Showing 33001 words to 36000 words out of 103785 words

Chapter 12 - IDAN AN CIZA..! Part 1 Complete by Janafty.txt

Janafty   

20 Dec 2024

4787

ba ta yi mgana ba sai da ta nisa kafin ta ce"Ba wanda yasan abin da ke zuciyarsa, ba na tunanin ita ya ke jira saboda ai shi ya fara yanke alaqa da ita ko bayan dawowarmu Mu'azzam kai ka faɗamin tana ta kiransa a waya ya ƙi ɗauka sannan shi ya yanke sauran alaqan da ta rage tsakanina da kakar yarinyar nan. Tun daga lokacin ban kara taka kafata gidan ba itama Hajiya ba ta kara nema na ba, abu ne ya riga ya faru sai a manta baya a fuskanci gaba kullum ya zo nan babanku zai zaunar da shi yana masa nasihan hakuri da rayuwa sai ya nuna kamar ya ji ammh sam Baban Inna ba'a gane in da ya dosa shi dai ƙwallon nan da ya saka gaba ita ya rike bansan kuma me yake tunanin ya mai da rayuwarsa ba."


Inna Meri ta ƙarishe faɗa cikin bayyana damuwarta Yaya Amina ta dafa kafaɗarta lokaci ɗaya tana faɗin"Bakomai Inna, zai wuce in sha Allahu Baban inna zai yi aure har ki ga ƴaƴansa" Bintu ta yi karaf ta ce"To ai abun haushin ma ko budurwa ba shi da ita." Mu'azzam ya yi jim kafin ya ce"Ai ina jin tun bayan rabuwarsa da Fatima Baban Inna bai kara son wata mace ba, ban jin ma mata yanzu suna burgeshi ta sauya shi fa fiye da tunanin ku, yanzu haka abokan mu sun gaji da min korafi sun hakura ana gari ɗaaya sai su yi wattani ba su gan shi ba ya koma rayuwar kaɗaici abin da na fahimta har gobe abun na ranshi ya kasa mantawa ne."
Yaya Halima ta ce"Nima abin da nake tunani kenan, cire abun a ranshi zai taimaka masa wajen fuskantar wata rayuwar a gaba." Mu'azzam ya ce"Yau ai wajen sa zan kwana zamu tattauna Allah yasa ya bani damar haka."
Inna Meri ta amsa da Amin a samam labbanta har aka kira mangariba suna tattauna abubuwan da suka faru a shekarun baya ne.


Kiran sallar Mangariba ya tada su Mu'azzam ya yi alwala zuwa masallaci su kuma matan suka yi na su agidan.
Yaya Amina ta fara tafiya tunda ta fi su nisa, Yaya Halima kuma daga baya Bintu dai har sai bayan Sallar isha'i da Baba Ɗanjuma suka dawo tare da Mu'azzam da Auwalu.
Har ɗakinsa ta bi shi suka gaisa Magajiya ke da miji sai kuma abin da Baba Danjuma ya gani ruwa ma Inna Meri ce ta kawo masa mai sanyi tunda tana da ƙaramin firiza a ɗakinta na Yaya Halima ne da mijinta ya siya mata Babba sai ta kawo mata wannan.
Sai da ya sha ruwan ya ji ka maƙoshi acikin ransa ya yi saka ma matar kirki irin Meri albarka yana tuna karamcinta a garesa tun na tsawon shekarun da suke tare.
ƴan Biyun Bintu suka hau jikinsa suna wasa yana dariya yake faɗin"Ku yi min a hankali kar ku ƙarisa ni domin na ga kuna ji da karfi." aka saka dariya gabaɗaya, Auwalu yace"In na kalle su sai na tuna yarinyar nan Bintu ai itama ta yi rashin jin mgana, ba domin Mansoor na tsawarta mata ba da sai Allah."
Bintu ta tura baki kafin ta ce"Haba Yaya Auwalu yaushe na kai yaran nan rashin ji."
Mu'azzam ya ce"Kin fa yi Bintu ai har gobe baki daina ba sai dai in yan abun naki ba su motsa miki ba."


