Showing 63001 words to 66000 words out of 103785 words

Chapter 22 - IDAN AN CIZA..! Part 1 Complete by Janafty.txt

Janafty   

20 Dec 2024

4808

ta manyan mata 8k*


Zaku sameta a Kan Lambar waya 08147832783 tana garin kano tana aikawa da kayanta ko ina da yardar Allah. Dadin dadawa kuma tana bada sarin komai cikin farashi me rahusa yadda zaki sami Alheri. Wani ƙarin jin daɗin ma free delivery withn kano take yi, koh ba yanzu zaku siya ba kuyi saving numbern ta dan nan na gaba Na gode. https://wa.link/pd4ie0


*Page 13*


*3rd June, 2011*


Suna zaune a ƙofar ɗakin Inna Meri ne gabaɗayan su. Satin da ya wuce a ka yi bikin Yaya Amina tare da Yaya Halima to labarin bikin su Bintu ke ta yi Inna Meri na biye musu. Mansoor da Mu'azzam daga baya su ka shigo gidan tare da Baba Ɗanjuma, sai suka barshi a bangaran Magajiya da tunda aka yi sha'anin nan take ta bala'i da ya da habaici.


A tunaninta Baba Ɗanjuma ya ƙarar da duka abin da ya mallaka a auran Amina da Halima ko a wajen taron bikin sai da suka yi hatsaniya da yayar Mahaifiyarsu Aminan Madina sai da Inna Meri ta shiga tsakani ta ce duk kowa ya yi banza da ita daman abokin yi take nema, kuma daman ita Magajiya burinta shi ne ta watse taron kar a gama lafiya tunda tana da ciwon hassada a cikin ranta ga duk abin da ya shafi rayuwar Inna Meri da ƴaƴanta.


Idanuwanta ya rufe a tunaninta duk kayan da aka yi ma Amina da Halima da abubuwan da akayi na hidimar biki daga aljihun Baba Ɗanjuma ne, abin da ba ta sani ba hatta da abincin da a ka ci a wajen bikin Inna Meri ta yi tanadin shi tuni, sannan game da kayan ɗaki da sauran
hidima dangin mahaifiyarsu sun yi matukar namijin koƙari sannan ita kanta Inna Meri bangaran su tukunya kayan aiki na mata duk ita ta yi su aikin da take fita kullum ba ta bar shi a banza ba duka tattalinta na wajen yara nan mata manya musamman Amina da Halima. Shi Baba Ɗanjuman ma lokacin da maneman auran Aminan suka zo cewa ya yi ba shi da abun aurar da Amina Inna Meri ce ta ce a saka shekara zuwa a ga abunda ubangiji zai yi. To an fa saka na Amina ko wata uku ba'a yi ba Halima ta samu Inna Meri ta ce a haɗa waje ɗaya tunda dangin Habiba sun ce su za su yi komai da yardan Allah.


To da Jajircewanta tare da tsayuwar yan'uwan mahaifiyar su Amina aka samu aka yi auran nan cikin rufin asirin Ubangiji a ka kai kowacce gidanta dake cikin gari, to tun bayan bikin Magajiya ba ta bar su sun zauna lafiya ba sai Allah ya isa take yi in an ci amanarta, ita masifarta ai zuwaira ma ta samu miji Ɗanjuma ya ce ba shi da Kuɗin aurar da ita yanzu sai dai kila zuwa gaba a tunaninta ya ƙi aurar da Zuwaira amman ya buɗe bakin Aljihu ya aurar da yaran da yake so duk ba ta san kokarin na matar kwarai ce irin Inna Meri ba


Suna shigowa lungun ɗakin Inna Meri Mu'azzam ya ce"Inna sai yaushe ne Magajiya za ta hakura da wannan zage zagen ne? Inna Meri na zaune a kofar ɗakinta ƙafafunta na mike, Bintu ta samu kafafun Inna ta yi filo da su, a yayin da kuma Walida ke can daga bayan Inna tana faman zuro kanta. Share tambayar na shi ta yi da kallon zaratan ƴaƴan nata, cikin Yanayin maganarta ta ce"Sai yanzu kuka dawo?
Mu'azzam ne ya samu gefen tabarman da suke zaune ya zauna lokaci ɗaya yana faɗin " Wlh Inna sai dai har yanzu ba'a dace ba duk inda muka san za mu samu hanya mun bi abun dai sai godiyar Allah kawai."
Sai inna ta jinjina kai kafin ta kalli Mansoor da ke tsaye ya jingina kansa da garu ga takardu a hannunsa.


