Showing 42001 words to 45000 words out of 103785 words
mgana ko kaji haushi ko ta yi maka daɗi shi kuma Mansoor saurin hasala da zuciya da masifa ko magana za ka iya yi ya ce da shi kake shi ya sa suke saurin samun matsala da Nasir ko a baya.
Bai yarda barci ya daukesa ba sai da ya je ya yi sallar azahar sannan ya dawo ya kwanta kuma ya samu barci sai uku da rabi ya tashi.
Ya ji kuma zuciyarsa ta rage nauyi tunda daman ya daɗe ba ya samun barcin dare sosai.
Wanka ya sake yi ya shirya cikin wata Riga ta kwallo ce an saka MESSI a jikin rigar saboda shi Mansoor allon ƙwaikwayonsa a kwallo tun a zamanin baya Messi ne har kuma yanzu da yake cikin kwallon dumu dumu bai sauya gwani ba, sai ya saka bakin wando mai kamawa ta kasa kaɗan ya yi zanzanro sannan ya saka wani bakin takalmi mai rufi ya kuma gyara gashin kansa da ya tara sai ya ɗora P.Cap saboda ba ya so Inna ko Baba su gani su yi masa faɗan rashin aski.
Ranar har da fesa turare abon da ya jima bai yi ba. Key din mota ya ɗauka da ita yau ya ke fita tunda zai kai ta gareji a yi juyen baƙin mai ya jima bai kaita an duba ta ba. Shifa ba domin Mu'azzam ya matsa masa ba bashi da ra'ayin siyan mota mashin ɗinsa ta ishe sa, farko mashi ɗin da ya siya Baba Danjuma ya ba ma wa, ko wata ba ta yi ba aka tare shi aka karbe mashin ɗin Allah ya sa ba su yi masa rauni ba sun dai dake sa, sai yanzu ya ke tunanin zai ba shi wannan mashin din sai ya siya babba mai kama da mota.
Daga anguwarsa ta Tunfere gareji ya je da yake kanukawan sun waye shi yana zuwa suka fara kiran sunansa "Aji Aji.!
Shi kuma yana ba su hannu suna gaisawa anan ya ɓata lokaci har wajen biyar na yamma Nasir ya kara kiransa ya ki ɗauka sai ga Ahmad ya kirasa shi kam daman sun jima ma ba su yi mgana ba.
Shi ya sa ya ɗauka sun fara gaisawa kenan Nasir ya karɓe wayar yana faɗin "Aji ni kake yi ma wulakanci ko? Duk abin ka dai yau a katifarka zan kwana."
Bai gama sauraransa ba ya katse wayarsa Nasir dai ba zai taba sauya hali ba.
Sai da aka gama duba motar ya ba su kuɗinsu sannan ya baro garejin zuwa gida, ya je ya iske Inna Meri ita kaɗai a bangarenta Walida ba ta nan ta tafi islamiya. Ya zauna suna gaisawa ta ce masa yanzu su Mu'azzam suka fita suna ta jiransa.
Shuru ya yi bai yi mgana ba, Inna Meri ta je ta kawo masa ruwa da abinci kamar ta san ya na jin yunwa.
Shinkafa da wake ne da manja ya na son dahuwar Inna wake ya dame da shinkafa.
Yadda ta ga yama cin abincin ne ya sa ta san ya daɗe bai ci abinci ba.
Cikin Tausayin shi ta ce" Baban Inna ka rika cin abinci don Allah, zama da yunwa babu amfani ka tattala lafiyarka tun kafin ta kubce maka." Kai ya gyaɗa mata kafin ya ce'" To inna."
Daga haka ya cigaba da cin abincin sa, tana lura da shi ana ta kiran wayarsa yana kashewa. Kuma tana jin Nasir kafin su fita dazu yana faɗin baya ɗaga kiransa, sannan Mu'azzam ya ce"Don Allah Inna ki roki Baban Inna kar ya ce zai ja baya a sha'anin nan na Makama kin san halinsa."
Shiyasa yana gama cin abinci ya sha ruwa ta kalle sa kafin ta ce"Su Nasiru sun fita suna ta neman ka, ka kira su kaji in da suke Baban Inna."
