Showing 51001 words to 54000 words out of 103785 words

Chapter 18 - IDAN AN CIZA..! Part 1 Complete by Janafty.txt

Janafty   

20 Dec 2024

4803

yazo ba, ita za ta iya raka Abin har Gonbe kuma ta bashi duk kulawan da ya dace. Ba ta kuma yi maaganar da kowa ba har su Hajiya ba ta kira ta ce ga yadda suka yi da Abi ɗin ba.


Sun dai yi waya da Mimi da ta tashi barci ta ji muryanta duk ya dishe alamun kuka sai ba ta neme ta da mgana ba, ballantana ta nuna mata sun yi mgana da Hajiya
Abi ta tambaya Mommy ta ce mata ya samu barci saboda ba ta so ta haɗasu ya yi mata wata mgana. Farinciki ta ke ji acikin ranta yau ko da ba wani abu a kallah ya sauke nauyin cin zarafin mutanenan da ya yi abu sam bai yi daɗi ba.


*****.


*Washegari.*
8:45pm.


Mu'azzam bai samu tafiya ranar lahadi saboda sanda suka koma gidan Aji a daran jiya baya gidan Allah ya sa Mu'azzan akwai key ɗin gidan ajikinsa da shi suka yi amfani suka buɗe gidan suka shiga suka kwanta..
Har safe suna ta kiran wayarsa bai ɗauka ba sai da rana Mu'azzam ya je Studio ɗin su ya same shi.
A camp ɗin su ya kwana sannan ya ki ba ma kowa damar da zai tattauna abin da ya faru jiya da daddare. Hakanan suka je suka raka Makama ango gidansa Nasir ya wuce gidansa Ahmad ma ya wuce gidansu gobe da Asuba zasu kama hanyar Mu'azzam zai rage masa hanya zuwa Kano daga nan ya samu motar kaduna.


Mu'azzam ya zo ya na ba ma Inna labarin abin da ya faru ta riƙe haɓa tana fadin"Allah Sarki Bintar Hajiya ashe ba ta manta da ni ba"
Mu'azzam yace"Wallahi Inna sai da ta tambaye ki."
Inna ta yi mirmishi itama tausayin Mansoor da Binta na cika ranta.
Kafin ta ce"Bakomai Ɗan Inna, komai ya yi zafi maganinsa Allah zai huce ka ga ya dawo da kanshi." Mu'azzam ya ce"Inna har yau Yaya Mansoor na son Anty Mami ni nake faɗa miki haka."
Inna ta ce" Har gobe ma Mu'azzamu, yana nuna cewa ba ya ta ita ne yanzu amman ƙarya yake yi duk wannan abubuwan da ka yana yi saboda ita ce kuma ina mai rantse maka in ba ita ya aura ba da wahala Baban Inna ya yi aure saboda ba zai iya zama da kowacce mace ba sai ta."
Mu'azzam yace"To inna ba za a iya yin wani abu ba? Haka za'a barshi ya karar da rayuwarsa cikin kunci?
Inna Meri ta yarfa hannu kafin Ta ce"Me zan iya yi a kai Mu'azzamu ban da addu'a? A gaban ka mahaifin yarinyar nan ya ce mu yi masa tsakanina da iarsa, shima kuma kana ji ya rantse sai dai ya mutu bai yi aure da ya aureta , ni na rasa wannan bakar zuciya irin ta Baban Inna da kafiya da riko, rikon da yake ma abun a ranshi ne yasa ka ga duk ya koma haka" Mu'azzam kamar ya yi y kuka ya ce"Inna ni dai in har ɗan'uwana zai yi rayuwar farinciki zan nemi Anty Mami mu yi magana , zan koma gidansu a Abuja na roki mahaifinta ya bari Yayana ya auri ƴarsa ko da zan mallaka masa duk abin da na mallaka ne."


