Showing 1 words to 3000 words out of 103785 words

Chapter 1 - IDAN AN CIZA..! Part 1 Complete by Janafty.txt

Janafty   

20 Dec 2024

4783

Follow this link to join my WhatsApp group: https://chat.whatsapp.com/FpA4NvQPg3XIRUQOgytNh5




*IDAN AN CIZA..!*


*Wattpad:Jamilaumar315*
*Arewabooks:Jamilaumarjanafty*
*Mallakar:Janafty*


*SADAUKARWA GA HAJIYA AISHA AHMAD IYA, NA GODE BISA YADDA KIKA YI TA JIMARIN BIBIYAN RUBUTU NA. ALLAH YA RAYA MIKI ZURU'A YA KUMA SADA KI DA DUKKAN ALHERI.*


*LABARIN IDAN AN CIZA. NA MUSAMMAN NE ZUWA GA AISHA UMAR IBRAHIM, DALILIN KI NA FARA ƊORA ALƘALAMINA A KAN WANNAN LABARIN, NA GODE DA ƘAUNARKI GA RUBUTUNA. FATAN ALHERI.*


*GARGAƊI*


*LABARIN IDAN AN CIZA HAƘƘIN MALLAKA NA JAMILA UMAR JANAFTY NE. A GUJI JUYA SHI KO SARRAFASHI TA HANYAR TAƁA SHI KO SAUYA SHI ZUWA WANI MANUFAR DA BA NI DA MASANIYA. YIN HAKAN KAMAR SAƁA MA DOKAR HAƘƘIN MALLAKATA NE A KIYAYE.*


*MANUNIYA*


*LABARIN IDAN AN CIZA ƘIRƘIRAREN LABARI NE. DUK ABIN DA A KA CI KARO DA SHI YA YI KAMCECENIYA NA SUNA KO HALLAYA, GARI KO DAƁI'A. TO A YI HAƘURI AN SAKA NE DOMIN ARASHIN LABARI BA DOMIN NUNIYA KO TOZARCI GA WATA ƘABILA KO AL'ADA BA*
*NA GODE*


_*DA SUNAN ALLAH MAI RAHAMA MAI JIN ƘAI*_


*Page 1*


*GOMBE STATE: Jihar Gombe*
*3rd, FEBUARY 2022: Uku ga watan Fabareru shekara ta dubu biyu da ashirin da Biyu*.
*DAY: WEDNESDSY: Ranar talata*
*TIME: 10:30AM, Ƙarfe goma da rabi na Safe*
*AREA: Wuri: No.442 Karamchi tv. G.R.A state lowcos*
*PROGRAM: Tare da taurarin Karamchi tv*


_Sunana *FATIMA KABIR SULAIMAN DABO* wacce kuka fi sani da (MIMIN KARAMCHI). Ni haifaffiyar jihar Gombe ce a jamhuriyar Nageria. Gombe jiha ce dake Arewa maso gabashin Nageria, ta yi iyaka daga Arewa da Arewa maso gabas da jihohin Barno da Yobe, daga kudu kuwa da jihar Taraba daga kudu maso yamma kuwa da jihar Adamawa sannan daga yamma da jihar Bauchi. Ta samo asalin sunanta ne daga babban birninta, kuma yanki mafi girma a jihar wato babban birnin Gombe. Kuma an ƙirƙire ta ne daga shashin Jihar Bauchi._


_Kamar yadda kuka ji sunan Mahaifina Kabir, wato Major Kabir Sulaiman Dabo. Soja ne da ya sha gwagwarmaya a gidan Soja har ya kai matakin Major kafin ya yi_ _Retire(Ritaya), sunan Mahaifiyata Barrister Murjanatu Soron ɗinki. Bakanuwa gaba da bayanta danginta gabaɗaya mazauna soron ɗinki ne da ke babban Jihar Kano._
_Lauya ce mai zaman kanta dake aiki a babban kotun Abuja wato Supreme Court Abuja. Mu huɗu cif iyayenmu suka haifa ni Mimi ne ce autar su_
_Dr. Sulaiman Kabir Dabo shi ne babba a yanzu haka likitan zuciya ne a asibitin Aminu kano._
_Sai mai bi masa Madiha kabir sulaiman Dabo, ita yar kasuwa ce ita da mijinta suke da kamfanin sarrafa cafet da jakunkuna tare da takalma suna zaune a garin Lagos._
_Sai Khadija Kabir sulaiman Dabo Lectureir ce a Kaduna state University, ita da mijinta dukkan su koyarwa suke yi a jami'ar ta kaduna kuma suna zaune a garin kaduna_