Ba musu ya ce To Inna ya ɗauko wayarsa ya Kira Mu'azzam sai yace suna kofar gidan su Ahmad. Sai ya ce yana gida su kariso, Bayan sun gama wayar Inna Meri ta kalle shi tana fadin" ka saki jikin ka bikin abokin ka ake yi ba na wani ba, Don Allah ka zama aboki nagari ban san kana zille zille nan."
Sai da kalaman Inna su ka bashi dariya sai ya girgiza kai kafin ya ce"Mu'azzam ne ya kawo miki ƙara ta ko Inna?
Inna ta ce" ba ruwa Ɗan Inna ni na haife ka ai na san halin ka."
Mirmishi kawai ya yi bai yi mgana ba Inna Meri ta zauna ta na ta masa nasihanta na kullum ya yi hakuri ya manta baya ya dawo da rayuwarsa kamar ta baya.
Jin ta kawai ya ke yi, shi fa bai ga wani Sauyawar da ya yi ba, ya na dai guje ma wasu abubuwan ne saboda gudun tuno da abjn da ya wuce a baya.
Kiran wayar Mu'azzam ya ƙwace sa ya mike ya ce bari yaje waje suna jiransa.
Yana fita ya gansu gabaɗaya Makama ne kawai babu Ango kenan, yana fitowa Nasir ya ɗauki dutse ya jefe dashi ya caɓe dutsen Ahmad na dariya ya ce"Ka ga Ajin ƙwallon kafa akwai iya kama saiti."
Mu'azzam na jikin Motar Mansoor ɗin shi da Ahmad suna dariya.
Nasir faɗi ya ke yi" yau fa sai mun raba hali ni da kai Aji."
Aji ya kallesa kafin ya ce"Nasir ka yi aure ba ka girma ba? Sai yaushe?
Ahmad yace" Sai matarsa ta haihu, daman tsohon ciki gareta."
Mansoor ya yi mirmishin saman fatar baki bai yi mgana ba, ya isa wajen Ahmad ya bashi hannu suka yi musababa Ahmad ya jinjina hannunsa yana faɗin" Aji an daɗe ba'a haɗu an gaisa ba."
Aji ya ce"Wallahi ya rayuwa.?
Ya amsa ma sa da Alhamdulillah.
Mu'azzam ya mika masa hannu suka gaisa ya tambaye shi ya hanya? Ina su Junior ya ce duk suna gaishe su.
Nasir ne ya warce hulan kan Mansoor ya ɗora bisa kansa Mansoor ya bisa da kallo kafin ya bata rai lokaci ɗaya yana faɗin. "Nasir ka rika yin abu cikin Aji don Allah mana."
Gabaɗayansu suka fashe da dariya, Ahmad da Nasir suka haɗa baki wajen faɗiin " Da girman Kujeran Aji Allah ya kara lafiya."
Mu'azzam nata dariya, shima Ajin sai da ya Murmusa kafin ya mika hannu ya warce hulansa daga kan Nasir yana faɗin"Kai yaro ne har yanzu Nasir na kara samun tabbacin tsawon kafan ka ne, ya ruɗeka ka yi saurin aure." Nan ma suka kara kecewa da dariya Mu'azzan na ta mirmishin jin daɗi ganin ɗan uwansa na hira har da mirmishi.
Makama ya tambaya Mu'azzam ya ce ya karbi motarsa ya je ya dawo, suna faɗa masa wai akwai kamu a gidan su Amarya kuma ana bukatar ganin Ango da abokansa. Aji ya kallesu a kaikace kafin ya ce"kamar wasu mata sai ku je kuma?
Ahmad ya ce"Ni kaina na ce ba za mu je ba."
Aji ya ce"Kana da girman ka Ahmad gwara ka kama kanka da harkan yara."
Ya faɗaa ya na nuna Nasir, Nasir kuma ya ce shi in ba za su je ba zai raka makama, Mu'azzam ma ya ce shi yanzu Tudun wada zai je ya kai wani sako saboda jibi ya ke so ya koma saboda aikinsa. Nasir kuma ya kira Makama ya ce ya shirya zai raka shi su tafi kamun tare da sauran abokan shi.