Da sauri Inna Meri ta ce"Kul kar ma ka fara, ka san ai kun gwaada haka a baya komai ya lalace. Ko ka je ya amince ya janye maganarsa ya za ka yi da Baban Inna? kana tunanin shi taurin kansa da wannan bakar zuciyar zata barshi ya yafe ne ya amshe ta ko da ya na sonta? Ai ya gwammace ya mutu da wannan bakinciki akan dai ya yafe abunda ya faru ya nuna ya na son yarinyar nan har yanzu, ai gani zai yi kamar ya ragu bakar zuciyarsa ba ta kitsa masa abu mai kyau a kan rayuwarsa addu'ata kullum Allah ya saussauta masa wannan baƙar zuciyar." Inna Meri ta karishe tana fashewa da kuka Mu'azzam sai ya koma yana ta lallashinta amman shi kanshi kamar ya yi kuka. Allah yasa Walida ba ta nan tana Gidan Bintu can za ta kwana.
Asuban ci zai yi na tafiya shi ya sa ma a gida ya kwana ɗakin Saddiqu, saboda Mansoor dai ya yi ma gidansa ya ji ba zai ji daɗin kwana shi kaɗai ba.


Amman ya kwana tunanin mafita a daran kuma ya kira wayar Anty Mami ba ta ɗauka shi dai zai kara kutsa kansa cikin wata kasadar a karo na biyu mai kamceceniya da kasadar da ɗan'uwansa ya kutsa kanshi a karon farko a shekarun baya.
Ko kaɗan ba su Bari Baba Danjuma ya fahimci akwai matsala ba Saboda kada su ɗaga masa hankali.
Amman fa ya fahimci daga Inna har Mu'azzamu yanayin su ba daɗi sai ya dauka saboda tafiyar Mu'azzamun gobe ne Tunda Ɗan inna ne in ya zo uwar tasa ba ta son ya tafi.


Mu'azzam ya yi ta tufka ya na warwara, sai dai abu ɗaya ya kashe masa gwiwa da ya tuna Nasir ya gayamasa an taba hira da ita acikin labarinta ta ce mahaifinta ya yi hatsari ba shi da lafiya? Abin da bai sani ba shin ya na nan a raye ko ya rasu?
Amsar da ya kasa samu har suka bar garin a mota ma ya ke tambayan Ahmad yace shi ba'a garin ya ke ba wlh bai sani ba sai dai ya Kira Nasir din ya ji ta bakinsa tunda yana garin zai iya sanin wani abu.


*****


30 April 2022


Yasan Mu'azzam ya bar garin duk ba su yi waya ba, saboda yasan yanayin aikinsa ba zai jima ba. Sai da a daran ranar litini ya koma gidansa daman baya son lokacin da zai samu kaɗaicewa wani na gefensa.
Tun haɗuwarsa da Mimi bai ƙara barci cikin salama ba. Ya ji ya tsani kanshi ta yadda har gobe zuciyarsa ba ta daina son wannan yarinyar da yake ganin bakinta fiye da kowa a duniya ba.


In da ya san yadda zai iya ciro zuciyarsa ya ciro son ta ya jefar ya maida zuciyarsa da ya yi haka domin ya cigaba da rayuwa cikin salama.. Tun da alaqan ta yanke bai taɓa kwana ya tashi bai tuna da ita ba, Soyayarta da kishin ta suke kara wahalar da shi.
saboda ita ya kasa kallon ko wa ta ƴa mace da sunan so, saboda ita ya kashe maganar aure acikin zuciyarsa gabaɗaya rayuwarsa ta zama kamar mattaciya saboda cutar da zuciyarsa take ciki.


Kwance ya ke a tsakiyar falon sa, a saman cafet ya y filo da hannayensa idanuwansa suna Rufe ne amman yana fuskantar POP ɗn da ke falon. Bashi da riga daga shi sai ƙaramin wando sannan babu nepa falon ya yi duhu
Tunani yake yi, tunani mai zurfi kamar a lokacin haka ya ke ji amon kukanta na shiga ransa, shi ya yi mata tsawa ya saka ta kuka amman ba ta kaishi shiga bakinciki ba.
Allah kaɗai ne ya kaisa in da za shi lafiya a ranar yana tuna kukan da take yi da yadda ya ture ta.
Saboda haka a daran ranar kusan kwana ya yi ya na gudu a studio sai da ya ji ya gajiyar da kanshi sannan ya sarara.
Muskutawa ya yi ya juya zuwa da jikinsa bangaren dama.


_Ya sunan ka?_


_Ni? Ke ya sunan ki?_


_Ni sunana Mimi Mimin Abi_


Ya tuna mirmishinta da dariyanta tun alokacin sai da kumatunta suka loɓa, ba zai manta amsar da ya ba ta alokaci ba


_Sunana Mansoor Aji."_


_"Aji ?_


Ta faɗa da sigan tambaya alokacin sai da ya yi dariya kafin ya yi magana ta yi zaraf ta ce.


