Showing 39001 words to 42000 words out of 103785 words

Chapter 14 - IDAN AN CIZA..! Part 1 Complete by Janafty.txt

Janafty   

20 Dec 2024

4804

sauran siyayyan kayan kitchen sai Atamfar yinin biki da suka siya tunda Mimi na dinner kaɗai ta turama Rukky kudin ta siya mata less ta ba da ɗinki a waje ɗaya tare da nata.
Na yinin bikin kuma Atamfa ce gold itama Rukky ta ce ɗinki iri ɗaya za su yi saboda haka waje ɗaya za ta kai musu ɗinki.
Mimi ta bar mata, tunda Rukky dai ta dage sai sun zama ƙawayen Bibi.
Satin bikin kaf ba su zauna ba tunda tana da mota mai kawai take sha suna shiga gari. Ko a wajen aiki ma bini bini Rukky ta ja ta sun fita Har Na misau sai da ya yi magana yace" Ke dai Rukky kina da son kuɗi, ki rage ciki ki siya mota ki daina lafe masu mota ana miki ɗani. Rukky ta rika hararan shi Mimi na yi musu dariya.
Sai dai shima yana zolayanta ne, tunda ai su san ƙawaye ne, kuma ga bikin Kanwar Rukkaya da kowa a an bashi katin gayyata. Zirga zirga ya yi musu yawa ba ta komawa gida sai dare har Hajiya sai da ta ce Rukkaya yar gaban goshin Mimi ce da har take iya janta suna faman zirga zirga.


Itama Mimin ta gaida matsayin Rukkaya a zuciyarta ita da ba ta yarda ta je ko'ina daga wajen aiki sai gida fita nan da Rukkaya ta matsa mata suke yi duk jikinta ciwo yake yi. Ana saura kwana uku biki suka je kunshi aka yi ma Mimi lallin Sticker a kafanta ja ya yi maroon a hannun ma an yi mata jan sai aka sirka mata da bakin zane.
Ya yi kyau sosai abun ka ga farar fata a can gidan kunshi ma ana ta santin kunshin saboda Mimi ta manta rabonta da kunshi tun bikin Auran yayarta Khadija in za ta iya tunawa.


Ita kanta haka ta riƙa kallon kunshin tana jin daɗi ana gobe jibi kuma gyaran kai suka je sun yi kuma yamma saboda sai da suka je kasuwa ita da Rukkaya sannan suka tsaya shagon Salloon suka yi gyaran kai Amarya Bibi tana tare da wasu kawayenta guda biyu yan makarantar su sai wata ƴar'uwansu da suka zo daga Bauchi.
Tunda su Rukkaya mamansu ce yar Gombe Babansu kuma ɗan Bauchi ne.
Ranar kuma ita ke da karanta labaran duniya na yamman dole daga Saloon Rukkaya ta wuce gida, ita kuma sai ta koma gida ta shirya ta wuce wajen aiki, ga shi ta zuba kunshinta ga gyaran kai goshi nan ya yi raɗau haka ta rika karanto labarai cikin zaƙin muryanta.


Ranar ta sha magana su kansu ma'aikantan kowa ya ganta sai ya ce ta yi kyau.
A lokacin da ta gama karanta labaran cikin harshen hausa sai ta koma na harshen turanci, a dai dai lokacin Mansoor ya shiga bangaren Inna Meri ba a anguwan ya yi sallar mangariba ba daga Studio yake ya tsaya ya yi sallar acan sai kawai yana shigowa anguwan ya shigo gidan kai tsaye.
Ya ɗaga labulen ɗakin Inna Meri kenan lokaci ɗaya yana faɗin" Innar m..."
Sauran kalamansa sun maƙale a fatar bakinsa lokacin da ya yi arba da ita.
Ba shiga ta yi mara kyau ko wanda ya saɓa mata addini ba, tunda doguwar riga ta saka mai ruwan kasa mai faɗii ba ta ma kama jikinta ba. Sai dai ras kunshinta ya fito tunda hannayen ta suna waje ne.
Kamar ya ga mutuwarsa haka ya ji, gabansa ya faɗi ras!.Haka ya ji kirjinsa na wani irin Dif! Dif! Kamar ya na da ciwon asma.
Inna Meri na ɗakii ta jin muryansa dai dai ta fito tana faɗin "Murya wa nake ji kamar ta Baban Inna"
Sai dai ta hangi bayansa ya na sakin L labulen ɗakinta ya wuce.
Walida ke tsakiyar falon tana sallah inna Meri ta leka daga wajen kofar ɗakin sai ta ga da gasken dai ya fita.
Sai ta dawo dai dai lokacin da Walida ta sallame salla.


