke yi hankalinsa na wani wajen kuma.
Walida ya ke hangowa ta cikin uwar ɗakin Inna Meri ta na karatu sai dai baisan me ta ke karantawa ba. Ya buɗe baki zai kwala mata kira kenan Inna ta riga sa, tana fitowa ta kalleta tana faɗin"Ke mara wayau baki kawo ma yayan naku ko ruwa ba?
Da sauri Ya ce"Ba na jin kishi Inna".
Kallonsa ta yi kafin Ta ce"To abinci fa?
Kai tsaye Ya ce"Inna zan ci tuwo ammh ba yanzu ba sai na kusa tafiya."
Daga haka ta girgiza kanta kafin ta ce"Shike nan kun dawo oafiya ko? Ina fatan an samu nasara? Cikin sakin fuska ya ce"Lafiya lau Innarmu, an samu nasara in sha Allahu."
Nan Inna ta cigaba da kwararo addu'o'i yana amsa mata da Amin Amin. Walida kuma tsalle ta buga tana faɗin.
"Yayanmu kun ci ƴan kano kenan? eyye na ji daɗi daman yau a makaranta ana ta labarin ƙwallon da aka buga tsakaninku da yan kanon"
Kallonta ya yi lokaci ɗaya yana hararanta kafin ya ce"Ke ba karatu ki ka je yi makaranta ba labarin kwallo yake kai ki kenan ko?
Ta na jin haka ta yi sum sum ta wuce ciki Inna Meri ta ce"A'a ƙyalemin Auta, ita ke bani labaran ƙwallon naku ni kasan ba gane abun na ke yi ba, ranar ma a tibi ta ga an nuno wasu ta ce min Innarmu wata rana za ki kalli Baban Inna acikin tibin na ce Allah ya nuna mana."
Yana Mirmishi ya amsa ma ta da Amin.
Hira suka cigaba da yi Inna Meri na faɗa msa ta yi waya da mutanen mallam Sidi sun ce ya ji ma bai je ba Goggonsa yalwa har ta yi rashin lafiya kwanaki.
Yana duba agogon fatan da ke hannunsa ya ce"Zan je Inna ba na samun zama ne, ammh zuwa karshen watannan zan ga abin da Allah zai yi."
Inna Meri ta ce"Ya dai kamata ko ba ka kwana ba, Mu'azzam yafi ka son zumunci yanzu haka duk zuwan da zai yi garin nan sai ya leka wajen yan'uwan mahaifiyarsa ya gaishesu ka ga hakan ai yafi da ace mutum kwata kwata baya zuwa." Kai tsaye ya ce" Hakane Inna zan kokarta in sha Allahu."
Wayarsa a ka kira yana ganin Coach ne ke kiransa ya ɗaga suka gaisa nan ya ke faɗa masa gobe da safe suna da morning Training, da kai ya amsa mishi sannan ya sauke wayar dai dai ookacin da ya ji gudu da dariyan yara daga koridon shigowa shashen inna Meri kafin ya yi mgana ya ji Inna na faɗin"To ga shugabanin yan kiriniya nan sun dawo." Kafin ma ya samu zarafin mganar sun faɗo ɗakin da gudu sauran kaɗan su ture Mansoor dake zaune.
Sai da ya daka musu tsawa sannan suka fahimci yana ɗakin.
Sai suka natsu sum sum suka koma bayan inna Meri suka tsaya suna fiki fiki da ido kamar za su yi kuka.
Inna Meri ta juya ta kallesu kamar tayi dariya sai kuma ba ta yi ba.
Ta jawo Hassan jikinta shi kuma Hussaini ya lafe a bayanta.
Cikin sigar lallashi ta ce"To sojojin Inna ba ku gai da kawun ku ba."
Daga jikinta suka hadɗa baki wajen faɗin.
"Kawu ina yini."
Kai tsaye ya ce"Barka da dare ake cewa ina yini ba gaisuwa ba ce kun ji ko?
A tare suka ɗaga masa kai, yan biyu ne masu tsananin kama da juna.
Inna Meri ya kallah kafin ya ce"Daga ina suke Inna? kuma wa ya kawo su?
Inna Meri ta mikar da Hassan ta na ce musu su shiga ciki wajen uwarsu Walida, sum sum suka wuce suna tafe suna taɓa juna ba Halin su yi mugun wasa yanzu kawun su ya za ne musu jiki su san Halinsa ai tunda a ɗakin Inna Meri suka yi yaye, bai damu da kankantarsu a lokacin ba, da sun fara ma Inna kukan banza in da yazo gidan sai ya zane su. Da suka gane shi suna ganinshi suke shiga taitayinsu yara ne yan shekaru biyar zuwa shidda.
