Showing 69001 words to 72000 words out of 103785 words

Chapter 24 - IDAN AN CIZA..! Part 1 Complete by Janafty.txt

Janafty   

20 Dec 2024

4800

dai ce ya yi ta faɗan da ta sani ba ta gaya masa ba, Hajiya ta ce"Kyaleshi dani sai dai in har zai sauya wata uwar ne." Mommy ta ɗauka kila wannan karon Major zai ji mgamar Hajiya abin da bata sani ba ita kanta Hajiyar tana shakkar abunda zai biyo baya. Bat are da sanin kowa ba ya kira Hajiya a waya suka gaisa ya saki fuskarsa ya ce yana son ganin yaron dake son Mimi acikin satin nan.
Hajiya tana murna ta ce"Ko kaifa sai ku yi mgana ka ga sai ka taimaka masa ai mai son naka mai sonka ne Kabiru."
Cikin takaici yavce"Haka ne ya zo sai mu ga abin da Allah zai yi." Amman acikin ransa yana cewa sai ya ga kalan tsaurin idanuwan mara kunyan yaron nan.


Hajiya ba ta san abin da Major ya shirya ba, da kanta ta saka direba ya kaita har gidan Wanzamai a tsakiyar ɗakin Inna Meri ta sanar da ita ta yi mgana da mahaifin Binta ya kuma amince har ya ce a tura masa Mansoor ɗin can Abuja su yi mgana.
Inna Meri sai ta ji yar salama tunda har Hajiya na faɗin"Kin san shima Soja ne, na ce ya yi masa ƙokari yaron dai ya cika Burinsa na zama Soja." Hajiya ta jima kuma tare da Mimin su ka zo sune har Mangariba daman ranar da wuri Inna Meri ta dawo gidan bayan ta ga ma Hajiya sauran aikace aikacen ta. Mimi sai murna take yi ita ba ta damu ba zata auri Aji ta zauna tare da su Inna Meri da su Binta


Ita ba ta damu ba, ta na son Aji a yadda ya ke kamar yadda shima ya ke sonta.
Ta na son salon soyayyarsa da salon kishinsa a kanta har da Mu'azzam Aji na nuna kishi in yaga ta na hira da shi yanzu sai ya sauya fuska. Hajiya ba ta tafi ba har sai da Baba Ɗanjuma ya dawo suka yi mgansa, Mansoor ya ji kamar an saka shi acikn Aljanna burinsa zai cika zai samu Mimi sannan burinsa zai cika na zama Soja.
Baba Ɗanjuma ya ce bakomai sai Mansoor ya shirya tafiya Mu'azzam ya yi karaf ya ce zai raka shi.


A bakin Bintu labarin abi da ke faruwa ya fita tsakar gida Magajiya da su Gaje suka fara manganganun Kwaɗayi ya sa yaro ya je inda aka fi karfinsa har Magajiya na faɗin da uban me zai yi auran ba shi da komai sai bakar zuciya duk Inna Meri ta toshe kunuwanta in da ace ta san abunda zai faru kenan da ba ta bari Baban Inna ya je Abuja ba da duk abin da ya faru bai faru ba abin da ta yi gudu ne ya zo ya faru a lokacin da ba ta yi tsammani ba. A cikin Satin Inna Meri ta haɗa musu kuɗin mota, shi da Mu'azzam su ka shirya tafiya Abuja ana gobe tafiyar suka haɗu da Nasir a masallaci Mu'azzam ke faɗa masa sai ya ce ai ya ji mgana ta shiga gari ana yawo da cewa Agolan gidan Wanzamai zai auri ƴar yayar Sanata Alhaji Hamza.


Shi a lokacin sai ya ba ma Mansoor shawara da cewa" Aji ni fa in da za ka ji shawarata da na ce ka hakura, domin ni ina ganin yanzu ka yi gaggawa gwara ka tsaya ka fara gina taka rayuwar kada ka manta kana da iyaye da ƴan'uwa, tare fa muka gama makaranta ni yanzu ina ji biyu Makama ma haka Ahmad ya kama sana'ar ɗinki, kai kuma fa? Kana zaune zaman jiran majirata."
Kai tsaye Aji ya ce masa" Kai dai ba ka gina taka rayuwar ba? to ka yi ta kanka Nasir."
Daga nan akayi rabuwar baram baram, shi kanshi in da ya san cin zarafin da za'a yi masa a gidansu Mimi kenan har Abada bazai taɓa zuwa ba.


