Showing 66001 words to 69000 words out of 103785 words

Chapter 23 - IDAN AN CIZA..! Part 1 Complete by Janafty.txt

Janafty   

20 Dec 2024

4815

neman rigima ina Baban Inna Ina Bintar ki?
Hajiya tace"To Ubangiji ya haɗa sai mu ce a'a tunda suna son junan su sai kuma mu hana su kudirin alheri."
Inna Meri ta ce"Hajiya Baban inna yaro ne yarinta ne ke damunsa shekaransa ashirin da uku ne da wattani, da me zai riƙe Binta? Sojan da yake ta ƙulafuci har yanzu bai samu ba kuma ya ki sauya ra'ayinsa don Allah Hajiya a bar mganar nan shakuwa ce kawai ba wai soyayya ba."


Hajiya ta ce"Duk na fahimci tunaninki, kina da gaskiya abin da za'ayi ai shima kabirun Soja ne zan kira shi mu yi mgana sai a zauna ko shi sai ya ne ma Mansoor ɗin makarantar Sojjojin a yi alkwari in Mimi ta gama karatu su yi auren su ba shike nan ba."
Inna Meri dai ta kasa mgana amman tana hango wani abu da ba zai tafi dai dai ba amman gudun kar Hajiya ta ga kamar tana gudun maganar sai ta amince da hakan, Kuma Hajiya da kanta ta kira Mansoor ta zaunar da shi ga shi ga Binta ta ce ya faɗa mata gaskiya yana son Binta?


Kai tsaye yake kallon Hajiya kafin ya ce" ba sonta nake yi ba, kaunarta nake yi Hajiya."
Itama Hajiya ta tambayeta lokacin Mimi an zama yan mata shekaranta sha tara, ta rufe fuska ta ɓoye bayan Hajiya tama yar dariya.
Hajiya ta ce kar su damu za ta yi mgana da baban Binta. A lokacin ita Mimi soyayya ta makantar da ita kamar yadda ya makantar da Mansoor dukkansu suka kasa gano abunda mutane ke hango musu.
Hajiya kuma ta manta waye Kabiru ta ɗauka haihuwarsa da ta yi ya isa ya sa ya bi abin da take so.


Major Kabiru bai san halin da ake ciki ba, Brr Murjanatu kaɗai ta sani tunda ita macece kuma yaran sun fi sabawa da ita shi kullum fuska ba fara'a tsoro tsoron sa ma suke ji, kuma Mimi in ta zo hutu daga baya nan tana yawan kamata suna waya da wannan yaron da ta ce Mimi ta bar maganan sa, ta yi ma Hajiya ƙorafi Hajiya ta ce ta kyaleta tunda har Binta na son wannan yaron to sai a zauna a ga abunda Ubangiji ya tsara, ita ba wai talauci ko yanayin rayuwa ba ɗaaya ba, abu daya take dubawa sun yi yarinta da yawa da maganar aure, sannan ta san waye mahaifin Mimi ba shi da tsarin aurar da ita yanzu to ko Madiha karatu take yi bai saka maganar auranta ba, ballantana Mimi da ta ke just 19 tabbas ta san akwai kura. Ita Hajiya ta fara kira akan maganar Saboda suna da kyakyawan alaqa na mutuntawa a matsayinta na surukarta, Mommy ta ji tsoron da Hajiya ta ce ta fara tuntuɓar Major da mganar cikin firgici ta ce"Hajiya wlh ba zan iya ba, kina ganin ko madiha wani yaron yayata na sonta da Major ya ji ba ki ji yadda yake ta masifa ba ya ce ba yanzu zai aurar da ita ba sai ta gama karatu ta fara aiki." Hajiya ta yi tsaki kafin ta ce"To ai wannan tsarinsa ne ba tsarin Ubangiji ba, karatun ya fi auren daraja a wajensa ne? ya bar yara sun zama manya bai aurar da su ba da an yi magana sai ya ce ba yanzu ba shi Sulaimanu ai ya na can cikin jajayen fata har yanzu bai dawo kasar ba." Mommy ta ce" Hajiya karatun likitanci yake yi, sai nan da shekaru biyu zai dawo in sha Allahu."
Hajiya tace"To dama dama shi tunda namiji ne amman matan ne ya le neman kashe musu rayuwa da tsatauran ra'ayinsa na banza, zan kirasa da kaina na yi masa mganar."


