Showing 15001 words to 18000 words out of 103785 words

Chapter 6 - IDAN AN CIZA..! Part 1 Complete by Janafty.txt

Janafty   

20 Dec 2024

4789

shekara biyu a kunne kuma a tare da ita, tunani take yi watarana zai iya nemanta abin da bata sani ba, sai daga baya ba ita kaɗai Aji ya shafe daga tunaninsa ba har da dukkan mafarkan rayuwarsa da ya tsara tare da ita.
Lokacin rabuwarsu sai da kamar Depression zai kamata daga baya ta ɗauki dangana dalilinta na yin karatu a ibadan kenan saboda ta tsani Abuja ta kuma tsani Gombe a lokacin. Haka ta rika bin sakonnin nan ɗaya bayan ɗaya tana karantawa, akwai wani sako da har abada ba za ta taɓa mantawa da dalilin turo shi ba.


"Mimi Na nifa na faɗa ma Inna da Baba aure zan yi."
Inna ta ce da me zan yi aure? ni kuma na ce duk a saida gonakin Baba na mallam Sidi a nema min auran fatima bintuNa"


Ta na karanta sakon tana dariya lokaci ɗaya da kuka, ba za ta manta ookacin suna yin jarabawar fita daga babban Sakandiri ne bayan ta dawo daga makaranta. Hajiya ce ta ɓata mata rai akan sai ta shirya ta je gidan Daddy(Alhaji Hamza) ta kwana ita kuma ba ta son tafiya saboda Mansoor.
Sai kawai ta yafo ɗankwalin doguwar rigan da ke jikinta ta fito haraban gidan tana kunkuni. Ta bar Hajiya aciki ita da Inna Meri ta na ba ma Hajiya Hakuri.
Kamar ba za ta sai ta ganshi a gabanta cikin mamaki da zaro ta ce"Yaushe ka zo ban sani ba? Ba zata manta kayan da ke jikinsa ba alokacin tunda ranar jumma'a ce ya saka farin shadda har da hula.


Yana mata irin kallonsa ya ce"Daga masallacin Jumma'a nake, na ce ba zan koma gida Mimi ba ta ga wankan Ajin ta ba."


Sai da ya faɗa taga darduma a hannunsa sannan ga kasa nan a saman goshinsa ya kuma bata tabbacin da gaske yake yi daga masallacin jumma'a yake.
Ita fa duk damuwanta in ta gan shi sai ta ji farinciki ya cikata.
Mansoor shine rayuwarta, suka tsaya suna ta hira yana bata labarin irin yadda yake wahala wajen neman makarantar sojoji tunda shi burinsa ya zama Soja saboda haka ma ya ɓata shekaru uku a gida bai shiga makarantar gaba da sakandiri ba.


A lokacin tura bakinta tayi kafin t ace"Aji kabar wannan Sojan nan ka yi karatun ka kawai ai ba ka ta zama ba."


"Ke bari Kamar yadda ba zan iya barin ki ba.Haka aikin Soja yake a wajena.."


A lokacin fushi ta yi ta juya masa baya tana kunkuni kafin ta ce"To ai shike nan tunda ka fi son soja a kaina." Ta juya taa masa yar shagwaɓa ya yi ta kiranta ta ruga cikin falon Hajiya da gudu tana dariya.
Shine da daddare ya turo mata wannan sakon na cewa ya faɗa Inna aure yake so. Ta tuna har amsar da ta bashi da cewa ba Soja ka zaɓa ba?
Sakon gaba da ta karanta ne ya saka ta ƙara fashewa da dariya tana kuka, saboda kamar muryansa take ji alokacin yana yi mata mgana.


_In ana salla ba'a mgana Mimi Na, sojan banza bari dai na fara samun ki, na tabbata in na same ki a hankali sauran burukana za su tabbata._


Kifa wayar ta yi a saman fuskarta tana raira wani irin kuka, ya za'a yi ma ta manta da shi? Ya haɗa komai na bukatar kowacce mace ya yi mata wani irin son da ya haɗa duka mafarkinsa a kanta.
Kuka ta ke yi kamar ranta zai fita har muryanta ta sauya, sannan ta mike ta kashe wayar ta maida ta ma'adananta.
Ta kuma maidata maboyarta, kuma a wajen ta dauko wani abu a nannade da kyalle ta warware shi. Sai ga hoto ya bayyana na jikin hoton yana tsaye a kamar studion ne akwai mutane a wajen.


