Showing 3001 words to 6000 words out of 103785 words
shi ganin har ya fara tafiya.
"Aji.."
"Coach.."
Ya faɗa lokaci ɗaya yana juyowa, kara kallon hanya Coach ya yi ya ga tafiya mai nisa kafin cikin gari kafin ya maida kallonsa kan Aji cikin lallashi ya ce"Kasan da wahala ka samun abun hawa zuwa cikin gari ko?
"Kafata fa? Miye amfanin ta?
Kai tsaye ya bashi amsar da haka, sannan bai tsaya ba ya juya ya cigaba da tafiya hannunsa daya rataye da jakarsa ɗayan kuma na cikin aljihun wandonsa, yana wannan tafiyar ta sa ta sassarfa ta cikakkun maza masu karfi da kuzari daga yanayin tafiyarsa zaka fahimci yana da zafin nama Zafzaf kamar wani ingarman doki.
Ɗan kwallo ne fa, har za'a nuna masa zafin nqma shi da jikinsa ya gini da komai cikin hanzari. Yana cikin tafiya motar ta zo ta wuce sa yana jin su Musa sun karaɗe da kiran sunan "Captain.."
Ya kuma gan su suna ɗagamai hannu, ammh ko yunkuramin maida musu martani bai yi ba, sai ma cigaba da tafiyarsa da yake yi, yana jin wani irin zafi a karkashin zuciyarsa kishin wani abu mai muhimmanci zai iya sarke masa numfashi in ya cigaba da zama acikin motar nan fitarsa shi ne mafita, adaidaita suna ta tsaya masa ammh bai tsaya ba tafiya kawai yake yi ba tare da ya gaji ba.
Da tafiyar ma taki masa sai ya koma gudu abinsa a saman hanya, zufa ta jika masa rigar jikinsa haka ta ke tsiyayo masa ta saman fuska, ammh bai dakata ba yana wannan gudun yana jin radaɗin dake cikin zuciyarsa yana raguwa tun daga farkon gari da kafarsa ya taka har anguwarsu ta arawa, sai anan ne ya samu abun hawa ya hau zuwa gidansa da ke tunfure, saboda baya so wani daga gidansu su ganshi labari ya kai kunnen Innar mu'azzam ko kuma ya haɗu da Baba.
A bakin kofar gidansa aka sauke shi ya fito da wallet ɗinsa daga cikin aljihunsa ya mika masa 500 ya juya mai adaidaitan na faɗin "Yallaɓai ga chanjin ka."
Ba juyo ba ya ce"Ka rike chanjin"
Maidaidaita ya fara godiya shi dai bai ko Juyo ba, ya lalubo key din gidansa na karamar Kofa get ɗin milk, ajikin jakar da ke hannunsa ya buɗe gidan.
Ya shiga ya kuma rufe ta ciki, daga waje sai ka raina gidan sai ka shiga zaka fahimci ma mallakin gida baya bukatar kyan gida ta waje ta ciki an zuba aiki na kwararrun magina sannan shi kuma mai gidan ya saki kuɗi.
Gidan akwai fili sosai domin ga wata bakar 4matic nan a haraban gidan sai kuma mashin shima roba roba fara fake a wajen.
Ko da ya isa gabaɗaya jikinsa sharkaf da zuba, Kofar falon ya isa ya saka kafa ya turata sai ta buɗe daman ba a kulleta da makulli ba. Falo ne mai girma ba sosai ba, ba kujeru sai cafet babba da ya malale falon sai Plasma(tv) babba na bango sai dakuna jere guda huɗu rufe suke da Kofofi na farko na ga ya nufa ya saka hannu ya buɗe ya shiga ciki ya rufe.
Shuɗewar nintina talatin sai gashi ya fito ya sauya kayan Jikinsa da alamun har wanka ya yi, tunda ga gashin kansa nan da sanyin ruwa sanye yake da wando three quater, sai farar singileti sai alokacin fuskarsa ta bayyana tarwai.
Baƙi ne shi, mai murɗewan jiki Kana ganinsa ka ga bafullatani ko daga yanayin rsawonsa da Baƙin gashin kansa mai santsi, har ta gashin giransa da na Idanuwansa suna sheki ga shi baki silik, ba shi da saje sai da daga kasan gemunsa yana da gemu kaɗan da ya fito masa shima baki silif da shi gwanin ban sha'awa. Sannan yana cikar sumar kai, mai yawa baƙi silik da ke shan gyara sosai.
