Showing 60001 words to 63000 words out of 103785 words

Chapter 21 - IDAN AN CIZA..! Part 1 Complete by Janafty.txt

Janafty   

20 Dec 2024

4814

faɗin"Ni ba yarinya ba ce."
Hajiya ta kalleta tana dariya yarinyar da ko nono ba ta da shi sai kirgan dangi da ta fara har kuma yau ba ta fara Jinin al'ada ba, Murja har damuwa ta fara yi Hajiya ta ce ta kwantar da hankalinta wasu matan ba sa farawa sai sun kai sha bakwai kila Binta ta na daga cikin su ne.


A ranar Mansoor bai zo ba, ya je filin ball sun je buga wasa da yan anguwan Tudun wada, Mimi ta riƙa leƙe ba ta ganshi ba Inna Meri na mata dariya ta ce"Baban Inna ba zai zo ba tunda kika ga har yanzu bai zo ba."
Mimi ta fara fushi har ta na cewa in yazo gobe ba za ta yi masa mgana ba tunda ya ce yau zai zo za ta ba sa wani labari mai daɗi.
Hajiya aka bari da lallashi abun ma sai ya koma ba ma Hajiya mamaki ko abinci ta ƙi ci a daran wai ta yi fushi da Aji.
Da safe da Inna Meri tazo hajiya ta ce"Meri maza ki aika Yaron nan naki yazo ya sakar min jika da ƙwarin da ya yi mata tun jiya nan da kika barta take fushi saboda bai zoaa tun jiya ba ta ci abinci ba.".
Inna Meri ta rike baki tana faɗin"Ikon Allah.


Sai da Inna Meri ta lallasheta da cewa zai zo sannan Mimi taci abinci ta yi wanka da Hajiya ta so ta saka a kaita gidan Daddy Mimi tace ba inda za ta je sai ta kyaleta.
Hajiya ta yi tagumi kafin ta ce"Ni dai yau ina ganin ikon Allah ni Binta."
Inna Meri na taya ta da dariya saboda su a tunaninsu yarinta ke damun Mimi a lokacin ba su taɓa tunanin Ubangiji ya ɓoye wani abu a tsakanin su ba. Kamar ko Mansoor ya sani da Yamma sai ga shi tare suka zo da Mu'azzam saboda ba makarantan islamiya daga filin ƙwallo suke yau Mu'azzam ne ya buga ƙwallo shi bai yi ra'ayi ba.
Daman ta yini leƙen waje tana ganinsu ta fita da gudu kamar ta kifa shi dai Aji sai dai ya ganta a gabansu tana haki da sauri yace"Bi a sannu kar ki faɗi ki ji ma kanki rauni." Sai kawai ta harare shi da fararen idanuwanta


Dariya ma ta bashi da sauri ya ce"Me na yi ni kuma yau"
Cikin yarinyarta ta ce"Ba kai ne ba kai ne jiya ka ce za ka zo ba ka zo ba, sai jiran ka nake ba"
Ta na faɗa sai hawaye sai ya ji ya damu da sauri ya durkusa a gabanta yana faɗin"Afuwan Mimin Aji na je wasa ne jiyan nan." Tana sharan ƙwallah ta ce"Jiya ma ban ci abinci ba, ko Hajiya ma yau ban yi ma mgana ba saboda ina fushi da kai."
Mu'azzam na tsaye na kallon wani abu na faruwa kamar a shirin film sai gani ya yi yayansa ya kama kunni yana faɗin "I am so sorry Mimi Mimin Ajii.."


"Kin haƙura?


Sai ta gyaɗa kanta tana mirmishi kafin ta ce"Yau ka zo mu je Hajiya ta ganka sai da ta tambayi Inna Meri wai ba ta san ka ba."
Dariyan maganarta ya yi sosai ya
na shirin mikewa ya ce"Haka za'ayi ranki ya daɗe tunda Hajiya ta ce ba ta sanni ba, ya zama wajibi ta ganni yau tunda haka Mimi take so."


"Barkan mu da Yamma Anty Mami."


