Showing 9001 words to 12000 words out of 103785 words
goma da suka ga ba ta ba. Wannan wani sabon Mansoor ne, wanda ya rasa mafarkinsa da burinsa wanda rayuwarsa ta juya daga farinciki zuwa baƙinciki.
******
Washegari.
*Karamchi Tv*
11:30am.
Yau ba ita zata karanta labaran dare fa Salim Bunza ne, shi ya sa bayan ta gama karanta labaran safe ta tattara sauran takardun hannunta zuwa Office ɗin manajansu bangaren labarai da al'amuran yau da kullum na gidan talabijin na karamci.
Mai alhakin editer ɗin su ba musulmi ba ne Peter tare da shi suka je wajen manaja tunda ranar lahadi da safe za su gabatar da shirin sharhin labaran karshen mako ita da Salim.
Ta ji ma a wajen Manaja suna magana har peter ya fito ya barta sai daga baya itama ta baro bangaren zuwa rest room ma'ana ɗakin hutawarsu.
Babban ɗaki ne mai cike da kayan alatu kamar falon wata mace, ga A.c ta ko'ina ga tuma tuman kujeru da suka zagaye wajen ga firiza domin sanyaya makoshin ma'aikata. Sanye ta ke da Abaya mai ruwan ash colur sai ta saka mayafin Abayan ta yi roling ɗin shi a saman kanta.
Kafarta sanye cikin takalmi sahu ciki kafin kaga Mimi da takalmi na sahu waje sai ka ganta da sau ciki sau goma.
Tana son takalma masu rufi sosai, jakarta karama kalan takalminta ash mai duhuwa, a can ta samu debora mai kula da shashen bangaren kula da masu shirye shirye ita da Na Misau suna hira. Zuwan ta ya sa aka cigaba da hiran da ita, duk da jefi jefi hankalinta na kan wayanta Mimi bayan aikinta sai wayarta ta fi ba ma muhimmanci. Chart suke yi da Dr. Sulaiman ya na shaida mata a satin mai shiga shi da iyalansa za su je Abuja saboda duba jikin Abi. Itama sai take faɗa amasa da safen nan sun yi mgana da Mommy tana faɗa mata Abi na a kiran sunanta ya kamata tazo ta ganshi. Sai ya ce mata to ta bari a satin da zai shiga sai ta shigo su haɗu a gida.
Tana can ta na chart ɗinta Debora ta musu sallama ta fita Na Misau ma daya ga yana mgana hankalinta baya kansa sai ya kwashi takardunsa ya fice, suna da shiri shi da abokiyar shirinsan nan da Karfe ɗaya na rana. Sai da ta ji ɗakin ya dauki shuru sannan ta juya ta ga ba kowa sai ita kaɗai sai kawai ta jawo jakarta ta ɗauko Blutooth ɗinta ta maƙala a kunnenta ta kuma yi connacting da wayarta ta sanya wakar da kamar ita kaɗai gareta acikin wayarta.
Tana fara sauraran wakar sai ta koma ta jinginar da kanta jikin Kushin ɗin kujeran da take zaune, Kafarta kuma sai ta ɗora ta saman ɗaya wayarta na saman cikinta ta saka ɗayan hannunta ta dafe jakarta dake gefenta. Cikin zaƙin muryanta kamar ita ta raira wakar ta fara bin karin wakar mai taken lafazina na khairat Abdullahi.
_Jarabta da soyayya zafinta na ɗanɗana matuka_
_Hakika da ƙuna gun kaifi fa ta sha gaban suka_
_Nayi wutar ciki nayi bakinciki na share kuka na. Ta shiga can ciki takai farmaki ta kama hanjina._
_Dakyar na ke fidda numfashi SO ya tushe Kirjina_
_Wata rana kamar in yi ihu ko wani za ya gano takaicina_
_Mashi ya soke ni wa za ya dubeni. Raɗadin zafin azaban ya zarce tunanina._
Ta daɗe tsaye tun shigowarta tana kallonta bata ma sani ba, ta yi nisa cikin sauraran waƙan nata da kuma salon yadda ta saba bin karin wakar a koda yaushe, mirmishin gefe baki ta sa ki kafin ta fara takawa zuwa gaban Mimi duk ko da yadda Takalminta mai tsini ke fitar da karamin sauti acikin tayless din dake falon. Sanda ta kariso gabanta dai dai Lokacin da ta ji ta na faɗin
_In SO ya doke ka! ƴa'yanka har Jika, ba za ka manta ba ya shiga tarihinka kenan..!_
Ba ta bari ta ƙara ɗaukan wani karin ba ta saka hannu ta dauke wayar dake cikinta lokaci ɗaya kuma ta tsaida wakar, cikin kasala Mimi ta buɗe idanuwanta da har sun fara sauya launi ta sauke su fes kan Rukayya Bala(Baby) Ma'aikaciya ce itama a shashin tallace tallace na gidan Talabijin na karamchi. Kuma kawar Mimi ce tare suka yi master ɗin su a Bayero kano sun zama kawaye tun a lokacin da jin sun fito daga jiha ɗaya. Mimi ta fara aiki da gidan Talabijin na Karamchi ita kuma ta kawo Rukayya da suke kira Baby aka ɗauketa wattani kaɗan da suka gabata.