Nan ya barsu ya wuce gida su kuma suna nan kofar gidan suna ta hira har aka kira mangariba. Abun mamaki Mansoor ya saki jiki suna ta hira da Ahmad.
Duk dai yawancin hiran ta ƙwallo ce daga nan suka aika cikin gida aka ba su butoci suka yi alwala suka wuce masallaci.
Daga nan Mansoor ya ɗuke su a mota zuwa Tudun wada gidan su Hibba ya kai mata sakon da ta ba da, daga nan dakyar ya roki Mansoor ya biya da su Bolari can gidan su mahaifiyar Mu'azzam kakarsa Innayi ta na nan da ranta da ta ga Mansoor sai da ta ce shiyasa ta ga an sha iskar rahama ashe shi ne zai zo.
Tunda ya daɗe rabon shi da zuwa a baya dai duk zuwa shi da kansa zai raka Mu'azzam gidan ya gaida kakaninsa.
A gidan suka ɗan jima shi ya sa ba su baro anguwan ba sai da suka yi sallar Isha'i.
Daga nan suka koma anguwan Arawa Ahmad ya ce zai ɗauki sako a gida suma sai suka shiga gida suka gaida Baba Danjuma.
Magajiya ba ta nan ta je kauyen su wani kawunta ya rasu. Tare da Mariya ta tafi duk yadda Baba Danjuman ya so ta kyaleta tunda akwai makaranta ta ce da ita za ta tafi. Mariyan ma ba ta so hakanan ta shirya suka tafi. Suna ɗakin Inna Meri tare da Baba Danjuma da Innar suna ta hira Walida ta zuba musu tuwon da Inna ta yi da yamman nan suka ci a kwano ɗaya tare da Baban su.
Ba su bar gidan ba sai goma lokacin da Ahmad ya kira su ya ce yana jiran su a waje, su daga nan suma wuce gidan Mansoor, a nan ne ma Mansoor ya ga kayan da Mu'azzam ya siya musu Shadda mai ruwan kasa su huɗu Ahmad ya dinka musu daman shi ya tura ma kuɗin ya siya musu shaddar. Daman shi ba'a iya masa sai da ya kalli Mu'azzam kafin ya ce" Sai kace wasu yara mu saka anko? Tunaninka ya koma na yara ne Mu'azzam".
Shi dai dariya kawai ya yi Ahmad ke faɗin. "Haba a baya ai muna ɗinka kaya iri ɗaya Aji ka manta ne"
Kai tsaye ya ce"Yanzu mun girma mun zama magidanta kai da matarka da yarka, Mu'azzam da matarsa da ɗansa Nasir ma haka ga shi Makama zai yi aure ace duk ba ku fita sahun yara kun fara halin manya ba?
Ahmad na yar dariya ya ce"Kuma fa hakane to daga wannan shike nan da bikin ka kowa kalan na shi zai saka."
Banza ya yi masa kamar bai ji ba suka haɗa ido da Mu'azzam suna dariya.
Su Nasir ne ba su dawo gidan da wuri ba megidan ya riƙa masifa yana faɗin"Ku kira su Nasir ku dawo kar na rufe gidana ya zageni, yana magidanci yana yawon dare"
Ahmad ya ce"Ba sun je kamun Amarya ba."
Aji ya yi ƙaramin tsaki kafin ya ce" kamun amarya ko kamun shirme."
Mu'azzam ya kira Nasir a waya ya ce ga su nan a hanya. Sai wajen sha biyu saura suka dawo Mansoor ya yi ta masifa yana cewa da sun kara mintina zai rufe gidansa ne.
Nasir na rungume da katuwar jakar kayansa ya shigo yana fadin"Mun ji to megida mun ji to."
Ya faɗa yana ture Mansoor ya shige falon.
Makama tare da wasu maza su uku biyun bai san su ba amman yasan ɗayan abokin makama ne Nura suna ga gida ga gida ne.
Hannu suka bashi dukkansu suka yi masabaha, daman da motar Mu'azzam suka dawo sai da ya fita ya rufe get sannan ya dawo. Allah ya taimaka nepa suka kawo wuta sai fanka ta fara kaɗaawa.