_Sai ni karamar su FATIMA wacce sunan kakarmu naci wacce ta haifi mahaifinmu wato Hajiyar Shagamu._
_Wacce ta samu asalin sunan Hajiyar shagamu dalilin in aka ce mata wani zai je garin lagos a lokacin sai ta ce zai je dai Shagamu shike nan sai sunan Hajiyar Shagamu ya kama sunanta, in ana kiran gata to ni gata ce da kafafunta, na samu sunan Mimi saboda ina da sunan Hajiya yasa Abi ke kirana da Mimi tun ina ƙarama sai kuma sunan ya yi ta bi na har girmana. Iyayena sun yi zama a garuruwa da dama saboda aikin Abi ammh ni na taso na buɗe idanuwana ne a garin Abuja, tare da iyayena da yan'uwa tun da kuma na taso na ke cikin gata mai suna gata, gani ina da sunan Hajiyar shagamu sannan na shiga ran Abi yana kaunata sosai, na yi karatun primary ɗina zuwa matakin Jss3 a wata private school mai suna Regent Collage Abuja, daga nan sai na koma Jihar Gombe wajen kakata Hajiyar Shagamu dake zaune a gidan marigayi Alhaji Sulaiman Dabo da ya kasance fitatten ɗan jarida, kafin rasuwarsa shine shugaban masu yaɗa labarai na gidan gwammatin Jihar Gombe a wancan lokacin baya da ya shuɗe_


_Tun kafin komawa ta garin Gombe da zama, tun tasowa ta na fahimci ina son tafiye tafiye ina son na ga ina zuwa mabambamtan wurare domin ƙarin ilimi, amma kuma ban san zuwa ko'ina ba sai Gombe duk hutu anan garin gombe na ke yin sa Saboda Hajiyar Shagamu na sona ko da Abi bai so ba ita za ta kira ta ce a saka direba ya kawoni na yi mata hutu, ina son garin Gombe sannan ina son yanayin iskar garin, kuma ina son mutanen garin. ba saboda yana tushe na ba, a'a saboda da garin na saba, kuma asalin kakanin su Abi mutumin AKKO ne. Karamar hukuma karkashin jihar hombe sakamakon fitowa nemen ilimi da kuɗi ya sa suka tarwatsu a cikin jihar Gombe, Kuma duka ƴan'uwan mu da na sani suna cikin garin Gombe ne, tun da Abin mu shine Babba yana da ƙanne guda biyu mace ɗaya namiji ɗaya Alhaji Hamza Sulaiman Dabo, ɗan siyasar da ya yi fice a Jihar Gombe wanda kuma ya riƙe mukamin Senator mai wakiltan mu a majalisa, Sai Hajiya_ Halima(Yaddiko) itama a garin _Gombe ta ke da zama ita da iyalinta, Shi ya sa in za'a ce na zaɓi garin da na fiso da kauna zan zaɓi Jihar Gombe sau shurun masaki ba tare da na sauya ba._


_Zama na a garin Gombe ya sa na cigaba da karatuna a makarantar Joy Acadmey Gombe anan nayi candy, Bayan na kamallah sai na bar gaban kakata na yi sallama da Jihar Gombe na koma Abuja da zama daga can na samu gurbin karatu a Univesity of Ibadan in da na zaɓi shashin da nake son na karanta wato Mass Commucation a faculty of Sciences, nan na samu shedar Digirina na farko a bangaren Bechelors of Imformation and Communication Technology. Bayan na gama na koma garin Abuja nayi service ɗina(Bautar kasa) bayan na gama sai na nemi gurbin Master ɗina a jami'ar BAYERO da ke kano BUK._
_A gidan yayana na zauna Dr.Sulaiman har na kamallah Master ɗina akan abin da ya shafi harkan Jarida, bayan nan ban koma gida ba sai da na samu Diploma akan abin da ya shafi Brodcasting saboda na karanta aikin jarida ne sakamakon sha'awata ta son karanta labarai a gidan Radio ko Tv. Bayan nan na karanta kwasa kwasai da dama wasu ta online wasu a makarantu dabam dabam sannan na hallaci Seminar kan abin da ya shafi Aikin jarida sosai domin na samu ƙwarewa akan haka, na koma gida ba daɗewa ba Abi ya samu hatsari daga hanyarsa ta zuwa Abuja daga gombe, ya samu tsinkewar Lakkansa ta baya(spinal cord) ayanzu haka baya tafiya sai akan keke yana garin Abuja tare da Brr. Murjanatu ta na kula da shi, ni kuma sai na nemi aiki a jihar Gombe da farko ba awannan gidan Tv na fara aiki ba, na fara aiki da wani gidan Jarida baya nan na bar su na koma nayi aiki da gidan Radion Sarauniya Amina na zama mai karanta musu labarai(News) daga nan ne gidan radion KARAMCHI suka nemeni nayi aiki da su na shekara ɗaya, kafin na samu promotion na dawo shashen telvesion a shashin labarai da al'amuran yau da kullum na gidan karamchi Tv. A takaice wannan shine cikakken Tarihin FATIMA KABIR SULAIMAN DABO._