Yana da faɗi daga saman sa jikinsa kuma duk a murɗe ne sakamakon training.
baƙinsa mai kyau ne tunda har shining ya ke yi, idanuwansa matsakai ta ne, sai dai yana da karan hanci dogo da bakinsa dai dai misali.
Ƙaramin firizan dake falon ya je ya buɗe ya ɗauki ruwan gora ya kafa kai yasha fin rabi, sai ya rufe firizan ya kuma ijiye ruwan a saman firizan ya Juya yana tafiyarsa na zafzaf ya koma cikin ɗakin da ya fito.
Ya jima aciki kafin ya sake fitowa wannan karon hannunsa ɗauke da wayarsa ya fito ɗayan kuma hannunsa ɗauke da kujera fara ta roba, ya zo ya kafata acikin falon ya zauna yana harɗe kafafunsa waje ɗaya.
Tun yana salla ya ji ana ta kiran wayarsa, tunda ya ji kiran yaƙi ya kare ya zargi mutane guda biyu
Ko Bintu ko Mu'azzam.
Sune suke yi masa mahaukacin kira rututu ko bai so ba sai ya ɗauka in bai ɗuka ba, ba za kuma su fasa kiran ba.
Wannan karon ba Bintu ba ne ɗaan uwanta ne Mu'azzam, sai da yaga kiransa sannan ya tuna ya ce masa sun zo kano buga wasa, kenan yana can yana tunanin in sun gama buga wasa zai shigo wajensa.
Shuru ya yi yana wani tunani, Mu'azzam kamar mai hankali kamar kuma ya girma ammh bai daina abun yarinta ba, shi fa bai ce masa zai zo ba ballantana ya ce yana jiransa ne, kawai daga sun je buga wasa sai a ga ya ce za shi wani waje? Kamar wani yaro ƙarami.
Yana wannan tunanin kiran Mu'azzam GADDAFI DANJUMA ya shigo cikin wayarsa kamar yadda ya yi masa Saving.
Sai da ta kusa katsewa ya ɗaga kiran bai yi mgana ba.
Dagacan bangaram Mu'azzam ya ce"Kana ina ne? Ai kace min tun a jiya za ku gama wasan ko?
Sai da ya lumshe ido sannan ya buɗe kafin cikin muryansa ta kai tsaye ya ce"Eh mun gama.," Mu'azzam yace"Suwa suka ci?
Kai tsaye ya ce"An ci masu gida."
Mu'azzam ya ce"Good Ajin Jihata nasan za ka yi musu cin cikin gida ne."
Mirmishi ya yi ba tare da ya yi mgana,
Mu'azzam ya ce"Yaushe za ka taho?
Yau saboda kai na dawo daga office da wuri fa"
Daman yasan za'a rina cikin dakushe muryansa ya ce"Na taho ina? daman nace maka zan zo ne?
Da sauri Mu'azzam ya ce"Ban gane ba? Kana ina ne?
Kai tsaye ya ce"Ina gida"
Mu'azzam baki ya saki kafin ya ce"Wani gida kuma?
Aji ya ce"Wani gida gare ni?
Mu'azzam ya ce"Mallam sidi ko anguwan Arawa ko Tunfure?
Cikin Kosawa ya ce"Mallam Sidi tushe na ne, anguwan Arawa kuma nan ne gidanmu, Tunfere kuma muhallina ne, ina Tunfere yanzu haka."
Cikin ƙarin Mamaki Mu'azzam yace"What! Gombe?
Sai ya juya yana kallon matarsa Hibba tana ta kai da kawo tsakanin Kitchen da falo domin shiryama ɗan uwansa abincin tarba ammh wai yana faɗa masa yana Gombe.
cikin jin haushi ya kira sunanshi.
"MANSOOR..!"
"MU'AZZAM.!"
Shima ya ambaci sunan shi, cikin takaici Mu'azzam ya ce"Tun safe da na faɗa ma Hibblove za ka zo wlh ta kasa zama waje ɗaya tayi maka girke girke yafi kala uku, akwai sarewa na faɗ mata ba za ka zo ba? ya za ta ji? Kuma don Allah ya kake son mu yi da abincin?
