Showing 81001 words to 84000 words out of 103785 words
faruwa shima ya ruɗe yace bari ya nema musu Jirgi.
Dr. Sulaiman cikin wani yanayi ya ce"Ka ga ya ma Madiha cikin hikima saboda kada ta ɗaga hankalinta."
Cikin tsananin tausayin su ya ce"In sha Allahu Dr, Allah ya jiƙan Abi."
Ya amsa mata da Amin wayar mijin Khadija ya kira sai kuma kawai ya ji ita ta ɗaga Wayar cikin karaɗinta ta ce"Dr yau ni aka tuna shi ne a ka kira mu da sassafe?
Sai ya kasa gayamata ya ce ta mika ma Mijinta wayar, yanayin muryansa ya sa sai da gabanta ya faɗi cikin in ina ta ce" Dr me ya faru? Jawahir da yara suna lafiya ko?
Kai tsaye ya ce"Ki ba ma Muhammad wayar da shi zan yi mgana."
Tun daga nan ta san wani abu mara ɗaɗii ya faru sabo ba ta mantawa lokacin da Abi ya samu hatsari Dr Sulaiman ɗin ne ya kira sannan ya ƙi magana da ita sai da Muhammad. Daman ya shiga Tiolet ne ya na fitowa jikinta na rawa ta mika masa wayar ta kuma lafe a kunnensa domin ita jikinta ya bata wani abu ne ya faru.
Sai dai ta yi nadamar yadda ta kara kunnenta ta jiyo ma kanta abunda ya kusa tsaida numfashinta.
Ihu ta rika yi da kuka tana faɗin "Innalillahi Abi ne ya rasu? Na shiga uku na lalace"
Muhammad ke kokarin lallashinta amman kuma taki sauraran shi. Ba su samu jirgi ba sai suka shirya tafiyan mota tunda daga kaduna ne zuwa Abuja. Khadi sun yi mgana da Madiha kowacce murya ta shake suna yi ma juna gaisuwan rashin da suka yi madiha ta ce yanzu za su taso ita kuma Khadija ta ce suma ga su nan a hanya. Khadi ce ta kira wayar Mimi sai dai tana ta ringing ba'a ɗauka ba wayar Hajiya ma haka , sai ta kira wayar Mommy sara ta ɗauka ta ce Mommy na cikin ɗakin da Abi yake, Sai khadija ta kara rushewa da kuka ta kosa su isa Mommy ba za ta iya ɗaukan wannan rashin ba ita kaɗai ba.
Ko kafin takwas na safe a kafafan Sada zumuta duk an saka rasuwar da sauran duk wanda ya kamata yaji rasuwar Major Kabir ya ji, musamman gidan Talabijin na Karamchi a Safiyar ranar suka tashi da wannan alhinin domin ko da Alhaji Hamza ya isa gidan Hajiya Mimi ta bar gida zuwa wajen aiki tunda labaran Safe gareta.
Tana ɗakin Labarai ana gyara mata fuskarta Wayar Daddy ta shigo mata sai da gabanta ya faɗi a lokacin ba ta ji kamar za ta faɗi ba sai da ya ce ta bar komai ta taho gida ita ta sadakar Hajiya ce ta rasu daman ta barta kwance ta na gayamata ba ta jin ɗadin jikinta. Haka ta bar wajen aiki a afujajan sai dai abin da ta je ta ji ne yasa ta ruɗe ta kasa mallakan kanta
Hajiya kuma sai ta yi dauriya ita ke lallashin Mimi Alhaji Hamza kuma ya na amsa wayoyin mutanen domin in za'a saka rasuwar Major Kabir sai an ce Yayan Alhaji Hamza tsohon Sanatan jihar Gombe.
Rukky ne ta yi ta kiran wayar Mimi ba ta ɗauka ba, saboda su san abin da ke faruwa sai Mimin ta rubuta sako ta tura mata.
"Rukayya ki sanar da Manaja Abuja za mu wuce yanzu Allah ya yi ma Abi rasuwa."
Allahu Akbar zukata sun raunana yawancin mutane ma sanarwa da gidan talabijin na karamci ta yi ne su kasan abunda ya faru ciki har da Inna Meri da ta na ma cikin ɗaki lokacin suna cikin karanta labaran duniya na Safe bayan sun gama suka sanar Walida ce ta rugo ɗaki da guda tana haki ta ce"Inna yanzu nagani a Tibi ana faɗin Allah ya yi ma mahaifin mai karanta labaran na rasuwa Mimi."