Ranar a tsure Mommy ta dawo daga wajen aiki, fargaban ta ɗaya ta san komai ya je ya dawo ita zai sauke ma bala'in zai ce tana sane da komai bata gaya masa ba sai da abu ya yi girma. A ranar da dadadde bayan ya dawo daga office Khadija na ɗakinta tunda ita a nan Abujan ta ke karatu Madiha ce ke BUK kano ta na karatun ta acan, Mommy duk jikinta ba daɗi Sai fama take da faɗuwan gaba tana Allah Allah ta ji ya ce Hajiya ta kirashi sai ta ji har sun gama cin abinci bai ce haka ba sai ta samu yar salama.


Sai dai bayan sun koma falo suna hutawa yake ce mata Mimi zata dawo nan ta yi jarabawa so ya ke yi ta ta fi Jami'a mai kyau ta yi karatun likitanci akan abin da ya Shafi mata tunda Sulaiman ya na karantar fannin zuciya, Mommy ta kasa magana sai zufa ke yanko mata duk ko da sanyin Ac dake falon. Kallonta ya yi cikin mamaki kafin ya ce"Honey lafiya? Ko baki da lafiya ne?
Da sauri ta ce"No am fine."
Saboda ya ga duk ta firgice sai ya yi dariyan basawa kafin ya ce" ko case ɗin dake hanunki ne ya ba ki tsoro.?
Dakyar ta yi yaƙe ta kasa mgana.


Ta fi kowa sanin waye Major ba shi da kyau ko ya yi wanka ko acikin Sojojin shi mugu ne sannan ba shi da uzuri ballantana ragowa ga ra'ayin riƙau ne da shi ita fa yanzu haka ba ta isa ta yi ba dai dai ba sai ya ce da gangan ta yi da farko ba haka yake ba daga baya lamarinsa ya kara ta'azzara.
Daman can halinsa ne sai kuma ya zo ya haɗe da kakin dake jikinsa sai takamarsa ta yi yawa. Daman shi fa ya tsani ace za'a haɗa ƴaƴansa da komai, yadda yake kaunar ƴaƴan to kila sai aikinsa ne za su iya gogawa. kuma ya ci burin akan su da sai ya gina su zai aurar da su ga wanda ya dace in ya ji wannan labarin na Mimi ai sai ya harbeta daga ita har Mimin.


"Kin ga ko na manta Ina Office Hajiya ta kirani ta na son yi mgana dani, na ce ma ta sai na koma gida, miƙo min wayata na kirata in har ma akan Mimi ne sai dai ta yi hakuri zan karɓi ƴata bazan iya kara barin ta a garin nan ba yanzu."


Can a sama Mommy ta ji Abi na mgana duk sai ta kara ruɗewa, ba ta tashin ba sai da ya ƙara mata mgana sannan ta mike ta ɗauko masa wayar wajen rawan jikin wayar ta faɗi ƙasa haka ta duka Jiki na rawa ta tattaro masa wayar ta mika masa ya karɓa lokaci ɗaya yana faɗin" Murja are u ok?
Sai ta gyaɗa mai kai, kasa tsayawa ta yi da sauri ta shige ɗaki ya bi ta da kallo, bai ɗauka wani abu ba sanin shi da ita akwai ta da saka dmuwar Case in dai ya na hannunta acikin ranta. Lambar Hajiya ya lalubo ya kirata, bayan ta ɗauka sun gaisa ya ce"Hajiya ban jima da dawowa ba, ina fatan lafiya? Hajiya ta gyara zama tana faɗin.
" Lafiya ƙalau, daman akan maganar Binta ne? Kai tsaye ya ce" Eh daman ina shirin miki maganarta nan zata dawo ta yi jarabawa so nake Bintar taki ta zama likitan mata Hajiya."


