Showing 54001 words to 57000 words out of 103785 words

Chapter 19 - IDAN AN CIZA..! Part 1 Complete by Janafty.txt

Janafty   

20 Dec 2024

4811

maka na ka ba watarana bayan kasa ta shafe idanuwanka ba.


Ba ta yanke hukunci ba sai da ta yi shawara da yalwa ita kuma sai ta yi mgana sauran ƙannen Ibrahim wanda acikin su ashe akwai wanda ya so ya auereta sai bai furta ba ganin kamar Inna Meri ta nuna ra'ayinta a kan Ɗanjuma saboda rike marayu sai ba su hanata ba saboda in dai kyawun hali ne da hakuri da kawaici da sanin ya kamata Danjuma ya cancanta tunda sun san shi tun ya na matashinsa kuma gidansu babban gida ne mai kunshe da tarihi. Sai su ka ba ta damar ta yi zaɓi cikin guda biyu ko kanin ibrahimu mai suna Muftahu ko Ɗanjuma ita kuma sai ta bar ma Allah zaɓinsa sai taji tafi natsuwa da auran babba wanda ya mallaki hankalinsa kansa tunda a lokacin Muftahu saurayi ne bai taɓa aure ba, ƙannen nasa maza uku ne Karimu ne babba sai yakubu yalwa sai muftahu shine ƙaramin su daman Ibarahimu ne babban su. Karimu ne ya yi aure da matarsa acikin gida yalwa ma ta yi aure nan makota da su, sai yakubu da shi ba agarin yake kasuwanci ba yana garin bauchi ne kuma shi bai wani damu da zumunci ba sai ya jima bai zo garin ba. Ita kuma Inna Meri sai ta yi duba da gwara ta auri Ɗanjuma ko bakomai Allah zai ba ta ladan rike marayun da suka rasa uwa a ƙananun shekarunsu.


Lokacin da ta gaya musu zaɓinta ba wanda ya nuna bai ji daɗi ba sun yi mata fatan alheri yalwa ce ma ta yi ta kuka tana faɗin za ta yi nesa da su Inna Meri tace suna tare ina nisa tsakanin garin mallam Sidi da Gombe za ta zo itama ai nan gidansu ne zata rika zuwa ta na ganinsu tana kuma kawo musu Mnsoor. Tunda akwai kyakyawan alaaqa da fahimta a tsakaninsu shi ya sa ba za su iya raba ta da Mansoor ba amma sai dai Ɗanjuma ya ba su tabbacin shima Mansoor ɗansa ne kuma yayi alkwarin yadda suka ba shi Amana to zai kula da amanar Mansoor har karshen Numfashin sa, sun kuma aminta da shi sai suka bashi Amanar Inna Meri tare da Mansoor ba daɗewa aka yi auran Inna Meri ta bar garin Mallanm Sidi tana kuka yalwa da Marliya matar karimu suna kuka sula kuma rakata har Gombe a ɗakinta na gidan Wanzamai.


Tun a ranar sula san Meri ta shigo wata rayuwar da ba ta saba gani ba, ba wanda ya karɓe su a gidan nan sai Harira Magajiya kuwa sai bala'i ta ke yi tana zage zage tun a ranar farko Inna Meri ta san sai ta ninka hakurinta kuma ba ta damu ba tunda Danjuma ya gaya mata komai bai rufe ta ba,
Abun bakincikin su ganin Inna Meri ta zo da yaro shikenn Magajiya ta rika sakin habaicin Ɗanjuma da kwashe kwashe ya je ya kwaso wata kuma mai ɗa ta zo musu da Agola acikin gida, kafin su Yalwa su tafi sai dai suka kara jadaddama Inna Meri hakuri da kauda kai ta ce in sha Allahu zata zauna da kowa lafiya suka rabu suna kukan sabo Mansoor kuma sai jin daɗi yake yi a ganinsa kamar irin sun koma sabon gida ne sai da su yalwa za su tafi ya saka kukan sai ya bi su dakyar aka lallashe sa sai da Danjuma ya ja shi shago ya siya masa alawa sannan ya yi shuru amman ya yi ta kuka ya na numfaashin zuciya.