Da Sauri inna Meri ta mike ta fita falo Sai ta ci karo da hoton Major kabir cikin kakinsa Soja ana sanar da rasuwarsa jiya da Daddare za'ayi jana'izarsa yau Jumma'a bayan an sauko daga sallar Jumma'a a gidansa dake Gwarimpa a Abuja.
Ba za ta manta da fuskarsa ba ta gane shi Allah Sarki rai bakon duniya daman ai ƴarsa ta ce ba shi da lafiya duk sai jikin Inna Meri ya yi sanyi a fili ta kaɗa kai kafin ta ce"Allah ya jiƙan sa da Rahama mu kuma Allah ya kyautata ta mu bayan tasu."
Walida ta amsa da Amin ita ba ta san shi ba amman ai ta san Mimi budurwan yayansu ne a baya kuma Inna Meri ta san su shiyasa ba ta yi mamakin ganin yadda jikin Inna Meri ya yi sanyi ba. Suna zaunen Baba Ɗanjuma ya shigo cikin shirin fita yana ga ya mata shima Jana'iza zai je ƙanin Mallam Hashimu ne ya rasu.
Ta yi salati kafin itama dire da faɗin "Kai Jama'a ana ta tafiya nima yanzu nake ganin sanarwan rasuwan mahaifin yarinyar nan da Baban Inna ya so mai karanta labarai anan yanzu suke faɗi jiya da dddare ya rasu." Baba Ɗanjuma ya ce"Innalillahi wannan Sojan? Inna Meri ta gyaɗa masa kai sai kawai ya jinjina kai kafin ya ce"Allah ya jiƙan su da rahma Allah yasa Aljanna makoma"
Shima yana tunawa da shekarun baya ne har an zo an gama jin ɗadin duniya kuma an koma. Kai Allah yasa mu dace, Allah ya sa mu mutu muna masu Imani Amin.
******
Kamar yadda aka sanar an yi Jana'izar Marigayi Major Kabir Sulaiman Dabo a gidansa bayan sallar Jumma'a Alhamdulillah ya samu jama'a kama daga yan siyasa abokan hulɗar Daddy tare da Abokan aikin Abi sojoji ritayas kamarsa har da masu kakin a lokacin sannan tare da mazajen yayan shi da kuma sai yan'uwa da abokan arzuka tare da dangin Mommy daga kano aka sallace shi zuwa gidansa na gaskiya. A ka bar mata acikin gida suna kuka sak abin da Mommy ta gani a mafarki shi ya faru ta riƙe gawan mijinta tana wani irin kuka sai da ƙanwarta Zainabu ta zo ta riƙe tare da sauran yan'uwanta da su Mama ko da aka fita da shi sai ta faɗi a sume ita da Mimi. Madiha da Khadi kuma sun kasa mallakan kansu ma.
Alhaji Hamza da Sulaimam suka yi ma Major wanka suka haɗashi saboda nisan makabartan sai bayan la'asar suka dawo daga kaishi. A makabarta Sulaiman ya sha kuka shi da Alhaji Hamza Jaheed ma ya iso da shi akayi jana'iza.
Shi ne ya rike sulaiman ɗin ya tada shi daga gaban kabarin Abi likita ne mai dakiya amman ya yi rashin bangon da har abada ba zai iya maida kamarsa ba.
Suna dawowa aka kafa tantuna a haraban gida domin zaman makoki.
Hajiya kuma ta yi tawakkali tana zaune da hijabi da carbi ko hawayenta ba wanda ya gani Lokacin da aka tafi kai shi bayan Mommy ta farfaɗo ta fara surutai tana faɗin
"Habibi yace na nema masa gafara wajen Hajiya, Hajiya ki yafe masa ya rasu da niyar a yau mu je Gombe ya durkusa ya nemi gafaran ki, ke ma Mimi da ke ya rasu kina bakin shi faɗi yake yi Murjanatu ki yi min alkwarin yi ma Mimi duk abin da zai saka ta farinciki ciki har da neman yaron nan ku rokesa gafaran ya yafe min."