Mu'azzam ya faɗa bayan ya duka shima har ƙasa, sai ta fashe da dariya tana rufe baki kafin ta ce"Laa ka girmeni kana ce min Anty? Yana dariya ya ce"Ai abun ba daga nan take ba, girman ne Allah ya baki kar ki damu da ƙananun shekarun ki."
Ya faɗa yana kallon ɗan uwansa dake masa kallon mamaki.
Mimi kuma ta samu abun yi sai cewa take yi ya maimaita sunan da ya kirata shi kuma ya na ta maimaita Anty Mami, ta saka dariya ta rufe bakinta da tafukan hannunta kafin Ta ce"Aji abokin ka ne?
Kai tsaye ya ce"ƙanina ne Mu'azzam."
Da sauri ta ce"Laa shima yaron Inna Meri ne?.
Sai ya jinjina mata kai sai ta fara tafa hannu tana faɗin"Kuma ba ku kama, kai baƙi shi kuma fari, kai dogo shi kuma gajere."
Yadda take lissafin ne tana kwantance ne ya sa dole suka yi dariya gabaɗayan su.
A ranar dai dole Mimi ta yi musu Jagora suka Shiga har falon Hajiya suka iske Inna Meri na yi ma Hajiya kitso tunda ita kan tsefe mata ta yi mata wani in ya tsufa.


Sai Ranar Hajiya ta ga Ajin Mimi, Mu'azzam daman ya sha shigowa wani lokacin ma acan shi kan rako inna Merin da safe kuma ya shiga har cikin falon ya gaida Hajiya.
Hajiya ta kalli Mansoor dake duke gabanta bayan sun gaisa ta kuma kalli jikarta da Mirmishin ya ki barin fuskarta
Kawai sai ta kaɗa kai kafin ta ce"Ai shike nan Aji ko? To ni dai wani ƙwarin ka yi ma jika ta, yau fushinka har shafa ta ya yi aka ƙi yi min mgana."
Kansa na kasa bai yi mgana ba Hajiya ta cigaba da faɗin "Binta kullum L
labarinta na Aji ne, to ni dai na lura jikata na yi da kai Allah ya haɗa jininku gata nan a kular min da ita Amana domin ina ji da ita ahto, in kuma kana sonta ne sai ka fara biyana kudin toshi har da kudin zence."


Mansoor a lokacin da sauri ya kalli Hajiya.
So? So kuma? Ita kuma Mimi fuska ta rufe ta kalli Hajiya tana yar dariya Hajiya ta kalli Meri tana yar dariya ta ce"To ke fa Meri kin samu shagwaɓɓiyar Suruka Allah ya tayaki riko." Abun da ya fallasa abin da ke zuciyar Mimi shi ne sai ta tashi da gudu ta shige ɗakin Hajiya wai ta na jin kunya..Hajiya kuma tun tana ɗaukan abun wasa har dai ta fahimci jikarta da gaske take yi.
Kai Tsaye ta kalli Aji kafin ta ce"Kai Mansoor to jikata da gaske take yi, maza ka fara kawo kuɗin toshi in kana son na shige maka gaba lokacin auran"
Mu'azzam da Inna Meri na ta dariya shi kuma gogan sai mirmishi yake yi abun mamaki. Ba su jima ba suka yi ma Hajiya sallama suka tafi, Mimi kuma ta ki fitowa alamun dai ta na jin kunya Hajiya na dariya tace "Meri ina jin dai Binta kunyar surukanta ya hana ta fitowa."
Inna Meri tace"Bari naje na lallasota."
Ƙarshe Inna Meri aka bari da lallaso Mimi sannan ta fito, Shike nan Hajiya ta samu tsokanar Mimi da Binta surukar Meri, Meri na faɗin bakomai itama ai tayi dacen Suruka.