Inna Meri ta shaida ta bangaran Miji ta gama dace sai dai ba za a haɗa samun Ibrahimu da na Danjuma ba acan ita kaɗai ne nan kuma ga magajiya da sauran yara to abubuwan dai sai godiyar Ubangiji kawai, sannan tun ranar farko da ta shigo gidan nan take hakuri da kowa kuma ta ko yi zaman lafiya da kowa in ka yi mata sharri sai ita ta saka maka da Alheri ba mai sonta a gidan hatta kannnen Danjuma su Ɗanlami kenan Mansoor kuma sai suka sanya masa suna Agola ba acikin gida ba har a waje shi kuma sarkin zuciya ko da yaushe cikin fada suke a dake shi kuma ya fara zuciya yana cika ya na batsewa bata mgana sai dai Danjuma duk wanda ya taɓa Mansoor sai inda ƙarfinsa ya ƙare kalamansa kenan yaron nan amana ne a wajena don Allah ku tayani kula da amanarsa.
Tun daga lokacin sai suke ganin kamar ya fifita Agola sama da ƴaƴan sa na cikinsa.
Tunda sanda inna Meri ta zo gidan ya'yan magajiya uku ne, Auwalu ne babba sai Jummai sai Zuwaira ashe ma alokacin tana da wani ƙaramin ciki amman cikin yara nan ba mai kallon Mansoor a komai sai a matsayin Agola, ko waje ya fita sunan da ake kiran shi kenan tunda sun gama gayama kowa shi ba ɗan gidan su ba ne Agola ne.




Ko ya dawo da kuka lallashinsa Inna Meri take yi sai taga ya damu ba shi da wani ɗan uwa na kusa da shi, sai ta yi tunanin gwara ta yi ma Danjuma mgana ya dauko mata yaran marigayiya ta haɗa su da yaronta ta rike kila su su karɓesa a matsayin ɗan uwa.
Yana dawowa ta yi masa mgana sai ya ce daman suna ransa ita ya ke jira kada taga kamar daga zuwanta ya takura mata jin ita da kanta ta ke son a ɗaukosu sai ya ce ta shirya su tafi tare su taho da yaran nan, Haka ko akayi tare su ka je can Bolari gidan su Habiba inda yaran suke, Amina ce babba sai Halima sai ƙaramin yaron Mu'azzamu.
Ganin kirkin Inna Meri da yadda ta nuna zata rike yaran sai Mahaifiyar Habiba ta amince ta ba su yaran tun acan gidan Mansoor ya rike hannun Mu'azzam a fuskarsa kaɗai Inna Meri ta ga ya yi farinciki, sai taji daɗi acikin ranta saboda ita macece mai son yara. Ta dauko su Amina ta rumgumesu kamar itace uwarsu ba su taɓa maraicin wani abu ba, Mu'azzam kuma ya ke ganin gata saboda karami ne shi Inna Mari ta rene shi har ta sanya masa suna wato Ɗn Inna shi kuma Mansoor tana kiran shi Baban inna.


Tunda Magajiya ta ga Inna Meri na riƙe su Amina kamar ita ta haife su sai ta fara bullo da rigima yau ta ce wannan gobe ta ce wannan a irin haka ne ta tada rigima sai da aka raba girki kowacce sai ta koma yin nata saboda a zauna lafiya, Ita a tunaninta kamar Baba Ɗanjuma na cutar da ita ba ta duba da cewa Ƴan uwan Habiba na yi ma yaranta sako itama daga su Yalwa tana samun alherai ma su yawa sai take rage ma Baba Danjuma wasu hidimdimun, sai da aka raba girkin Magajiya ta gane kuranta tunda a baya da girken ke haɗe komai Meri ta barshi a na su gabadaya da aka raba kuma sai ta ja bangarenta ita da ya'yanta.
Ba ta shekara a gidan ba ta samu ciki lokacin Magajiya ta haihu an samu Namiji Saddiqu, ita kuma sai ta haifi mace aka saka mata suna Fatima suna kiranta Bintu, sai ta haɗe kan Ƴaƴanta gabaɗya saboda ba ta nuna bambamci suma kuma yaran ba su da wata uwa da ta wuce Inna Meri.