Tana ganin ita ce sai ta yamutsa fuska kafin ta ce"Baby ya za ki kashe min wakata?
Wacce aka kira da Bby gajera mace fara mai dan kaurin jiki, itama wani material ne ajikinta na yadi baki ta yi dinkin Bubu, amma sai ta saka wani karamin hijabi fari daga saman kanta zuwa wuyanta, ta kuma sakalo I.D card ɗinta na wajen aiki ɗauke da sunanta na Rukayya Bala da shashin da ta ke aiki.
Kusa da Mimi ta zauna lokaci ɗaya tana Faɗin "Mimi kamar wannan wakar kaɗai gareki acikin wayarki? Ko da yaushe ita kike saurara kuma ni nasan ba soyayya kike yi ba, ballantana nace wani mara rabon ne ya yi breaking heart dinki, wayarki cike suke da irin waɗaanan wakokin Mimi."
Ta faɗa ta na mai kureta da ido da kokarinta ta fahimci wani abu, kamar Mimi ta sani sai tayi sauri tashi ta gyara zamanta dakyau lokaci ɗaya tana warce wayarta hannun Rukky ta haɗa Blutooth ɗin da ke kunnenta ta tusa cikin jaka sannan ta kara Juyowa ta na faɗn"Ina jin ki me ma kika ce?
Hararanta Rukky ta yi kafin ta ce"Ke dai kika sani." Mirmishinta mai kara mata kyau ta yi kafin ta ce"Hajiya Baby mai sunan yan gayu in ji Hajiyar shagamu"
Rukayya ta saka dariya ta na faɗin"Allah Sarki Hajiyarmu na jima ban je ko na dubata ba ko na biki na je yau ne.?
Mimi tace"Oho miki, ko ɗazu sai da ta ce wai ni Binta ina ƙawar nan taki mai sunan yan gayu nace ki nan nan abun ki."
Rukky tace"Tab yan adawa sun shiga ciki dole yau naje na duba Hajiya, ya ya kin tashi aiki yau ne?
Nima na tashi sai na mu tafi tare"
Mimi tace"Na tashi tun dazu Manaja ne ma ya tsaida ni, amma ba gida zan sauka ba daga nan sai na biya gidan Yaddiko na gaisheta ko da zan fito da safe sai da Hajiya ta rokeni da Allah da Annabi na biya na gaisheta."
Rukky tace"Ba matsala sai mu fara biyawa ta can, ammh fa da yammah zaki kai ni gida in na gama miki yini."
Mimi ta mike ta na faɗin"A'a ba wajena kika zo ba, sai dai ki samu adaidaita ba na tuki in yamma ta yi"
Rukky ta mike ta rumgumota ta na mata magiya da fadanci tana faɗin"Haba Hajiyata Mimi, mimi mai kyau da ado."
Take faɗa da sigar waka, Mimi sai mirmishi ta ke yi, a haka suka fita har main falon na ma'aikatan nasu ga sauran ma'aikata nan a zazzaune suna ganinsu ahaka aka sakar musu dariya.
Na misau da zuwan shi kenan ya kallesu kafin ya ce"Yanzu haka Rukkaya maula ta ke yi tunda naga ta na rage murya"
Hararansa ta yi kafin ta ce"Shisshigi ba kwarjini ina ruwanka da shiga tsakanin ƙawa da ƙawa."
Sai ya ɗaga hannu yana faɗin"Ba ko ruwana kun fi kusa."
Mimi na dariya ta ce"Fadanci ta ke yi min Na misau wai dole sai na yi mata lift a motata."