Inna Meri ta kalleta tana faɗin"Ba Baban Inna ba ne ya shigo yanzu?
Walida ta ce"Shi ne yana ɗaga labule kuma na ga ya juya da sauri ya fita."
Inna Meri na gyaran hijabin jikinta rike da casbaha ta koma cikin ɗakinta tana faɗin" Walida ki rage karan talabijin ɗin nan, a haka kika yi salla da shi ƙara ya yi yawa."
Walida ta juya ta na kallon Mimi tana karanto labarai cikin turancinta mai kyau kamar ba'amurkiya. Sai ta fara tunanin ko ita Baban Inna ya gani ya juya.
Zai iya zama gaskiya saboda akwai wata rana da ya taɓa zuwa yaga sun kamo tashar kuma ita ce ke karanta labarai da safe. Da kanshi ya saka hannu ya tuge soket ɗin talabijin ɗin har ya yi ma Walidan tsawa da cewa su daina barin Tv a kunne in babu kowa a falon.
Ajiyar zuciya ta sauke duk da bata santa ba koma me ya faru ta na ƙarama ya faru.
Amman ta ga dacewar Yayansu da wannan yar gayu. Kuma Inna ta ce gidansu na can cikin Gra, inna ta gaya mata ta yi zaman yi ma kakar mai kyau da iya turancin aiki wacce ake kira da Mimi mimin karamchi.


Shiko iskar bangaren Inna Meri ne ya fara yi masa kaɗan saboda yadda yake jin zuciyar na zafi, ko tunanin tsayawa bai yi ba ya hau mashi dinsa ya bar anguwan.
Yana tafe iska na kaɗashi amman kuma acikin zuciyarsa babu wannan iskar sai wani irin tukikin zafi da yake ji.
Kishi ya ke ji a kasan ranshi, me ya sa ta yi kunshi ta bayyana adon ta a duniya?
Maza nawa suka kalleta? Sannan maza nawa suka yaba da wannan kunshin da ta yi? Yana tafe sai faman sakin huci ta baki ya ke yi, yana tuna shi fa a kwanaki nan yana kai idanuwansa in dai bai kamata ya kai ba.
Sai kwana ya ke yi acikin kuncin zuciya, haka yaje ya ga hotunta a shafin su na Karamchi Tv a Faceebook hotonta na barka da sallah wanda ta yi a madina.
Ta saka bakar Abaya ta yane kanta da mayafi amman gabadaya hakoranta suna waje ne ta yi dariya. Karin bakincikinsa ma yadda ya shiga comments section ya ga ana yabawa da kyan da ta kara ita kuma har ta na ba da amsa tana dariya. Ranar bai iya barci ba saboda bakinciki da Kishi.


Yanzu ma ya ƙara wani mugun gani, saboda haushin da yake ji yasa ya koma gida kuma sun yi waya da Makama ne za su haɗu. Saura kwana biyu bikin sa Mu'azzam sai gobe zai shigo garin.
Yana saman mashin ya ji kiran wayarsa sai da ya isa gida ya duba ya ga makama ne.
Sai ya kirasa daga baya, ce masa ya yi yana anguwan yana jiransa shi kuma ya ce ya koma gida. Makama bai yi fushi ba ya ce zai zo ya same sa su yi mgana.


*Janafty*
*IDAN AN CIZA..!*


*Wattpad:Jamilaumar315*
*Arewabooks:Jamilaumarjanafty*
*Mallakar:Janafty*


*SADAUKARWA GA HAJIYA AISHA AHMAD IYA*


MMN MUJAHID KAYAN MATA AND SUPPLEMENT


SHIN KINA DA LABARIN MACCE MAI GYARA DABAN TAKE GA ZUCIYA MIJIN TA
MUNA DA KAYAN MATA MASU ZAFI NA BUGAWA GA JARIDA


HAJIYA TA KUDI DA KUDI AKE NEMAN SU


INA MASU FAMA DA MATSALA RAMA BA GABA BA BAYA KINA ZAUNE ANA KWATANCI DAKE KINA CI BAKI KOSHI MUNA DA MAGUNGUNA DA ZUMA 3 IN 1 KIBA BRST HIPS TA CIKO MIKI KU INA KIYI FRESH MUNA DA KWAYOYI MUNA DA GARI DUK MASU CIKO JIKI NE KIYI DUM


