Showing 12001 words to 15000 words out of 103785 words

Chapter 5 - IDAN AN CIZA..! Part 1 Complete by Janafty.txt

Janafty   

20 Dec 2024

4785

ɗauka lokaci ɗaya ta buɗe murfin motan ta fice.


Ajiyar zuciya ta sauke kafin itama ta ɗauki jakarta ta buɗe kofar bangaran mai zaman banza ta bi bayan Mimi wacce megadi ke ta yi ma maraba da zuwa da Slsauri take tafiya shi ya sa bata ma ji sa ba, sai Rukky aka bari da amsa masa gaisuwarsa sannan cikin son jin menene ya faru da rayuwar Mimi haka? Sannan wanene wanda maganarsa kaɗaai ke rikita Mimi? duk kokarin Rukky sai da Mimi ta rigata shiga falon Hajiya.
Da Baaba Uwani suka fara cin karo wata mata dake zaune tare da Hajiyar Shagamu.
ƴar'uwansu ce daga can Akko aka zo da ita mijinta ya rasu ƴaƴan ta huɗu kuma suna wajen dangin babansu, ta zauna acan saboda rayuwa ya sa Hajiya ta ɗaukota ta dawo wajenta da zama gabaɗaya shekaru biyar da suka gabata.


Ita ke faɗin "Binta har an dawo? barka da dawowa." Da yake da Binta kowa na gidan Hajiya ke kiran Mimi, ammh yau kam Binta bata saurareri Baaba Uwani ba a tsakiyar falon ta watsar da jakar hannunta da key ɗin motarta da gudu kuma ta karisa ta shige wani koridon da zai sadata da ɗakinta kamar kuka ta fashe da shi kafin ta karisa cikin ɗakin. Tunda har suna Jiyo gunjinta daga falon.


Baaba Uwani ta kalli Rukky da ta tsaya a tsakiyar falon cikin rashin mafita kafin ta ce"Topa yau kuma me ya samu Binta?
Rukky ta karisa ta kwashe jakar Mimi da key din motartaa, sannan ta kalli Baaba Uwani tana faɗin"Baaba Uwani yadda kika ganta nima haka na ganta, Ina Hajiya?
Baba Uwani tace"Hajiya na cikin ɗaki tunda ta shiga salla bari na yi mata mgana."
Daga haka ta wuce ta Koridon da Mimi ta shiga Rukky kuma ta samu ɗaya daga cikin Kujerun da suka yi ma Falon kwanya ta zauna. Wani abu ne ya bata mamaki bata taɓa tunanin Mimi ta taɓa yin wani relationship ba, tun suna kano duk wanda ya ce yana sonta kamar makiyinta haka take ɗaukanshi. Ta saka Mimi ckin sahun matan da Soyayya ko aure baya gabansu ta fi ɗaukanta a matsayin macen da take ba ma aikinta muhimmanci fiye da komai a rayuwarta. Sai dai mganar Yaddiko ta sakata shakku da kuma halin da Mimi ta nuna yanzu, abu ɗaya take son sani shi wannan waye shi ake mgana a kan shi? wani matsayi gare shi a wajen Mimi da tuna shi kan ɗaga mata hankali?


Tunaninta ya katse sanda taji sallamar Hajiya da sauri ta mike tana sakin mirmishi. Hajiyar Shagamu kenan tsohuwa lafiyayya da ba ta da irin ƙananun cuwukan zamani na tsoffi da kafafunta da karfinta sannan da idanuwanta da bakinta ras tana gane kowa fara ce sai ɗau duk da ta tsufa sannan gashin kanta duka ya koma fari Saboda furfura, a tsaye take ma'ana tana da kaurin jiki fatar jikinta har wani kwanciya ya yi saboda hutu da jin daɗi kuma a kiyasi za ta kai shekara Saba'in da wani abu a duniya. Amma kana ganinta ka ga Mimi za ka san ita sak mimi ta kwaso kuma zaka so ka ga hotunanta tana matashiyarta Kila sai dai aga Mimi na biyu saboda tsabar kamar su.
Abin da na lura shine gabaɗaya Ahalin Sulaiman Dabo suna ɗiban kamanni da juna.