_To wajen wa ka zo?. Wajen Hajiya?


_A'a ni wajen Innata na zo_


_"Inna Mari mai girkin Hajiya?_


Dariya ya yi alokacin kafin yac e"Eh ita, ai innata ce."


Baki ta buɗe tana yar dariya har kayan jikinta bai manta kalansu ba, a lokacin iyakarta shekaru sha shidda kuma wannan shine gani na biyu da ya yi mata kuma maganar su ta farko shi da ita..!


Me ya sa ya kasa mantawa da ita?
Me ya sa ya kasa mantawa da duk abinda ya shafe ta?


"Saboda har yau kana sonta Mansoor."


Amsar da wata zuciyarsa ta bashi kenan.
Da gaske yama sonta? To me ya sa zai cigaba da sonta ahalin akwai bambanci mai tarin yawa a tsakaninsu?.
Kaddara ba ta haɗa su domin su zauna waje ɗaya ba, ita kaddaran da kanta ta raba tsakanin su.




*BOOK 1 FREE NE, 2,3 PAID NE REGULAR N500, VIP 1K NE, KU BIYA KUƊIN KARATUN KU TA WANNAN ASUSUN BANKIN 0552179550 JAMILA UMAR GT BANK, SANNAN SAI KU TURA SHAIDAR BIYA TA WAƊANNAN LAMBOBIN.*
*09069067488*
*80032773332*
*Ƴan kasuwa masu bukatar a tallata musu hajojinsu cikin farashi mai sauƙi, ku yi min magana ta wannan lambar*
*09069067488*
*NA GODE.*






*Janafty*
Follow this link to join my WhatsApp group: https://chat.whatsapp.com/FAtGNQc8Y8pB008TuxFJVo


*IDAN AN CIZA..!*


*Wattpad:Jamilaumar315*
*Arewabooks:Jamilaumarjanafty*
*Mallakar:Janafty*


*SADAUKARWA GA HAJIYA AISHA AHMAD IYA*


MMN MUJAHID KAYAN MATA AND SUPPLEMENT


SHIN KINA DA LABARIN MACCE MAI GYARA DABAN TAKE GA ZUCIYA MIJIN TA, MUNA DA KAYAN MATA MASU ZAFI NA BUGAWA GA JARIDA


HAJIYA TA KUDI DA KUDI AKE NEMAN SU


INA MASU FAMA DA MATSALA RAMA BA GABA BA BAYA KINA ZAUNE ANA KWATANCI DAKE KINA CI BAKI KOSHI MUNA DA MAGUNGUNA DA ZUMA 3 IN 1 KIBA BRST HIPS TA CIKO MIKI KU INA KIYI FRESH MUNA DA KWAYOYI MUNA DA GARI DUK MASU CIKO JIKI NE KIYI DUM


INA MASU FAMA DA MATSALA BRST KU TSUHU YAFI SON YAGA NONO A TSAYE DUK MAI MAGANIN DA TACCE MIKI ZATA BAKI MAGANIN NONO KAI TSAYE YAYI MIKI KARYA CE MAGANIN BRST SAI KIN SHA ADADIN WANDA ZAI MIKI SBD DUK CIKIN GYARAN JIKI NA BRST YAFI WAHALA YI


INA MASU FAMA DA MATSALA SANYI MUNA DA MAGANIN SANYI ORIGINAL


INA MASU ZAMAN BANZA BABU SANA'A KINA KONE DATA KI GA BANZA WURIN TSEGUMIN KALLON STATUS DIN WASU GA DAMA TAZU MUNA HAR GIDA GA WAYAR HANNUN KI KI MALLAKE MOTA MILLION 8 HAR FIYE GA ALBASHI GA RIBA GA KYAUTA KAYAYA KI
08066726866




*Page 11*




A Jihar Gombe a kafatanin manyan unguwannin da suka zagaye anguwan Arawa da ma nesa da anguwan da kuma waɗanda ke gabas zuwa yamman da su ba wanda bai san da zaman gidan marigayi salihu wanzam ba, wanzancin gidan ba haye ba ne gadon shi suka yi, abun sai yake bin jini, in uba ya gada sai ya gadar ma ɗa, ɗa ya gadar ma jika jika ya gadar ma jikan jikan to a haka tushe da asali gidan Wanzamai ya fara.


