Showing 75001 words to 78000 words out of 103785 words
ya ke yi zuciyarsa na wani irin suka, yana ji kamar ya zama asarrare mara amfani, duba yadda Mahaifiyarsa da wanda ya zame masa uba da ƙaninsa suke kuka saboda shi, kalli yadda suke duke gaban wani hallita na Ubangiji saboda shi , yau saboda shi an kira sunan mahaifinsa an zage shi da gorin ya mutu a kauye bai taba shiga birni ba, shi ba yana kukan dukan da ya ci ba ne da dai ya ba ma wannan mugun hakuri gwara ya kashe shi, Shi ko da wani suna zai iya kiran kalmar Soyayya? Tun jiya ya ke son yaji ya tsani Mimi acikin ransa amman ya kasa, ji yake yi kamar ya mutu baƙinciki da yake cikin zuciyarsa tunda ya zo duniya bai taɓa tsintar kansa aciki ba. Ba shi da niyar saduda ya so ne su bar shi ya kashe shin in dan har zai iya, Sai dai Kukan Inna Meri da na Baba Ɗanjuma tare da Mu'azzam suna masa magiyan ya bashi hakuri saboda ya tsira Inna Meri ta san halin abin da ta haifa yasa a fusace ta ce"Ko ka bashi Hakuri ko na ce sai ka biyani Nonona da ka sha"
Baba Ɗanjuma ya kira sunanta da karfi cikin tashin hankali.
"Meramu.."
Hajiya ma sai da ta kira sunanta ita kuma ta yi hakane saboda ya ba da hakurin ta san halin Baban Inna da kafiya sai yace sai dai a kashe shi. Kuma hakan da ta yi sai a ka samu masalaha domin Mu'azzam ya rike sa ya durkusa saman gwiwiyonsa tare da Iyayensa kansa na kasa ya na jin taruwan hawaye acikin idanuwansa, ko dukan da aka yi masa bai saka shi kuka irin wannan tozarcin ba muryansa ba ta fita ma sosai Saboda wahala ya furta" Ka yi hakuri..!"
Yana gama faɗin haka sai ya ji wasu hawaye masu zafi sun sauko masa.
Nan Major Kabir ya Koma ya zauna yana Faɗin"Good. za ku iya tafiya da shi amman ya kiyaye sharuɗɗana.
Inna Meri da Baba Ɗanjuma suna rawan jiki masa godiya su ka miƙe jiki na rawa Hajiya nauyi da kunya su ka hanata mgana Alhaji Hamza ne ya ce su tsaya mana a nema musu Jirgin komawa da sauri Baba Ɗanjuma ya ce"Mun gode da karamci ranka ya daɗe ya isa haka."
Hajiya ta yi saurin kallon Major kafin ta ce"Kabiru ka dubi halin da Binta ke ciki Hausawa su ka ce idan An ciza a hura watarana kada ka zo kana nadamar abunda ka aikata ma wannan yaron"
"Ni? Kamar ni Major Kabir My Daughter ta auri talaka Agolan da ubansu har ya mutu a can wani kauyen kurmus, uban rikonsa wanzami uwarsa yar aiki? Over my dead body Mimi za ta yi wannan auran ƙaskanci ba ta isa ba, ko za ta mutu bazan aura mata wannan talakan ba, jinin takalawa wanda bashi da wata kyakyan makoma ko anan gaba." Ya karishe faɗa a fusace kamar ba da Hajiya ya ke mgana ba, kawai sai ta girgiza kai kafin ta ce"Shike nan Allah ya hana mu jin kunya watarana."
Ta faɗa ta na kallon yadda Idanuwan Mimi suka kumbura saboda kuka, Mommy ma sharan kwallan take haka ma Khadija kowa kuma yasan ba'a kyauta ba, amman kowa yana tsoron ya yi mgana wanda bai girmama maganar uwar da ta haifesa ba ai ba wanda kuma ya isa ya yi masa mgana ya saurare shi.
Mu'azzam ya riƙo sa tunda ba ya iya tsayuwa gefe kuma Baba Ɗanjuma ya kama shi za su fita daga falon da gudu Mimi ta ƙwace daga jikin Mommy ta ƙarisa gaban Abi cikin kuka Ta ce.