Hajiya ta na ganin Rukkaya ta washe baki ta na faɗin "A'a mai sunan yan gayu ne yau a gidan?
Rukkaya kanta na kasa ta amsa lokaci ɗaya kuma ta durkushe kasa ta na gaida Hajiya.
Sai ta amsa mata itama ta na zama kan ɗaya daga cikin kujerun falon tana ce ma Rukkaya ta tashi ta koma saman kujera ta zauna. Ba ta yi musu ba ta ta shi ta zauna lokacin kuma Baaba Uwani ta kawo mata ruwa da lemu a wani ƙaramin faranti da ƙaramin Kofin silba.
Bayan gaisuwa da tambayan gida da aiki Hajiya ta kalli Rukkaya kafin ta ce"Ita Bintan tunda ta shige bata fito ba? Hala kun biya wani wajen ne kafin ku kariso nan ko?
Kan Rukkaya na kasa tace"E. mun biya gidan wata Yaddiko."
Nan da nan fuskar Hajiya ta sauya lokaci ɗaya tana faɗin "Me ya sa Yaddiko ba ta jin magana ne? Ta yi kuma ƙorafin Binta ba ta zuwa gudanta, kuma in ta je bakinta baya iya shuru sai ta ja abin da kafin Binta ta koma gidanta sai an yi ta fama kai jama'a."


Hajiya ta faɗa ta na mai lokarin bayyana takaicinta kafin ta ce"Allah ya sauwake to."
Rukayya ta tashi taje gaban Hajiya ta mika mata zogalen da Mimi ta barta da ɗauka lokaci ɗaya da jakar Mimi da key ɗin motarta tana faɗin.
"Hajiya ga sakon zogale Yaddiko ta ce a kawo miki. Wannan kuma jakar Mimi ce da key din motar ta"
Hajiya tace Rukayyan ta ijiye a kan Kujera, sai ta ijiye mata sannan ta tashi ta koma wajen zamanta ba ta jin kishi amma kada Hajiya tayi mganan bata sha komai ba ya sa ta zuba ruwa ta sha kaɗan.


Falon ya yi shuru kowannensu da tunanin da ke cin ransa. Rukayya ce ta kauda shuru bayan ta kalli Hajiya ta ce"Hajiya Mimi kamar kuka take yi acikin ɗakinta fa?
Hajiya ta sauke numfashi kafin ta ce"Shi zata yini yi yau tunda aka famo mata wannan tsohon ciwon, yau kuma kamar gidan makoki haka zai kwana."
Rukky ta gyara zama kafin ta ce"Hajiya shin wane ne naji yaddiko na mata maganar shi? Domin bayan an yi mganar ne Mimi ta shiga cikin tashin hankali tun muna hanya ta fara Koke koke." Hajiya ta yi shuru na wani lokaci kafin ta ce"Wani shuɗaɗɗen labari ne Rukayya, shekarun sun daɗe amma In Binta ta tuna kamar yau abun ya faru haka take ji." Sai kuma ta yi shuru Rukayya kuma ta kosa taji ko waye wannan da tunashi kaɗai kan iya haifar da tashin hankali a rayuwar Mimi


Cikin ƙaguwa Rukayya ta ce"Hajiya to wane ne wannan mutumin da tuna shi kaɗai barazana ne ga kwanciyar hankalin Mimi?
Hajiya ta yi wani iri kafin ta kalli Rukayya ta ce"Wani ne, wani saurayin Binta ne da suka yi soyayya da jimawa."
Rukky ta ware ido kafin ta ce"To yanzu ya na ina? sun rabu ne ko ya rasu ne?
Hajiya ta girgiza kai kafin ta ce"An ya? Bai rasu ba ya na nan da ransa. Irin soyayyar nan ce tun na tashen balaga Rukayya ya so Binta itama Binta ta so shi kamar ta mutu, amma faruwan wasu abubuwan ya sa suka rabu tun shekaru sama da takwas ina jin."
Rukayya ta yi jugum kafin ta ce"Me ya hana su aure tun a wanchan pokacin Hajiya? Kuma anan garin ne ko acan Abuja?