Inna Mari ta tsinci kanta da aure a gidan wanzamai mai cike da tsohon tarihi tun bayan rasuwar mijinta na farko, Inna Meri mai suna Maryama ba'arata daga shiyar kasar gida ta Argugun ta fito daga cikin wani yanki na garin Argugun ne, kuma duka danginta da ahalinta arawane sai dai mahaifinta ya rasu sai ta tashi tare da mahaifiyarta wacce a ke kira Inno soro.
Mallam Ibrahim sufi mutumin kwami ne karamar hukumar dake jihar Gombe a arewa maso gabashin Nageria. Mazaunin hedikwatan mallam Sidi dake garin kwami.
Kuma ya kasance manomi ne kuma mai sana'ar kamun kifi, tunda mutanen garin Mallam Sidi sun fi karfi a noma da sana'ar kifi tunda suna da ruwa sosai a garin.
A dalilin sana'arsa ta kifi ya sanya yake da mu'amalan arziki da mutanen argugun kuma yana zuwa garin sosai ta sanadin wannan mu'amalan Allah ya haɗa auran mallam Ibrahim da meri wato Maryama.
Ta baro garinsu shiyar Argugun zuwa garin mallam Sidi yan'uwan Ibrahim suka zame ma Meri uwa da uba da dangi gabaɗaya.

Uwa uba kuma mijinta na sonta kuma ya na tattalinta sannan ita kanta Meri mace ce mai alheri da maida kowa nata shi ya sa ta kasance a bar son kowa suka riketa kamar ƴar su, duk da shima ba shi da iyaye amman yana da kanne da yan'uwa.
Duka duka auransu bai kai shekaru biyu ba ta haihu ta samu ɗa namiji sai aka sanya ma sa sunan mahaifin Meri wato Mansoor, shi ne silan da Meri take kiran Mansoor da suna Baban Inna, a farkon rayuwarta ba ta taɓa tunanin wata rana mutuwa za ta yi sanadin rabata da wannan rayuwar da take ciki ba, ta zama yar garin mallam Sidi sai dai in ta je gida ziyara da ganin ƴan'uwa kowa sha'awarta yake yi ganin ta kowani Fanni ta samu jin daɗin rayuwar da kowacce mace take fatan ta samu.


Sai dai kash ita mutuwa ba ruwanta da jin daɗi da zaran lokacin ka ya yi sai ka tafi.
Mansoor na da shekara biyar a duniya Mallam Ibrahim ya rasu sakamakon kayar kifi da ta makale masa ya yi ta amai dare zuwa safe an yi an gama, Meri ta yi kuka kamar ranta zai fita ba abin da ke kara saka ta kuka sai in ta ɗaga ido ta kalli Mansoor mai kuruciya da kananun shekaru da bai san komai na rayuwa ba har ya zama maraya, yan'uwanta sun zo har akayi bakwai sannan Inno soro ta zauna tare da ita har akayi arba'in ta so ta tafi da Meri can gabanta ta ida sa takabanta sai ƴan'uwan Ibrahim suka hana suna kuka suna rokon Inno soro ka lda ta raba su da Meri da Mansoor su kaɗai suke gani su tuna da ɗan uwansu Ibrahimu.


Sai inno soro ta tausaya musu kuma ganin ba abin da Merin ta nema ta rasa sai ta bar ta a nan ta koma argugun, Allahu akbar Allah mai tsara komai yadda ya so a hanyarta ta komawa gida har ta sauka a garin argugun ta samu a kori kuran dake ɗaukan mutane zuwa cikin kauyakun su to anan ajalinta ya sauka suka samu hatsari nan take Allah ya yi ma Inno soro rasuwa
Meri ta yi kamar ta haukace ga rasuwar miji ga ta uwa abun sai ya yi mata yawa dole ta shirya ita da Mansoor da Yalwar kanwar Ibrahim suka tafi can har aka yi bakwai da farko Meri ta so ta yi zamanta a garinsu ne sai 6an'wan ibrahim suka ce ko bayan kasa ya shafe idanuwan Ibrahim ba za su bari Iyalansa su rasa mafaka ba, da roko da ban baki kawun Meri mai suna Surajo ya amince ya ba su Meri da ɗanta Mansoor suka dawo garin Mallam Sidi da zama a kuma cikin dakin mijinta suka riketa ita da ɗanta. Bayan ta fita takaba saboda halin rayuwa duk da suna kokari a kanta ba za ta ce ta zauna a haka ba.