"Abi ka yi hakuri Abi ina son shi don Allah kada ka raba mu da juna"
Cikin tsawa Ya ce" Sai dai ki mutu, amman Wallahi tallahi ba za ki auri wannan talakan yaron nan ba, ba shi da makoma mai kyau, ina tambayan ƙwalin karatun shi Hajiya na gayamin iyakarsa Secondary school. Soja yake son zama ire iren su ma ba su da wani rabo a duniya." Mimi ta katse shi cikin gunjin kuka tana kara faɗin.
"Abi ina son shi.."
"Ke yarinya ce Mimi, karatu nake so ki yi ba yanzu zan yi miki aure ba"
Ya faɗa shima bayan ya katseta cikin kaushin Murya.
"Abi Ina son shiiiii..."
Ta faɗa cikin wani irin karyayyen sauti kamar za ta shiɗe.
"Murja ki ɗauke min Mimi kada raina ya ɓaci na fasa kanta da bindigata"
Ya faɗa ya na kokarin sarrafa fushin sa domin ji yake yi kamar ya tokareta ta faɗi in ta na haɗa shi da wannan ƙasƙantaccen yaro nan mara makoma mai kyau.
Ba zai manta da wannan kukan da ta rika yi lokacin da mahaifiyarta ke rike ta ba, har gobe yana jin Sautin wannan kukan acikin kirjinsa. Ya tuna ta na miƙo hannunta Mahaifiyarta da yayarta khadija suka riƙe ta suka tafi da ita zuwa cikin wani ɗaki.
Yayi ƙokarin danne abin da ke taso masa amman sai ya kasa, kafarsa ya makaleta ya kasa tafiya da ya sa su Mu'azzam su ka tsaya su na kallonsa ba su san abin da zai aikata ba da ba su barshi ya kara yin mgana ba.
Sai juyawa kawai su ga ya yi ya na faman ɗingisa kafa idanuwansa a like ga kaya duk sun yage ba hula ba takalmi kamar wani almajiri cikin muryan da ta galabaita ya fara faɗin.
"In har ni Mansoor na haifu cikin uwata Meri da uba na Ibrahim ƴarka ko ita kaɗai ta rage a duniya nan sai dai ta mutu nima na mutu ban yi ba aure ba,"
Ya faɗa ya na sakin numfashi Inna Meri na kokarin toshe masa baki amman sai da ya ida sa faɗin abunda ke ransa a lokacin.
"Nayi alkwarin toshe kunnuwana daga jin ta da ganinta na yi alkwarin sauya duniyata daga duniyar ta na yi alkwarin sauya mattacen mafarkina a kanta, na kuma gode maka da ka fahimtar dani darasin rayuwar dana daɗe ana ga ya min ban ɗauka ba, na kuma fahimci akwai tazara mai kimanin kilomita tamanin tsakanina da ƴarka, na kuma fahimci matsiyaci kamata ya yi shisshigi wajen tusa kansa in da bai dace da shi ba, yadda ka saka iyayena kuka a kaina kai ma watarana sai ka yi kuka saboda ƴarka."
Yana gama faɗin haka ya juya kamar zai kifa saboda yanayin jikinta Major Kabir ya yi wani kayattacen mirmishi kafin ya ce" Ku ja ma ɗan ku kunne, na ga alaman tsageranci na damunsa sannan ku yi masa iyaka da ƴata domin ruwa ba sa'an kwando ba ne, zan sake shi na yanzu amman ko kallon Mimi ya sake yi sai na ɗaure shi da kakin jikina." Baba Danjuma bakinsa na rawa ya ce"Ba ma zai kara kallonta ba In sha Allahu ka yi hakuri."
Haka su ka fita da Mansoor a rirriƙe da shi saboda halin da ya ke ciki, kuma ba wanda ya bi bayan su. Shima Major ɗin mikewa ya yi a fusace ya shige cikin ɗakinsa har yana banko kofa Hajiya ta bi shi da kallo tana Sassauta fushinta domin kada ya zama masifa ga rayuwar Kabiru. Amnan ita ta so da aka Ciza sai a Hura saboda ba'a san abunda gobe za ta haifar ba.