Hajiya ta ce"Mahaifinta ya hana al'amarin, A nan garin ne anan kuma suka haɗu lokacin tana zuwa min hutu,"
Rukayya cikin ƙarin mamaki ta ce"Kuma tun bayan rabuwarsu yana nan a nan garin nan?
Hajiya ta yi shuru kafin ta ce"Gaskiya ba na jin ya bar garin nan, tun da tun bayan faruwan lamarin zumunci mu ya yanke tsakanina da mahaifiyarsa ba ni da labarinsu, ba ta zuwa in da nake nima kunya da nauyi sun kasa barina har yau na nemeta. Allah Sarki Inna Meri wata mace kwara ɗaaya da na zauna da ita mai kirki da mutumci mai kawaici da yaƙana mai hakuri da sanin darajan ɗan adam ta zauna dani kamar ni na haifeta daga baya abubuwan da suka faru ba ma su daɗi ba ne shi ya sa sai alaqan da ta haɗamu tun a wanchan lokaci ta jima da lalacewa daga kuma Lokaci ban kara jin labarinsu ba amma ina da tabbacin suna nan a garin nan


Rukayya ta yi tagumi tana jin Hajiya kafin ta ce"To Hajiya me ya sa Abban Mimi ya hana su aure tun da Mimi tana son shi?
Hajiya ta ce"Ai shima ya sota, ya so ta sosai so mai tsanani wallahi. sai dai kinsan komai sai Allah ya yi, alokacin duka an yi abun ne cikin rashin lura da gaba, shi ya sa ake son in mutum ya ciza to ya busa saboda gaba kar ya zo yana nadamar abin da ya aikata, labarin ba shi da daɗin faɗa mai sunan yan gayu ki bar maganar kawai, gwara ki tashi ki karisa gida yau sai sa'a Binta zata fito daga cikin ɗakinta" Ba haka Rukayya ta so ba, ta so ne taji mafarin labarin, ba za ta iya gaddama da Hajiya ba ya sa ta mike ta yi mata sallama ta fita.


Sai da ta taka da kafarta har can babban titi sannan ta samu adaidaita zuwa gida.
Kuma ita duk tunanin ya tafi akan me ya hana wannan auran? Sannan taji Hajiya na faɗin alaqar dake tsakaninsu ta lalace tun daga wancan lokacin, a kuma yadda ta fahimta Hajiyar kanta bata ji daɗin abin da ya faru a wanchan lokacin ba sannan kuma duk yadda akayi Mimi na son wannan mutumin kuma shi ne dalilinta na har yau ba ta yarda ta ba ma wani namiji dama ba, duk ko da tarin masoyanta. Za ta so ta ji oabarin wannan Soyayyar domin kuwa tana da tabbacin akwai abun al'ajabi acikinsa.


Za ta yi ta bin Mimi a sannu sannu har sai ta san komai, ƙarin abun mamaki yadda Mimi tace bai yi aure ba shima a gidan Yaddiko. Kenan tana labarinsa? ta kuma kila san a in da yake rayuwa? Ammh me ya sa bata neme shi ba, tunda dai saboda soyayyarsa ta ki ba ma kowa dama ya kamata ta nemeshi saboda ta ba ma zuciyarta abin da take so.
Har ta isa gida jukinta a sanyaye yake, sai taji Mimi ta ba ta tausayi soyayya ai kamar guba ce, ita kanta da suka rabu da saurayinta faisal ta sha wahala kafin ta farfaɗo balle na Mimi da aka ce sama da shekaru takwas da suka gabata


*****


*7:30Pm*


Tun da ta shiga ɗakinta bata fito ba, duk ko da magiyan da Baaba Uwani da Hajiyar da kanta suka zo suna yi mata akan ta fito ta samu wani abu ta saka ma cikinta. Sai ta yi kamar ba ta ji su ba har suka gaji suka kyaleta. Mimi ta yi kuka kukan da sai ta ɗauki lokaci ba ta yi irin shi ba, ammh duk lokacin da tunaninshi ya bijiro cikin duniyarta haka yake maida ta.


Har zuwa yaushe ne zuciyarta za ta daina tunanin sa da begen sa?


Sai yaushe ne za ta iya cire sa a cikin zuciyar ta? yaushe ne za ta sauya rayuwarta ta daina zaman jiran warrabuka?.
Jiran da ta san har gaban abada na cire tsammani ne?
Ita tasan ba zai dawo gareta ba ya tafi kenan kamar yadda ya faɗa da gaske yake sun yi rabuwan Abadan Abadan ne tsakaninta da shi.