Ya faɗa cikin yar dariya Hajiya ta haɗa rai kamar yana ganinta kafin ta ce" Eh to za ta iya zama likita amman daga baya yanzu dai aure take so."
Ya ɗauka wasa Hajiya take yi sai da ya yi dariya kafin ya ce"Haba Hajiya aure kuma? Mimi ai ba ta san me ake kira aure ba."
Hajiya ta ce"Ai ba jaririya ba ce shekaranta sha tara da gaske nake yi Akwai wani yaro ɗan wajen Meri dake min aikace aikace sun shaku da Binta kuma yana sonta da gaske itama Bintar na son shi.."


"Wait Hajiya kika ce yaron waye?


Ya katse Hajiya cikin mamaki shi fa gani ya ke yi kamar ta tsuniya Hajiya ke karanta masa
Hajiya tace"Eh yaron Meri ne matar dake taya ni zama."
Mamaki ya hana shi magana Hajiya na son gayamasa wai yaron ɗan wajen mai aikinta ne ke son Mimi, Shi haka ya yi sakacin da ƴarsa ta za ma a arha da wani yaron talakawa zai ganta ya ce ya na so. Ai bai gama mamaki ba sai da ya ji Hajiya na faɗa masa Mimi na son yaron kuma ta yarda ta aure shi kuma yaron iya sakandiri ya gama ya na son ya zama Soja to shi ya taimaka masa ya samu sojan daga baya komai menene sai ayi.


Huci kawai ya ke yi ya kasa mgana, daman Hajiya ta matsa ya bar mata Mimi ne saboda ta bari wani yaron talakawa mara tarbiya su hore ma ƴarsa kunne lalle ko idon sa idon yaron nan sai ya harbe shi. Kuma sai ya taka wuyan Mimi da har da bakinta take faɗin za ta iya auran wani banzan yaron da bai da wata makomai mai kyau nan gaba.
Kawai amsa ma Hajiya ya yi da Toh ko gama mganar ma ba ta yi ba ya katse wayar Hajiya da sauri ya kira ɗan uwansa Alhaji Hamza.
Cikin masifa ya fara gayamasa yana garin har ahaka ya faru wai Mimi ke faɗin tana son auran wani yaron talakawa?
Alhaji Hamza ya ce bai sani ba nan Major ya sanar dashi abin dHajiya ta ce ya kara da cewa"Hamza ka je ka samu Hajiya ina bukatar sanin tarihin yaron nan tun daga farko har ƙarshe, sai na ji waye mai wannan tsautsayin da zai hure ma ƴata kunni."
Daga haka ya kashe wayarsa ya miƙe a fusace kamar ya yi bindiga tun daga falo ya ke ƙwalama Mommy kira.


"Murja.."


"Murja.."


Khadija na ɗakinta tana karatu sanda ta ji wannan kiran sai da hantar cikinta ya kaɗa domin a muryan Abi ta fahimci yau akwai bala'i a gidan nan, Mommy kuma tana jin yana kiranta tasan rufa rufa kuma ai ta kare. Shi ya sa ta sadakar ta fito da sauri tana gyara ɗaurin ɗankwalinta lokaci ɗaya tana faɗin"Ga ni nan Habib...'


"Da sanin ki Mimi ta fara soyayya da wani banza yaron talakawa? da sanin ki Murja Mimi take son ta bijirema tunanina? da sanin ki na ce.?


Ya faɗa a fusace kamar ya kai mata duka sai ta kauce cikin rawan jiki ta ce,"Ban ban sani.."


"Sai na harbe shi, ko waye wlh sai na ga da abin da yake takama da shi. Ko madiha ban saka maganar auranta a kaina ba, sai Mimi? Mimi fa? Hajiya ba ta kyautamin ba wlh zan yi abin da zukata ba za su ji daɗi ba.". Ya ke faɗa ya na huci cikin ƙara daka wata tsawa ya hau kiran sunan Khadija.


"Khadija.."


"Khadija.."


Mommy jikinta na rawa ta ce"Khadija ba ta san komai ba Habibi."


"Murja zan miki tijara na ce, ƙarya kike yi kin san komai, Hajiya zata gaya miki kuma Mimi yarki ce kina sane da abin da ke faruwa, Wlh tallahi in har da saka hannun ki a abin da ke faruwa zan iya sakin ki a kan haka." Khadija ta ɗora hannu akanta san da ta fito ta ji maganar Abi Mommy kuma sai kawai ta juya tana kuka ta shige ɗakinta acikin zuciyarta tana fadin" Inna lillahi wa'inna ilaihirraju'un.."