Yana sanye da kayan kwallo riga da wando ja da fari da takalmi ja mai igiyoyi.
Ya ɗaga Kofi a sama ya na ɗan mirmishi a kasan hoton an saka.
MANSOOR AJI GOMBE UNITED CAPTAIN!
lokacin da Katsina pillars suka zo suka buga wasan cikin gida suka kuma ci su da bugu uku ba ko ɗaaya kuma duka bugun kwallon nan Aji ne ya buga su a raga.


Rumgume hoton ta yi tana ji zuciyarta na bugawa sama sama. Tunaninta kuma ya tafi akan shin kamar yadda take bibiyan rayuwarsa shima ya na nibiyanta haka?
Tsintar Aji a duniyar kwallon kafa ya sa ta sare ta yarda da mganarsa ya sauya mafarkinsa tuni. Ita ce shaidan yadda Aji ya so zama soja ƙwallo ma ra'ayin Mu'azzam ne ba ra'ayin Mansoor ba, kuma ko a baya ƙwallo bata burgeshi duk ya na buga ƙwallo amma tasan ya na zuwa kallon ƙwallo sosai.
Sai gashi rana tsaka ta ganshi tsamo tsamo acikin ta, duk me ya faru bayan rabuwarsu?
Shi ne ba ta da wannan amsar ta jima Rumgume da hoton tana kuka kafin ta gaji ta nannade hoton ta kuma maida shi ma'ajiyarsa. Sallar isha'i ta yi yunwa take ji har ta fara ganin jiri.


Shi ya sa bayan ta idar da ta ji Baaba Uwani na buga mata Kofa taje ta buɗe
Abinci ta kawo mata sai ta ce ta koma da shi ta haɗo mata tea ne.
Sai ta Juya ta na fadin"Binta ki fito falo Hajiya fa ta damu."
Cikin dashewar murya ta ce"Ki faɗa mata kar ta damu da ni ina lafiya."
Daga haka ta juya ciki ta koma ta zauna ta yi tagumi. Tana tunanin makomar rayuwarta anan gaba, ko ta amince ko kar ta amince rabuwarsu da Mansoor ta har Abada ce kuma da gaske yake yi da ya ce zai gogeta daga tunanin sa da mafarkin sa gabaɗaya.


*****


*08 Feb 2022.*
6:00pm


Yana studio ɗinsu yau sun yi afternoon training ne ya samu wayar mijin Bintu Bashir yana faɗa masa tun safe Bintu ta rufe Kitchen ta kuma ɓoye makulli ta ce ta ga wanda ya isa ya dafa abinci ya ci acikin gidan nan, Bashir ɗin ya ce ya yi ta roƙonta bata saurare shi ba, sai yaji ransa ya ɓaci daman ya na ta so yaje gidan sai kuma wasu abubuwan suka ɗauke masa hankali.
Amma tunda abun har ya kai ga haka ai shike nan zai je gidan yaji ta inda iskancin na Bintu ya fara.


Coach ɗin su ya sanar ma zai je gida ana nemansa daman da mashi ɗinsa yazo sai ya sauya wandonsa jikinsa daga gajere zuwa dogo tunda gidan surukai zai je kuma a matsayin sa na babban yaya ya rike girmansa. Cikin lokaci ƙankani ya iso gidan tun da nan anguwan Arawan ne daga can baya ba su da nisa daga gida.
A kuma Kofar gidan ya ci karo da Bashir ɗin yana jiransa. A yadda ya gansa duk ya yi wani firgai firgai sai ya fahimci Bintu na iskanci kala kala acikin gidan nan tunda har mijinta na tsoronta.