Sai ta fara sana'ar cikin gida saboda dogara da kai ba domin yan'uwan Ibrahim ba su barta ta neme wani abu ta rasa ba amman ai ba zaka zama a kwance komai sai an dauka an baka ba a kallah dai kai ma a ga kana wani abun domin taimakawa.
Ta zauna da su na tsawon shekara ɗaya har Mansoor ya fara makaranta fimari anan cikin garin Mallam Sidi. Tun tana garin Mallam Sidi a ke kiranta da Inna Meri, saboda ita Innar kowa ne yara da manya kowa nata ne kyauta da Alherinta ya sa ta ke zaune da kowa lafiya
Mansoor kuma ya na ganin gata saboda su na ji da shi suna kallonsa kamar makwafin ɗan uwansu Ibrahimu ne, tun Mansoor ya na ƙaraminsa Inna Meri ta fahimci cewa ya na da bakar zuciya da kafiya ga naci ko faɗa ya haɗasu da yara sai ya yi kwanaki bai bar mganar ba, tun mahaifinsa na da rai in ta yi mgana sai ya ce zai bari yarinta ne.
Ko ita ce ta dakesa sai ya kame a waje ɗaya yana huci da kumburi kamar wani mai Aljanu in za ta kara masa sai ƴan'uwan uban su hana su a tunaninsu yarinta ne ya na girma zai daina sannan ga shi da fitina komai shi a wajensa na fitina ne, saukinta ɗaya suna tare da masu kaunar su shi ya sa abun sai bai cika damunta sosai ba sai da kaddara ta sake jefa ta a wata rayuwar sannan ta san illar halayen Baban Inna a wani muhallin.


Gaddaafi Ɗanjuma wanzan. Ya kasance wanzamin dake yin wazanci a tsakanin kauyen su na karamar hukumar kwami saboda sunan da gidan su ya yi, ya sa duk tsukin nan suna zuwa cire beli ko kaciya ko wani abu da ya shafi kuna suna ba da maganin gargajiya sai a samu dacewa. To Ɗanjuma ya kasance wanzamin gidan su Ibrahim Sufi sannan har shayi ma shi ke yi ma yaran gidan in aka haife su, Mansoor ma shi ya yi masa shayi lokacin da ya cika shekaru uku, sannan akwai abota tsakaninsa da Ibrahim tun ya na raye, ya na siyan Kifi a wajensa akwai dai mu'amala mai kyau domin hatta Inna Meri ta san shi, har bayan rasuwan Marigayi Ibrahim in ya shogi garin yana zuwa ya ganta har ya yi ma Mansoor kyauta baya dai zuwa hannun rabbana.
Tun Meri ba ta fahimci akwai wani abu a zuciyar Ɗanjuma ba har su Yalwa suka fahimta sai ba ta ɗauki abun da gaske ba, tunda ta san matansa biyu a lokacin ashe abunda ba ta sani ba ɗaya daga cikin su Allah ya yi mata rasuwa ta rasu ta bar Ƴaƴa uku mata biyu da ƙaramin yaro namiji.
Kuma ta san hakane bayan Danjuma ya gama zagaye zagayensa ya fito ya sanar da Inna Meri manufarsa na son auranta domin ta taimaka ta riƙe masa yaransa duk da yanzu suna hannun dangin ita matar tashi ne, amman ya fi son shi ya rike ƴaƴansa da kansa.


Bai ɓoye mata komai game da labarin matarsa ba wato uwargidansa Magajiya kenan. Fitinanniya ce mara kirki, ta yi rantsuwan ba za ta rike masa ƴaƴa ba nata sun isheta har ga Allah da farko Inna Meri ba soyayyar Ɗanjuma ya sa ta amince da auransa ba, sai illah tausayin yaran da aka mutu a ka bari tunda yace har da ƙaramin yaro dan shekaru uku da wani abu da ba ya yarda da kowa, Sai ta juya ta ga itama marayan da aka mutu aka bar mata ɗa na kowa ne ba ka san wanda zai rike

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login