Khadija ya kallah da ke tsaye tsuru tsuru, tsawa ya daka mata kafin ya ce"Ke ma kin fara soyayya ne? za ku tsallake umarnina ne?
Jikin Khadija na rawa ta duka tana faɗin "Abi karatun ka ce za mu yi kuma shi nake yi, wlh ban taɓa soyyayya da kowa ba."
Yana faman sakin huci ya saka kafa ya daki tuberin gabansa kayan ciki suka watse da karfi yake taku zuwa cikin ɗakinsa Khadija ta zura da gudu zuwa ɗakin Mommy tasan bindiga Abi zai fito da shi ai su yau sun shiga uku.




*Janafty,*
*IDAN AN CIZA..!*


*Wattpad:JamilaUmar315*
*Arewabooks:Jamilaumarjanafty*
*Mallakar:Janafty*


*SADAUKARWA GA HAJIYA AISHA AHMAD IYA*


Ina kuke mata yan kwalisa.. *KHADYS EMPIRE* Ta Kawo muku kayan mata masu kyau da saukin kudi💃🏻 kamar haka.


*Zumar Matsi Guarantee 3500*
*Maganin sanyi komai nacinsa 4k*
*Zumar kacha kacha 2500*
*Zumar kiba 4k*
*Setinn kayan mata na yar gata 8500 Me abubuwa har kala Takwas a ciki*
*Dahuwar kaza ta manyan mata 8k*


Zaku sameta a Kan Lambar waya 08147832783 tana garin kano tana aikawa da kayanta ko ina da yardar Allah. Dadin dadawa kuma tana bada sarin komai cikin farashi me rahusa yadda zaki sami Alheri. Wani ƙarin jin daɗin ma free delivery withn kano take yi, koh ba yanzu zaku siya ba kuyi saving numbern ta dan nan na gaba Na gode. https://wa.link/pd4ie0


*Page 14*


Mommy na zaune a gefen gadota tana sharan hawaye daman abin da take gudu kenan, da gudu Khadija ta faɗo ɗakin tana faɗin "Mommy mun shiga uku bindiga ina ga Abi zai ɗauko." Ta faɗa lokaci ɗaya tana hawa saman gadon ta lafe a bayan Mommy, tana ta haki tare da sauke numfashi.
Mommy ta yi ajiyar zuciya kafin ta ce"Allah ya duba mu, yau sai abin da Allah ya yi."
Khadija ta ce"Mommy me ya faru ne? me Mimi ta yi ne?


Nan Mommy ta karanta mata abunda ta sani sai Khadija ta zaro ido kafin ta ce"Mommy ke ma me ya sa ba ki hana ba? Mimi tana hauka ne? Wani yaro ƙarami da bai wuce a wanke masa kashi ba ne za ta jawo ma na bala'i muna zaman zaman mu?
Mommy ta karɓe da faɗin "Hajiya ce ta mara mata baya, me zan ce Khadi?
Khadija ta ce" Mommy ke ma me ya sa kika yi shuru? Kin san fa halin Abi wlh ba Mimi kaɗai ta shiga uku ba har dake har damu gabaɗaya." Mommy ta yi tagumi kafin ta ce"Khadi addu'a za mu yi Allah ya sausauta zuciyar Habibi."


Khadija sai ta kasa mgana wayar Mommy dake kan gado ta ɗauka ta kira lambar Madiha tana ɗauka cikin ruɗewa ta fara gayamata abunda ke faruwa. Daga can bangaren Madiha ta ce"Subhanallah Ita Mimin ce ta ce aure take so?
Khadija ta ce"Mommy ma ta ce ta sani tun zuwanta Gombe take tare da yaron, wai kiji ma yaro ƙarami kila ma sa'an Mimin ne."
Madiha ta ce" Ba su da hankali ne, ita kuma Hajiya ta fara tsufa me ya sa mommy ba ta hana ta kiran Abi ba? Mommy na gefe tana jin khadija na maida ma Madiha zencen bayan Madiha sai da ta kira Sulaiman bai ɗauka ba ta tura mata saƙo.


