Showing 99001 words to 102000 words out of 103785 words

Chapter 34 - IDAN AN CIZA..! Part 1 Complete by Janafty.txt

Janafty   

20 Dec 2024

4797

kafin ta ce" Ki kawo musu ruwa." daga haka ta gyara zaman hijabin jikinta ta fita falo, abun ya kara ɗaure mata kai ganin Hajiya da wata mata ƴar gayu sai da ta zauna anan kasan Cafet suka gaisa da Hajiya da matar sannan Hajiya ta kalleta tana faaɗin "Sai kika gan mu ko? Murja ce ta ce gwara mu zo kawai, mahaifiyar Binta ce matar marigayi."


Sai da Hajiyar ta faɗa sannan ta gane ta gani ɗaya ta taɓa yi mata kuma ganin ba na cikin kwanciyar hankali ba ne. Cikin gyaɗa kai ta kalleta kafin ta ce"Allah Sarki Hajiya ya karin hakuri? Allah ya jikan sa da rahma."
Mommy ta amsa da Amin Amin ta na ƙare ma falon kallon tsab tsab daman Walida tun safe ta gyara shi ta share Inna Meri na cikin faɗin da basu wahalar da kansu ba,da ita ta zo gidan Hajiya. Mommy ta yi mirmishi kafin ta ce"A'a ai muke so gwara mu bi yo sahu, ni na ce ma Hajiya ta bari mu za mu zo da kanmu."
Inna Meri ba ta ce komai ba, tunanin ta ɗaya yanzu magana zai yaɗu acikin gidan da zuwan su Hajiya ba ta son abun mgana.
Walida ta kawo musu Pure water a filet Hajiya ta yi mata sannu ta na tambayan Bintu tace ta na gidanta, daganan ba ta zauna ba sai ta zari hijabi ta fita. Tana fita da ga shashen Magajiya su Gaje da Harira sun yi zaman dirshan suna kuskus suna ganinta sai su ka yi shuru sai ta yi kamar ba ta gansu ba, ta yi ficewarta daga gidan gidan Dije mai waina ta shiga wajen ƙawarta Bahijja.


Mommy ce ta sha ruwa Hajiya kuma ta ce cikinta ya cika sai dai kafin su tashi tafiya, Hajiya mike kafarta ta yi tana faɗin"Meri haka waje ya sauya,gabaɗaya na kasa gane gidan sai da muka yi tambaya bayan kuma mun shigo shima dai gidan duk ya sauya."
Inna Meri ta ce"Eh an yi gyara sosai an raba mana bangare da su Gaje mun koma farko, nan ma ciki an raba bangarena da na Magajiya aikin duk na Baban Inna ne."
Hajiya ta washe baki kafin Ta ce" Masha Allah Allah ya sa albarka." Inna Meri ta amsa da Amin. Kafin shuru na wani lokaci sai can Hajiya ta muskuta kafin Ta ce.
"Meri magana ce mai muhimmanci ke tafe damu, ina fatan megidan na nan?
Inna Meri Ta ce"Gaskiya ya fita amman dai ba nisa ya yi ba ina kyauta ta zaton yana kan hanyar dawowa."
Sai Hajiya ta kalli Mommy kafin ta ce" kin ji Murja, ko za mu jira har ya dawon ne?
Sai Mommy ta ce"Hajiya shi yaron fa?
Sai Hajiya ta kalli Inna Meri lokaci ɗaya tana faɗin"Meri har da shi Mansoor ɗin Murja ke son gani za ta sauke nauyin marigayi ne da ta ɗauka."
Inna Meri ta yi kasaƙe kafin ta ja gauran numfashi Ta ce"To sai dai na kirasa a waya Allah yasa yana kusa." Ta faɗa lokaci ɗaya tana miƙewa Walida ta ke kira sai taji Shuru sai Mommy ta ce in wayarta taje nema gata nan saman Kujera. Sai ta ɗauka ta shiga ciki da yake Inna Meri ba ta da duhun kai ta iya dubo suna ta yi kira.