Shekaru goma kenan ammh soyayyarsa acikin zuciyarta tana jin ta kamar sabuwa.
Babu abinda bata yi ba saboda ta manta da shi amma ta kasa, babu kalan addu'an da ba ta yi a gaban ka'aba saboda Allah ya cire mata soyayyarsa a cikin zuciyarta ba amma lamarin kamar yana kara nisa ne, ba ta jin ko ɗigon soyayyarsa ta ragu daga zuciyarta sai ma take ji kamar duk ƙarin minti ɗaaya na bugawar numfashinta kara son shi take yi. Ta fara son shi tun bata son menene so ba, ba zata taɓa manta garkon ganinta da shi ba, tana da shekara goma sha shidda a lokacin hatta date ɗin ya kasa ɓace mata a cikin tunaninta.


20 December 2008.


A cikin hutun third tearm da makaranta kan ba su mai tsawo Hajiya ta kira Abi a waya ta ce maza maza ya saka akawo mata Bintu tayi hutu a wajenta, alokacin Abi bai so ba saboda baya so Mimi na yin nesa da shi amma Hajiya ce tanna kaunar Mimi bai isa ya ce mata a'a ba. Ba za ta taɓa mantawa cewa tafiyar Jirgi Abi ya so tayi zuwa Gombe ita kuma ta ce tafi son na mota saboda ta rika ganin gari, direban su Mallam Sale Allah ya jikansa ya rasu a hatsarin da suka samu da Abi shi ya tuko ta tun daga Abuja har gombe. Ba kuma ta yi barcin hanya ba ta yi ta kalle kalle duk abin da ta gani sai tayi tambaya shi kuma Mallam Sale na bata amsa a wannan tafiyar ta haddace sunayen garuruwa da dama kuma tafiyar na ɗaya daga cikin tafiye tafiyen da ba za ta taɓa mantawa da su ba.


Da yammah suka shigo garin ta san tana manne jikin window mota tana kalle kalle har ɗage mata glass din mallam Sale ya yi da suka shigo cikin gari. A kofar gidan Hajiya daga nesa kaɗan ta fara ganinshi.
Sanye cikin riga da wando baki da fari, rigar mai dogon hannu tana da layi layin baki a jikinta ya sanya duka hannayensa cikin aljihun wandonsa. Kansa na ƙasa yana danna karamar wayar dake hannunsa.
Lokacin da Mallam Sale ya yi hon shi kuma sai hankalinsa ya kawo wajen dai dai lokacin da ya ɗago yana kallon motar ita kuma tana kallonshi a a dai dai lokacin suka haɗa ido.
A lokacin ba za ta taɓa mantawa ba, ta yi masa mirmishi har kumatunta suka loɓa sannan ta ɗaga masa hannu.
Shi bai ɗaga mata ba, amma ya maida mata martanin mirmishinta. Wanda in za ta iya tunawa daga wannan mirmishin Allah ya haɗa zukatansu waje ɗaya zata iya rantsewa da Allah ta fara son shi ne daga wannan ganin farko da ta yi masa tana yar shekara goma sha shidda a duniya wacce ta yi jarabawar JSCE.


Tana wannan tunanin ta na tuna shi a can baya acikin idanuwanta, tana wannan kukan ta tashi ta yi sallar la'asar ta yi sujjuda mai tsawo tana rokon Allah ya cire mata soyayyar MANSOOR acikin zuciyarta da tunaninta gabaɗaya, haka da ta yi sallar mangariba tana addu'a tana kuka domin ta gaji ta sare ta na bukatar ta yi rayuwa cikin zuciyarta ba wannan nauyin da wannan ciwon.


Me ya sa ya kasa fita daga cikin zuciyarta?
Me ya sa take ganin duka maza a matsayin mata in har bashi ba?
A wajenta shi kaɗai ne namiji kwara ɗaya da ta yi tunanin zata iya zaman aure da shi, shi kuma rayuwarsa ta yi ma rayuwarta nisa.Babu abin da ke kara sakata kuka in ta tuna RANAR! ranar da ta sanya mata suna bakar rana a wajenta.
Kalamansa har gobe in ta tuna su sai ta ji kamar ta mutu.