Ranar a ɗaki ɗaya Khadija suka kwana da Mommy saboda tsoro Abi kuma ko runtsawa bai yi ba bindiga a gabansa yana shan alwashin harbe wannan shegen yaron.
Shi a tsarin rayuwarsa ba tsarin ya aura ma ƴarsa kowani datti, haka kurm rana tsaka wani ɗan talakawa zai zo ya lalata tarbiyan Mimi, duk laifin Hajiya ne ita ce ta matsa sai da ya bar mata Mimi shi ne daga karshe ta yi masa wannan sakayyan.
A washegarin ne kuma Alhaji Hamza ya isa gidan Hajiya ya sameta da maganar, Hajiya ta zauna ta yi masa bayanin komai game da Mansoor har tana gayamasa maraya ne mahaifinsa ya rasu shi ya sa Inna Meri ta yi aure a nan gidan Wanzamai, shi bai gayama Hajiya sun yi waya da Kabiru ba amman shi kanshi sai da ya nuna ma Hajiya abun bai dace ba.


Kai tsaye ya ce"Hajiya kema me ya sa za ki bi ye ma Mimi? Har yaushe take yarinya ƙarama gaskiyan Major ne ta maida hankali a karatunta, shima yaron ya je ya yi fafutar rayuwarsa a gaba in suna da rabon auran juna sai su yi auran lokacin sun san dai dai da rashin sa amman yanzu dai ko ni ban goyi bayan wannan shirmen ba Hajiya."
Hajiya ta fara faɗa tana faɗin" To ai ba abu mara kyau ba ne, kuma sun yi yarinta da auran ne? ni ban ga illar haka ba ni fa magana na ce ayi ko da ba yanzu za'ayi auran ba ya samu ya taimaki yaron ya cika burinsa daga baya sai ayi auran."
Alhaji Hamza yace"Hajiya to ai ke ba ki da wannan ikon, magana na wajen Major kuma kinsan yadda ya ke da burin ƴaƴansa su yi karatu." Hajiya ta fara shiga tana fita Alhaji Hamza ya ga ba za ta gane ba ya yi mata sallama ya fita kuma shima ya saka an yi masa binciken Mansoor abun ka ga ɗan siyasa mai jama'a tuni ya samu cikakken bayani akan Mansoor. Kuma nan take ya kira Major ya zayyana masa.
Amman sai da ya ce"Ka bi komai a hankali Major a lallashi Hajiya a fahimtar da ita illar haka, shi kuma yaron ba sai an yi masa wani abu ba, bakin ka alaikum ka ɗauki ƴarka ta koma hannunka, In ma ta kama sai a sauya ita mahaifiyar yaron da wata mai aikin Hajiyan saboda a samu masalaha."

Ko alama bai ɗauki wannan shawaran ba, ai sai ya nuna mana wannan yaron ya taɓo tsuliyan dodo ashe ma Agola ne mai tsaurin ido zai gane ya shigo gonar Soja, da wuri ya tashi daga Office ya na komawa gida ya shige ɗaki Mommy ba ta nan tana wajen aiki itama Khadija ce kaɗai acikin gida tun safe ta ke waya da Madiha Sulaiman ma sun yi magana ta gama fesa musu abin da ke faruwa duk da suna can amman a tsorace suke. Khadijan da ta kira Mimi tana mata faɗan abunda ta aikata da cewa"Mimi are u mad? maganar Abi zaki warware? Ko Madiha ba ki ga an mata aure ba sai ke tun baki tafasa ba zaki ƙone?
Mimi ta tura baki kamar tana ganinta kafin ta ce"Ni ai ban ce bazan yi karatu ba, amman bayan mun yi Aure da Aji sai na cigaba da makarantar ko?
Khadija ta zage ta daman ga su saƙo da sakon haihuwa kafin ta ce"Ko ba Aji ba, ai Abi zai Aje miki kanki a kasa da bindiga wawiya kawai."


Ba wanda yasan abin da Abi ya shirya tunda Mommy da safe ta kira Hajiya sun yi mgana, amman sai ta kasa gayamata abunda ya faru ta

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login