Baba Ɗanjuma ta fara kira ta tambaye shi ko yana ina ne? ya ce ga shi ma a kofar gida sai ta ce ya kariso suna da baƙi.
Baban Inna kuma kira byu ta yi masa bai dauƙa ba tana shirin ijiye wayar ta fito sai ga kiran shi Muryan shi a Cunkushe ya ce mata ya ɗan kwanta ne, ba ji kiranta daga farko ba Itama Innan muryanta a cushe ta ce ya zo gida tana son ganin shi, bai kawo komai ba ya ɗauka ko wani abu ne ya taso, bai taɓa tunanin wani abu daya danganci yarinyar da sanadinta mafarkinsa ya ruguje ba.


Inna Meri na dawowa falon ta faɗa musu Hajiya ta kira su a waya sai ga Baba Ɗanjuma shi tun a waje ma ya ga mota, Gaje ce ta shigo samun ruwa wajen Magajiya ta ga shigowar su Hajiya shi ne ta je ta kira Harira suna ta tsegumin son sanin su waye suka zo wajen Meri masu kudi haka sun tambayi Magajiya ta ce ita bata sani ba, Walida kuma da ta fito sanin halinta yasa ba su tambayeta ba domin su san ba za ta gaya musu ba. Kuma ganin Baba Ɗanjuma ya shigo kuma ya wuce bangaren Inna Merin da sauri ya sa su ka san tabbas da wani abu. Kuma suna son sanin abin da ke faruwa amman ba hali ita kanta Magajiya sai tunane tunane take yi Hajiyar ne take ganin kamar ta taɓa ganin ta sai dai ta rasa in da ta santa amman acikin ranta tana tunanin kamar akwai wani abu daya danganci zuwan da yarinyar nan mai aiki a gidan tibi ta yi, jikinta na bata kamar taron ya na da alaqa da ita.


Cikin girma da arziki Hajiya suka gaisa da Baba Ɗanjuma yana zauna a kasa kusa da Inna Meri Mommy ma ta sauko ƙasa ta zauna lokaci ɗaya ta gyara zama Inna Meri ce ta faɗa masa matar Marigayi ce shima nan take ya yi mata gaisuwa ta amsa kafin ta ɗora da faɗin" Bisa abin da ya faru shekarun da su ka gabata ne tsakanin yaron ku da ƴar mu Mimi wanda har ya jawo rashin fahimta abubuwa suka faru da ba su yi ma kowa daɗi ba, dalilin haka ya sa sai zumunci ma ya yanke gabaɗaya, saboda kalaman major a kan yaron wajen ku sai dai wallahi tallahi kun ji rantsuwan Musulami Habibi ya rasu ana gobe za mu zo Gambe da niyar ya zo ya baku hakuri ya kuma jemi gafaran Mansoor sai dai Ubangiji bai amince ba yana gangaran mutuwa yana jaddamin wasiyar na nema masa gafara a wajen sa daku iyayensa shi ne naga ya dace na tako da kafata na zo na wakilce sa don girman Allah ku yi hakuri, ku yafe abunda ya faru kuskure ne kuma kowani ɗan adam ba ya wuce kuskuren sa domin tara yake ba mu cika goma ba. Ku duba Allah ku yafe masa tunda ba shi a duniya nan kuma kafin rasuwarsa ya yi nadama matuka har ya so ya nemi gafaran abin da ya faru da kansa."
Mommy ta dakata tana sharan ƙwalla da gefen mayafinta kafin ta cigaba da faɗin.


"Habiba ya cika a gabana sannan da Mimi a bakinsa ku yi hakuri ku yafe masa."


Baba Ɗanjuma ya yi saurin tare ta da faɗin"Haba Hajiya ki daina kuka, wallahi ba komai tun a lokacin mu ba mu riƙe ku a ranmu ba mun yafe Allah ya yafe mana gabaɗaya, shi kuma Allah ya jiƙan sa da rahma ya sa ya huta."
Gabaɗaya su ka amsa da Amin Inna Meri Ta ce"Ai na gaya ma Hajiya tuni wannan ya wuce a wajen mu tuntuni."
Baba Ɗanjuma Ya ce"Kwarai ma kuwa kuskure duka aka samu tun a wancan lokacin, rayuwar duka nawa take ma Allah na tuba? Allah dai ya sa mu dace ko da ba ku zo ba ma Hajiya babu komai."
Hajiya tace"Hakane mun gode kwarai Allah ya bar zumunci Amin."
Mommy kuma kanta na ƙasa Ta ce" Ina son ganin Mansoor domin shima na bashi hakuri." Inna Meri tabce" Yana hanya zai zo in sha Allahu."