_In har ni Mansoor na haifu cikin uwata Meri da uba na Ibrahim ƴarka ko ita kaɗai ta rage a duniya nan sai dai ta mutu nima na mutu ban yi ba aure ba_


_Nayi alkwarin toshe kunnuwana daga jin ta da ganinta na yi alkwarin sauya duniyata daga duniyarta, na yi alkwarin sauya mattacen mafarkina a kanta, na kuma gode maka da ka fahimtar dani darasin rayuwar da na daɗe ana faɗa min ban ɗauka ba, na kuma fahimci akwai tazara mai kimanin kilomita tamanin tsakanina da ƴarka, na kuma fahimci matsiyaci kamata ya yi shisshigi wajen tusa kansa in da bai dace da shi ba. Yadda ka saka iyayena kuka a kaina kai ma wat rrana sai ka yi kuka saboda ƴarka.._


Kara tuna hakan da ta yi yasa sai da ta saki kuka ta faɗi nan saman dardunan da ta idar da sallah ta na gunjin kuka, kamar kuma wacce aka tsikari haka ta tashi ta nufi waje makeken Wardrope ɗin dake ɗakin acan kasa ta fara lalubo wani abu.
Wata jaka ta dauko karama daga gani ta jima a boye duk ta yi kura. Sannan ta zo ta zauna ta buɗe jakar ta fito da wata karamar waya kiran Nokia ta da domin an jima da daina ya yin wayar a wannan zamanin.
Ta saka hannunta na rawa ta kunna wayar sai ga shi ta yi kara da wannan yar wakar ta Nokia, yadda hannunta ke rawa haka jikinta ke rawa. Ta gama saituwa wayar ta nufi ma'adanar sakonni.
Tunda hatta layin wayan bata cire ba, sai da jimawar da akayi ba'a yi amfani da layin ba Mtn sun kulle layin gabaɗaya amma abin da ta ijiye wayar saboda shi yana nan aciki. Kuma ta je ta ƙara yin rigister ta sabunta layin, ita duk tunanin ta watan wata rana zai neme ta! Wata ƙila zai tuna da ita. Saƙonsa na karshe ta buɗe kuma ajikin sunan wanda ya turo sakon ne kamar haka.


"Aji Na.!


_Kada ki ƙara kirana, ki manta dani daga zuciyarki da duniyarki gabaɗaya. Ki ɗauka bamu taɓa sanin juna ba, soyayyarmu alkwarin mu da mafarkinmu ki saka wuta ki kona su acikin tunaninki, ki kauce ma ganina kamar yadda zan kauce ma ganinki, ki kauce ma jina kamar yadda nima zan kauce daga jin ki gabaɗaya. A da ne na ke hango kaina a matsayin mai sonki ina tunanin wannan soyayyar ta isa komai a wajena ashe na yi kuskure, saboda haka ki ɗauka ma baki taɓa sanina ba kamar yadda nima zan shafe ki daga tunanina da zuciyata gabaɗaya._


Wasu hawaye ne masu zafi ke gudu kan kunci Mimi wasu na koran wasu, har da kwanan watan da sakon ya shigo da kuma lokaci 16 ga watan March 2012, da misalin karfe 9:45pm na dare ranar Laraba.
Ba zata taɓa mantawa da ranar ba, tun bayan tafiyarsu take ta kiran wayarsa ta ji ya suka sauka gida da kuma jikinsa tun da sun fita Mu'azzam na rike dashi yana ɗingisa kafarsa sannan ga raunika a jikinsa.
Ammh wayarsa bata shiga ta kira na Mu'azzam shima baya ɗauka. Wajen kwana uku tsakani sai ta koma tura masa sakon don Allah ya kira ta.
Ba ta so su yi wannan rabuwar ba, ta so ko sallama su yi da juna.
Ammh Mansoor ya tabbatar da kalamansa na shafe ta daga duniyarsa.
A kwana na biyar ne ya tura mata wannan sakon kuma daga kuma ranar ba'a ƙaara amfani da layin ba.


Ita kuma ta kasa daina amfani da nata layin, wayar tafi

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login