Gaisawa suka yi bayan sun yi musabaha Bashir ɗin ya fara faɗin "Wato yayanmu lamarin ne ya fara fin karfina. Wajen sati ɗaya gidan nan ba ma zaman lafiya."
Mansoor ya kaɗa kai kafin ya ce"Ka yi min izini mu shiga gidan tare."
Ya na jin haka ya fara sosa kai yana Faɗin"To to shike nan Yayanmu ammh don Allah kar ka ce za ka yi mata faɗa a bi ta a sannu." Takaici yasa ya wuce yana faɗin"Kai dai ba ta gagare ka ba? to ni ba za ta gagare ni ba don ubanta."
Ya na faɗin haka lokaci ɗaya ya yi sallama acikin gidan. Bashir na binsa a baya jikinsa na faman rawa..


Uwar gidan Bintu ce a tsakar gida ita ta amsa masa sallamansa, ba saninsa ta yi ba domin bata ta taɓa ganinsa a gidan ba amman ganin yadda ya shigo gidan ga Bashir a bayansa yana wani sunne kai.
Kafin ma ta yi mgana ya yi saurin tare ta da cewa"Hadiza. Yayan Bintu ne"
Kai tsaye ta kallesa tana faɗin"Ayya ina yini? Bai kalleta ba ya ce"Barkan mu da yamma, ina ne ɗakin Bintun?
Ya faɗa ya ma kallon Bashir saboda shi dai yasan gidan ammh bai taɓa shigowa ba, shima abin da ya sa ya sani saboda Mu'azzam sun ne taɓa wucewa ta kofar gidan ya nuna masa ya ce ga gidan da Bintu ke aure. Da dai Mu'azzam ne shi kam kamar wani mace gida gida na mata ya iya shiga.


Bashir na gaba yana bayansa har ɗakin Bintu Hadiza ta bi su da kallo, ko shi ne yayanta ɗin ɗan ƙwallon kafa wanda a kace zuwa da shi garin aka yi? domin ta san ɗayan yayan nata ɗan sanda ne tun da yana zuwa gidan in yazo garin, kuma ga dukkan alamu wannan bashi da wasa, kuma sai yanzu ta ga kamansu abu ɗaya ne ya bambamta su ita Bintu fara ce shi kuma baƙi ne. Taɓe baki ta yi domin ita abun ya isheta Bashir ya zama sallamame tsoron Bintu yake ji, bai iya wani kuzari in tana wajen shi ya sa take yin abin da ta ga dama.
Ita dai ta faɗa masa ta gaji, ko ya ɗauki mataki ko ta bar masa gidansa ya zauna da yar so Bintu.


Duka duka s haihuwanta ɗaya ne ya karo mata kishiya da fitinanniyar yarinyar nan tunda ta shigo gidan ta daina barin su cikin sukuni. Tana kokarin shiga ɗakinta bata san mai ya faru ba taji muryan yayan Bintu cikin tsawa yana faɗin"Ina za ki je kuma? dawo nan ki zauna munafuka."
Kuma ta ji ko motsin Bintu bata ji ba, a ranta tace kila dai wannan ne mai maganinta. Tana yar dariya ta shige ɗakinta.


Abin da kuma ya faru shine suna shiga ɗakin nata, Mansoor ya zauna a falo Bashir kuma har ya mike jikinsa na rawa zai je ya kirata sai ga ta fito.
Sai dai jikinta ya yi sanyi da ta ga Baban Inna ai ta shiga uku. Sai ta juya da sauri za ta koma shine ya daka mata tsawo ya ce ta dawo ta zauna. Sai gata ta dawo sumi sumi jikinta na rawa ta zo ta zauna kan kujera ta kuma ga mijinta a ƙasa wani kallon da Baba inna ya yi mata ta bakin ta yasa ta sauko kasa bata shirya ba.