Sai da Mama ta rufe mata baki sai sakin maganganu take yi kamar ba ta cikin hayyacinta.
Sai a lokacin Hajiya ta yi hawaye cikin kuka ta ce"Na yafe masa duk laifin da ya taɓamin da wanda ya sani da wanda bai sani ba, ina masa fatan salama da aminci da kuma dacewar wannan rana ta Jumma'a mai daraja Allah ya jiƙan ka Kabiru".
Sai Hajiya ta fashe da kukan da take ta rikewa Mimi ta koma jikinta ta kwanta suka haɗe suna ta gunjin kuka. Mommy faɗi kawai take yi" Habibi ya rasu? Ni murja ina zan sa ka kaina a gabana fa ya rasu Allah ya jiƙan ka Habibi."
Ƙanwarta Zainabu ta ce"Ki daina kiransa da wani suna in ba sunan shi ba mala'iku da sunan shi suka san shi ba Habibi ba, ai yanzu wani Habibi ya kare Murja gafaran Ubangiji zaki yi ta neman masa shi ne kawai gata da Soyayyar da za ki nuna masa"
In ka kalli Ahalin nan sai ka tausaya musu, duk da yanayin Abi amman fa tsayayyen Uba ne mai yin komai saboda ƴayan shi, shi ya gina su har su ka kawo matsayin da suke a lokacin kowacce ka gani ido ya Kumbura murya ta dishe saboda kuka,
Mutanen arziki daga ko'ina sun zo musu gaisuwa daga Gombe Rukky tare da Salim Bunza da Na Misau da wasu daga cikin ma'aikatansu da aka wakilta ranar biyu sun zo musu gaisuwa, Rukky ma nan ta kwana sai ranar uku ta koma Gombe ita ma Khadi abokan aikinta da na mijinta duk sun zo musu gaisuwa haka Dr. Sulaiman sannan Jawahir ma yan'uwanta suna ta zuwa.Haka dangin Mommy su ma sun yi mata kara kwarai da gaake.
Ana ta zaman gaisuwa manyan manyan mutane nata zuwa gaisuwa su kuma shiga har cikin gida su yi ma Mommy gaisuwa wacce ta za ma abun tausayi.
Mimi ta samu wayoyin mutanen da ba ta san wasu ba ma, a rana ba ta san adadin masu kira su yi mata gaisuwa ba, kaf ma'aikantan su har da masu Inten ba'a bar su a baya ba. Sannan ba ta yi tunanin za ta samu kiran wayar su Nasir ba.
Sai ga shi Mu'azzam ne ya fara kiranta ya yi mata gaisuwa ya ce a kafafen sada zumunta ya gani sai kuma da ga baya Usman ke faɗa masa, sannan Usman ya kirata Ahmad ma tare da Nasir sun yi mata gaisuwa kuma ta ji daɗii kwarai. Sai dai Aji bai kirata ba kuma tana da tabbacin ya sani rashi fa ta yi rashin kuma na Mahaifi, tunda ta karɓi lambarsa ba ta samun kwarin gwiwan kiransa ba. Sai ta ce bari ta gani zai iya yi mata gaisuwa?. Sai ta ɗauki wayarta ta tura masa sako.
"Aji Nah Abi ne ya rasu yau kwana biyar."
Mimi ce Fatima"
Ita kanta ta san bazai taɓa mata gaisuwa ba, tunda ya kasa mantawa da abin da ya faru a baya, abunda ba ta sani ba tun a ranar yaji rasuwar domin a daren ya je gaida Inna take gaya masa a cikin ransa ko a fili bai ce Allah ya jiƙansa ba.
Sai da Inna ta ce"Kanin ma mallam Hashimu shima ya rasu yau. Allah ya jiƙan su da Rahma."
Ba saboda shi ya amsa ba sai Saboda ƙanin Mallam Hashimu amman yadda yake jin tsanar wannan mutumin ba zai iya nema masa jinƙai wajen ubangiji ba, ba domin ya na musulmi ba da sai yace Allah ya kara nauyin kasa.
Kuma Mu'azzam ya kira sa ya gaya masa ya ce to ina ruwan sa? Bayan nan har Makama sai da ya kirasa yana gaya masa ya yi tsaki ya kashe wayarsa ya rasa waye ne baban Mimi a wajensu da suka damu da Mutuwarsa. Nasir ne da ya kirasa sai da suka yi faɗa kamar abun arziki Nasir ya ce"Ya ƙarin haƙurin mu kuma Aji?