Ko kwana ba su yi a Abuja ba Hajiya ta ce gida zata koma, Mimi kuma ta zauna wajen mahaifinta ba za ta kara amsar ta riko ba tunda ga abunda ya biyo ba, Mommy ta yi tayi Hajiya ta kwana Hajiya ta rantse ba za ta kwana ba. Hajiya na ba ta hakuri Mommy ma na ba ma Hajiya hakuri ta yi mirmishin takaici kafin ta ce"Bakomai Murja wata rana Kabiru zai yi nadama, sai dai ina fatan Lokacin da zai yi nadamar lokaci bai kure masa ba.
Alhaji Hamza a lokacin ya nema musu jirgi suka juya zuwa Gombe kuma har suka bar gidan Major bai fito daga ɗaki ba, Mimi dai kuka ta yi kamar zata ba ma uku lada domin ta so ta bi Hajiya su koma gombe Hajiya ta girgiza kai kafin ta ve"A'a ki zauna ki yi ma mahaifinki biyayya shi ya haife ki ya fini iko da ke, ina miki fatan Allah ya sanya hakan ya zama alheri a rayuwar ki Binta ki yi Hakuri kin ji ko? Mimi tana ji tana gani Hajiya ta tafi ta barta daga nan ta fahimci ta rasa wani hop, domin Mommy ba ta isa da ja da hukuncin Abi abunda ya faɗa tabbas haka din ne zai kasance.
Tun daga wannan daran Mimi ta ke kukan Rashin Aji a rayuwarta kukan da har tsawon shekaru goma ba ta taɓa dainawa ba.
Kuma wannan zafin da kirjinta ya soma tun daga ranar ne, to shi ya haifar mata da ciwon da har gobe bai warke ba.
******
Labarin abin da ya faru da Mansoor ya za ga gari ba wanda bai sani ba. Wani tarihi ne da shi kanshi ba zai taɓa mantawa da shi a rayuwarsa ba, sannan tarihin dafin soyayyar da ba shi da magani.
A ranar kwanan hanya suka yi zuwa Gombe tunda Mota ce ga Mansoor ba lafiya kafin su isa duk jikinss ya kara tsami, Allah ya sa Baba Ɗanjuma ya riko kuɗi a Hannunsa Inna Meri na cikin tashin hankali ba ta tuna da wannan ba.
Motar da su hayo ma daga tasha Sai da Baba sani ya biya, suna ta faɗa da masifan yaro ya jawo musu bala'i, sai dai suna ganin halittar da Mansoor ya koma sai suka yi shuru domin su kansu sun san yaron ya kai kanshi in da ya kusa mutuwa.
Jinya ce sosai Mansoor ya yi domin ya samu targade da gocewar kashi sama da huɗu a jikinsa ga raunika a saman kansa ga tsamin jiki ga raunin dake cikin zuciya wanda ido ba ya iya gani.
Shi kaɗai yasan irin ƙunar da zuciyarsa take ciki, ciwo dai idanuwana ba sa iya gani sai shi kaɗai da zuciyarsa ke cikin kirjinsa ya san halin da ya ke ciki. Makota haka suka yi ta tururuwan zuwa ganinsa wasu duk saboda gulma ne, wasu kuma domin ganin abunda ya faru mata kuma suna ta zuwa yi ma Inna Meri barka da arziki.
Su Baba Sani ke kara ma lamarin magi da gishiri suna ƙara abunda bai faru, har suna cewa shi kanshi Yaya Ɗanjuma da Merin dakyar suka sha domin yaron ya je ya jawo Yar soja an kusa kashe shi fitinarsa ya sa yau ya kusa janyo abin da zai saka har su a kashe su a banza. Nasir da makama kullum suna gidan wajen Mansoor dake kwance ya na jinya, Ahmad kuma sai da ya dawo garin ya zo ya ga yadda Mansoor ya koma shuru shuru ba ya mgana kamar an sauya shi. Baya cin abinci baya mgana ba ya fara'a ko da yaushe ya na kwance yana fama da kuncin zuciya.