Sun yi shuru na wani lokaci sai Baba Ɗanjuma ya miƙe da niyar fita sai Hajiya ta kira shi ya dawo ya zauna.
Mommy ta kallah ta ga kuka take yi sai ta girgiza kai kafin ta ce"Meri tun kwanaki na faɗa miki kafin rasuwar Kabiru ya janye kalamansa kan Mimi ya ce ya amince in har ta na son Mansoor to a aura mata shi saboda farincikinta"
Inna Meri ta yi shuru kafin Ta ce"E, kuma ai tun a lokacin na gaya miki ni ba ni da matsala, in ma da matsala yana wajen Baban inna ne"
Baba Ɗanjuma Ya ce"Gasikiya sai dai a jira a ji ta bakinsa ko ba haka ba Hajiya?
Hajiya tace to shike nan sai a jira ɗin, nan Hajiya ta cigaba da ga ya musu saboda Mansoor har yau Mimi ta kasa kula kowa kuma har gobe yana ranta shi take so farincikinta na tare da Mansoor.
Inna Meri ta yi shuru ba ta yi mgana ba domin ta san halin abin da ta haifa shi kuma Baba Ɗamjuma kai tsaye Ya ce"Dama mu ba muki ta ba, matsalan daga bangaren kune amman tunda ku da kanku kun amince sai ayi mgana da shi Mansoor ɗin sai muji ko yana ra'ayinta har yanzu, mu namu fatan alheri ne kawai."


"Assalamu Alakaimu."


Muryan Mansoor ta katse Baba Ɗajuma da zence da ya kwararo, gabaɗayansu suka ɗaga kai ya na tsaye a kofar ɗakin bayan ya ɗaga labulen ɗakin, sai dai fuskokin da ya gani ne ya sa bai shigo ba.
Biri daman ai ya yi kama da mutum, ya ga mota a kofar gida sannan ya shigo ya ga su Magajiya na binsa da wani kallo ya zo kuma ya yi mummunan gani. Da ga Hajiyar har Mommy ba wacce bai gane ba, shi ya sa ya wani ƙara haɗe rai kamar an aiko masa da sakon mutuwa. Ƙokarin ma komawa da baya ya ke yi Baba Ɗanjuma ya kira sunanshi ya amsa ya kuma ba shi Umarnin Shigowa.


Kamar ma ba zai shigo ba ya na ta tukubiri ya cire takalmin kafarsa ya shigo daga barci ya tashi daga shi sai jallabiya mai ruwan kasa da dogon wando. A kofar ɗakin ya durkusa yana gaida su Inna da kwana bangaren su Hajiya kuma ko kallo kamar ya ga kashi. Su kuma suna ta kallonsa da mamakin sauyawarsa ya kara girma fiye da tunaninsu Hajiya ma ta fi mamakinsa duk ko a baya ta san shi da tsawo amman bai kai haka buɗewa da kiba ba, ita kuma Mommy daman ba wani ganinsa ta yi sama da sau uku ba, ta dai san ya samu bambamci mai yawa tsakanin baya da yanzu.


Inna Meri ce ta kalle shi kafin Ta ce"Ba ka ga baƙi bane? Ko ba ka gane su ba ne?
Kai tsaye ya ce"Na gansu Inna, kuma na gane su." Ya faɗa cikin saka mamaki a cikin ganin nasu a gidansu kafin ya cigaba da faɗin"Naga kakar Mimi naga mahaifiyarta abun mamaki me ya kawo su? ko sun manta cewa babu sauran wata alaqa a tsakaninmu ne?
Ya faɗaa ya na mai kallon fuskokinsu ɗaya bayan ɗaya sai kuma a cikin su aka rasa wanda zai fara magana daga Hajiyar har Mommy ya yi musu ƙwarjini.
Sai Baba Ɗanjuma aka bari da rattaba masa bayanin da Mommy ta yi musu bai ko gama saurara ba ya kausasa murya Ya ce.