Wani abu ne da ake kira magana daga ƙarami sai ya girmama a zuciyar Mimi da gaske tana son Aji shima acikin zuciyarsa Mimi ce aciki ba tare da tunanin me gobe za ta haifar ba suka kamu da tsananin kaunar juna da ƙananun shekarun su, Saboda Aji Mimi ta buga tsalle lokacin da Abi ya zo da kansa ya dauketa domin ta koma Abuja ta shiga matakin Sakandiri ta saka kuka da rigiman wajen Hajiya za ta zauna, ba za ta iya tafiya ta bar Ajinta a nan ba.
Hajiya kuma ganin yadda Mimi ke kuka ta ce ba inda za ta je ya barta anan Hamza ya saka ta a makarantan da ya'yansa ke zuwa.
Bai so hakan ba amman Hajiya ta ce in har ya matsa sai ya tafi da Mimi za ta ce ba ta bashi har Abada kalaman Hajiya su saka sanya a ka bar mata Mimi a hannunta Alhaji Hamza ya saka ta a makaranta da yaransa ke zuwa kuma Mimi da kanta ta yi ma Hajiya maganar tana so a saka ta a islamiya ita kuma Hajiya ta yi ma Inna Meri mgana, Daga karshe dai Mansoor ya kaita makarantarsu islamiyasu ta mallam Ɗahiru aka jarabata aka ga tana da ƙokari sai aka sanyata a ji huɗu ya so a sakata Ajin su Bintu amman ba zai yuyu ba tunda ta girme ta kuma sannan ta fi ta gaba a karatun.


Saboda ita Mansoor ya koma makaranta lokacin suna rubuta jarabawar fita daga makaranta Sakandiri ne shi da su Nasir.
In bai je makarantar islamiya ba Mu'azzam za'a ja ma kunnen ya Kula da Mimi in aka tashi sai da ya tabbatar da ya rakata har gida. Tun suna Nasir ba su gane ba har suka fahimci wani abu saboda yadda Aji ke kafa kafa da yarinyar masu kuɗin nan suka fahimci yana sonta
Nasir ne ya fara magana, ganin abun na Aji na yin yawa kishin yarinyar yake yi ko miye abun kallo a jikinta Oho. Yana tafe tare tare da ita baya so ta yi ma kowa mgana sai shi in ko ta na yi musu mgana yanzu zai ɓata rai amman in ita da shi ne sai ka ga yana wani annurin farinciki.
Kuma in aka ce wacece ita? Iyaka yace jikar Hajiyar e da Inna ke zuwa mata aiki ce.
Amman Sai ayyukansa suka tona shi ita kanta Mimin ba ta iya ɓoye kaunar da take yi masa ko a gaban waye sai ta kira shi" Aji Nah." Kuma in yamman ta yi gidan su Mansoor ke wucewa da ita sai an gama sallar mangariba zai rakata gida suna tafe suna hira.
Hajiya kuma hankalinta kwance yadda ta aminta da Meri haka ta aminta da ƴaƴanta
Wata rana ma Mimi har kwana ta ke yi a wajen Inna Meri Hajiya ta ce in duhu ya shiga a daina wahalar da su Mu'azzam ta rika kwanciyar ta nan, ita kanta ta fi son haka acikin gida Magajiya ta rika habaicin kwaɗayi da wahala tunda suna gani kamar kwaɗayi ne yasa Inna Merin da ƴaƴanta ke tafe tarairayan Mimin.


Wata rana sun dawo daga islamiya Mimi na tare da su Binta daman Mansoor ya ba ma su Yaya Amina Amanarta da an tashi za su je su nemeta saboda su kamo hanya tare, ta na hango shi daga nesa tare da su Nasir ta ƙwalamasa kira sannan kuma ta nufosa yana ganin haka ya yi saurin barin su Nasir ya nufeta yana faɗin"Ba na ce ki daina biyo ni cikin maza ba, ba ki ga ke mace ba ce?
Sai ta tura baki kafin ta ce"To ni ai ba ina son ganinka ba ne"
Sai ya ƙarya wuya kafin ya ce" To tunda kin ganni koma wajen su Yaya Amina kin ji ko?.
Kafa kafa ya rakata har wajensu Amina suna gaba su kuma suna bin su a baya Nasir da Makama suna ta haɗa ido suna gulma.
Sai da suka zo layinsu, suna tafiya Mimi ta tsaya ta na waigen Mansoor Nasir kuma ya na tafiya bai ganta ba ya taka mata igiyan takalmi shike nan sai ta faɗi ƙasa goshinta har ya kuje.
Ranar Nasir ya ga masifa haka Aji ya dinga masa masifan yaa gani ya tureta ta faɗi
ran Nasir ya ɓaci cikin ƙufulwa ya ce"Eh ina gani, tunda da gangan ne zan tureta Aji."
Mansoor ya ce"Wa ya sani ko da gangan ɗin ne? Nasir ya ce"To wai kana ta wani jijiyan wuya Aji anya anya? Ko dai son yarinyar nan kake yi ne?
Da ƙarfi ya ce"Eh INA SONTA ko za ka hana ni ne?
Sai Ahmad da su makama su ka kama baki Mu'azzam daman ya jima da ranfo yayan nasa.