Tura baki ta yi tana faɗin"Baba ka gansu ko? Ka yi mu su mgana."
Baba Damjuma yace"Ku bari mana Fatima Bintu sunanta mai daraja ne babu ruwanta da rashin arziki."
Nan fa suka yi ta wasa da barkwanci har Bashir ya zo tafiya da Bintu gida Inna Meri tun ɗazu ta yi mata mgana ta tafi gida ta ce ita fa a kusa ta ke daga zuwa gida Inna ta fara cewa ta zo ta tafi, Ahalin tun safe ta zo ta riga kowa ma zuwa shi ne take cewa ba ta daɗe da zuwa ba Inna na koranta gida tunda ta ji haka sai ta kyaleta ta sanya mata ido da kila Baban Inna ya zo ne shi ne dodonta yana cewa me take yi har dare ba ta tafi gida ba? Jikinta na rawa zata haɗa Ƴaƴanta ta wuce tana tura baki iyaka dai ta kwana biyu ba ta zo ba in Inna Meri ta aika walida a duba ta sai ta ce tana nan lafiya ai Baban Inna ne ya koreta kuma a gaban inna ba ta yi mgana ba. Sha'anin Bintu ai sai ita ɓauɗɗiyar mace ce irin Mansoor wasu Lokacin suna da kamceceniya ta bangaren hallaya. Ko domin suna matsayin uwa ɗaya ne?


Mu'azzam sai wajen tara da rabi ya bar gidan nan zuwa Tunfere gidan Mansoor daman ya tura masa sakon in bazai zo ba shi zai je Camp ya kwana gobe suna da morning trainig shi ya sa ya yi ma su Inna sallama da Baba ya wuce tare suka fito da Auwalu ya rage masa hanya ya sauke shi a gidan shi sannan ya wuce.
Lokacin da ya isa wayar Mansoor ya kira ya ce masa ga shi a waje, sai da ya ɗan ɓata lokaci sannan ya fito ya zo ya buɗe masa get ya shiga da motar Ciki ya yi parking ɗin ta kusa da ta mai gidan.
Yana tsaye a bakin falonsa daga shi sai gajerun wando, ba nepa akwai kuma zafi a garin shi ya sa ya zauna haka, bai koma ciki ba har sai da Mu'azzan ya buɗe bayan motarsa ya ɗauko karamar jakarsa ya shiga falon sannan ya maida kofar ya rufe ya bi bayan sa.


*******


Dukkansu sun sake wanka, Mansoor daman baya shiri da zafi sai ya yi wanka sama da sau huɗu a dare ɗaya.
A ƙaramar katifan Mansoor suka kwanta dukkansu, shi Mansoor filo bai dame shi ba sai ya ba ma Mu'azzam ya dora kanshi a saman matashin, daman ya saba kwana in dai ya shigo garin tuni ɗakinsu na samartaka na gida su ka bar ma Saddiqu yanzu shima yana ƙokarin siyan fili ne ya fara ginin muhallin da za su rika sauka shi da Hibba in sun zo garin.


Suna kwance Mu'azzam na ta Juye juye Mansoor ya ce"Kana jin zafi ne? duba bayanka akwai mafita sai ka yi amfani da shi."
Mu'azzam ya ce"Gaskiya ya kamata ka saka solar tunda wutar nageria ta zama sai Allah ya kyauta." Kamar bazai yi magana ba sai can ya ce"Zan sa ka in sha Allahu"
Shuru ya kara biyo baya bayan Mu'azzam ya amsa masa da Allah ya sa.
Mansoor ya katse shurun da cewa" Ina Junoir? Mu'azzam ya ce" Suna Tudun wada can za su kwana sai jibi in zamu koma."
Kai Tsaye yace"Gobe da la'asar zan zo gida ka kawo min shi na gan shi."
Sai Mu'azzam ya amsa mi shi da toh kawai wayar Mansor din dake gefensa ya laluɓa ya ɗauka yasan password ɗin watan haihuwan Mu'azzam ɗin ne mabuɗin buɗe wayar Mansoor.


Yana buɗewa a fuskar wayar hoton Junior ne ya fara masa maraba wanda aka yi masa ne na cika 2yrs shi ya tura masa ya yi kyau yaron yana ta bangala dariya.
Mu'azzam ya juya ya kalli ɗan uwan da jini bai haɗa su ba amman ya zame masa wani irin ɗan uwan da babu kamarsa.
Cikin yar driya ya ce"Sai aka cire hotona aka sanya na Junoir har an gama ya yi na kenan Baban Inna?
Ya juya masa baya shi ya sa ba zai fahimci yanayin fuskarsa ba.
Kamar baya son mgana ya ce"E, kai ka girma yanzu."
Mu'azzam ya ce"Ni fa ban yarda ba, dole gobe Inna ta yi alƙalanci."
Har sai da yaji karan sautin dariyansa Lokaci ɗaaya ya juyo ya yi matashi da duka hannayensa idanuwansa na kallon rufin POP ɗin dakin cikin shakewar muryar da gajiya ta saukar masa ya ce" Hausawa suka ce abun cikin ƙwan ai yafi ƙwan daɗi Mu'azzam"