Hajiya ita ta hana su bin motar haya ta saka Alhaji Hamza ya ba da direbansa ya ɗauke su Mansoor da Mu'azzam, sai garin Abuja Aji ya yi shigar manyan kaya shi da Mu'azzam har da hulunu ko alama bai karaya ba.Sun yi kyakyawan sallama irin ta Masoya da Miminsa, sun iso Abuja da yamman saboda tafiyar mota.
Sai dai tun daga bakin get suka fara raina kansu wani makeken gida mai cike da tsaron dakarun Sojoji.
Sannan Sojan dake kofar get ya ce bai san da zuwan wasu baƙi ba saboda haka ba za su shiga ba sai ya samu izini daga cikin gida.
direban ya kalli su Mansoor lokaci ɗaya yana faɗin"To ku kira mana, ina ce asan da zuwan ku."
Mu'azzam sai ya kasa mgana sai zaren ido yake yi, Mansoor kuma yana shirin kiran Mimi sai ga saƙon ta.


"Aji Nah kun isa?


"Eh mun Iso, amman wani soja ya hana mu shiga ya ce sai ya samu izini daga cikin gida."


Shima ya maida mata da amsa, tana ganin haka ta yi saurin tashi ta je ɗakin Hajiya ta gayamata, Hajiya tace bari ta kira Kabiru sai dai kuma ta yi ta kiransa bai ɗauka ba alhalin sun yi waya da safe ta gaya masa zuwan su Mansoor. Ganin bai ɗauka ba sai ta Kira Murja itama kiran wajen huɗu sannan ta ɗauka cikin yar damuwa Hajiya tace"Murja kina ina ita faman kira shuru? Baki sun iso suna waje an hana su shiga."
Mommy na jin wani iri ta ce"Hajiya ba ni da wannan ikon, Major ya ce sai shi da kanshi ya ba su izinin shigowa."
Hajiya tace"Lafiya me ya faru? Shi kabirun ya ce haka? Mommy ta ce"Hajiya ya hana ni mgana ne, amman na so na kira ki na ce kada yaron nan yazo wlh major ya shirya wulakanta yaron nan ne Hajiya"


Da sauri Hajiya ta ce"Innalillahi wa'inna illahirraju'un.."
Da kuma sauri ta yanke kiran Mimi hankalinta ya tashi ta ce"Hajiya lafiya?
Hajiya ta ce"Maza ki kira Mansoor ki ce direban da yakai su ya juyo da su."
Mimi ta dafe kirji kafin ta ce"Me ya faru Hajiya? Abi ne ya kore su?
Hajiya ta mike tana faɗin"In ma koran ne da sauki, Kabiru ya rufeni a baibai."
Hankalin Hajiya duk ya tashi ta kuma ta da hankalin Mimi sai dai Mimi ta yi ta kiran wayar Aji ba ya tafiya, Hajiya ta saka ta kira Alhaji Hamza Daddy shi kuma suna wajen taron siyasa bai ɗaga wayar ba
Hajiya ta kasa zama waje ɗaya faɗi kawai ta ke yi" In har kabiru ya wulakanta yaran nan ba zan yafe masa ba."
Hankalin Mimi ya tashi ta fara kuka ta yi ta turama Aji sako.


"Aji Nah kun shiga gidan?


"Hajiya ta ce ku juyo Abi ba zai amince ba.".