INA MASU FAMA DA MATSALA BRST KU TSUHU YAFI SON YAGA NONO A TSAYE DUK MAI MAGANIN DA TACCE MIKI ZATA BAKI MAGANIN NONO KAI TSAYE YAYI MIKI KARYA CE MAGANIN BRST SAI KIN SHA ADADIN WANDA ZAI MIKI SBD DUK CIKIN GYARAN JIKI NA BRST YAFI WAHALA YI


INA MASU FAMA DA MATSALA SANYI MUNA DA MAGANIN SANYI ORIGINAL


INA MASU ZAMAN BANZA BABU SANA'A KINA KONE DATA KI GA BANZA WURIN TSEGUMIN KALLON STATUS DIN WASU GA DAMA TAZU MUNA HAR GIDA GA WAYAR HANNUN KI KI MALLAKE MOTA MILLION 8 HAR FIYE GA ALBASHI GA RIBA GA KYAUTA KAYAYA KI
08066726866


Follow this link to join my WhatsApp group: https://chat.whatsapp.com/JMpd8nXr7TIDD3ILDXh64z


*Page 8*


Sai da Makama ya zo ƙofar gidan sannan ya kira Aji ya ce masa gashi ya iso yana wajen get yana jiransa. Ba jimawa ko sai ga shi ya fito har ya sauya kaya zuwa wata jallabiya mai ruwan ƙasa. Hannu ya bashi suka yi musabaha da mirmishi kaɗan a saman fuskar Mansoor ya ce"Makama ango."
Makama ya fashe da dariyan farincikin da yawanci angawaye a satin bikin su suke kasancewa kafin Ya ce" Aji namu, a waje zamu tsaya ba za a bani izinin shiga cikin gidan ba ne?


Mansoor bai yi masa magana ya wuce gaba Makama ya biyo bayansa duk da ya taɓa zuwa tun ana aikin gidan ba a gama ba.
Ya zagaye haraban gidan sannan ya ci burki a falon gidan yana faɗin.
"Aji gaskiya ka tsara gida komai ya ji ban da abu ɗaya wlh."
Yasan abin da zai ce shi ya sa ya yi masa banza ya isa ga ƙaramin firizan dake falon ya ɗauko masa ruwan gora guda ɗaya
Sai ya haɗo masa da ƙaramin ƙofin dake saman firizan.


Ya kawo masa har gabansa ya ijiye yana faɗin"Ka sha ruwa Makama."
Makama da ya yi rashe rashe a zaune ya ce"Zan sha ruwa, Aji ya kamata ace akwai mace a gidan nan gaskiya zai fi kyau."
Ya kallesa a ɗage bai yi mgana ba sai ma ya kauda kai, shi kuma makama ya sha ruwa ya sauke kofin yana faɗin" Daman alfarma na zo nema a wajen ka."
Sai ya juyo ya na kallonsa bai yi mgana ba Makama ya gyara zama yana fadin"Ba ku yi mgana da Mu'azzam ko Nasir ba?
Sai ya girgiza kansa kafin ya ce"Ina Studio a gida na bar wayata ban sani ba ko sun kirani.". Ya faɗaa kai tsaye yana wani tsuke fuska shi fa baya son takura Allah yasa ba wani abu za su ce zai yi a bikin nan ba.
Allah ma ya sani shi har addu'a ya riƙa yi Allah yasa ranar ma suna da wasa a wani garin ya bar garin sai bayan bikin sai ya dawo.