"Masha Allah kyakyawan tarihi mai cike da darasin rayuwa tambayata ta gaba me ya sa kika zaɓi aikin jarida a matsayin ki ta ƴa mace? tun da na ga kamar mu maza mun fi yawa a wannan bangaran?


Sai da ta yi shuru na wani Lokaci kafin ta saki kayattacen mirmishin da sai da dimples ɗin ta hagu da dama suka loɓa kafin ta gyara zama ta fara faɗin.


_Tun farko Burin Abi a kaina shine na zama likita irin yayana, sai dai ni ra'ayi na ba shi anan wajen, ban taɓa tunanin zan iya zamowa yar Jarida watarana ba, sai dai kasan Allah abin da ya kaddaro ma bawa bai isa ya kauce ma wannan bingiren ba._


"Ba ki faɗa min yadda kika tsinci kanki a matsayin yar jarida ba?


_Uhm ni ma na tsinci kaina ne a matsayin yar jarida, sai dai akwai wasu kalamai da suka yi tasiri a rayuwata, tun ina yar shekara goma sha biyar wani ya taɓa ce min zan fi dacewa da yar Jarida mai karanto labarai saboda ina da zaƙin da karaɗin murya tun a wanchan lokacin, kenan kuma tun daga lokacin sai naji sha'awar haka ya ɗarsu acikin raina gaskiya wannan shine mafarin komai._


"Dakyau kina ɗaya daga cikin manyan taurarin gidan Tv na karamchi, mutane suna yaba miki sosai sannan kin kasance kamar madubin karamchi wani saƙo gare ki zuwa ga masoyan ki?


_Ina godiya sosai da yabawarsu a kaina ina kuma jin daɗin hakan. Saƙon da nake da shi zuwa gare su shi ne su cigaba da kasancewa da gidan talabijin na karamchi domin ganin shirye shiryen mu a ko da yaushe, babu kosawa acikin aikin mu, in sha Allahu ni Fatima Kabir dabo( Mimin karamci) zan cigaba da kawo muku labarai dabam dabam da suke faruwa a jamhuriyarmu ta Nageria cikin Harsuna guda biyu wato turanci da hausa, kudai ka da ku matsa kusa da akwatin talabijin ɗin ku, Mimin karamcinku tana nan tare daku a koda yaushe in sha Allahu_


"Ba ki faɗa mana ko shekarun ki nawa ba?


_Shekaruna 30 talatin cif a duniya._


"Jikin ki sam bai nuna shekarunki ba. An ya ba kin ƙara ba ne saboda masu kallo su ƙara ganin girman ki ba?


Dariya ta saki da siririyar miryanta kafin Ta ce.


_Haba dai Na misau kai ma kasan ba haka tsakanin mu, ƙaramin jiki na ne ke ɓoye shekarun nawa. Ammh tabbas shekarata 30 kamar yadda na faɗa farko_


Dariya ya yi mata kafin ya gyaɗa kai yaba faɗin" Na yarda tun da kin dake a hakan ne ammh har yanzu ina da ƴar tamtama to maganar aure fa? Akwai ko an kusa?


Rufe bakinta ta yi da mayafinta kafin ta girgiza kai tana faɗin.


_Kowa ya sani ba ni da aure._


"To niyya fa? Ko babu niyyar ne?


_Akwai mana in Allah ya kawo wanda ya dace zan yi aure Na misau._


A yadda ta faɗi mganar sai da yanayin muryanta ya sauya, lokaci ɗaaya sai fara'an ta ya ragu kuma an fahimci hakane saboda kowa yasan Mimi mace ce mai fara'a kowa ya ya ta sauya masu kallo suna ganewa. Na misau ya kalleta itama sai ta kallesa
Mirmushi ta yi masa bata ƙara mgana ba shi kuma yace za su buɗe layukan wayarsu domin ba ma masu kallo damar kira, nan da nan ya zayyano lambobin da masu kallo za su kama su kamar yadda suka saba.