Amman ina shuru kuma ko an kira wayar ba ta shiga, su kuma a lokacin suna nan a kofar gida kamar wasu kayan wanki, saboda direban da ya kai su ya ce kai su kawai akace ya yi nan ya zube su ya juya mota ya yi tafiyarsa, abun tausayi Mansoor da Mu'azzam zaune a kofar gidan su Mimi tun karfe biyar har aka yi mangariba, sojan nan ba Imani a ranshi tuni ya shige ciki ya rufe get sai a Aji ne ya gangara can bakin hanya ya siyo musu ruwa suka yi alwala suka yi salla akan dandalin Kofar gidan su Mimi. Mu'azzam ya gaji ga yunwa ga kishi cikin galabaita ya kalli Mansoor dake nuna dakiya ya ce"Yayanmu ka kira Mimi mana, wlh na gaji da zama anan."
Shuru ya yi ya na wani tunani, da gaske a san da zuwan su amman me ya sa za'a kira su daga wani gari kuma a tozarta su?.
Ƙaramar wayarsa ya duba sai ga layinsa Emergency ba ya iya ma kira sai kawai ya kalli Mu'azzam kafin ya ce"Ba Network, mu kara jira dai mu gani."


Tun suna ganin abun wasa har dai suka tabbatar da an kira su ne domin aci zarafin su. Sauro sun yagi rabon su ajikinsu, su ne anan kamar wasu almajirai har karfe goman dare. Mu'azzam yunwa ya ke ji kuma gashi anguwan ta masu kuɗi ce babu masu saidae saide a wajen. Mansoor yace bari ya je can bakin titi ya gani ko zai samu ko mai doya ne ya siya musu. Mu'azzam ya rike masa hannu ya na faɗinn"Mu tafi gida, daman an kira mu ne domin a ga an wulakantamu." Aji ya yi shuru yana kallon ƙaninsa da yunwa ta galabaitar dashi daman a hanya gurasa kaɗai suka siya kuma ba ta da wani yawa..
Shi kan shi ya na yin dauriya ne, amman ya ku sa gazawa. Soyayyar Mimi ta makantar da shi da ganin laifin abin da ke shirin faruwa.


Kafin ma Aji ya samu zarafin mgana sai ga wata katuwar mota ta zo za ta shiga gidan, direban ma soja ne sun ga dai ya tsaya Sojan da ke gadi ya sunkuya ya yi masa mgana su ka ji yana faɗin" Yes Sir..!
Motar na shigewa Sojan ya zo ya ce musu su tashi su shiga ciki in ji Oga.
Jiki duk ya saki Aji ne mai kaurin jiki Mu'azzam duk ya gama laushi.
Ashe ba cikin gida za'a kai su ba nan katon haraban gidan aka ce su zauna su jira tun suna san ran ganin an zo an kira su har suka sare haka Mu'azzam ya fara amai sai ruwa saboda yunwa. Hankalin Mansoor ya tashi saboda Kaninsa na gaba da soyayyar Mimi.
Kokarin fita daga gidan ya ke yi saboda ya je ya samo ma ƙaninsa abunda zai saka a bakinsa. Sojan nan ya ce Oga bai ce su bar shi ya fita ba, ransa ya ɓaci zuciyarsa ta yunkuro daman ga shi ba ta da kyau balle kuma an ɓata mata.
Sai ya yi kokarin fita da karfi wannan Sojan ya saka katon takalmin kafarsa ya shure shi sai da ya faɗi. Mu'azzan na ganin haka ya tashi sai ya ma daina jin jiri ya je ya rike ɗan uwansa yana ba ma Sojan hakuri da har ya fara nuna Mansoor da bindiga.
Dakyar ya hakura sai da wani sojan su masu tsaron kofar shiga gidan ne ya yi masa mgana cikin harshen turanci sannan ya ƙyaleshi.