Mu'azzam ya yi mirmishi bai yi mgana ba ma'adanan hotuna ya shiga yana ta kallo gabaɗaya hotunan shi ne na kwallo sai na yan Club dinsu sai kuma na Mu'azzam da suka cika wayar da Junoir sai hoton Inna Meri da Baba Danjuma da kuma nasu gabadayansu shekara biyu kenan da wata salla shi Mu'azzam ya matsa aka yi saboda tarihi kuma shi ya tura ma Mansoor din hotunan. Ba magajiya domin ta ce ba za ta yi ba, kowa dariya ya ke yi a hoton ban da Mansoor da Mu'azzam ya dafa kafaɗansa ya sunkunya da kansa ta wajen fuskarsa tunda Mansoor din ya fi sa tsawo.
Ya daɗe ya na kallon hotunan yana Mirmishi kafin ya wuce kaf ya bincike hotunan wayar har ya kai kan wani tsohon hoto. Su biyar ne acikin hoton kuma zai kai kimanin shekaru goma sha ɗaaya da ɗaukan hoton.
Mu'azzam bai manta wannan hoton domin hoto ne ma na kati aka yi snaping ɗin sa a waya ina zai manta Shagon Aci kwalba mai hoton yan gayu a anguwansu ta Arawa ya ke. Shi ne a tsakiya sai Ahmad a gefensa na dama hegensa na hagu sannan Nasir.
Makama da Mansoor suna da Tsawo sai suka tsaya agefe da gefe.


Da ka gansu kasan an baya an sha gayu da ji da kai, Mu'azzam ya fashe da dariya shi kaɗai Mansoor ya kallesa kafin ya ce"Daman ka na da wannan hoton?
Ya faɗa ya na nuna masa hoton kansa ya gyaɗa kafin ya ce"Kai ka taɓa turamin shi."
Mu'azzam ya ce"Bari ko na tura ai na manta na tura maka ina ta neman sa ko wajen su Nasir ban samu ba suma ba su da shi, ina tunanin har na hoton duk sun ɓace mana."
Mansoor ya ce"Ni ina da su acikin tsoffin takarduna na makaranta"
Mu'azzan ya ce zai kai a wanke masa na Tarihi nan da nan ya ɗauko wayarsa ya tura lokaci ɗaya ya na faɗin" kalli wuyan makama kamar lagwani kyan shi a tura ma yarinyar da zai aura ta gan shi a haka."
Mansoor na jin sa bai yi mgana ba sai shi Mu'azzam ɗin ya cigaba da faɗin"Bayan sallah da Sati huɗu ne bikin Makama, in na zo sallah na koma sai bikin zan kara dawowa in sha Allahu."
A shake Mansoor ya ce" Allah ya kai mu."
Shi kuma Mu'azzam ya cigaba da bashi labarin shirye shiyen biki ya na faɗin su abokai sun ce za su shirya dinner
Mansoor ya ce"Makama ya bar Ustazan cin ne da zai yi bidi'a bikin sa.?
Mu'azzam ya ce"Gidan su yarinyar ke son haka ina ganin."
Gyaɗa kai kawai ya yi ba tare da ya yi mgana ba, Mu'azzam ke gaya masa za su yanke ko nawa ya kamata kowa ya ba da.


Kai Tsaye Mansoor ya ce"Kar ku fara sani cikin yarintar ku, in na tashi zan turama Makama guddumuwata ba ruwana da wani sha'anin sakarcin banza shima dai kamar wani yaro."
Mu'azzam ya yi dariya kafin ya ce"To yaro ne mana, tunda yanzu zai yi aure kai ma ka bari ka ga yadda zamu raya bidi'a a naka bikin."
Wani kallo ya watsa ma Mu:azzam kafin ya kira sunan shi "Mu'azzam..!
Ya amsa da "Na'am'" yana dariya.
Sai kawai ya juya masa baya bai kara magana ba.
Ya bar Mu'azzam na mirmishi ya na tuna shekarun baya akwai wani abu da ya faru da ya kasa mantawa yasa sai da ya kara saka dariya. Da karfi Mansoor yace"Mu'azzam za ka fita falo ka kwana, junior ne kai da za ka rika motsin kwanciya?