Gyara zamansa ya yi shi cikin kaushin murya da ba wasa ya kalli Bashir yana faɗin"Me ya faru ne? Ka yi mini bayani tun daga farkon rigimar har zuwa yau.
Bashir ya gyara zama ya fara faɗin duk fa rigiman akan less ne da ta gani a jikin Hadiza ne shine ta saka rigiman ya ci amana ya siya ma Hadiza leshi bai siya mata ba, shi kuma ya rantse mata da Allah ba shi ya siya ba da kuɗin adashenta da ta kwasa ta siya saboda ƙaninta zai yi aure.
Shi ne Bintu taki yarda ta rika zage zage tana cewa ya ci amananta shima sai ya siya mata wannan leshin za'a zauna lafiya, ganin abun nata yaƙi wucewa ya sa ya ce in ya samu kuɗi zai siya mata amman ta ce ba ta yarda ba har abun ya kai yau ta rufe kitchen ta ce ta ga mai girki a cikin gidan balle aci abinci."


"Wlh karya yake yi, shi ya siya mata saboda cin amana..!"


Kafarsa ya saka ya hambareta ya ma manta ba a filin ƙwallo ya ke ba, da ace da karfi ya haureta da sai ta ci haɓo da bakinta.
Cikin tsawa ya ce" Ashe baki da mutumci ban sani ba? mijin naki kike ƙarya ta wa?
Ya faɗa cikin takaicinta yarinyar nan fa ta yi nisa. Ita kuma sai ta koma gefe ta fashe da kuka tana faɗin"Wlh ba gaskiya ya faɗa ba, shi ya siya mata ni dai na ce wanda ya zalunce ni ban yafe ba."


"In kika ƙara mgana ba tare da nace ki yi ba, na rantse da Allah sai na yi biji biji da rayuwarki anan wajen."


Ya faɗa mata cikin tsawa ganin yadda yake huci ya sa ta shiga taitayinta kar ya yi ƙwallo da ita ya za ta ko ball ce ya samu, ta kuma san shi da bakar Zuciya kamar Kuturi ya yi zuciya to sai fa ran kowa ya ɓaci.
Shi ya sa ta koma gefe ta yi shuru ta na hararan Bashir kamar Idanuwanta za su faɗo. Ba dai ita zai haɗa da Baban Inna ba, sai ya gane kuransa. Kuma duk yana ganinta ta na harare harare, kuma abun haushi Baahir din na bata hakuri da hannu.
Sai ya ji ba Bintu ba ce abun duka harda Bashir din tunda ya fahimci sakarai ne.
Bai yi mgana ba sai da ya saka Bashir ɗin ya kira matarshi Hadiza.


Ta sako hijabinta tazo ta zauna itama ta tambayeta ta maimaita abin da Mijinta ya ce ta karishe da faɗin "Wlh ni na siya leshin nan da kuɗina, ba Baban Afra ya siyamin ba gaskiyan magana kenan." Ba domin Baban Inna na wajen ba mikewa za ta yi ta karyata su ammh tasan ta sake magana sai an yi abun kunya a gaban kishiyarta.
Shuru ya yi na wani lokaci kafin ya kalli Bintu ya na faɗin "Ba ki da kaya ne da za ki ta da rigima saboda leshi? Ko a tsirara kike yawo ba mu sani ba?
Bintu ta yi kwalkwal kafin ta ce"Ina da shi, amma Baban Inna."


A tsawace ya ce"Ke sunan nan ya fita daga Bakin ki ko naci ƙaniyan ki wlh."
Daga nan ta san kuskuren da tayi da sauri ta gyara da faɗin" Yayanmu shi ya siya mata fa, kuma ai ina da haƙƙin nima ya siyamin tun da adalci aka ce ayi."
Ta gama faɗa ta na harare harare. Cikin jin haushi ya ce"To na ji ya siya mata ke bai siya miki ba sai aka yi ya ya? uwarsa ce ke da dole sai ya siya miki duk abin da bai yi niyya ba? In ma ya siya mata da ita kika zo gidan kika gansu kuma gidansa ne yana da Ikon ya yi abin da ya ga dama, kin rufe kitchen kin ce ba wanda ya isa ya ci abinci nace abinci daga gidan Wanzamai kika zo da shi?. Na ce daga can kika zo da shi?
Ya karishe faɗa cikin tsawa sai Bintun ta saki kuka za ta sake mgana cikin ƙara daka mata tsawa ya ce"Ba da ke nake mgana ba?
da sauri ta ce"A'a.