Haka dai aka rabu da faɗa saboda haushi daga nan ya tasa Mimi zuwa anguwansu ko gidan ma bai bari ta shiga ba.
Mu'azzam kuma ya je ya na gayama Inna Meri labarin abin da ya faru.
Ta yi dariya kafin ta ce"Shirmen ne kawai irin na shi, ita da ba yar nan garin ba ko yau mahaifinta ya so zai ɗauketa ta koma wajensa."
Mu'azzam ya ce"Inna ba fa wasa ba ne Yaya Mansoor na son Anty Mami."
Inna Meri baa ta ɗauki abun da wani gaske ba tace"To kawai."
Da irin haka da suke ɗauka ne lamarin ya yi nisa ba su sani ba. Saboda Mansoor na gida tunda suka gama sakandiri bai cigaba da makaranta shi a dole sai ya samu makarantar Sojoji, kuma a lokacin makarantar na wahalan samu shi kuma ya dage in ba nan ba bazai yi wata makaranta ba. A zuwa lokacin komai da ya danganci Mimi Aji ke fara sanin kafin kowa har Jinin al'ada da ta fara shi ta samu tana kuka ta gayamasa yana kunshe dariya ya ce ta je ta samu Hajiya ta sanar da iya, sai da ta je ta gayama Hajiya ta zaunar da ita ta yi mata bayani sai ta dawo tana jin kunya.
Lokacin da ta gayama Hajiya Aji ta fara gayamawa.
Hajiya ta ranƙwasheta akai lokaci ɗaya tana faɗin"Me ya sa kika faɗa masa? Ni kika tsallake ni Binta?.
Ta na tura baki ta ce "Hajiya shi fa zan aura kuma ni to."
Sai ta kasa ƙarisawa sai ta bar Hajiya da rike baki daga nan Hajiya tasan Binta da gaske ta ke yi ta na son yaron nan tunda har ta iya furtawa. Kuma har zuwan da Mommy ta yi ganinta sai da Mimi ta ba ta labarin Aji.


Mommy ta gaji da jin Labarin Aji ta samu Hajiya tana faɗin "Hajiya wai waye wani Aji ne? Tunda na zo Mimi ke yi min hiran sa,?
Hajiya ta ce"Mijin da za ta aura ne.,"
Mommy ta zaro ido ta na kallon Hajiya Mimi kuma sai ta rufe fuska ta tashi ta bar wajen tana dariya. Nan Hajiya ta zaunar da Mommy ta ba ta labarin tun daga farko sannan ta ƙarishe da faɗin"To kin ji ba sai ki shirya Binta ta samu miji a gombe."
Mommy ba ta wani ɗauka da gaske ba ne har da Inna Meri ta zo gaisheta ta ce a ce ma Mansoor ya zo ya gaishe da surukarsa.
Ta faɗa cikin Raha saboda ta na kaunar ƴarta kuma abin da yarta take so shi take so. Mansoor ya zo ya gaida Mommy tare su ka zo da Mu'azzam da Nasir makama shi ya fara zuwa jami'a ba ya samun zama sosai. Ahmad kuma babanshi ya kai shi shagon ɗinki. Mommy sai ta ga shi kanshi Mansoor ɗin ai yaro ne sai a ranta ta ce yarinta ne kawai irin na Binta da kuma jaaɗuwar Jini.