Shi kuma Mansoor sai faman sakin huci yake ke yi, an riga an yi sara kan gaɓa Kuma a dai dai lokacin megidan ya ce a shigo da su kamar zai ce sun fasa shiga sai kuma wata zuciyar ta ce ya je ya ga waye wannan Mutumin da ya ke da zarran wulakanta shi, sai ya miƙe shi da Mu'azzam sun yi laushi kamar lawashi, Allah yasa daga su sai kayan jikinsu da ai sun rena kansu.
Soja nan na gaba suna bin shi a baya haka suka shiga falon gidan, Ba kowa a falon sai Abi ya na zaune kafa ɗaya kan ɗaya ga bindiga a saman tuburen dake gabanshi suna shigowa ya mike a fusace bayan ya yi ma Sojan da ya rakaso alamun ya bar falon.
Sai da ya fice sannan ya musu wani matsiyancin kallo Mu'azzam ne ya yi saurin zubewa a saman cafet domin ya kasa iya tsayuwa cikin muryan da ta ji jiki ya gaishe da Abi ko kallonsa bai yi ba cikin Ƙaraji ya ce"Wane ne daga cikin ku yake son Mimi?
Ya faɗa kai tsaye cikin takama Mu'azzam ya tsorata domin ko iya kallon Major Kabir bai yi ba saboda ya yi masa kwarjini sannan muryansa ma kaɗai abun tsoro ne.


Mansoor na tsaye ƙi kam ya ce"Ga ni nan.."
Major Kabir ya tako har kusa da shi ya kallesa daga sama har kasa a ransa yana fadin lalle yaga tsaurin idon yaron.
Cikin Yanayin maaganarsa ya ce" Wani zarra gare ka da ya sa har ka iya takowa gidana acikin falona kana gayamin kai ne kake son Mimi? Kai ne ka hure mata kunni take kokarin saɓa ma umarnina miye matakin da ka taka a rayuwa?
Ya faɗa yana kallon Mansoor da ya yi kamar bai ji shi ba, ya dunkule hannunsa kamar zai kai naushi sai faman huci yake saki kamar shi ne Sojan ma.
Major kabir ya kallesa cikin mamaki kafin ya daka masa tsawa yana faɗin" Ina tambayarka kana min shuru? kuma ina mgana kana tsaye? Ka rage tsawon ka a ƙasa na ce.!"
Ya faɗa a tsawace amman goganka ko gezau sai ma Mu'azzam da ya kallah cikin fitar numfashi ya ce"Tashi mu tafi Mu'azzam."


Major kabir ya ga kamar Mansoor ya raina shi ya zo har gidan shi bayan ya aikata masa wannan laifin kuma yana masa mgana shi zai nuna ma jan wuya lalle bai san me ake kira da Soja ba yau zai sani.
Magana kawai ya yi sai ga sojoji kusan huɗu sun bayyana afalon cikin huci nan da nan ya ba su umarnin su rike masa Mansoor su banƙare shi, Mu'azzam ya fashe da kuka yana faɗiin"Ka yi hakuri don Allah kada ka saka a dake shi."
Cikin fusata Major kabir ke faɗin "Kamar ni? Kamar ni wani talakan agolan da ubansa har ya mutu a ƙauye, tarihin rayuwarsa kaf babu abun mamora. Yaron da uwarsa ke aiki a karkashin mahaifiyata ba ka da wani Future mai inganci anan gaba, ka yi min laifin ka yi soyayya da ƴata ba da sanina ba ka hure mata kunne ta saɓa ma umarnina maimakon ka nemi afuwata sai ka zo har gabana kana min takama. Who are u.?


"I SAID WHO ARE U...?


Ya ƙara faɗa cikin matsancin tsawa, ya kuma saka kafarsa lokaci ɗaya ya daki kasa sai da suka ji karan bugun takalminsa Mu'azzam tsoro ya kama shi ya fara makyarkyata shi kuma Mansoor Major Kabir ya ce su banƙare masa shi nan da nan ko suka cika aikinsu yana fizge fizge riko ɗaya suka yi masa sai ga shi a hannunsu to in takamarsa zuciya ya zo gidanta.
Mommy dake cikin ɗaki tana jiyo duk abin da ke faruwa ita da Khadija..ta yi kuka har idanuwanta sun sauya oauni
Me ya sa Major zai yi haka? Me ya sa zai saka a kira yaro nan saboda kawai yaci zarafin su?. Tun ɗazu Hajiya da Mimi ke kira ta kasa ɗaga wayarsu. Khadija ce ke leke ta kofa ta dawo da sauri tana faɗin"Mommy Abi kada fa ya yi kisan kai ga shi can ya saka soldeirs sun riƙe shi."