Jamilu Adam Na misau kenan mai gabatar da shirin tare da taurarin karamci Tv, sai Kuma bakuwar mako wato Fatima Kabir Sulaiman Dabo(Mimin karamci).


********


*12:40pm.*
Laraba.


Wata doguwar mota ce kamar kiran macapolo, sai dai bata kai ta tsawo ba keta sharara gudu a hanyar babban titin shigowa jihar Gombe.
Motar an yi mata kalan fenti yellow da Blue sannan a jikin motar an rubuta *GOMBE UNITED* da manyan harrufan baki.
Daga cikin motar hayaniya na tashi kaɗan kaɗaan, na hango cikinta kaf matasa ne masu jini ajiki acikin motar. Sannan suna sanye da kaya su ma rigar blue mai ratsin fari haka ma wandunan jikinsu duk kalan blue ne da Fari.


Ba'a jiyo mganganunsu tunda motar tana gudu sosai ga iskar mota, ammh sun yi gungun daga can baya suna kallon wani abu a wayar ɗaya daga cikin su.
Daga farkon kujerun daga na direba sai wasu guda biyu masu zaman mutum ɗai ɗai ta bangaren hannun hagu wani mutum ne ke zaune shima Irin kayan sauran ne ajikinsa, ammh shi ya fi su shekaru zai iya kaiwa hamsin da uku a duniya 53 sannan yana da saurin furfusa, tunda ta saman kansa ga furfura nan sun fara cika masa gashin kansa har wajen tsillin tsillin gemunsa. Waya ya ke yi acikin wayar yana faɗin.


" Eh gamu a hanya mun kusa shigowa Gombe ma."


"Eh Kano pillars muka je, an tashi 2:01 an je gidansu an ci su wasa ba."


Ya faɗa ya na sakin karamar dariya kafin ya ce" Shi ya sa nake faɗa maka samun *AJI* a cikin gombe United alheri ne, gayen ya iya buga kwallo fiye da yadda kake tunani."


Ya faɗa ya na kallon gefensa kujerun dake hannun damarsa, wani matashi ne yana zaune shima da irin kayan dake jikin sauran sai dai shi ya sanya wata bakar Jaket a saman rigarsa sannan kansa akwai Pcap ya rufe rabin fuskarsa ya kuma lafe ajikin motar kamar mai barci, wata bakar Jaka a gabansa kamar irin ta yan makaranta baka.


Girgiza kai ya yi lokaci ɗaya da yar dariya kafin ya ce" kasan shi ya fi miskili iya miskilanci, tunda muka taso bai yi mgana ba kuma nasan ba barci yake yi ba, Ok zamu yi waya da zaran mun sauka. Yauwa take care."


Daga haka ya katse kiran yana kallon na gefensa cikin muryansa mai kaushi kaushi ya kira sunanshi.


"Aji.."


"Captain.."


Bai amsa ba, illah motsi da ya yi kaɗan alamun yana jin sa sanin halinsa ya sa ya cigaba da faɗin" Coach na katsina pillars ne ya kirani ka gane shi? Madaki?


Kansa ya ɗan ɗago kaɗaan kafin kuma ya gyaɗa kai kaɗan alamun eh ya gane shi, ba tare da ya jira mganarsa ba sanin da ya yi daman ba mganar zai yi ba, ya sa ya ce" Ya ce na faɗa maka weldone an je kano an ci masu gida."
Mirmishi kawai ya yi tunda ga saitin yadda bakinsa ya juya nan sai kuma daga karshe ya jinjina kai.


Tun da suka taso idanunsa biyu yana jin hayaniyar da ta fara cika motar, baya jin mgana ne ya so ya tsawartar musu sai kuma ya basar baya so ya zama mai yawan takura gare su, su ɗin Ƴan Team din shi ne a matsayinsa na Captain ɗin su kamar babban Yaya ya ke a garesu yasan suna jin tsoron sa, in ya tsawatar za'a ji kuma za a kiyayewa ammh ya kan zama mai ɗauke kansa akan wasu abubuwa ba saboda komai ba sai saboda tsira da mutumcinsa.
Ya na shirin gyara zamansa daga can baya yaji muryan musa Zinder yana faɗin"Kai jama'a ni dai Allah na gani ina son wannan baiwar Allah nan, tana burgeni, ta iya magana ga iya kwalliya mallam"


Ya faɗa har yana tagumi, Aji ya juya kaɗan yadda ba za su fahimci yana kallonsu ba a nan ya ga sanda Musa ya yi tagumi shi ke da wayar a hannunsa suna kallo.
Koma menene ya ke mgana akai a cikin wayar suke kallo.
Shuru ya yi ya natsu sai yaji ya fara jiyo sautin ta in da ta ke cewa.