Kai tsaye ya ce"Ku yi ta ci har sai kun gaji, ni ban ce maka zan zo ba, faɗa maka kawai na yi mun shigo kano buga wasa, wa ya ce ka je ka faɗa ma matarka na ce zan zo? Mun yi haka dakai tsakanin ka da Allah Mu'azzam? sai Mu'azzam ya kasa mgana cikin ajiyar zuciya ya ce.
"Baban Inna."
"Ɗan inna."
Shima ya maida masa, daga haka Mu'azzam ya saki huci kafin ya ce"Ai shike nan." Sai kuma suka katse kiran a tare, mirmishin gefen baki ya yi kafin ya jinjina kai yasan yanzu za'a kai ƙaransa wajen Inna , yau in ya je anguwan Arawa ya san zai sha faɗan bai kyauta tunda bai je ya ga Mu'azzam ba.
Har zai sauke wayar sai kuma wani tunani ya faɗo masa da sauri ya kunna data ya shiga Facebook searching ya shiga ya saka sunan Karamci Tv.
Sai ga jerin shirye shiryensu ya bayyana, da ga vadion ma kafin ya shiga fuskarta ne cikin mirmishi tare da loɓawar dimple ɗinta Daga kasa ya ga daga ɗora vadeo 1hr ago har an masu kallo 2k comment kuma 1k.
Ƙankancewa Idanuwansa suka yi, ƙaramin tsaki ya ja kafin ya fita daga wajen gabaɗaya, ya koma ya na hura iska daga cikin bakinsa, sai ya ji kamar cikinsa ya ɗauki zafi rau ita kanta isar bakin nasa ma zafi take fitarwa.
Duk iya ƙokarinsa na kar ya kara komawa sai da ya kara shiga ya kuma danna hannunsa ya yi cliking ɗin vedeo.
Daman suna ɗora duka shirye shiryensu ta shafinsu dake facebook wato karamci Tv.
Tausayi ne ya kaishi ko nace rabon yau ya yi kwanan bacin rai da bakinciki, fuskar ta tar take kamar ko yaushe babban abun jan hankali daga gareta zaƙin muryanta.
Iya tsara kwalliya da shiga mai kyau da tsari yanzu ɗin ma wani leshi ne ajikinta mai kalan blue mai duhu da pich, ta yi ɗinkin doguwar riga fitted ta saka mayafi pich mai raga raga na ya yi, sai kuma ɗaurinta mai taken Zahra Buhari, kunnuwanta da hannayenta gold ne hatta ko zabban hannunta ta yi ƙayatacciyar kwalliyarta ta saka kalan jan bakin da ta ke yawan Amfani da shi mai kalan kalan deep blue ja ja kuma, in ta yi dariya sai fararen hakoranta su kara haska kyakyawan farar fuskarta su bayyana tare da hakorin makkanta shima yana kyalli sai ya kara mata kyau da kwarjini.
Fatima Mimi kyakyawa ce ajin farko acikin mata, daga saman kanta kwantattacen gashi da kana gani zaka fahimci tana da sumar cikar gashi.
Hancinta dogo da ƙaramin bakinta wanda saman ya yi tudu kaɗan ga cikar naman lebe, sannan fuskarta tana da ɗan faɗi kaɗan ƙaramin jiki gareta da ya dace da kyakyawan suranta.
Shekarunta ya fi ba ma mutane mamaki, ammh tarihinta bai ba su mamaki ba saboda daga ganinta yar manyan mutane ce, ko daga yanayin shigarta da yadda take hawa kaya masu tsada da yarari.
Tsabar yadda ya ke jin zuciyarsa na wani fat! fat! Kamar zata faso kirjinsa ta fito ya sa ya sauka daga vadeon sai dai rawan da hannunsa ke yi ne ya sa ya faɗa comments section bai sani ba, nan ya ga abin da ya kusa tarwatsa masa tunani da zuciyarsa gabaɗaya.
"Adadin mutane nawa ne suke kallonta?
"Maza nawa ne suke jin ta na burgesu?
"Maza nawa take ba ma sha'awa? Maza nawa take ɗaukan hankalinsu da kyan suranta da kwalliyarta?
Tambayoyin da suka cika masa zuciya kenan, lokacin da ya ga comments ɗin maza rututu.
Yawanci suna faɗin jikinta ya ɓoye shekarunta, sai masu faɗin.
"Mimi mai kyau ki na burgemu"
"Dimple bbym Tauraruwar karamchi"
"Ni dai ina son ki Hajiya Mimi, kin iya kwalliya da ado."