Ko can gidan kakkaninsu suka je ba su da labari sai Inna ta ma na kaza tana mana kaza sai iyayen Habiba suka samu salama da cewa su Amina sun samu wata uwar kamar Habiba sai su ma suka maida Inna Meri kamar ƴa duk wani abunda za'a yi a gidan tare da ita a ke yi sannan in yaran suka samu hutu suna zuwa can su yi musu Hutu shima Mansoor tana tura shi can wajen su yalwa ya gaishe su.
Tana da cikin walida Muftahu ya rasu har ya yi aure ba jimawa ciwon ciki shima daga dare zuwa Safe, Inna Meri ta yi kuka nata mutuwan mijin kawai take tunawa, duk da shekarun sun ja amman ta kasa mantawa, sannan ga halin rayuwar da suke ciki samun Baba Ɗanjuma ya ragu ga iyalai da hidimdumu Allah ma yasa su Amina suna samun taimako daga dangin Habiba shima Mansoor daga can mallam sidi ana yi masa saƙo Yakubu dake bauchin in ya zo can kwami yana ba da saƙon kayan sawa masu kyau sai Yalwa ta aiko yaronta da shi ko kuma ita ta zo ta kawo masa da kanta.


In kuma aka kawo kayan Mansoor zai ɗauki kaɗan sauran ya ba ma ƙaninsa Mu'azzam in Inna Meri ta ce sun yi masa yawa sai ya ce"In ya ƙara girma sai ya saka Inna." Tun suna kananunsa kaunar junnasu yake cikin jininsu duk da Mansoor ya girmi Mu'azzam kusan da shekaru biyu da wani abu, amman ji yake yi da shi kamar abokinsa duk abin da ya samu sai ya raba shi biyu ko uku ya ɗauki kashi ɗaya kashi biyu kuma yace na Mu'azzam ne.
Kuma ya na faɗa da duk wanda yace Mu'azzam ba ƙaninsa ba ne, Saboda su Jummai suna yawan gwaba masa magana da cewa Mu'azzam ba ƙaninsa ba ne shi kuma sai ya ce" ƙanina ne saboda innata take ke rike da shi, in ƙanin ku ne me ya sa magajiya ba ta rike shi ba?
Saboda fitinasarsa ya sa suke shayin masa mgana ya ga dama ka zage shi ya rama kuma ba wanda ya isa ya taɓa Mu'azzam ko a makaranta yanzu sai aga tashin hankali.
Yadda ya ke kafa kafa da shi ko su Bintu da ke mace baya yi musu irin haka Baba Ɗanjuma daɗi ya ke ji in ya ga haka sai ya ce ko bayan raina Meri Mu'azzamu da Baban Inna su ne za su rike mini iyalaina.


A can waje kuma bangaren abokai in kana son abota da Mansoor sai ka yi abota da Mu'azzam shi ya sa Mu'azzam ya taso ba shi da abokai sai abokan Mansoor, Mansoor ma ba shi da abokai sai abokan Mu'azzam an sha faɗa da tsiya sai an fara abota abu kaɗan zai haɗasu Mansoor ya watse abotan su Nasir ne abokan gasken da ko an yi faɗa bayan kwana biyu bayan an gama gaba za'a zo a shirya. Sannan islamiyar su ɗaya kuma boko ma duk tare suke sai abotan su ta jima sannan ko an yi tsiya bayan wani lokaci za'a haɗu ko da a filin kwallo ne, da farko Mu'azzam ne ya ke son ƙwallo Mansoor kuma shi kwallo ba ta gabanshi, Saboda Mu'azzam ya fara zuwa kallon ƙwallo har ya fara bugawa duk da shi ra'ayinsa in ya gama makaranta soja yake son zama shi kuma Mu'azzam ya ce yana son ya zama ɗan kwallon kafa.