Kullim mganar Inna Meri shi ne" Baban Inna ka mike ga kanka wannan kwanciyar ba zai yi maka kyau ba"
Sai kuma ta saka masa kuka, Baba Ɗanjuma shima ko da yaushe cikin yi masa nasiha yake yi.
Su Nasir ma koda wani lokacin cikin faɗin " Aji ba fa karshen rayuwarka ba ne ya zo, Mimi ba ita kaɗai bace mace a duniya ka mike ka gina rayuwarka zaka samu wacce ta fita a gaba."
Mu'azzam kuma kamar yafi kowa damuwa maganar kenan" Ka manta da abin da ya faru ka tashi ka kula dani kamar yadda ka saba, ba na jin daɗin ganinka a haka"
Haka su Yaya Amina suna tafe zuwa duba shi kowa na bashi mgana
Har can mallam Sidi inna ta aika Yalwa da ya'yanta sun zo har Baban shi Karimu sai da ya zo duba shi.
Inna Meri ba ta ɓoye musu abunda ya faru ba ta gayamusu komai.
Yalwa na kuka ta ce"Allah ya isar masa ba mu yafe ba."
Karimu kuma cikin fusata ya ce"Ke sakarai miƙe ga kanka, ubanka har ya bar duniya ba lusarin namiji ba ne ka tashi ka zauna da kafafunka domin gina ma kanka kyakkyawan rayuwa anan gaba."
Ya san duk abin da su ke faɗa gaskiya ne, amman shi a cikin Kirjinsa wutar ƙiyayya ke bayyana, daddare haka zai kwana bai yi barci ba yana kukan zucci, Auwalu bai taba tausaya masa ba sai dai ya riƙa dariya yana faɗin"Maganin ma su janye janye kenan in ban da karfin hali ina kai ina wannan yarinyar? Tabbas gaskiya ya fada soyayya ta rufe mishi ido da ya sa ya kai kansa inda bai dace ba.
Yana so shima ya manta amman ya kasa ji yayi ya tsani duk abunda ya danganci wani aiki mai kaki burinsa na zama Soja tuni ya za ma mattace acikin zuciyarsa.
So yake yi ya zauna ya yi kuka amman kuma ya kasa sai ranar da Mu'azzam ke masa mgana ya samu ya riko hannunsa ya danna a kirjinsa yana faɗin "Ta nan ne,a nan na ke jin ciwo da zafin abun. Ina so na manta amman na kasa."
Kawai sai ya fashe da kuka ya dunƙule a jikin Mu'azzam ya na kuka kamar ransa zai fita Mu'azzam bai hana shi ba domin yana so ya samu sukuni. Tun daga wannan kukan da ya samu sararin yi ya samu sauki acikin zuciyarsa, wannan abin da ya faru Shine silar sauya rayuwar Mansoor ya koma rayuwa shi kaɗai ya koma Shuru Shuru sannan mai riko sannan bakar zuciyarsa ta kara ninkuwa sama da sau goma.
Daga lokacin Inna Meri ba ta kara takawa gidan Hajiya ba, Hajiya ma ba ta kara nemanta ba alaqar ta ƙare.
Ana ta masa mganar ya koma makaranta shima sai ya yi tunanin gwara hakan zaman ya ishesa. Da taimakon gonakinsa na gado aka saida ya samu ya fara karatu a gurbin Jami'ar Gombe state University.
Sun ba shi Agric kuma bai sauya ba saboda shi ya riga ya gama sarewa da duk wani burin shi. Da farko tare da Mu'azzam za su shiga sai kuma Alhaji Mustapha ya kawo maganar zuwa Police Acadmy Wudil a matsayin Mansoor ya je tunda shi ke son aikin Kaki, amman ina ya ce har Abada da ya zama ɗan sanda gwara ya mutu.
Sai ko Mu'azzam ya ce zai je tunda Aminin Alhaji Mustpaha ke shugabantar makaranta Kuma shi ya bashi Upper ta mutum ɗaya.