"Ni kuma ina son yanayin turancin ki, zaƙin muryan ki na tafiya damu."
"Ina son dariyan ki Mimi,kin haɗu kin haɗu kin ga ji da haɗuwa."
Gabaɗaya sai yaji jikinsa na rawa jiyoyin kansa suka mike raɗau zufa kawai ke keto masa kamar an watsa masa ruwa, ya dunkule hannunsa na hagu ya ɗaga zai naushi fuskar wayarsa sai wata zuciyr ta ce" Mansoor kana da dalilin yin hakan ne?
Ka manta sharaɗin da iyakar dake tsakanin ka da ita? In ma maza dubu ne zata burge su ji sha'awarta bai kamata ya dame ka ba"
Sai kawai ya koma ya sauke hannunsa ya na sakin huci a fili ya furta."Hakane bai kamata na damu ba, ita ɗin banza ta je ko mazan duniya za ta aura ma bazai damu MANSOOR AJI ba, ba zai dame ni ba."
Ya ke faɗa yana kara ma kansa karfin gwiwa, dalilin da yasa wayarsa bata sha naushi ba kenan, sai ma tashi da ya yi ya koma ciki.
Bedroom ne mai ɗauke da cafet da katifa sai kuma hanger mai Dlɗauke da kayansa na sawa, sai takalma ga su nan zube a gefen dakin duk an warwarsa su.
Kwanciya ya yi saman katifar kwanciyar sama ya hard'e hannayensa yana kallon rufin ɗakin wayarsa kuma ya kasheta gabaɗaya.
Vya daɗe yana kwance kafin ya samu barci sai bayan la'asar ya tashi ya yi sallah key ɗn motarsa ya ɗauka ya fita. Sai da ya buɗe get din ya fita da motar sannan ya dawo ya rufe ya koma ya shiga motarsa ya fita.
Abinci ya je restaurant ya siyo da ruwa da lemun maltina kowanne katan, dag anan gida ya dawo ya ci abincin. Farar shinkafa da miyan naman rago. Bayan ya natsa anan tsakiyar falon ya fara training ɗin sa.
Yana sama ya na kasa zufa ya ke yi ammh bai dakata ba har aka kira sallar mangariba.
Sannan ya tsaya ya koma ɗaki ya yi alwala ya sauya kaya zuwa manya kaya na shadda mai ruwan kasa harda hula saboda ya rufe sumar kansa tabbas in Baba ya ganshi da sumar nan sai ya yi masa faɗan rashin yin aski.
A mashin wannan karon ya bar gidan sai anguwam Arawa, a masallacin layinsu ya tsaya ya yi mangariba.
A masallacin ya haɗu da su Baba ɗanlami da Baba Sani. Sun rigashi fita daga waje shi kuma sai da ya gama addu'o'in shi sannan ya fito.
Daga nesa ya hangesu tun da akwai hasken inji a bakin masallaci.
Shi kuma yana fitowa matasan anguwan suka yayyameshi suna masa kirari da sunansa.
Wato Ajin jihata.
Shi kuma ya ba su hannu suna musabaha, suna mgana sai da ya yi mirmishi kuɗi ya lalubo aljihunsa ya diɓo baisan adadin su ba, ya mika ga wani daga cikinsu ya ce su raba a tsakaninsu.
Suka saki Ihu suna faɗin"Allah ya taimaki Ajin jiharmu da ikon Allah sai ka ɗauko mana Kofin duniya."
Mirmishi kawai ya yi musu ya wuce zuwa in da ya kafe mashin ɗinsa, kusa da mashin din su Baba Ɗanlami ke tsaye suna kuskus.
Suna ganinsa suka fara washe masa baki suna fad'in"A'a Mansoor ne an dawo garin kenan?
Baba Sani ke wannan rawan bakin mganar kallo ɗaya ya yi masu kawai sai ya ɗaaga musu hannu yana Fadin"Barkan ku da dare" Daga haka ya hau mashin ɗin sa ya tada kuma ya bar wajen da sauri.
Baba Ɗanlami ya rike baki yana kallon kaninsa Muhammad Sani.
Kafin ya yi mgana Baba Sani ya kaɗa kai ya ce"Eh lalle wato dai shi wannan Agolan yaron bazai taɓa sauya halinsa ba ko?