Amman a fili Aji in yana buga balla sai ya baka mamaki ya ƙware in dai ya na fili sai ya buga kwallo a raga shi yasa lamba goma yake bugawa tun yana matashinsa Mu'azzam kuma dake son ƙwallon har cikin jinin jikinsa bai iya taka kwallon haka ba
Su Nasir su yi ta faɗin "Aji da za ka sanya ra'ayin ka a kwallo da kila kai ma watarana ka iya zama Ahmad musa ko mu ji ka a turai ka koma buga kwallo da irin su Muhammad sala" in suka faɗi haka sai ya gwasale su da cewa"Ina meye wani ƙwallo kuma? Malamai ni fa Soja ne, Sojan kasata in sha Allahu." Kwatan kwacin yadda Mu'azzan ke son zama ɗan kwallon kafa kwatan kwacin yadda Mansoor ke son zama Soja, kowanne bawa daman yana da na shi burin da mafarki sai dai daman ba duka mafarkan mu ke zama gaskiya ba wasu suna zama a raye wasu kuma har kuma ga Allah suna matsayin mattatu ne.


A komai na Mansoor ya sha bambam da na Mu'azzam a ra'ayi da hallaya Mansoor yana da faɗaa ga zuciya da naci sannan ga riko a cikin kwakwalwarsa har wani waje garesa na musammn kamar blacklist ko sau ɗaya wani abu ya taɓa haɗa ku to ya kulla da kai kenan har gaban Abada. Saɓaanin Mu'azzam ba ruwan shi mai hakuri ne sannan ba shi da fitina shi kuma mai son zaman lafiya ne amman Mansoor bai ƙi gayyar duk ta watse ba, Allah ya sa ma kada a zauna lafiya tun yana ƙaraminsa yan gidan wanzamai suka sa ya fahimci ba nan ne asalinsa ba saboda tun baya gane kalmar agola har ya fara sanin ma'anarta.
Yasan kan tsiyatu kala kala sannan komai na shi na daban ne, gaisawarsa ma ba irin ta kowa ba ce a cewarsa Ina yini ba gaisuwa ba ce sai dai barka da yamma ko barka da safiya in ya gaisheka a haka ruwanka ne ka amsa ko kar ka amsa shi dai ba zai ce ina yini ko ina kwana ba, shi ya sa ake ganinsa wani mara kunya kuma mara tarbiya.


Da gaske ya ci sunan shi na Aji saboda mai Ajin ne ya na da kamewa a kan karan kansa yana yin komai cikin Aji ne da isa, gaye ne da ba ya son reni ko ƙankani. Shi y ssa koda yaushe maganarsa da su Nasir su zama masu aji su rika abun masu Aji duk da yana da son shiga mutane amnan kuma ya iya miskilanci za su yi ta abubuwan su ba ya saka musu baki sai ya ce su na abu kamar marasa aji, sannan shi mai ra'ayin ya yi aure da wuri ne saboda matarsa ta rika taimaka ma Inna sannan yana so ya ga ya taso da ya'yansa kamar matsayin abokan juna sabanin Mu'azzam da yake so sai ya mallaki wani abu da zai rike kansa da iyayensa tukunnah.


Ko magana ake yi sai Mansoor ya ce shi fa yana da gadon gonaki a garin su, su zai saida in ya tashi aure, sai ake ganin kamar abun nashi wasa shirme shirme shi kuma bilhaqqi a kan gaskiyarsa yake yi.
Dukkansu wata makaranatar Gwammati ta cikin gari su ke zuwa rayuwa ta yi wahala tunda Baba Ɗanjuma girma kuma yazo, sai a hankali ba domin Inna Mari macece mai tsayawa ga kanta ba da ai tuni rayuwarsu Mu'azzam ta jima da sauyawa sannan kuma tana samun taimako daga bangarori da dama ko daga can garin su Argugun ana yi mata sako itama ta kan je in wani abu mai bukatar zuwanta ya ta so.
Ko bayan haihuwan Walida ta je gaisuwan Kawu Surajo kuma ta jima acan sai dai ta dawo ta ga Magajiya ta sauka an samu Mariya daman ta bar ta da ciki.