Kai tsaye ya ce"To ashe iskanci ne a cikin kanki ban sani ba, ba ki da mutumci na jima ina jin labarin ki kuma daman ina jiran wannan ranar, daga nan wajen wallahi na kashe wannan mganar, ko da wasa kika kara tada mganar leshi na ji labari zan yi miki abin da ba ki yi tsammani ba, sannan ki ɗauko Key din kitchen ki ba ma mijinki ki kuma bashi hakuri, sannan kar na sake jin kin fito kin yi zage zage ko rashin kunya, kin sanni kin san halina ba ni da kyau ko nayi wanka kika bari na kara takowa cikin gidan nan sai nayi miki dukan mutuwa wlh, kuma kinsan ina faɗar abinda zan iya aikatawa ne ba wanda bazan iya ba."


Ya karishe faɗa lokaci ɗaya yana mike wa Bashir ma ya miƙe shima da sauri yana faɗin "Ai Yaya Mu'azzam ma ya kirani ya ce shi zai siya mata leshin ma."
Da sauri Mansoor ya ce"Ba zai siya mata ba sai dai ta mutu, hakkinta baya kan mu yanzu ya na kan mijinta ne, abin da ka yi mata ta yi hakuri da shi, zan kira shi Mu'azzam ya siya mata leshinan shima sai na ɓata masa rai."
Ai daga Bintu har Mijinta ba wanda ya samu bakin mgana Hadiza kuma sai jin daɗi take yi a ranta tana faɗin daman akwai mai maganin Bintu haka aka barta tana iskancinta.


Har sanda zai fita sai da ya juyo ya kalleta yana faɗin"Ki natsu ki zauna lafiya kar ki kara tada ma Inna da Baba hankali in ba haka ba kin fi kowa sani na."
Daga haka ya fice Bashir ya bisa, Bintu ba ta saki baki tayi ihu ba sai da ta tabbatar da Baban Inna ya bar gidan.
Sannan ta kwanta anan in da ya barta tana kuka Hadiza ta mike ta na yar dariya ta fice daga dakin. Bashir kuma daga raka Mansoor bai dawo ba yana tsoro.
Shi dai Mansoor ya faɗa masa in bai gyara gidansa ba wani na waje ba zai iya zuwa ya gyara masa gidansa ba. Bintu tasan halin Baban Inna wajibi yasa ta fito da key ta mikama Hadiza sannan bakinta gum.


Sai dai Bashir ne ya gane bashi da wayau ta fara gaba da shi, shi kuma yana ta bin ta yana ba ta hakuri, ita bakincikinta ɗaya faɗan da Baban Inma ya yi mata a gaban kishiyarta, Har Mu'azzam ta kira tana kuka ta gaya masa lallashinta ya yi shima yana faɗa mata yadda Yayan nasu ya kirashi ya yi masa faɗaan cewan da ya yi zai raba gardama da siyan leshin. Daman Mu'azzam ne ke biyema iskancin Bintu ya yi ta lallashinta, dole dai ƙanwar naki Bintu ta hakura da maaganar Leshi.


Haka ta je gida tana Inna abunda Baban Inna ya yi bai kyauta mata ba, zaginta ya yi ta yi a gaban kishiyarta.
Inna meri ta ce"Dakyau gwara da ya yi miki haka tunda sakara kike mara wayau."
Saboda Inna ta goyi bayan ɗanta ya sa bata daɗe ba ta gudu gidan Yaya Amina.


Itama nan ta sanar mata da abin da aka yi mata, itama dai hakuri ta ba ta to wa ya isa ya ce Baban Inna bai kyauta ba?
Ko su Inna bai faɗama ya je gidan ba ammh kowa fa ya ji daɗin haka tunda Bintu ta natsu tana tsoron ta kara wani abu Bashir ya sanar da Baban Inna ta shiga uku.
Wai kura ma tayi lafiya kenan da ace a baya ne kila sai ya barta kwance zai bar gidan.


*BOOK 1 FREE NE, 2,3 PAID NE REGULAR N500, VIP 1K NE, KU BIYA KUƊIN KARATUN KU TA WANNAN ASUSUN BANKIN 0552179550 JAMILA UMAR GT BANK, SANNAN SAI KU

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login