Baba D'anlami ya ce"Uhm ka gani dai, yaron nan fa ya raina mu ba mu ci darajan ya zo gabanmu ya gaishemu ba sai dai kawai ya ɗaga mana hannu yana faɗin barkan ku da dare kaamar wasu sa'aninsa"
Ya karishe faɗa yana kwaikwayon yadda Mansoor ya yi musu mgana.
Baba sani ya ji ciwon abu fiye da kullum maganar gaisuwa ba ta dameshi ba daman ai sun saba in dai yaron nan ne bazai taɓa ganinka ya ce maka ina yini ba? Sai dai barka da safiya in da safe ne in kuma da rana ne yace barka da rana.
In kuma da yammah ne yace barka da yammah in dare ne yace barka da dare.
Ba za ka taɓa cin darajan ya ce maka ina yini baba wanne ba? Ai shi bai san wannan tarbiyan ba, ko yara ne suka ce masa ina yini? Sai dai yace barka yaro kamar ya gagari kowa. Shi abin da yafi damunshi suna ganin shi su san za su samu kuɗi sun tsaya ya zo su yi masa maula susan in ya tashi ba ka kuɗi ba kaɗan ya ke ba ka ba babbar kyauta yake yi shi.
Baba Ɗanlami ne ya katse shi da faɗin"Kuma duk Yaya Ɗanjuma ne ya sangarta yaron nan komai akace ya yi sai ya ce ayi hakuri maraya ne, amana ne a hannuna ku tayani rike amanar yaron nan Sani don Allah."
Baba Ɗanlami ke mgana yana ƙwaikwayon mganar yayan nasu Ɗanjuma.
Baba sani ya yi ajiyar zuciya kafin ya ce"Ai fa ga shi nan Agola yazo yafi masu gida arziki da samun ɗaukaka, kaf ƴaƴanmu ba wanda ya kai yaron nan nan samun duniya." Baba Ɗanlami ya ce"Kai ina rabaka an ce Ƴan ƙwallo kudi suke samu mahaukata ma kuwa, kai daga yanayin gyaran da ya yi ma gidanmu zaka fahimci yana da kuɗi ga yadda ya gyara ma Meri ɗakinta kamar na wata yar boko, ni fa Auwalu ke gayamin a kungiyar da yake buga kwallo shi ne shugabansu ko Kaftin ne ake kiranshi da turanci na dai manta, ammh maganar gaskiya yaro nan ya sha kwana shi ya sa ya ke mana kallon haɗaarin kaji."
Baba Ɗanlami ya ja gauran numfashi kafin ya ce"Mu tafi gidan Sani, duk tsiyarsa bai isa ya sallami Yaya Ɗanjuma mu bai sallame mu ba"
Baba sani yace"Kwarai kuwa."
Haka suka jera suna tafe suna mganganganu Baba sani faɗi yake yi"Har Yaya Danjuma in ka lura ya fara famkama a anguwa shi wai adole Agolan da ya rike ya samu duniya, ba ka ga ko wamzanci yanzu baya zuwa ba sai da ya yi mana mgana ba."
Ɗablami yace"Wlh na lura ko jiya sai da muka yi mgana da Gaje ta ce sai fankama yaya Danjuma yake yi, Meri kuma daman kasan halinta dariyan hakori ita a dole ɗanta ne mai arziki a gidan Wanzamai gabaɗaya."
"Ka daina fa danganta shi da gidan Wanzamai, ka ce Agolan gidan wanzamai kuma bai fi ƴayanmu ba sa'an rayuwa kawai ya samu su ba su samu ba, ni fa kamar na ce ko Yaya Danjuma na shige shige ne, ka duba fa duka ya'yansa sun samu duniya yanzu Mu'azzam fa babban Ɗan sanda ne yana kano in ya tashi zuwa kaga motar da yake zuwa da ita da shi da matarsa da ɗansu gwanin sha'awa ga kayan abinci da yake zuwa da shi cikin alfahari Meri ke rabawa sasa sasa ita adole ya'yanta masu arziki."
Baba sani ya faɗa bayan ya katse Baba ɗanlami.
Dukkansu a tare suka kalli juna kafin su ja gwaron numfashi.
Suka cigaba da tafiya da sauri sauri suna kuma tafe suna zagin Yaya Ɗanjuma da matarsa Meri da ya'yanasu Mansoor da Mu'azzam.
****
Har cikin gida ya shiga da mashin ɗin sa Mariya na cikin ɗakin Magajiya taji karan mashin da sauri ta fito da ya ke Sashen magajiya ke Farko kafin