Cikin Marairecewa ta ce"An ya Baban Inna ba za ka hakura da neman Sojan nan ba kuwa? Abu kusan shekara uku da gama sakandirin ka, kana zaune gida ba cigaba abokan karatun ka tuni sun san matakin da suka taka, ni tsiyana da kai nacin tsiya ba ka jin shawara ka yi ta kafiya kan abu ɗaya har ga ƙanin ka nan shima ya gama shekeran da ta gabata shima yana so ya biye ma ka da sai ya zama ɗan ƙwallo tunda naku burin Allah bai yarda ya cika ba sai ku watsar da ra'ayin ku, ku nemi zaɓin Allah ku samu in da kuka laɓe domin gyaran goben ku."
Ta ke faɗa cikin bayyana yadda abun ke damunta Baban Inna fa shekarunsa uku da gama makaranta amman ya ƙi cigaba ya ki kuma zuwa wajen sana'a ya na ce shi sai ya je makarantar Sojoji, kuma an yi nema har an gaji ba sa'a a wanchan shekaran wani kawun su Mu'azzamu har hanya ya yi masa ya je kaduna ya yi jarabawa amman da ta fito sunan shi bai fito ba, duk inda ya san za'a samu yaje amman ba'a dace ba shima Mu'azzam ya gama wanchan shekaran shima ba yadda Alhaji Mustspha matsayin uba yake a wajen mahaifiyarsu bai yi da shi ya nema masa jami'a ya cigaba da makaranta ba ya ce shi Ɗan ƙwallon kafa ya ke son zama yayansa kuma ya ɗaure masa kugun cewa a bar shi ya bi ra'ayinsa.


Abokan da suka tashi tare tuni kowa ya kama kanshi, hatta Nasir ya samu Jami'ar Nasarawa keffi ya na can ya na karatunsa ban da su, kullum sai dai neman yawo da takardu sune gidan ɗan siyasa da gidan wanda suka ji labarin zai taimaka shi kan shi Baba Ɗanjuman ya ɗaure musu kugun a kyalesu Su nemi abunda suke so a dai tayasu da addu'a kawai. Ko uffan Mansoor bai ce ba ko su Binta da suka gaishe shi bai amsa ba, Mu'azzam ne ganin Inna ta fusata tana faɗa ya sassauta murya yana faɗin "Inna ki yi hakuri ki yi mana addu'a amman ni kaina na karaya yanzu haka da kika ganmu daga gidan Couch ɗinmu na Nasara muke Tunda su suna da hanyar da za'a ɗauki mutum daga manyan kungiyoyin kwallon kafa ta Nageria a bashi horo amman duk sanda muka je sai ya ce wai ba kungiyar dake neman ɗan wasa in ana nema zai neme mu, kin san me nema mun koma ne mu kara masa tuni in ana nema kar ya manta damu"


Inna Meri ta kallesa cikin takaici kafin Ta ce"Mu'azzamu ka daina bi ta kan wannan yayan naka, shi kanshi baisan me yake so ya za ma ba. Ka bar batun neman za ma ɗan Ƙwallon nan ka zo ka yi karatunka Allah ya sa maka albarka kana gamawa ka samu aikinka ya fi ye maka wannan zaman da kake yi kana biye ma wannan da bai san ina zai dosa ba."
Mu'azzam ya ce"Inna ya sani fa, Soja yake son zama."
Ƙaramin tsaki ta ja kafin ta ce"Ai sai ya zama muna nan muna jira." Mu'azzam yayi dariya yana kallon Mansoor da hankalinsa ke kan karamar wayarsa ya na ɗan mirmishi
Inna Meri ya kallah kafin ya ce"Hajiya na gaishe ki da gajiyar biki, yanzu daga can mu ke." Ya lalubo aljihunsa ya ɗauko Sweet da yawa yana mika ma Bintu da har ta zuro kai yana faɗin"Anty Mami ta ce na kawo ma su Bintu."