Mommy na jin haka ta mike jikinta na rawa ta ce" Ba zan bari hakan ta faru ba Khadija yau sai na karya dokar Major."
Khadija na riketa ta fizge ta fita saboda ji ta ke yi kamar abunda ya ke shirin aikatawa bai kyautu ba. Kuma daman ya ce kada ta sake ta fito in shi bai kirata ba.
Tana fita dai dai lokacin da Major ya ba da umarnin su yi ta dukan Mansoor har sai ya gane kuran shi. Mu'azzam na kuka yana roƙon shi ya daka masa tsawa da cewa ya rufe masa baki ko shi ya tashi kansa da bindiga. Mu'azzam ya koma gefe yana danne bakinsa, ji ya ke yi kamar ya saki fitsari saboda tsoro.


Mommy da gudu ta ƙarisa gaban Major ta duka tana faɗin"Please Habiba ka ce su rabu da shi, na ji bai kyauta ba sai ka gaya masa ba yanzu zaka aurar da ƴarka ba, shike nan ka bar su tafi."
A fusace ya kalleta kafin ya ce"Wa ya baki izinin fitowa? .How dare are u Murja?
Ya faɗa cikin tsawa sai kawai ta fashe da kuka tana kallon yadda sojojinsa ke dukan bawan Allah da bai ji bai gani ba.
Ta yi rokon duniyan nan ya kauda kai ya ce in har Mansoor ba zai ba da hakuri da bakin shi ba su yi ta dukan shi har gobe da safe.
Mommy na kuka ta ce" To in suka kashe shi fa? Da ƙarfi ya ce"In ya mutu banza ne ya mutu, rayuwarsa ba ta da wani amfani da ni zai yi wasa? Am i his mate? da Major zai yi gogayya yana ɗan talakawa irinsa? Agola yaron mai aiki a ƙarkaahin mahaifiyata , su dake shi in ya mutu zan saka su wurga shi daji namun daji su cinye banza a banza kuma babu abin da zai faru."


Ya faɗa ko a jikinsa sai ma hannayensa da ya goya a baya ya na jin daɗin a abunda su ke yi. Kukan Mu'azzam da na Mommy ya cika falon a gaban idanuwansu sojoji suka sumar da Mansoor gau saboda duka Sannan kuma anan take ya saka su suka dauke shi yace su je fa shi a cikin kurku zuwa safe. Sannan ya kalli Mu'azzam yanq faɗin"Kai kuma zan baka wajen kwana, da safe ka san in da dare ya yi maka, yaron nan ba zai bar gidan nan ba sai ya gane ya ja da Major Kabir sulaiman Dabo sai na ƙarar da rashin kunyarsa.,": Mu'azzam ya kwanta a gaban Major yana fadin"Don Allah Sir ka yi mana rai ka yafe masa."
Mirmishi ya yi irin mirmishin basawa kafin ya ce"Sai na ga waye Boss tsakanin ni da shi."Daga haka a fusace ya bar falon ya taka zuwa ɗakinsa bayan ya ba ma wani Soja umarnin a kai Mu'azzam ɗaki ya kwana zuwa da safe.


Sai bayan shigewarsa Khadija ta fito ita kanta sai da ta yi kukan tausayin Mansoor da Mu'azzam wanda shima ɗaya daga cikin sojan ya zo ya ja shi sun bar falon Mommy haka ta ke kuka khadija na hawaye.
Dakyar ta iya tashi ta shiga kitchen ta zuba abinci a faranti ta fita kofar falon da kanta ta yi ma shugaban sojojin tsaron gidan mgana ta mika masa abinci ta ce a kaiwa Mu'azzam wanda aka fitar da shi daga baya.


Khadija kuma ta saci wayar Mommy ta kira Hajiya ta na hawaye ta labarta mata abin da ya faru Hankalin Hajiya ya tashi acikin daren ta Kira Alhaji Hamza tace gobe gobe ta ganta a Abuja, Mimi daman ta ji a jikinta tun kafin Hajiya ta sanar mata abunda ya faru ta ke kuka abun tausayi.
Hajiya har kuka sai da ta yi na wannan cin zarafin da Kabiru ya

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login