Mu'azzam ya tashi zaune yana faɗin"Wani abu na tuna ka tuna muna a yara in su Jummai su ka ganmu tare sai su ƙwace hannuna daga hannunka suna cewa kai mu ne fa yayyenka wannan ba babanmu ya haife shi ba.
Kai kuma sai ka ƙwace hannuna daga wajensu kana faɗin"Eh din ba Babanku ya haife ni ba, amman ai ɗakin Innata yake kwana take kuma bashi abinci saboda haka ya zama ƙanina ka tuna lokacin?
Mansoor ya Juyo ya na mirmishi shima lokacin yana dawo masa girgiza kai kawai ya yi, Allah sarki Kuruci dangin hauka.


Mu'azzam ya koma ya kwanta yana cigaba da duba wayar Mansoor ya na yar dariya.
Sai dai ya bata fuska lokaci ɗaaya da ya gama bincike wayar bai ga hotonsa da uniform ba, kuma tare ya tura masa da hoton Junior cikin kufuluwa ya ce" Baban Inna ina hotuna na a office da na tura maka? Kai tsaye ya ce" Na share su."
Baki buɗe ya mike zaune yana faɗin "Ka share su kuma? To saboda mene?
Kai tsayen ya kara cewa"Kai ma kasan dalili."


Mu'azzam ya yi tagumi kafin ya ce"A masu kakin ma har da ƙaninka ka tsana?
Mansoor ya yi masa banza kamar bai ji sa ba sai da Mu'azzan ya kara faɗin" kuma ai tun a wancan Lokacin kai kace na je na zama duk abin da nake son zama."
Mansoor ya yi shuru kamar ba zai yi mgana ba sai can ya mukusta ya gyara kwanciyarsa Lokaci ɗaya yana faɗin" A lokacin saboda ka matsa ne, amman ni har abada bazan so duk wani aiki mai sanya kaki ba, na tsane su har acikin raina saboda ƙakin su na basu damar cin zarafin mutane yadda suka ga dama." Mansoor ya faɗa ya na jin wannan abun da ya tokare masa kirji ya taso masa sama duk lokacin da ya tuna sai ya ji kamar ya fama damuwar da ya danne shekara da shekaru ne.


Mu'azzam kuma ajiyar zuciya ya sauke kafin ya ce"A ba duka aka taru aka zama ɗaya ba, a ko'ina akwai na kirki akwai na banza" A tsawace ya ce"Kana gaya amin haka ko Mu'azzam? Ni ban ga na kirkin ba na banzan na gani, kuma da shi zan yi misali."
Kamar Mu'azzam zai yi kuka ya ce"Ni yanzu na banza ne Yaya Mansoor?
Sai ya kasa bashi amsa sai ma koƙarin mikewa zaune da ya yi ya sauka daga kan katifar ya mike da kafafunsa.
Shi kuma Mu'azzam ya b shi da kallo kafin ya ce"Saboda ita ne ko?
Saboda ita ce ka kasa mantawa da abin da ya faru da daɗewa Baban Inna."
Har ya kai bakin ƙofar tiolet sai ya Juyo ya na kallonsa cikin kaushin murya Ya ce.


"Saboda ita wa???


Kai Tsaye Mu'azzam ya ce" Saboda FATIMA! Itace silar da ya saka ka tsani masu ƙaki, itace silar rugujewar tuninaninka na zamo wa sojan kasar ka."
Ƙurama Mu'azzam ido ya yi yana jin wani abu a kirjinsa na wani dif dif, me ya sa zai ce saboda ita ne? Ba saboda ita ba ne.
Cikin ɗaga sauti ya ce"Ba Saboda ita ba ne Mu'azzam."
Yana direwa ya taso mai da cewa"To in ba saboda ita ba ne, saboda waye da zai saka har ni ba ka iya kallona da ƙakin yan sanda a jikina?
A tsawace ya ce"Saboda mahaifinta ne Saboda shi ne wannan MAJOR KABIR ɗin ne. Saboda shine komai ya ruguje."
Ya faɗa lokaci ɗaya yana tura kofar tiolet ɗin da ke ɗakin ya shiga da sauri ya kuma maida kofar ya rufe ta da karfi har sai ta yi ƙara bam!!.