Da gudu Bintu ta warce ta na ihun Murna Mansoor ya kalleta a karkace kafin ya ce"Ke ashe wawiya ce bansani ba? tana jin haka ta yi gum da bakinta ta na raba ido.
Walida ta mika hannu ta na faɗin"ki ba ni Nawa " Bintu ta make kafaɗa kafin ta yi mgana Mu'azzam ya ce"Sai kin bata ko wlh ke ma ya haramta gare ki, yarinyar nan son kai gareta." Hararansa ta yi kafin ta tura baki shi kuma sai ya mika hannu zai kwace da yasa ta kwashi uku ta mika ma Walida sauran kuma ta tura cikin sikat ɗinta ta mike da gudu zuwa cikin ɗaki.
Mu'azzam ya girgiza kai kafin ya ce"Inna Allah yasa Bintu ta jiƙan ki wata rana."
Inna na yar dariya ba ta ce komai ba illah kai da ta daga sama tana kallon taurari kafin ta dawo da kallonta kan Mu'azzam ta na fadin"Hajiyar tana lafiya ko? Allah Sarki Hajiya gobe zan shiryar takanas ba domin aiki ba na je na yi mata godiya."
Mu'azzam ya ce" Ya kamata Inna Hajiya tana da kirki, duk abun Yayanmu sai da ya yabi kirkin Hajiya." Inna Meri ta yi shuru ba ta yi mgana ba ita fa akwai wani abin da ke ba ta tsoro shakuwar bintar Hajiya da Baban Inna soyayya suke yi, tun tana ganin abun yarinta ne har dai yanzu ta yardan ma kanta da gaske ne. Ban da Baban Inna da rigima ina shi ina ƴar masu kudi, ai wannan jawo ma kai fitina da jidali ne.


Yarinyar nan kunyar surukan take yi mata in dai taje gidan ba ta iya haɗa do da ita, ita kuma Hajiya ba ta damu ba domin ta ce abunda Binta ke so shi ta ke so. Ba za ta taɓa mantawa da sun taɓa maganar da Hajiya saboda Hajiyar da kanta take ce mata yara nan fa da gaske suke son juna su ke yi. A lokacin Dariya Inna Meri ta yi kafin ta ce"Haba Hajiya yarinta ne da shirme irin na Baban Inna sai kuma shakuwa amman ai ruwa ba sa'an kwando ba ne, kuma ina shi ina aure yanzu? Duka duka nawa yake?
A lokacin sai Hajiya ta ce"To ai ko ba yanzu ba Meri sai iyaye su shiga mganar, kamar yadda ya ke son zama Sojan nan ya je can ya na karatunsa itama tana nan ta na yi sanda ya gama ya dawo itama ta gama sai su yi auransu ai ba wani abu, ni fa ba na ƙyamar zuru'arki Meri ke macece mai kirki da mutumci ya'yanki masu tarbiya ne, kuma maganar ruwa ba'a san kwando ba ne bai taso ba abin da Binta ke so shi nake so, matukar kuma ta ce Mansoor ta ke so ni kuma zan shige gaba wajen na ga ta samu abin da take so."