Makama da abokinsa Nura da sauran ƴanwansa suka kwana a falo.
Nasir da Ahmad da Mu'azzam da mai gidan suka kwana a ɗakin Mansoor.
Dolensa ya bar katifa nan ya kwana a ƙasa saboda yana kwanciya Nasir yazo ya shige tsakiyar su shi da Mu'azzam yana faɗin
"Ni fa na saba da katifan matata ba zan iya kwanan ƙasa ba."
Mansoor ya yi ta tsaki ya na faɗin" Nasir sam ba ka da Aji."
Ya na dariya ya ce"Na ji Aji mai Aji ba."
Karshe kasa ya kwana shi da Ahmad da Asuba shi ya ta da su suka yi alwala zuwa masallaci daurin auren na safe ne misalin sha ɗaya ne. Shi duk haushin su yake ji wannan abun fa sai ya yi kamceceniya da abin da mata suke yi.
Ko a baya da yake cikin su ba haka halinshi yake ba yana komai da class ne shi ya sa ma a nan ya fara samun ssalin sunansa na *AJI*
******
*SATURDAY, 28 APRIL 2022*
8:50PM.
A cikin anguwan Dubai Quaters Usman makama ya kama gidansa mai kyau anan aka saka Amarya.
Tun 7:30pm na yamma aka kawo Amarya gidanta saboda yanayin tsaro, daga nan Amarya da gayyarta za su wuce wajen dinner da abokan Ango suka haɗa. Acikin motocin da suka kwaso Amarya da tawagarta har da motar Aji amman ba shi ya ja motar ba Ahmad ne domin shi ya ce ba zai je ba, Nasir ya ce ya ara masa ya ce bazai ba shi ba sai da ya ba ma Ahmad aro.
Nasir ɗin yana da mota saida ita ya yi daga baya, ana ɗaura aure Aji ya zille musu ko hotunan da aka je gidan Amarya aka yi bai je ba gida ya koma ya kwanta ya juta abun sa.
Sun je dai Reception suka ci abinci daga nan ya hau mashin ya koma gida tunda daman key ɗin motarsa na wajen Ahmad. Dinner dai sun ce ko ya so ko bai so ba sai ya je, ga shi ya yi musu tsiya bai sanya kalan kayansu ba wani farin yadi ya saka mai shara shara. Wai shi ba yaro ba ne ko mace da zai saka anko.
Hakanan suka kyale shi, ya saka nashi dabam a wajen ɗaurin auran ma dakyar ya bari suka yi hoto cewa ya yi wai hoto na yara ne, komai sai ya ce ba aji aikin yara ne.
Sun je gidan su Amarya sun sha hotuna, Mu'azzam ya so ya ga yayar Amaryan da Nasir ya ba su labarin ta kankame komai a sha'anin bikin, sai Makama ya ce Bibi ta ce Anty Baby ta je karɓo ɗinki ita da kawarta Anty Mimi.
Kuma har suka gama hotuna su ka tafi ba su dawo ba, suna tafiya sai ga su sun dawo tella ne ya yi musu tsiya.
Mimi sai masifa ta ke yi tana cewa "Rukky ke kika ja mana da kin bari na kai ma tela na da tuni ya ɗin ka mana."
Rukky ta ce"Ina na san haka Habu zai yi mana ,ai ya ci taliyan karshe."
Ko makeup ba su samu yi ba mazan ma'aikansu daga karamchi Talabijin da suka zo musu ɗaurin aure ma ba su haɗu ba sai dai suka yi ma Rukky fatan alheri ta waya. Matan ne kaɗai suka samu tunda su sun jira su, saboda bakin ne yasa ba su samu zuwa kwalliya ba Rukky ta ce su bari anjuma su yi na dinner.
Tun Safe Mimi ta baro gida sai da za'a kai Amarya ta ɗauki Rukky a motar ta suka koma gida ta ɗauki jaka da takalmin da za ta yi amfani dashi tare da ɗan kunne da sarka suka tafi wajen kwalliya daga can za su wuce dinner.