Sai dai addu'arsa ba ta karɓu ba sai ma watan gobe su ke da wasa kuma Kano pillars ne za ta zo wasan cikin gida za a buga, yana wannan tunanin ya ji makama na faɗin " Dama alfarman wajen kwana nake nema akwai abokai na ko na ce yan'uwa ne daga Zariya za su zo sh ine zan sauke su a gidanka sai sauran dai abokan mu na nan ai duk kasan su."
Mansoor ya kallesa a karkace kafin ya ce"Ban san su ba."
Daga haka ya cigaba da faɗin "Su nawa ne? Kasan ba na son takura kuma duk wanda zai zauna a gidana ina da dokoki."
Makama ya ce" Ba za mu wuce mu goma ba." Mansoor ya kallesa cikin mamaki kafin ya ce"Ba ni da katifa, kuma ɗakin da nake kwana ne kaɗai a gyare"
Makama ya ce"Bakomai ga falo tunda akwai cafet sai ayi amfani da barguna., Ni da kai da Nasir da Ahmad da Mu'azzam sai mu yi amfani da cikin ɗakin naka."


"Wani ɗakin kenan?


Har Mansoor na sauri wajen tambaya Makama ya nuna masa ɗakin da hannu kafin ya ce"Nan ciki mana ai muma gobe duk nan zamu kwana Aji."
Mansoor ya yi shuru bai yi mgana ba yana jin Makama na sanar da shi Ahmad ma gobe zai shigo garin cikin zolaya ya ce"Gobe akwai kwanan hira za mu tuna baya ne Aji."
Kallon Makama kawai yake yi ya ma kasa magana sai dakyar ya buɗe baki yace" Ni da Mu'azzam kaɗai zan kwana, ku sai dai ku kwana a falo."
Ya faɗa kai tsaye kuma da gaske yake yi Makama ya kallesa kafin ya ce"Ba ka isa ba, kai ko da yaushe sai ka nuna son kai wato Mu'azzam ƙanin ka ko? Ba ka isa ba Allah tare duk zamu kwana sai dai ka koremu in mu baka son ganin mu.".
Ya karishe faɗa a kufule, Mansoor ya yi masa banza bai tanka sa ba sai cewar da ya yi" Ahmad da Nasir suna da mata fa to miye haka na wani zuwa su kwana a gida na? Mu fa ba yara ba ne mun girma Makama mu rika abu na masu Aji mana."
Makama ya fashe da dariya har ya na dafa kafaɗan Aji kafin ya ce"Aji Aji! Aji namu ba zaka taɓa sauyawa ba kai komai sai kace an yi abu na rashin Aji, Ahmad ai ya tafi da matarsa kaduna in da ya ke ɗinki Nasir kuma ya ce gamu za mu kwana waje ɗaya ba zai ware kansa ba"


Mansoor ya yi ƙaramin tsaki ya sauke hannun Makama daga kan kafaɗarsa yana faɗin " Ka ji ba, to shi yaro ne?
Makama sai faman dariya ya ke yi, Mansoor kuma haushi duk ya kama shi, yaushe ne su Nasir za su girma su daina aikin yara ne?miye wani abun zuwa a cakuɗi a kwana waje ɗaya sai kace masu shiga itfikafi.
Haɗe rai ya yi ba halin ya ce kada su zo ya san su mayu ne domin su kure shi ma Nasir sai ya ce su zo, kuma ya na da tabbacin Mu'azzam ya kasa gaya masa ne ya sa ya ce makaman ya zo da kansa.
A rayuwarsa ta yanzu ya fi son ya zauna shi kaɗai ta fi yi masa daɗi in ka ganshi da mutane yan Club ɗinsu ne ko wani taro na buga wasa ko abin da ya danganci haka.
Ko a baya da yake da sakin jiki da son mutane bai yi aikin yaran da su Nasir ke yi yanzu ba.


Sama sama ya ji Makama na faɗin"To yanzu dai ka amince mu zo ni da baƙina ko?
Mansoor ya kallesa kafin ya ce"Ba na son mata a gidana, ko shaye shaye kai ko sigari na kama mutum na busamin sai na koresa, sannan 9pm nake rufe gidana in suna yawon dare ka faɗa musu su kiyaye sannan kwana nawa za su yi ne?
Makama ya buɗe baki cikin mamaki kafin ya ce"Waɗanan dokikin kamar na shiga Villa? Mansoor yace" Gidan Aji ya fi Villa martaba da matsayi."
Makama ya jinjina kai kafin ya ce" Ba shakka kar ka damu iyakarsu kwana uku, kuma duk abin da ka zayyano ba sa mu'amala da ko ɗaya mu kuma ka san mu tun muna matasan mu in ma muna da wani halin banza za ka fi kowa sani."
Kamar magana ce ya gaya masa, shi kuma bai damu ba sai ma kafaɗa da ya ɗaga masa ma'ana is better.