Sai da suka Shige Inna Meri ta fara faɗa masa cewa Bintu ce ta kira waya ta ce Walida tazo ta na son ganinta ashe wai faɗa tayi da miji da kishiya shi ne ya sa ta ce Walida ta tattaro yaran ta kawo mata su yi kwana biyu a hannunta
Cikin takaici ya xe"To Inna makarantar su fa? Inna ta ce"Walida ta ce ko an basu hutu, sai ranar litini za su koma, Bintu finitinanniyar yarinya ce Baban Inna ba ta jin mgana tunda Basiru ya aureta wlh bai huta ba, ta addabeshi ta addabi matarsa, kuma shi yana jin kunyar Babanku ne shi ya sa yake raga mata amma al'amarinta sai kara gaba gaba kawai yake yi, Walida ta gaya min ta ce sanda ta shiga gidan Bintu na tsakar gida tana na bala'i uwargidanta na cikin ɗaki ba ta fito ba amma haka Bintu ke zage zage kamar ɗiyar maguzawa."
Mansoor ya yi shuru na wani lokacin yana jin Inna na faɗin "Ku shiga mganar kai da Mu'azzam Babanku bazai iya da fitinarta ba." Sai kawai ya jinjina kai kafin ya ce"Ko Bintu ta fara hauka ne ba mu sani ba Inna?
Inna meri kamar tayi kuka ta ce"To ga dai shi, abubuwan da take aikatawa ba na masu hankali ba ne."
Kai tsaye ya ce"Inna laifin ku ne, kunsan cewa Bintu bata san ilimin zaman aure ba me ya sa kuka aurar da ita? kuma shima Bashir ɗin wawa ne kamar shi yana namiji ashe ban sani ba sakarai ne? ta ya ya yana namiji zai zauna mace ƙarama kamar Bintu na juyasa? Ita ke auransa ko shi ke auranta?
Ya karishe faɗa cikin ɓacin rai, yana jin takaicin yanzu nan in ransa ya ɓaci sai ya ta ka ya je har gidan ya ci mata mutumci tunda ya fahimci ta fara zama mahaukaciya.
Ganin ya fara harzuka ya sa Inna Meri ta sausauta tana faɗin"Ka bari zuwa gobe ka kira shi Bashir ɗin da ita kanta Bintu ka ji abunda ya faru, nima ban ce ka raga mata ba, ka ci min mutumcinta tunda sakara take mara wayau." Karamin tsaki ya ja kafin ya ƙwalama Walida kira ta fito da sauri tana faɗin gani yayammu. Idanuwansa har sun fara sauya launi ya kalleta yana faɗin"Me kika je kika iske Bintu nayi a gidanta?
Walida ta ce"Sai faɗaa ta ke yi tana zage zage wai duk wanda yaci amanarta ba ta yafe ba tac e na tafi da su Hassan sai Yaya bashir ya gane bashi da wayau."
Inna Meri tace"Kai Jama'a me Bintu take son zama ne ni Meri?
Shuru ya yi yana wani tunani, bai ɗauka haukan Bintu ya kai haka ba.
Yana ji Inna na faɗin "Fitinar Bintu ya yi yawa, fitannannu biyu Allah ya bani cikin ya'yana da kai da Bintu kai na samu saukin naka Fitinar itace yanzu take son kasheni da bakincikinta."
Da sauri ya ce"Ki daina haɗaani da ita Inna ni halina ba irin na Bintu ba ne, wannan fa mahaukaciya ce."
Inna Meri tace"Hmm ka ma fita, yanzu ne ka daina jawo fitinar da ta fi karfinka Baban Inna."
Ya na jin ta ɗauko wannan mganar ya yi saurin mikewa ya fice yana ce mata an kira sallar Isha'i zai je ya yi sallah ya dawo.
Daman tasan bazai zauna ba, shi da bayason mganar kwata kwata. To kuma gaskiya ne shi ai fitinarsa ba mai iya kwantar da ita sai Allah. Ga bakar Zuciya kamar Kuturi ga kafiyan tsiya ita fa tana ganin Bintu ko kama kafar Baban Inna ba ta yi ba wajen fitina da taurin kai.
Shi zata iya cewa ta wajen dangin Ubansa ya ɗauko wannan hallayar, ita Bintu fa? Ta rasa gidan uban da ta ɗauko hallayan fitina da rashin son zaman lafiya.
Tana jin Walida na faɗa mata ɗakin Bintu duk an fasa kwalaben turaren wuta tana tunanin kila ma dambe tayi da yaya bashir ɗin kafin ya fita. Inna Meri ta mike tana faɗin"To Allah shi ya ye ma Bintu wannan bala'in bani iyawa da halinta ni kam in ya gaji shi basirun ya sakota ta dawo gida ta zauna." Daga haka ta mike ta shige ciki domin ta da sallah.