Dariya ya kwashe dashi lokaci ɗaya yana faɗin"Rukky gaskiya ki rage son kudi ki siya mota ga kudin albashin ki, sannan ga ki lashe money ni kaina kin cuceni kudaɗe sun fi dubu ɗari biyar."
Jin abin da ya ce ne ya sa Rukkaya ta saki Mimi ta waigo tana kallon Na Misau da ya ɗaga kafaɗa yana fadin"Karya nayi? Ke kika ja har a na fallasa maganar nan, tunda kika ce ba za ki aureni ba."
Ido ta ke wurga ta na neman abun duka shi kuma Na Misau ya ɓata fuska ya juya yana faɗin "Justice for Na Misau."
Rukky ta kasa mgana sai kawai ta rarumo laptop din da ke gaban Nura ta bi Na Misau da shi shi kuma ya saka gudu yana fadin to ba gaskiya na faɗa ba.
Suka bar su Mimi da dariya Rukky da Na Misau sun saba rigimansu na fama sai sun saka cikin ka ya kulle.
Manaja ne kaɗai ke iya raba wannan faɗan shima irin su ne shi ya sa yake biye musu.
Sai ɗaya saura na rana suka bar Ma'aikansu Mimi ta ɗauki Rukky a motar ta wata fara ta kamfanin Toyata mai kyau da yarari motar har ɗaukan ido take yi, suna tafe suna hiran bikin kanwar Rukky da za'ayi nan da wattani huɗu.
Mimi ta kalli Rukky, hankalinta na wajen tuki ta ce"Baby wai waye Bibi zata aura ne?
Rukky ta ce"Wani Usman ne ɗan gidan makama yana aiki a bankin First Bank."
Mimi ta maimaita sunan Usman da Makama acikin ranta sai dai ya bayyana a saman bakinta. Cikin mamaki Baby ta ce"Ko kin san shi ne?
Da sauri Mimi ta girgiza mata kai alamun a'a acikin ranta tana tunanin ko dai Usman ɗin da ta sani ne shekaru masu yawa a baya.
Kai ba shi ba ne, shi wannan da makama ta san shi ba Usman ba.
Saurin kauda wannan tunanin tayi ganin sun shigo yankin fantami in da gidan Yaddiko yake, a kofar gidan Mimi ta faka motar ta saboda gidan na masu karamin karfi ne, tunda Mijin Yaddikk ɗan kasuwa ne mai karamin jari ya'ya ne ma suka taso suka kara gyara gidan ya yi kyau ya koma na zamani.
A kofar gidan sun ga dandalin matasa tunda gidan yana da dakali kuma tun a zamanin baya Mimi tasan kofar gidan Yaddiko baya rabo da matasa.
Suna ganinta sanda suka fito daga motar zuwa kofar da zata sada su da cikin gida.
Suka fara kiran sunanta tunda duk wanda ke garin Gombe ya san fuskar Mimi , tunda gidan Talabijin na Karamci na gaba gaba cikin sahun manyan gidajen talabijin a garin. Fuskarta ba ɓoyayyiya bace a garin.
Hannu ta rika ɗaga musu tana mirmishi Rukky na gefe tana faɗin"Hajiya Mimi kin fa samu ɗaukaka ina ga ko Manaja baya fita ayi masa wannan kiran."
Ture ta Kaɗan Mimi ta yi ta na hararanta har suka shiga gidan nan wasu ba su daina kiran sunanta ba. Gidan Yadikko cike yake da jikokinta duka ya'yanta ta aurar da su amma tarin Jikokin da suke gidan sun isa gayya duk da Yaddiko na da faɗa jikoki na son zama a gidanta saboda Allah ya dora mata son yara.
Suna shiga aka fara musu oyoyo Anty Mimi, itama ta na son zuwa gidan saboda yaran ammh saboda Yaddiko ya sa ba ta son zuwa duk lokacin da ta zo sai ta yi mata maganar da zai ɓata mata rai.
Rai rai tare da yaran har falon Yaddiko wacce ke zaune a saman cafet tana sakan huluna daman sana'arta kenan tun tana matashiyarta har kuma ta manyanta bata daina ba. An yi an yi ta bari ta ce ba za ta bari ba yana deɓe mata kewan zama ita kaɗai. Har kasa suka zube ita da Baby suna gaishe da yaddiko.
Aneesa daya daga cikin jikokin Yaddiko ta lafe a jikin Mimi saboda yadda take kaunarta sai faman yi mata cancare take yi da Anty mimi na ganki a Tv jiya.