Hajiya ta ga yadda Mimi ta yi kyau cikin Atamfar yinin biki saboda ajikin Atamfar akwai ja, a cikin ranta addu'a take yi mata Allah ya haɗata da wanda zai sauya mata rayuwa a daren nan.
Baaba Uwani kuwa har hqraban gidan ta raka su tana faɗin" Binta Allah ya tsare ya sa a dawo lafiya, Rukkaya Allah yasa a watse taro lafiya." Suka amsa mata da Amin, sun je shagon kwalliyan daman sun yi booking, Rukky aka fa ra yi mawa.Wacce za ta yi ma Amarya gida suka tura ta. Sai kira Bibi take yi ta na faɗin an gama mata kwalliya ta shirya suna jiran angwaye ne yanzu za su tafi can in da za'ayi Dinner ɗin.
Da za su jira sune, Mimi ta ga yanzu ma aka fara mata nata kwalliyar sai ta ce kawai su tafi in sun gama sai su zo daga baya.
Haka aka yi Amarya Bibi da tawagan ƙawayenta da ƴan'uwa suka yi gaba su Nasir suka zo da motoci suka kwashe su.
Sai wani Hall haɗaɗɗe mai kyau wanda, ya ke tashe a garin Gombe wajen yin bukukuwa. Ko da suka je an gama tsara komai daman kuma sai da Ango ya jira zuwan Amarya sannan tare da ƙawaye da abokan ango suka shiga wajen.
Wajejen goma na dare aka fara gudanar da Dinner ɗin Amarya ta yi shigan Blue ne shima Angon kalar shaddar jikinsa kenan.
Ƙawaye kuma Less ɗin su mai ruwan ash ne da zanen pick, sun yi ɗinkin fitted gown gabadaya sai suka yi amfani da head pick.
Makama ya tambayi Bibi da cewa shi fa yau kwata kwata bai ga Anty Rukky ba
Bibi na danna wayarta ta ce"Suna wajen kwalliya ita da Anty Mimi su nake kira ma yanzu."
Makama ya ya fito Ahamd da hannu yana faɗin " Nima wani abokin mu muke jira, bai zo har yanzu."
Bibi ta kalle shi kafin ta ce" Wai wannan ɗan ƙwallon da kake ba ni labarinsa,?
Sai ya gyaɗa mata kai dai dai karisowan Ahmad yana faɗin" Ango ya aka yi ne?
Makama ya duba agogon fatan hannun shi yana fadin" Aji ba zai zo ba ko?
Ahmad ya ce" Mu'azzam ya je ya ɗauko sa, na kirasa ya ce suna hanya."
Makama ya sauke Nunfashi kafin ya ce" Allah ya ɗorani akan sa kenan ya ga dama zai zo." Ahmad na dariya ya ce"Gaskiya ka ci babbar sa'a."
Ita Bibi rabin hankalinta na kan wayanta sai ji suka yi tana faɗin"Anty Mimi ku yi sauri an fara fa tun ɗazu"
Sai da ta gama wayar ne angonta ya ga duk ta bata rai sai ya ramkwafa ya na lallashinta.
Aji da Mu'azzam sun shigo hall ɗin Sha ɗaya dai dai na dare.
Aji na sanye da wata ɗanyan shadda mai Ruwan ƙasa shi ya na son abu mai ruwan ƙasa da bakin abu da kuma fari.
Hulan kansa dara ce baka, gefe da gefe gashinsa kansa da ya tara ya samu wajen zama a gefe da gefen hulan kansa, kafarsa kuma baƙin takalmi mai rufi na gata mai kyau agogon hannunsa ma baƙi ne na fata.
Suna shigowa Nasir ya je ya yi ma Mc raɗa sai hall ya kaure da muryan Mc da ya ratsa ya shiga kunnuwan mutane da faɗin.
"Kai jama'a ashe dai yau kila sai na tafi gida da kujeran hajji, bikin na masu ƙasa ne yanzu na ke samun ,labarin Aji jiharmu Captain ɗin kwallon kafa na kungiyar Gombe United matashi nan mai tashe MANSOOR AJI aminin Ango ne kuma ya shigo wannan Katafaren