A lokacin tuni shima Mu'azzam ya watsar da mafarkinsa yace shi zai tafi Wudil Mansoor kuma ya ce ƙaninsa ba zai yi aikin kaki ba.
Inna Meri tace bai isa ba sai Mu'azzam ya tafi, Mu'azzam ɗin ma ya nuna ya na son ya je. Kawai sai Mansoor ya ce"Ka je ka je, ka za ma duk abin da kake son zama Mu'azzam amman ka sani har Abada bazan taɓa kaunar wani aikin kaki ba."
Mu'azzam ya ɗauka zuwa gaba Yayan nashi zai rage wannan kiyayyar sai dai kash kiyayyar ta shi mai girma ce har Mu'azzam ya tafi Wudil bai kaunaci wannan karatun na shi ba, Tafiyar Mu'azzam ta kara saka ya zama ya na son kaɗaici, Saboda zaman shuru in ba shi da karatu sai yake zuwa ya na tsaren wani shago a kasuwa yana samun kudin abun hawa zuwa makaranta, ya daina neman kowa hatta su Nasir ya Guje su. Ko sun neme shi ba ya zama in da za su gan shi, su ma sun gaji da nemansa sun kyale shi a tunaninsu nan gaba zai dawo dai dai. Yana Aji biyu a jami'a Coach na Team ɗinsu na Nasara tare da na Tudun wada Team suka zo nemansa akan suna bukatar wani yaro matashi wanda ya iya buga kwallo za'a bashi horo na shekara biyu wata kungiya zata ɗauke shi. Mansoor suka nema tunda daman tare da shi suka rika bin shugabannin manyan Team ɗin su na yan ƙwallo daga na manyan anguwanni har na ƙananu.
A lokacin sai ya ga ya mu su Mu'azzam ne kuma ya tafi Police Acadmy baya nan, Coach ɗin su na Nasara Team yasan Aji ya iya taka kwallo shi ya matsa akan cewa shi Ajin ya zo a matsayin Mu'azzam ɗin mana.
Da farko yaƙi amincewa sai daga baya ya ga to miye aciki? daman shi tuni mafarkinsa ya daɗe da sauyawa amman bai amince ba sai da ya yi mgana da Inna Meri da Baba Danjuma suka sanya ma lamarin albarka.
Sannan ya amince ba zai taɓa mantawa da Coach din su na nasara Team ba wato Shehu Master Allah ya jikan sa ya rasu shi ya ɗauke shi ya kai shi wajen Coach ɗin su na Gombe United a lokaci suka yi mgana sosai ya jaraba shi ya gani sai ya ce za'a bashi horo na shekara biyu, shi kuma sai ya ga ya masa yana karatu sai ya nuna masa hakan bazai shafi karatunsa ba.
Kwatsam ne fuskar Aji da sunan shi ya bayyana acikin yan kwallon kafa, Ya yi horan shekara biyu sannan aka gabatar da shi a Kungiyar kwallon kafa ta Gombe United lokacin kontiragin Captain ɗin kungiyar saura shekara ɗaya ya kare, tare suka ƙarisa wannan shekaran ɗayan da Aji bayan kuma ya bar Club ɗin ƙokarin Aji ya saka ya samu matsayin Captain saboda daman dalilin da ya sa a ka kawo shi kenan. Shi ne sanadin da ya sa ya zama duk abin da ya zama a ƙwallon kafa, kuma tunda ya riga ya hakura da mafarkinsa sai ya maida kansa ga karatunsa sannan ga wasan kwallon kafa.
Shima ya yi singing kontiragin na shekara goma ne da Gombe United sun kuma fara biyan shi albashi bayan alawun da yake samu in suka fita wasa, da haka ya gama karatun shi ya yi service ɗin sa anan garin Gombe zuwa Lokacin rayuwa ta mika abubuwa da dama sun sauya ciki har da gama makarantar Mu'azzam ya fito da matsayin Assistant superintendent of police ASP, ya kuma samu an ijiyesa a garin kano sai dai ya riƙa zuwa ganin gida.
Kuma har a lokacin Mansoor bai kaunar aikin kaki duk ko da matsayin Mu'azzam na Asp. Ya