Yadikko ta ijiye julan hannunta tana amsa gaisuwarsu kallon Rukayya ta yi alamun rashin sani da sauri Mimi ta ce"ƙawata ce Rukkaya tare muke aiki da ita."
Sai ta gyaɗa kai kafin ta ce"Fatima kenan sai yau na ke ganin kafarki , kina garin nan ammh bakya zuwa gaisheni sanda zan je duba Hajiya kuma kina wajen aiki."
Kan Mimi na kasa ta ce"Ki yi hakuri yaddiko zan gyara in sha Allahu."
Sai ta taɓe baki, da ka ganta kasan ta haɗaa jini mai karfi tsakaninta da Mimi Saboda suna ɗibar kama.
Mimi Allah Allah ta ke yi su tafi sai ta ji Yaddiko ta ƙwalama ɗaya daga cikin Jikokinta kira tace su kawo ma su Mimi abinci da ruwa. Mimi bakinta na rawa ta ce"Yaddiko gida za mu wuce, Rukky za ta je ta gaida Hajiya."
Kai tsaye yaddiko ta ce"Eh na sani ku ci abinci ku yi sallah sai ku tafi, ba daga wajen aiki kuke ba?
Rukkaya ce ta amsa mata, ba su da mafita dole Yaddiko ta saka aka shigar musu da abinci wani daki da ke cikin falon nan suka shiga suka cakuli abincin kaɗan Jalop din shinkafa mai Kifi sai zobo mai sanyi.
Bayan sun gama suka shiga tiolet suka yi alwala. A ɗakin akwai dogon hijabi suka yi salla sannan suka gyara fuskarsu suka fito.
Har kasa suka duka suna yi ma Yaddiko sallama Ta ce.
"Har zaku tafi?
Mimi ta gyaɗa kanta sai kawai Yaddiko ta gyara zama tana faɗin"Fatima mganar nan ce da ba ki so wato maganar aure!"
Gaban Mimi ya amsa sai ta sadda kanta kasa bata yi mgana ba.
Yaddiko ta cigaba da faɗin"Ya kamata ki manta abin da ya faru a baya ki ba ma manemanki dama ki fito da wani ki yi auranki Fatima shekaru suna ta gudu kuma kinsan dai ba niran ki lokaci zai yi ba."
Idanuwan Mimi suka tara kwallah ammh ba ta yi mgana ba.
Yaddiko ta cigaba da faɗin" Wannan yaron da kike yi ma wannan kulafacin ba ki da tabbacin yana nan bai yi aure ba, tunda mahaifinki ya yi muku tsakani kika yi alkwarin kin rabu dashi to kuma zaman jiran duk na menene?
"Yaddiko shima bai yi aure ba fa "
Ba ta san lokacin da bakinta ya kuɓce ba sai ji kawai ta yi ta faɗa.
Daga Yaddiko har Rukky suka bi ta da kallon mamaki, ita yaddiko ba ta yi mamaki ba daman ta faɗa maHajiyar shagamu yarinyar nan yaron nan data kwallafarai a kansa ta ke zaman jira shi ya sa ta zaɓi ta zauna ba aure ita kuma Rukky ta na mamakin waye wannan a cikin rayuwar Mimi da ba ta taɓa sani ba?
Sai dai Yaddiko ta katse mata tunani da cewa"Au ko shi kike jira ya zo ya aure ki?
Da sauri Mimi bakinta na rawa ta ce"A'a wlh yaddiko ba shi na ke jira ba, tunda nayi ma Abi alkwari na rabu da shi to da gaske nake yi wlh." Yaddiko ta kura mata ido cikin nazarinta kafin ta sauke numfashi tana faɗin"Tashi ku je jibi ina nan shigowa na duba Hajiyar ki gaishe ta."
Daman kamar akan ƙaya Mimi take ,ta mike da sauri Baby ta mara mata baya duk da haka sai da ta tsaida suka karɓi sakon Hajiya dafaffiyar zogale a leda da kuli ta ce a kai mata, Mimi ta karɓa suka yi ma Yaddiko sallama suka fita bayan ta ba ma yaran 2k ta ce su raba.
Mimi bata sauke numfashi ba sai da suka bar layin, sai dai yadda ta ke tukin za ka fahimci Mimi ta rasa natsuwarta sai gudu ta ke yi abin da ba halinta ba ne.