Tunda lokacin Maganar sai ta fara damunta ta turke Mu'azzam kuma ya tabbatar mata da gaske Baban Inna na son Mimi irin soyayyar da ba zai iya kwantatawa ba, in ba ta manta ba yana da kuma ra'ayin aure tunda ya na da ƙananun shekaru, ita abu daya ke damunta da shi nacin tsiya da kafiya sannan ga ɗauko fitinar da ta fi karfinsa in ba neman jawo zaune tsaye ba ina shi ina Binta yarinyar da Ubanta ma akan dole ya bar ta hannun mahaifiyarsa ita fa tana hango ma Baban Inna nadama kan wannan shegen kafiyar nashi. Kan nacin sa da zama Sojan nan har Mallam Sidi ta shirya ta je bikin yaron yalwa da shi ma taso tafiya ya ce shi ba zai je ba, ta ma ta zencen Babansa yakubu ya kira shi ya je can Bauchi ya same shi ya yi masa faɗa ƙo ya ji Yalwa ta ce to in Yakubun yazo ko in sun yi waya tunda yanzu ya yi ƙarfi kasuwanci yake a Bauchi yana can shi da iyalansa.
To kila dai ba ta samu magana da shi ba ne, bai aiko ba kuma sannan ba ta kara ji daga Yalwa ba, ta so shi Yakubun ya kira shi ya matsa masa kila ya watsar da wannan ra'ayin na sa na zama Soja ya nemi wata hanyar.


"Inna me kika dafa ne?


Mu'azzam ya katse mata tunani sai ta yunkura ta mike tana faɗin "Tuwo ne miyar yauki bari na zubo muku."
Ta zubo musu kenan sai ga Baba Ɗanjuma ya shigo gabaɗayan su suka yi masa sannu da zuwa ya amsa ya na ƙokarin sakin fuskarsa. Cikin ƴaƴan na shi ya zauna suka ci cin tuwon Mansoor ne ya fara ƙoshi ya tashi Baba Danjuma ya kallesa yana faɗin"Ka ƙosh ne Baban Inna?
Yana nufar randar Inna ya ce"E Baba.!"
ruwa ya diɓa a buta ya shiga makewayi ya kama ruwa sannan ya wanke hannunsa ya kuskure bakinsa. Bayan ya fito sai ya zo ya durkusa gaban Baba Ɗanjuma kansa na kasa, Inna Meri na gefe tana kallonsa kafin ta yi mgana Baba Danjuma ya ce"Ya aka yi ne Baban Inna? da wata matsala ne."


"Baba Aure nake so na yi.."


Gabaɗayan su suka kalleshi a tare Mu'azzam sai da ya ƙware da tuwo duk da ya san hakan zai iya faruwa amman bai tsammanci maganar da wuri ba, inna Meri ta yi tagumi kawai tana kallon Baban Inna yaro ƙarami na neman saka kanshi a wahala shekararsa fa duka duka ashirin da uku ne tsawon kafa ke jansa yake ganin ya isa ya yi aure har ya riƙe mata yana zaune ba shi da sana'a naira biyar ma na bashi sha'awa. Baba Ɗanjuma sai ya dakata da cin tuwo ya miƙe yana faɗin"Babban mgana, taho ka zuba min ruwa na wanke hannuna sai mu yi maganar sosai"
Haka ko akayi ya zuba masa ruwa a bakin magudanar ruwa ya wanke hannunsa sannan ya koma ya zauna yana kallon Mansoor mirmishi ya suɓuce masa ai shima ya taɓa gaya masa haka tun bai kai haka shekaru ba.


"Baba ni fa ba zan bari sai na fara tsufa zan yi aure ba, da wuri zan yi aure saboda ba na so ya'yana su taso su ganni ƙarfina ya ƙare."


Ko a lokacin da ya ce masa haka sai da ya yi dariya kuma yana da yaƙinin Baban Inna zai maimaita mganarsa lokaci kaɗan tunda shi baya faɗin abin da ba shi ne acikin ransa ba, Inna Meri ya kallah kafin ya ce"To ke fa Meri kin ji, za ma ai bai gan ki ba Baban Inna Aure yake so yayi"
Inna Meri ta ja katon tsaki Mtsewwww kafin ta ce"Ai sai ya yi auran tunda auran faɗe ne a fatar baki, ban da shegen rigima kana yaron ka da kai ba ka ba wani ajiya ba, kai ba ka ijiye mai ba ka ba sai kawai rana tsaka ka ce wai aure za ka yi? Anya Baban Inna..!"
Ta faɗa tana nuna shi da yatsa kai tsaye ya ɗago yana kallonta kafin ya ce"Inna ina da gado na, a saida gonakin baba na Mallam Sidi ayi min aure da shi."
Ai sai Inna Meri ta hau tafa hannu tana faɗin" Yai naji sheganta ka, zan ɓace ka Mansoor yanzu nan wlh."
Baba Ɗanjuma da ya ga ranta ya ɓaci yayi saurin tare ta da faɗin" Kar ki yi masa faɗa ai ba laifi ya yi ba, kuma bai yi ƙanƙanta ba, waɗanda ba su kai shi ba ma su na yin aure yanzu dai mu saurare shi mu fara sanin in da ya samu matar"
Inna Meri gabanta na faɗuwa ba ta son ta ji ya kira sunan da zai ba ta tsoro.