Aji ya ce"Ni babana ya ji ma da rasuwa, Innata kuma da ranta sannan Babana uban riƙo na yana cikin koshin lafiya."
Nasir ya yi dariya kafin ya ce" Gaisuwan Major mana baban Mimi, ya kamata ka kirata ka yi mata gaisuwa sanda na kirata sai da ta tambaye ni ka sani kuwa?
A fusace Aji ya ce"Nasir ba domin kai ba ne wallahi da sai na zage ka, kada ku ƙara kirana da irin wannan shirmen na ku"
Nasir ya ce"Aji rasuwa fa aka yi? mutuwa ce fa" ƙaramin tsaki ya ja kafin ya ce"ka bari in ka mutu in ta kirani ta min gaisuwa sai na haɗa na yi mata a lokacin."
Daga haka katse wayarsa ya bar Nasir da sakin baki, Kuma a daran ta turo masa saƙo. Mamaki ya kama shi wato kenan sun ba ta lambar sa kenan.
Goge saƙon ya yi ya kuma ɗauki lambar ya saka ta a blacklist duk abunda zai haɗasa da abin da zai hana shi barci yana kokarin yin nesa da shi. Ko alama bai ji tausayinta domin wai ta rasa mahaifinta ba, shi a tunaninsa wannan in ya rasu ma abun murna an rage mugun iri a kasa ne, sauran kaɗan ya maida mata amsa da cewa Allah yasa kasa ta kara danne shi sai kuma ya fasa shuru ma ai amsa ce ga mai hankali.
*BOOK 1 FREE NE, 2,3 PAID NE REGULAR N500, VIP 1K NE, KU BIYA KUƊIN KARATUN KU TA WANNAN ASUSUN BANKIN 0552179550 JAMILA UMAR GT BANK, SANNAN SAI KU TURA SHAIDAR BIYA TA WAƊANNAN LAMBOBIN.*
*09069067488*
*80032773332*
*Ƴan kasuwa masu bukatar a tallata musu hajojinsu cikin farashi mai sauƙi, ku yi min magana ta wannan lambar*
*09069067488*
*NA GODE.*
*Janafty*
*IDAN AN CIZA..!*
*Wattpad:Jamilaumar315*
*Arewabooks:Jamilaumarjanafty*
*Mallakar:Janafty*
*SADAUKARWA GA HAJIYA AISHA AHMAD IYA*
Ina iyayem yara kuke kuzo MAIDALILI LACE AND THRIFT takawomuku ingantattun overralls bodysuit da longsleeves domin inganfa lapia dakuma kawara suturun yaranku.kamar yanda kuka sani damuna saida overall kisaqa bebynki ki sinkumeshi bakinki alaikum baruwansa da kamuwa da sanyi.akwai na yammadatan yara kamar yan 3yrs dabasan lulluba da sanyinnan kiyuta rufe yaro yana budewa tokizo kisaya musu overrall kawai dare nayi kizura yaro ciki kisamasa sock da saf wannan shi ake kira blanket huta🥰kiyi kokari ki killace yaranki awannan damunar dan gujewa kamuwarsu da damshi.inanan kano unguwar sharada ina tyra kayana ko ina a nigeria.08033627255
*Page 17*
Kimanin sati uku kenan da rasuwar Major Kabir Sulaiman Dabo, zukata sun fara ɗaukan dangana tuni baki na nesa da na kusa sun gama zaman makoki sun koma gidajen su. Ciki harda Dr. Sulaiman da iyalansa sai Madiha wanda daman mijinta ana yin bakwai ya koma da yara ita kuma sai da akayi kwana goma sannan ta koma.
Khadija kuma sati biyu ta yi sannan itama ta koma, itama dai kamar mijin Madiha ranar bakwai mijinta ya koma tare da yara, sai a ka bar Mimi da Hajiya sai Inna Zainaba sai kuma Inna Ladidi wacce take autarsu mahaifiyar Mommy mai rasuwa ita kaɗai ta rage musu a raye a ɗakin su.