Rukky ta kalleta kafin ta ce"Mimi wannan halin da kika shiga yana da alaqa da mganar Yaddiko ne?
Wane ne na ji tana mgana akan shi?
Da sauri Mimi ta ce"Plz Rukayya ki yi min alfarman toshe kunnuwanki kamar ba ki ji mganar yaddiko ba, wannan mganar ta shuɗe daga tunanina da duniyata ba na son tunawa kwata kwata a rayuwata."
Tana maganar idanuwanta sun tara kwallah lokacin da ta dire mganarta sai hawaye sharr suka zubo mata kuma ta kasa share su. Yaushe ne zata daina tunanin shi? Sai yaushe ne za ta manta da shi?
*Janafty*
*IDAN AN CIZA..!*
*Wattpad:Jamilaumar315*
*Arewabooks:Jamilaumarjanafty*
*Mallakar:Janafty*
*SADAUKARWA GA HAJIYA AISHA AHMAD IYA*
MMN MUJAHID KAYAN MATA AND SUPPLEMENT
SHIN KINA DA LABARIN MACCE MAI GYARA DABAN TAKE GA ZUCIYA MIJIN TA, MUNA DA KAYAN MATA MASU ZAFI NA BUGAWA GA JARIDA
HAJIYA TA KUDI DA KUDI AKE NEMAN SU
INA MASU FAMA DA MATSALA RAMA BA GABA BA BAYA KINA ZAUNE ANA KWATANCI DAKE KINA CI BAKI KOSHI MUNA DA MAGUNGUNA DA ZUMA 3 IN 1 KIBA BRST HIPS TA CIKO MIKI KU INA KIYI FRESH MUNA DA KWAYOYI MUNA DA GARI DUK MASU CIKO JIKI NE KIYI DUM
INA MASU FAMA DA MATSALA BRST KU TSUHU YAFI SON YAGA NONO A TSAYE DUK MAI MAGANIN DA TACCE MIKI ZATA BAKI MAGANIN NONO KAI TSAYE YAYI MIKI KARYA CE MAGANIN BRST SAI KIN SHA ADADIN WANDA ZAI MIKI SBD DUK CIKIN GYARAN JIKI NA BRST YAFI WAHALA YI
INA MASU FAMA DA MATSALA SANYI MUNA DA MAGANIN SANYI ORIGINAL
MUNA ADASHEN GATA SBD YANA YIN DA MUKE CIKI 500 DUK SATI IN KIN KAMALLA ABAKI DUK ABINDA KK SO
INA MASU ZAMAN BANZA BABU SANA'A KINA KONE DATA KI GA BANZA WURIN TSEGUMIN KALLON STATUS DIN WASU GA DAMA TAZU MUNA HAR GIDA GA WAYAR HANNUN KI KI MALLAKE MOTA MILLION 8 HAR FIYE GA ALBASHI GA RIBA GA KYAUTA KAYA IRIN SU WAYA
BLENDER
WASHING MACHINE
08066726866
MMN MUJAHID KAYAN MATA AND SUPPLEMENT Y'AR MUTAN SAKWATO
*Page 3*
Hashidu Estate.
Har suka iso anguwan hashidu Estate kuka Mimi tae yi, Rukky kuma tunda ta ce ta kyaleta ba ta ƙara takura mata da mgana ba. Ta dai ba ta hanky acikin karamar jakarta ta tsane hawayen fuskarta da shi.
Ji take yi kamar ta cire zuciyatar acikin gangar jikinta ko za ta daina jin irin abin da take ji, tabbas zuciya itace rayuwar ɗan Adam, in ta samu matsala to dukkan gangan jiki zai raunana. Zuciyar Mimi ta jima cikin ciwo ciwon da kuɗi ko muƙami ba zai iya samar mata da mgani ba, alokacin sai gaybom ya koma ɗanye ciwon ya yi ruwan da kamar a lokacin aka ji sa.
Ko a yadda ta rika sakin hon zaka san ba lafiya megadi ɗan baba tsoho da shekara da shekaru tun marigayi Alhaji Sulaiman Dabo na raye, bayan rasuwarsa ɗansa ya ga ji aikin gadin, shi ya zo jikinsa na rawa ya buɗe mata get ɗin gidan da gudu ta shiga gidan parking ɗin ma ba a natse ta yi shi ba.
Rukky ta kalleta lokacin da ta kashemotar ta cire key din, jakarta ta