"Baba."


"Baba."


Baba Ɗanjuma ya amsa da na'am domin shi kanshi yasan akwai rigima. Cikin shan alwashi ya cigaba da faɗin" Na rantse da wanda raina ke hannunsa ba zan iya yafe masa. Shari'a da ni da shi sai a gaban Ubangiji." Ya karishe faɗa ya na jin wani irin nauyi acikin ƙirjinsa an ma raina masa wayau bayan an gama tozarta shi an lalata masa rayuwa shi ne za'a zo ana gaya masa mganar banza.
Uban kuturu to ya yi kaɗan ma yana jin Hajiya ta fara masa nasiha tana faɗin "Shi kabirun ma ya rasu ba za ka yi hakuri ba?
Kai tsaye Ya ce"Kowani mai rai ai mamaci ne, nima wata rana zan mutu za muje gaban Ubangijin da ya yi talaka da mai kuɗi a gabansa sai ya fitar min da haƙƙina"
Daga nan sai jikinsu ya yi Sanyi Mommy na jin haka sai ta fashe da kuka tana faɗin"Wlh ya yi nadama don Allah ka bar komai ya wuce." Kamar a fusace Ya ce" Ba komai ba ne ballantana na bar shi ya wuce, rayuwata gabaɗaya ne aka lalatamin kinga kuwa ba kamar a bar shi ya wuce ba ne. Akwai hisabi tsakanina da wannan mutumin kuma yadda ya sha alwshin yarsa ta fi karfina nima yanzu na fi karfinta da duk abin da ya ke takaman tana da shi."


Hajiya ta ce"Ka yi hakuri ba laifin Binta ba ne, har gobe tana sonka ka amince ka aureta sai ku manta baya ku fuskanci gaba."


"Ni ba ni da kudin auranta. Har yanzu ni talaka ne, sannan mahaifina har ya mutu a kauye ne kuma har gobe ni agola ne a gidan nan kinga kuwa har gobe ban chanchanta ba."


Ya ba ma Hajiya amsarta sai su ka kasa mgana Baba Damjuma ne ya ce" Mansoor ka yi hakuri ka ji ko! Ko Allah muna yi masa laifi ya yafe mana."
Inna Meri ta amsa da cewa"Kuma ba'a son kafiya ba a son a yi ta ba ma musulmi hakuri ya nuna kafiyarsa."
Kansa na kasa ya na jin wani iri zuciyarsa na wani irin zafi sai yaji kamar a yanzu komai ke faruwa. Taruwa suka yi da na su iyayen da na shi suna ta ba shi mgana.
Mommy na kukan ta na fadin farincikin Mimi ya na tare da shi ne ya taimaka mata don Allah. Inna Meri na ta faman fadin ya Sausaauta ma kamsa in kuma ya ciza ya hura saboda kada ya zo ya yi nadama.


"Inna na yi rantsuwa, kina so na yi azumin kaffara ne?


Ya faɗa yana kokarin saka wani tunani acikin ranshi, shi ya kasa ma sarrafa yanayin da yake ciki a lokacin Mommy kuma ta tare shi da faɗin"Shima har azumin kaffaran ya so ya yi Allah bai amince ba."
Mirmishi ya yi mirmishin da ko inna da Baba sun jima ba su gan shi cikin wannan Mirmishin ba.


"Na amince zan yi azumin kaffara a kanta, zan aure ta."


Hajiya da Mommy su ka haɗa baki wajen fadin"Alhamdulillah."
Inna Meri kuma kallonsa take yi domin a jikinta taji ba ta yarda da maganarsa ba.
Baba Damjuma kuma na ta saka albarka ya na fadi "Ko kai fa? Ai gwara ka manta komai." Mommy ta rike Hannun Hajiya tana fadin"Habibi zai yi farinciki yau ya ga Mimi ta samu abin da take so."


Munafukin mirmishi ya yi kafin ya ce"Kafin nan ina da wasu sharuɗɗa guda huɗu, biyu zan faɗe su kafin aure. Biyu kuma zan kafa su bayan auran."
Ba tare da tunanin komai ba Mommy ta ce ba komai sun amince nan take Aji y ace zai tura ma Mimi sharudɗan ta wayarta da amincewarta zai yi amfani daga nan ya tashi ya fice kuma bai nuna alamun wasa yake yi ba kuma bai nuna alamun ya yafe ba.