"Mimi ce, jikar Hajiya in da Inna ke zuwa aiki."


Inna Meri ta ɗora hannu a saman kanta lokaci ɗaya tana faɗin"Na shiga uku ni Merama, da gaske daman son yarinyar nan kake yi baban Inna? Me ya sa ka cika fitina ne? Ina kai ina wannan yarinyar?


Kai tsaye ya ce"Inna tana sona itama, kuma Hajiya ai ta sani kuma ta amince da hakan."


Inna Meri ta aika masa da dakuwa lokaci ɗaya tana faɗin"Ka ga naka nan, In Hajiya ta sani Hajiya ce ta haifeta, babanta Soja ne kuma ko Hajiyar ba ya jin maaganarta wlh ba zai aura maka ƴarsa kana zaune ba ka da wani tunani ba, ko a addini mai sana'a aka ce ba mai burin banza ba, ka fita idona da wannan mganar na ma gaya maka."
Daga haka ta tashi ta shige ɗaki tana ta faɗa, shi kuma Mansoor yana gayama Baba Ɗanjuma ai ya na neman karatun Soja in ya samu zai iya rike Mimi, Baba Ɗanjuma ya samu ya lallaɓashi yace za su yi mgana da Safe.


A can ɗakin su ma Mansoor Mimi ya kira a waya yana faɗa mata ya faɗa ma su Inna zai aueta, tunda itama yanzu tana da waya da ta saka Hajiya ta sa Daddy ya siya mata mai kyau da ita yar yayi. Mu'azzam bai isa ya ce ma yayansa wani abu ba, amman shi kanshi ya na hango ma kansa ya yi gaggawa sannan Soyayya ta rufe mishi ido ya kasa gano abunda Inna ke hango masa. A daran shima Baba Ɗanjuma yayi ta fama da Inna Mari ta sauka daga fushinta su yi mgana ta ce in ta sauka sai Baban Inna ya bar maganar Jikar nan ta Hajiya, shi ko Baban Inna ya yi nisa da ba ya jin kira yadda yake jin Mimi a zuciyarsa in ya rasa ta sai ya iya mutuwa. Kuma shi ya gayama Mimi da kansa cewa Inna Meri ta ce ta fi ƙarfin shi.
Kuma su sun tsara rayuwarsu da cewa zai tafi makaranta Sojoji kafin nan za'a ɗaura musu aure sai ya barta wajen Inna ta cigaba da kararunta.


Mmi kuka reras ta riƙa yi ma Hajiya akan abin da Inna Meri ta ce, Hajiya ta ce za ta aika a kira mata Merin ta ji me ya sa ba ta son jikarta ta zama surukan ta? Ba ta ma kai ga aikawa ba sai ga Inna Merin ta zo ma Hajiya Godiya domin 100k ta ba ta da bikin nan bayan ƙananun alherinta a gareta sannan ta bata hutu ta ce har sai gajiyan Biki ya sake ta sannan ta dawo. Tana zuwa da niyar yi ma Hajiya godiya sai tace su shiga cikin ɗakinta ta na son mgana da ita. Tana jin haka tasan kwanan zencen, illai ko Hajiya ta tsareta akan me ya sa ba ta son alaqar Mansoor da Binta?
Inna Meri sai ta saka kuka cikin kukan take faɗin"Haba Hajiya ban da

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login