Shi kuma Aji in su Nasir suka ce auran Mimi zai yi? Sai yace eh Nasir ya sha faɗa masa wata mgana bai taɓa tsayawa ya duba mganar ya ga ko za ta yi masa amfani tun a wancan lokacin ba, sai daga baya yake ganin gaskiyan Nasir a wancan Lokaci.
Nasir kan cewa Mansoor" Aji gaskiya ka saka kanka a wahala, Yarinyar nan ta fi ƙarfin ka, ba auranta iyayenta za su baka ba, ba ma haka ba kai a yanzu kamata ya yi ka zauna ka yi tunanin makomar rayuwarka ba ka saka kanka a maganar aure da ƙananun shekarunka ba, kai baka tara ba. ba kuma ka ba wani ajiya ba.".
A lokacin da ya faɗi haka sai da Mu'azzam ya shiga tsakaninsu shi Aji ya na ganin Nasir ya raina shi ina ruwansa da rayuwarsa.
Shi kuma Nasir yana ganin Aji ya shiga inda ƙaren sa bai kai ba ma'ana ya janyo abin da yafi ƙarfinsa.


Saboda Aji ya sa Mimi ba ta son zuwa Abuja in su ka samu hutu sai Abi ya kira waya ya ce Daddy ya sakata a jirgi zuwa Abuja haka zata je ta yi hutuntaduk ba daɗi Mommy dai ke shan labaran Aji har ta gaji, ta taɓa ce mata" Mommy Aji ma fa Soja ya ke son zama ki yi ma Abi mgana ya yi masa hanya, so yake yi in aka yi auran mu sai ya tafi ya barni wajen Inna Meri."
Daga nan mommy ta fahimci yaron ke kara saka ma Mimi wani tunanin, sai dai alokacin ta yi karaf ta ce mata'" kul na kara jin mgamar auran nan a bakin ki Mimi ga sauran ƴan'uwan ki nan karatu suke yi, ba wacce take mganar aure sai ke in kika bari Abin ku ya ji maganar nan sai ya harbe ki."
Mimi na tsoron bindiga sai ta fara rawan jiki tana cewa" Mommy shi fa yake cewa zai aureni nima ai ina son shi."
Mommy ta tsawar ta mata da cewa" To ba na son jin haka, in ya ce miki zai aure ki, ki gayamasa ke ba yanzu za ki yi aure ba sai kin girma kin gama karatu."
Abin da Mommy ba ta sani ba dukkan abin da ta faɗa Mimi na dawowa Gombe ta kwashe komai ta faɗa ma Hajiya.
Har ta na mata kuka da cewa"Ni hajiya Aji zan aura kuma ya ce in muka yi aure zan yi karatuna." Jikin Hajiya sai ya yi sanyi wato kenan yan zantukan da suke gudana a tsakaninsu kenan? Lalle yara nan da gaske su ke yi.


Dakyar ta lallashi Mimi ta yi shuru amman Aji na zuwa ta kwashe komai ta sanar masa.
Shi kuma sai ya kalleta yana faɗin"Ki gayama Mommy ba zan hana ki karatun ki ba sannan ni nafi son na aure ki kafin ki kara girma, in kika kara girma zaki iya fin Ƙarfina" Kuma sannan ya fahimci Mimi ba ta son ya ce zai zama soja.
Da ya fara magana sai ta ɓata rai, ranar dai ya tsareta sai da ta gayamasa dalilinta.
Abun ya bashi tsoro tana hawaye ta ce" Abi sai ya yi ta ma mommy tsawa wata rana ma har ya na saka ta kuka, ni ba na son ina ganin bindiga irin ta Abi in muka yi laifi sai ya ce zai harbi kan mutum."
Daga nan ya fahimci mahaifin Mimi ba Dattijon arziki ba ne amman duk a lokacin bai karaya ba, yana nan akan bakansa na zama soja kuma da gaske yake yi yana son Mimi kuma auranta zai yi in sha Allahu.






*Janafty*
*IDAN AN CIZA..!*


*Wattpad:Jamilaumar315*
*Arewabooks:Jamilaumarjanafty*
*Mallakar:Janafty*


*SADAUKARWA GA HAJIYA AISHA AHMAD IYA*


Ina kuke mata yan kwalisa.. *KHADYS EMPIRE* Ta Kawo muku kayan mata masu kyau da saukin kudi💃🏻 kamar haka.


*Zumar Matsi Guarantee 3500*
*Maganin sanyi komai nacinsa 4k*
*Zumar kacha kacha 2500*
*Zumar kiba 4k*
*Setinn kayan mata na yar gata 8500 Me abubuwa har kala Takwas a ciki*
*Dahuwar kaza

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login