Makama bai ƙara wasu mintina ba, ya ma Aji sallama ya wuce gida saboda ya san ko ya zauna ba biye masa zai yi su tattauna ba tunda yasan hali, shi ko Mansoor Makama na tafiya ya ɗauko wayarsa ya kira Mu'azzam. Yana ɗauka ya fara masifa ta in da yake shiga ba ta nan ya ke fita ba.
Faɗi yake yi" kai ne ka ce su zo su kwana a gidana ko Mu'azzam? ka san me ka jawo ko? Mu'azzanm dai sai cewa ya ke yi"Ni fa ba ruwana ya yi min mgana ne na ce ya je ya same ka ya ji ta bakin ka."
A Fusace Mansoor ya ce" Mu'azzam ka fara zama mara jin magana yanzu ko? Yaushe ka zama haka? To ka guji haɗuwarmu sai na saɓa maka." Daga haka ya katse wayarsa ya bar Mu'azzam da dafe kansa dagacan bangaren.


Hibba na gefensa daman suna cin abinci ne kuma a wayar akwai kara taji faɗan da Mijinta ya sha. Cikin kwantar da murya tace"Ka taɓo Baban Inna yau."
Mu'azzam ya yi shuru kafin ya ce" Na rasa me ya sa ya ke gudun mutane yanzu? Alhalin a baya ba haka Dan'uwana yake ba." Ya fad'a kamar zai yi kuka, Kansa take shafawa kafin ta ce"Ka yi hakuri mu cigaba da gayama Allah In sha Allahu komai zai wuce" Huci kawai ya saki ta baki wani abu na sukan ranshi.
Hibba ita ta yi ta lallaahinsa har ya samu ya saki ranshi. Shifa Nasir ne ya matsa masa amman yasan haka za ta faru bayan shi Mansoor ba ya son raɓar kowa ciki harda abokan da suka taso tare tun suna yara.


A bangaren Mansoor kuwa kwana ya yi ya na sakawa yana warwara, kamar ya gudu ya je Camp ɗin su ya kwana sai dai kuma ba ma evining training gare su gobe ba Morning ne haka kurum y ji baya son wannan haɗuwar, haɗuwar tana nufin tuna wasu abubuwan da suka shuɗe a baya. Da ace kafin ya sauya rayuwarsa ne ya san zai fi kowa murnan ganin sa a waje ɗaya tare da makama , da Ahmad da Nasir, saboda abokansa ne tun lokacin da Inna Meri aure ya kawo ta Gombe a kuma anguwan Arawa su ya fara sani bayan Mu'azzam. Har gari ya waye bai samu mafita ba hakanan ya shirya ya tafi Studio din su yana shiga wajen daman shi kaɗai ke jira sai ji kawai kake yi " Barka da safiya Captain" shi kuma yana ɗaga musu hannu dukkansu suna sanye da yellow din riga da ƙannanun wanduna takalman kafarsu ma mai ruwan kwai ne, suna shirye waje ɗaya a layi dukkansu kowa ya harɗe hannayensa a bayan hannunsa sun kame waje ɗaya.
Wajen Cauch ɗin su ya nufa shima yana Shirye da irin kayansu hannun ya bashi suka yi musabaha. Cikin yanayin maganarsa ya ce"Barka da safiya Coach."
Shima ya amsa masa da cewa" Barka da safiya Captain."
Nan da nan aka hura usir members suka fara gudanar da training ɗin su.


A gida ya bar wayarsa saboda ya san za a yi ta kiransa a waya sai wajen sha biyu ya koma gida ya yi wanka ya ɗan kwanta kafin azahar sai a lokacin ya duba wayarsa ya ga an kira shi da yawa harda Mu'azzam sai Nasir. Kiran Mu'azzam ya bi, bayan ya dauka sun gaisa yace gashi ya iso yanzu ba da jimawa ba. Shi kuma sai ya ce yana gida zai huta sai zuwa bayan la'asar zai shigo anguwan, ko kiran Nasir bai bi takai ba ya share shi saboda tun a zamanin baya sun fi yawan samun saɓani da Nasir.
Nasir akwai daɓa

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login