Su Hassan sun yi barci ba mugun wasa.
A can masallaci Mansoor ya haɗu da Baba da abokinsa makocinsu Mallam Hashimu, albarkacin Baba yasa suka dawo masallaci tare da su Baba Sani, a kofar gida suka tsaya wannan yace bashi da abinci Baba sani ke faɗin ko ƙwayan hatsi babu a bangaransa Mansoor ya taimaka masa.
Baba Danjuma na gefe kamar ya saka kuka gabaɗaya ƴan uwansa sun zubar da kimarsu da Allah ya basu, sun koma maula wajen wanda ya ke matsayin ɗa a wajensu.
Bai ce bazai ba su ba, kudin da ke Jikinsa duka ya kwashe ya ba su 20k ammh ya ce musu in ya dawo zai ƙara musu, suka karɓa ko Godiya domin sun raina abunda ya ba su. Ko kunya suka wuce bangarensu Baba Ɗanjuma ya sauke Numfashi kafin ya ce"Ka yi hakuri Mansoor kaji ko?
Kansa na kasa ya ce"Haba ba komai Baba suma iyayena ne yadda zan yi maka abu suma suna da haƙƙin na yi musu."
Jinjina kai kawai Baba Ɗanjuma ya yi yana ta saka albarka. A kofar gidan suka tsaya Mansoor ɗin ya kawo masa mganar Bintu.
Baba Danjuma ya ce"To ni sha'anin Bintu ya fara isata yarinyar nan ba ta jin mgana."
Mansoor yace"Baba ba ita ta haifi kanta ba. Ubanta zata ci wlh tunda na lura ba ta da hankali."
Baba Ɗanjuma ya ce"To kila kai in ka yi mata magana ta gyara, ammh ni da Meri har mun gaji da yi mata nasiha mun ƙyaleta, yaro nan kunyata yake ji shi ya sa bai ɗauki wani mataki akanta ba, ammh sha'anin Bintu ya wuce hankali, kwata kwata ba ta daraja mijinta ta zame ma sa fitina a gidansa." Mansoor jinjina kai kawai yake yi yana tunanin gobe daga studion gidan Bintu zai wuce yana so ya ga Iskancin da aka ce tana aikatawa ne.
Ga shi shegiya bata san komai ba sai hauka, ya'yanta ma ba ta iya kula da su sai dai ta kawo ma Inna ta dinga wahala da su, to a gobe zai saka Walida ta maida mata ya'yanta in bazata zauna da ya'yanta ba to ta aika su wajen kakarsu ta bangaren uba,
Amma ba gidan su ba.
Tare suka shiga gida da Baba Ɗanjuma, ranar Magajiya ke da Miji tana ganinsu tare ta fara masifa tana manganganu ganin haka yasa Mansoor bai tsaya ɗakin Baba Danjuma dake tsakanin Korodon Inna Meri ba, sai ya shiga falon Inna Meri ya zauna Walida ta zuba masa tuwon masara da miyar kuka yana ci suna hira da Inna har ya kamallah yace kuma a ijiye masa ɗumame da safe in ya dawo training zai shigo ya ci.
Karfe goma ya bar gidan ko ɗakin Baba Danjuma bai leka ba tunda Magajiya na ciki yana shiga sai kuma ya jawo tijara, tunda ita kam tun yana ƙarami yasan ta tijararriya ce ba ta raina abun mgana musamman ma shi da ta ke ganin ba ɗan gida ba.
Ya isa gida goma da rabi, da ne ya kan zauna majalisar su matasa a anguwansu amma yanzu majalisar ba kowa, dukkansu sun kama kansu wasu sun yi aure wasu kuma ba ma a garin suke sana'ar su ba ya na jin daga shi sai Nasir sai makama suke garin Gombe. Nasir kuma ya yi aure sannan anguwar da ya ke zaune da matarsa akwai nisa a tsakaninsu sai su jima basu haɗu ba.
Makama ne kaɗai da shi suka rage ba su yi aure ba, ko kuma ya ce shi kaɗai ya rage tun da Makama an kusa bikinsa ma'aikacin bankin First bank ne, shi ya sa in ya shiga anguwan sai dai ya zauna a gida ya yi hira da Inna ko Baba ya ci tuwo ya fito ya koma gida ya kwanta. Shi kanshi yasan rayuwarsa ta sauya, abubuwa masu dama sun sauya daga rayuwarsa. Mafarkinsa, burinsa da komai nashi ya sauya, shi ya sa yake jin kansa kamar bashi ba.
Tabbas Mansoor Ajin yanzu ba shine Mansoor Aji a shekaru