Hatta iyalan Alhaji Hamza sun dawo Gombe Hajiya kuma da Mimi sai da aka yi sati uku sannan suka yi shirin dawowa saboda ita Mimi aikinta, ita kuma Hajiya saboda makota suna ta zuwa mata gaisuwa ba ta nan. Mommy dai ta ɗauki dangana amman fa sai ana yi ana lallashi duk sanda ta tuna sai kuka rana ba ta taɓa fitowa ta faɗi ba tare da ta tuna da yau ta yi rashin miji ba. Ranar da su Hajiya su ka koma sai mutuwar ta dawo musu sabuwa Hajiya ta yi kuka, kukan da ba ta yi ba lokacin da aka yi mutuwar sai yanzu Mimi ma kamar ita kaɗai aka yi ma mutuwar duk ta rame kamar ba ita ba, itama ta kasa gasgasta yau babu Abi gani take yi kamar in ta shiga Bedroom din Mommy za ta ganshi. Sai dai ina wanda ya mutu ba ya dawowa tafiya ce ta har abada sai dai fatan Allah ya haɗamu a darussalam.
Mommy ma ai ta ga kara daga abokan aikinta Saboda macece mai kirki da fara'a ita Mimi ta ɗauko wajen fara'a da iya mu'amala. Haka su Hajiya suka dawo suka bar Mommy cikin kewa Allah yasa ma ga Inna Zainabu da Inna Ladidi, ita dai Inna Zainabu ana yin arba'in za ta koma kano Inna Ladidin ne za ta zauna da Mommy har ta fita takaba. Tun da suka dawo daga Abuja yan anguwa da makota su ka ji Labarin Hajiya ta dawo a ke ta shigowa yi mata gaisuwa daga bangaran abokan siyasar Daddy ma suna ta zuwa waɗanda ba su samu zuwa can Abujan ba, har da yan'uwan su Anty da Mama da suma ba su samu zuwa can ba duk jin Hajiya ta dawo ya sa suke ta zuwa yi mata gaisuwa tare da yan'uwan mijin Yaddiko da sauran mazajen ya'yanta da ba su zuwa can Abuja ba, daman ita saboda ba ta jin daɗi kwana takwas ta yi ta biyo Alhaji Hamza suka dawo gida.
Ita Mimi ana zuwa mata gaisuwa daga wajen aikinta harda wasu mutanen da ba ta taɓa sani ba kiranta kawai a ke yi ace ta ba da address, ita kam ai ta ga kara kuma har acikin ranta taji daɗii Rukayya kaf da iyayenta sun zo mata gaisuwa har Bibi sun zo tare da Usman kamar ta yi masa maganar Aji amman sai ta fasa. Saboda ta na da tabbacin ya ji labarin babu amfani ta ci gaba da bibiyar ya sani ko bai sani ba tunda ita da ta tura masa sako da hannunta tana da tabbacin ya sani. Tun da suka dawo ba ta koma ma wajen aiki ba so take yi sai ta samu yar natsuwa.
A halin da ta ke jin zuciyarta a lokacin ba za ta iya samun wani sukunin komawa wajen aiki ba. Sai dai ta yi ta kwanciya a gida da kumburarrun idanuwana ba ta da aiki sai tunani Hajiya kuma kullum da carbi tana falo ita da Baaba Uwani, ita da ba ta nan ma aka yi rasuwar ta je kumo.
Hajiya ce ta koma ma lallashin Mimi in ta ganta cikin damuwa ta kan ce ma ta"Binta ba kuka ko damuwa Kabiru ke bukata yanzu daga garemu ba, addu'armu ita ya fi bukata shi ya sa na ce gwara ki koma wajen aiki zai rage miki zaman kaɗaici da tunane tunanen rayuwa."
Jin Hajiya kawai ta ke yi ai ita duniyarta cike take da abun tunani saboda haka ya zame mata dole ta yi kuka sannan kuma ta yi tunani. Ko bayan dawowarsu Mu'azzam ya sake kiranta ya yi mata gaisuwa sai take gaya masa sun baro Abuja suna gida ita da Hajiya, nan ya yi mata alkwarin zuwa ya yi mata gaisuwa in sha Allahu in ya shigo garin. Yadda ba ta yi ma Makama maganar Aji ba shima ba ta yi masa ba, ita a tunanin nutuwa ta kore komai,