_Akwai mana in Allah ya kawo wanda ya dace Na misau._


Kamar ɗaukan iska haka yaji muryanta ta shigo jinsa, ita muryan ai bazata ɓoye masa ba, muryan da ya santa tun a zamanin da ba ta kai haka zaƙi da garɗi ba, wani abu ya ji ya daki zuciyarsa har sai da ya runtse idanuwansa saboda yadda yaji jikinsa ya fara rawa.


"Kai fa duk gidan Tv Karamci ba kyakyawa yar gayu irin Mimi wlh"


"Ni Mirmishinta ke burgeni.."


"Ni kuma salon yadda ta ke mgana ke sumar dani Baaba"


"Ni kuma kwalliyarta. Kai matar nan ta san kan kwalliya kowani kaya ta saka sai ya dace da ita."


"Ni duk ina jin kune, kun ga in tayi mirmishi dimple ɗin ta suka loɓa sai naji kamar zuciyata zata fito waje, ba domin nasan ba za ta so ni ba, ai da tuni na gabatar da kaina wajen Mrs Dimple."


Gabaɗayansu suka kwashe da dariya Kb ya daki Kafaɗan Sagai yana faɗon" In ma mafarki kake yi sagai gwara ka farka, kana jin tarihinta ubanta soja uwarta lauya ce yan'uwanta kaf masu kusa ne a kasar nan, kai a hakan kaka ke tunanin zata kula ka? Waye kai? Tarihin ka kenan ace kai Sangai ɗan kwallon kafa ne na kungiyar Gombe Untied wato golan su, baya nan ba ka da wani tarihin da wannan yarinyar za ta soka gwara ma ka daina mafarkin da ba zai taɓa zama gaskiya ba."


KB na dariya yace"Kuma ta girme shi, tace she is 30yrs old sangai wannan uwarka ce ma, tunda in ka yi sauri ne 25 tsawon kafa ne kawai yasa ka ke ma kanka zarra da tusa kanka in da baka da Muhalli."


Gabaɗayansu suka saka mai dariya suna jan rigan jikinsa, shi kuma sai ya wani warce wayar hannun Musa ya ƙamkame yana faɗin"Age is just a number, ni dai ina sonta in na ganta sai naji kamar zuciyata zata fito waje.." Ya faɗa cike da shaƙiyan da ya saba.


"Ina bukatar sauka a nan."


Suka ji muryan Captain a kausashe, da ta yi sanadiyar katse musu shagalinsu.
Nan take kowa ya shiga taitayinsa cikin lokaci motar ta natsu kowa kuma ya koma wajen zamansa ya zauna yana zaren ido.
Direba ya juyo yana faɗin"Captain ba mu isa Camp ba fa?
Kai tsaye ya ce"Eh! Anan yau nake da ra'ayin Sauka"
Ya fad'a muryansa na shakewa kamar yana mura. Coach ya juya yana kallon Aji kafin ya koma yana kallon hanya.
Yanzu suka shigo gombe akwai nisa kafin cikin gari.
Da mamaki ya kalleshi kafin ya ce"Aji da nisa da cikin gari fa"


Kai tsaye ya kara faɗin"Ina bukatar sauka anan"


Direba ya juya yana kallon Coach kafin ya yi mgana ya gyaɗa masa kai alamun su tsaya.
motar na tsayawa ya tashi ya ɗauki jakarsa ya rataya ta bangaren hannunsa na hagu ya sauka daga cikin motar kafarsa sanye cikin wani katon booth din takalmi baki mai igoyoyi.


Sai da ya fita sannan ya ɗaga ma Coach ɗin su hannu, su musa sai leke amma ba bakin mgana, Kb ya yi ma Sangai raɗa yana faɗin"Ko surutun mu ne ya damu Captain ya sauka a farkon gari?
Sangai ya yi shuru bai yi mgana ba, amma baya tunanin haka, in da sun dame shi zai yi mgana ya ce su bari ko kuma ya ce za su yi gudun kilomiter 10 in suka koma Studion ammh yanayinsa yanzu ya nuna akwai wani abin da ke damunsa.


Couach ya buɗe window gefensa ya leka yana kiran sunan

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login