Inna Meri sai ta rasa gane in da ya dosa a jikinta taji kamar ya na shirya wani abu.
Hajiya da Mommy suna ta godiya,Inna Meri ta rakasu har wajen mota jikinta duk ya yi sanyi Magajiya da su Gaje kamar za su rasu saboda son jin gulma ai tunda suka ga Mansoor suka san babban abu ne ke faruwa ita kuma magajiya ta so ta gane Hajiya Shiyasa Inna Meri na dawowa daga rakasu ta tare ta da Fadin"Ikon Allah wannan kamar Hajiyar da kika yi aiki a gidanta ko?
Inna Meri ba ta iya karya ba sai tace mata Eh ita ce. Daga haka ta wuce bangarenta Magajiya ta yi wani munafukin dariya kafin ta ce"A yi dai mu gani."
Gaje kuma fadi take yi"Kwanaki yar ta zo yau kuma kakar da kanta anya lafiya kuwa?
Harira ta ce"Da fa wata mgana, duk boyen su dai ai za ta bayyana har mu sani."
Duk Inna Meri na bangaranta ta na jinsu ta ma rasa abunda ke yi mata daɗi.
Baban Inna yafi ba ta mamaki wai ya amince cikin sauki haka?.
Ko da ta san shima ya na sonta ba ta ɗauka lamarin na shi zai zo da sauki haka ba.
Baba Danjuma daganan masallaci ya tafi saboda ana ta kiran sallah itama daga wajen ta ɗauro alwala ta shiga daki ta yi nata sallar.


*****


Mimi ta dawo wajen aiki ta ga Hajiya da Mommy ba sa gidan da ta yi ma baaba uwani mgana sai ta ce sun fita har ga Allah ta ɗauka suna gidan Daddy ne yasa ba ta Damu ba. Sai kawai ta kwabe kaya zafi ya isheta ta koma ta kwanta tana duba wayarta kuma Hoton Aji ta ke kallo har barci ya ɗauketa. Sai da taji muryan Mommy na kiran sunanta sannan ta farka.
Ta ga Mommy na ta fara'a amman ba ta ɗauka wani abu ne ya faru ba.
Ce mata ta yi ta tashi ta yi sallah tana tashi ta shiga tiolet wajen Mommy ta gyara mata wayarta sai ta ga Hoton da take kallo tunda wayar nata ba tsaro.
Mirmishi ta yi kafin ta ce afili"Kin kusa samun abin da kike so ƴata."
Daga haka ta ijiye mata wayarta ta fita zuwa ɗakin da ta sauka itama kwabe kaya tayi sai da ta yi wanka sannan ta yi sallah.


Dukkansu suka hadu afalo su ka ci abinci har da Mimi sai bayan sun gama ne Mimi ta kalle su kafin ta ce"Mommy ina kuka je ne?
Mommy ta yi mirmishi kafin ta ce"Gidan surukan ki mana"
Cikin mamaki Mimi tace"Gidan surukai na kuma? Ta faɗa da sigan tambaya.
Mommy ta kalli Hajiya suka yi dariya kafin Hajiya ta maida kallonta wajen Mimi dake musu kallon tuhuma da mamaki.
Cikin tausasa murya Hajiya ta ce" Eh mana mun je neman gafara abin da ya faru ne a baya." Mimi ta yi wani iri da fuska kafin tace"Ban gane ba"
Saboda ita dai ba ta san da mganar ba.


Nan Hajiya ta zayyana mata komai sai ta tuna lokacin rasuwar Abi Mommy ta yi ta jadadda cewa kafin rasuwar Abi ya so ya zo gombe ya nemi gafaran Hajiya ashe ciki har da Ajinta a ranta sai taji wani irin sanyi da Sauri tace"To shi ya ce yafe din Hajiya?
Hajiya tace"Bai yi mgana ba amman mun fahimci yafiyar sa tunda ya karɓi tayin mu ya amince zai AURE KI.!"
Mimi ta waro ido cikin mamaki kafin tace"Aure kuma?
Cikin

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login