Da ta dawo ne tafara sana'ar cikin gida na saide saide ta na samun rufin asiri to abubuwan sai a hankali da an tarfa jari sai ya darkane, kuma ga shi acikin gida ba zaman lafiya kullum fitinar Magajiya na yau daban na gobe dabam kuma har kwanan gobe ba'a taɓa jin Inna Meri na tanka in tanka da ita ba shi ya sa ba a wajen Baba Danjuma har a makota kowa ya shaida hakuri tsabar shi wajen Inna Meri mace mai kauda kai da yakana babu ruwanta mai rama Alheri ko da mutum ya yi mata sharri.


Bintu ce ta ɗauko irin fitinar Baban Inna itama an sha fama da ita acikin gidan ita da baban Inna ba'a daga musu yatsa su bar shi haka sai sun karya shi, ga su Amina da suke manya amman sai Bintu dake da karancin shekaru ta tare musu mgana acikin gida Inna Meri in abun ya isheta sai ta yi tagumi tana faɗin"Ni wannan fitina na yaran nan na rasa in da suka gado shi, ni dai Allah ya shaida ba ni da fitina amman Allah mai ganin dama ya bani fitinannun ƴaƴa guda biyu Allah dai ya ƙara shiryamin su."
A koda yaushe kalamanta kenan, to yau da gobe bata bar komai ba dole rayuwar ta yi wahala da ya sa Inna Mari ta nemi shawaran Baba Ɗanjuma ya barta ta nemi aikin da za ta rika yi a cikin gidajen masu kuɗi suna samun abun rufin asiri saboda Aminci da yardan dake tsakaninsu ya sa ya amince mata, Harira ta yi mata hanyar samun aiki gidan wata mata ma'aikaciya ce mijinta ma ma'aikaci ne sai dai aikin kula da yara ne acikin gari gidan su yake, nan Inna Meri ta fara aiki kuma albashin mai tsoka ne sai dai dalilin mazan dake gidan sun yi yawa ya sa ta ijiye aikin gidan tana ganin ita uwa ce bai dace ta zama mai aikin mace ita kaɗai acikin maza ma'aikata sama da biyar ba sai ta ga aikin bai bata sha'awa ba ta ijiye.


Da kamar ma ta hakura tunda tana ta nema ba ta dace ba nan makotan su matar mallam Hashimu Dije ita ta yi mata hanyar aikin da ta ke yi yanzu a gidan Hajiyar shagamu. Tunda a baya kanwar Dijen ke yi sai kuma ta zo ta yi aure sai Hajiya ta ce a samo ma ta wata yar babba haka sai Dije ta yi ma Inna Meri mgana jin Hajiyar ce kaɗai a gidan zata riƙa zuwa da safe ta yi girki da gyaran gida sai kuma zaman kadaicin zata ɗebe ma Hajiyar ai da gudu ta amince
Kuma sai Allah ya haɗa jininta da na Hajiya za ta je da karfe 9 na safe ta yi share share sannan ta dafa ma Hajiya abinci sai kuma su zauna su yi ta hiran duniya da Hajiya.
Inna Meri na jin daɗin zama da Hajiya ba domin alherran da ta ke yi mata ba, a'a sai saboda ita ɗin mai kirki ce da sanin ya kamata, karfe 4:30 da rabi na yi za ta ce Inna Meri ta koma gida ta yi ma yaranta girki sannan kuma in za ta tafi sai ta ce sai ta ɗaukan ma yaranta abinci kuma wani kayan sawa na jikokinta za ta ce su Yadddiko su haɗo mata

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login