*BOOK 1 FREE NE, 2,3 PAID NE REGULAR N500, VIP 1K NE, KU BIYA KUƊIN KARATUN KU TA WANNAN ASUSUN BANKIN 0552179550 JAMILA UMAR GT BANK, SANNAN SAI KU TURA SHAIDAR BIYA TA WAƊANNAN LAMBOBIN.*
*09069067488*
*80032773332*
*Ƴan kasuwa masu bukatar a tallata musu hajojinsu cikin farashi mai sauƙi, ku yi min magana ta wannan lambar*
**09069067488*




*Janafty*
*IDAN AN CIZA..!*


*Wattpad:Jamilaumar315*
*Arewabooks:Jamilaumarjanafty*
*Mallakar:Janafty*


*SADAUKARWA GA HAJIYA AISHA AHMAD IYA*


MMN MUJAHID KAYAN MATA AND SUPPLEMENT


SHIN KINA DA LABARIN MACCE MAI GYARA DABAN TAKE GA ZUCIYA MIJIN TA
MUNA DA KAYAN MATA MASU ZAFI NA BUGAWA GA JARIDA


HAJIYA TA KUDI DA KUDI AKE NEMAN SU


INA MASU FAMA DA MATSALA RAMA BA GABA BA BAYA KINA ZAUNE ANA KWATANCI DAKE KINA CI BAKI KOSHI MUNA DA MAGUNGUNA DA ZUMA 3 IN 1 KIBA BRST HIPS TA CIKO MIKI KU INA KIYI FRESH MUNA DA KWAYOYI MUNA DA GARI DUK MASU CIKO JIKI NE KIYI DUM.


INA MASU FAMA DA MATSALA BRST KU TSUHU YAFI SON YAGA NONO A TSAYE DUK MAI MAGANIN DA TACCE MIKI ZATA BAKI MAGANIN NONO KAI TSAYE YAYI MIKI KARYA CE MAGANIN BRST SAI KIN SHA ADADIN WANDA ZAI MIKI SBD DUK CIKIN GYARAN JIKI NA BRST YAFI WAHALA YI


INA MASU FAMA DA MATSALA SANYI MUNA DA MAGANIN SANYI ORIGINAL


INA MASU ZAMAN BANZA BABU SANA'A KINA KONE DATA KI GA BANZA WURIN TSEGUMIN KALLON STATUS DIN WASU GA DAMA TAZU MUNA HAR GIDA GA WAYAR HANNUN KI KI MALLAKE MOTA MILLION 8 HAR FIYE GA ALBASHI GA RIBA GA KYAUTA KAYAYA KI
08066726866


Follow this link to join my WhatsApp group: https://chat.whatsapp.com/JMpd8nXr7TIDD3ILDXh64z


*Page 7*


Kofar ya ƙurama ido wasu shuɗaɗɗun al'amura da suka wuce a baya suna gilma masa, in hasashen sa ya zama gaskiya Mansoor bai manta da Mimi ba har kwanan gobe tana cikin ransa kuma saboda ita ne har gobe ya kasa iya kula kowacce ƴa mace.
Shi da kuma ya yi rantsuwan ko zai mutu bai yi aure ba, ba zai taɓa auranta ba kuma ga shi har gobe yana sonta shi kam ya rasa ta in da zai saka tunanin wannan al'amarin.


Komawa ya yi ya kwanta yana wasu tunane tunane, shima tun bayan abin da ya faru ba su kara haɗuwa ba shi daman ya bar Gombe ya koma Kano. Nasir dai kwanaki can da jimawa ya ce sun taɓa haɗuwa har ta karɓi lambarsa to ba ta taɓa kiransa ba shima kuma daman itace ta karɓi Layin nashi shi bai karɓi nata ba sai dai suna ganinta a akwatin talabijin ɗin, tunda tana aiki a sananniyar gidan talabijin sannan ta yi suna kowa ya santa. Shima dai yana ganinta lokaci bayan Lokaci in yazo garin a tibin Inna in Walida ta kunna, Mansoor ne ba shi da wani masaniya a kanshi sanin shi fa ba ka gane gabansa ballantana bayansa to kila har gwara shi ya kan tsaya su yi magana mai tsawo, wasu tuni ya yanke wannan alaqar a tsakanin su.


Bai taɓa tunanin haka soyayya ke da zafi ba sai akan Mansoor a lokacin ma daga shi har Mimi suna da karancin shekaru shi ya ɗauka a shekarun da suka ɗauka ba sa tare soyayyarsu za ta disashe ashe ba haka ba ne, tana nan ta kara

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login