Showing 30001 words to 33000 words out of 103785 words

Chapter 11 - IDAN AN CIZA..! Part 1 Complete by Janafty.txt

Janafty   

20 Dec 2024

4788

kafin ta ce"Kun fasa tafiya can tudun wadan ne? Sai ta girgiza kai kafin ta ce"Ya ce yana wajen Yaya Mansoor in sun gama zai taho."


Bintu na jin an ambaci sunan shi ta yi saurin cewa"Baban Inna, uhm ban faɗa muku abin da ya yi min ba?
Nan ta shiga ba su labarin faɗan da yaje ya yi mata a gaban kishiyarta da mijinta.
Cikin takaici Binta ta ce"Ni ba abin da yafi ban haushi sai cewan da ya yi sai ya yi biji biji da ni na kara mgana a wajen."
Jummai ta ce "Kan uba, shi fa daman masifaffe ne, har yanzu bai daina masifarsa ba." Halima ta ce"Ya rage masifa amma ya kara ninka bakar zuciyarsa."
Hibba na jin su ta na dariya sau ɗaya ya taɓa zuwa gidanta na kano sai dai su hadu in sun zo garin nan. Ta san shi tun suna yanmata tunda suna zuwa gida nan.
Ita dariyansa ne ba ta taɓa gani ba, Kamar baya son zama acikin mutane ne.
Nan aka buɗe caftan Baban Inna ana ta gulmansa.


Hibba na saurare tana dariya farar mace ce doguwa mai kyau da ita ga gashi da ka ganta ka ga bafullatan gombe.
Suna cikin mgana Inna Meri ta leƙo tana faɗin " Duk ina jin ku, ku gama za ge min Babana na gode."
Sai gabaɗaya suka saka mata dariya har da Jummai tana faɗin"Ni dai inna ban da ni kar ki hanani tsaraban Mu'azzam"
Domin jummai akwai son abun duniya zata iya kwantar da kanta saboda abun duniya.


*An samu kuskure a page 1, in da na ce Mimi ta karanci Mass communication Faculty of Sciences, kuskure ne zan ce ne a faculty of Social Sciences*








*Janafty*
*IDAN AN CIZA..!*


*Wattpad:Jamilaumar315*
*Arewabooks:Jamilaumarjanafty*
*Mallakar:Janafty*


*SADAUKARWA GA HAJIYA AISHA AHMAD IYA*


MMN MUJAHID KAYAN MATA AND SUPPLEMENT


SHIN KINA DA LABARIN MACCE MAI GYARA DABAN TAKE GA ZUCIYA MIJIN TA
MUNA DA KAYAN MATA MASU ZAFI NA BUGAWA GA JARIDA


HAJIYA TA KUDI DA KUDI AKE NEMAN SU


INA MASU FAMA DA MATSALA RAMA BA GABA BA BAYA KINA ZAUNE ANA KWATANCI DAKE KINA CI BAKI KOSHI MUNA DA MAGUNGUNA DA ZUMA 3 IN 1 KIBA BRST HIPS TA CIKO MIKI KU INA KIYI FRESH MUNA DA KWAYOYI MUNA DA GARI DUK MASU CIKO JIKI NE KIYI DUM


INA MASU FAMA DA MATSALA BRST KU TSUHU YAFI SON YAGA NONO A TSAYE DUK MAI MAGANIN DA TACCE MIKI ZATA BAKI MAGANIN NONO KAI TSAYE YAYI MIKI KARYA CE MAGANIN BRST SAI KIN SHA ADADIN WANDA ZAI MIKI SBD DUK CIKIN GYARAN JIKI NA BRST YAFI WAHALA YI


INA MASU FAMA DA MATSALA SANYI MUNA DA MAGANIN SANYI ORIGINAL




INA MASU ZAMAN BANZA BABU SANA'A KINA KONE DATA KI GA BANZA WURIN TSEGUMIN KALLON STATUS DIN WASU GA DAMA TAZU MUNA HAR GIDA GA WAYAR HANNUN KI KI MALLAKE MOTA MILLION 8 HAR FIYE GA ALBASHI GA RIBA GA KYAUTA KAYAYA KI
08066726866


Follow this link to join my WhatsApp group: https://chat.whatsapp.com/JMpd8nXr7TIDD3ILDXh64z


*Page 6*


Mu'azzam bai shigo gidan nan ba sai bayan la'asar Hibba har ta gaji da jiransa, sanda ya shigo har lokacin Jummai tana bangaren Inna Meri ba ta tafi ba daman Mu'azzam ɗin take jira ko za ta samu kuɗi a hannunsa.
Tsaraba kuma sauran wanda ya rage na bangaren Inna Meri ta raba gida biyu ta ba ta rabi, daman dankali ne sai wake da garin rogo, sai siga da ya kan zo da shi a raba ma yan gida da makota.


Turamen zani guda biyun da ya zo da shi yace ɗaya Inna Meri ɗaya kuma Magajiya kuma an kai mata nata amman a inda Mariya ta sauke kayan kallon banza ta yi musu ta kauda kanta nan suka kwana kuma ba ta kauda su ba, ballantana ta ga abin da ke ciki. Ita babban bakincikin ta ita ce mace ta farko da ta auri Danjuma a matsayin saurayi da budurwa tun ya na matashin sa, amman yau daga karshe ita ce koma baya a cikin gidansa. A ce har wata banzan bassakwata ta zo ta fita matsayi aciki gidanta da tun tana da kuruciya take cikin shi. Sannan karin takaicinta gabaɗaya inna Meri ta siye kowa na gidan da kirkinta, sannan ƴaƴan gidan masu kuɗin duk ta tattare su a ɗakinta ita sai abin da ta raba ta aiko mata da shi.


Ai in da gaskiya acikin lamarinta Mu'azzam ɗan Danjuma ne, ba ita ta haife shi ba in ta rike kayan da AGOLAN ɗanta ya kawo mata tana kan daidanta, amman na wajen Mu'azzam ko na wajen Amina ko Halima ba ta da hakki a kansu tunda ba ita ce uwar su ba, Magajiya duk ta manta lokacin da uwarsu ta rasu da Ɗanjuma ya ce ta rike su tsalle ta da ka ta ce ba za ta iya rike ƴaƴan wata ba. Itama nata sun isheta duk ba ta duba wannan ba sai yau da suka zama wasu take tunanin ba a yi mata adalci ba.
Tana tsakar gida tana jajjagen kayan miyan abincin dare da za ta ɗora Mu'azzam ya shigo gidan cikin shigan kananun kaya gefe ɗaya key ɗin motarsa wata bakar Jeep katuwa ne a hannunsa yana tafe yana kaɗawa shi fari ne sai dai bai kai Mansoor tsawo ba da ka ganshi ka ga Baba Danjuma saboda suna bala'in ɗibar kama da shi sosai.


Cikin ladabinsa ya gaisheta kamar yadda ya saba shi dai ta na amsa masa cikin sakewa ba kamar ɗan uwansa da ta ce gaisuwan reni yake yi mata. Har ya gota ta zuwa bangaren Inna Meri tana kallonsa ji be sa yadda ya zama kato ya yi kiba saboda ya samu duniya. Kwallah suka cika mata ido, kaf ƴaƴanta ba mai jin daɗi a gidan auran sa, har gwara ma Zuwaira akan Jummai ita Jummai ai kullum a gida a ke ba ta, ba ta kawo ma uwa ba. Sai dai ta bi ta karɓe Auwalu ne Namiji babba shi kuma ya ƙi karatu sai yanzu take jin haushin yadda ta zura masa ido ya ƙi makaranta in da yau ya yi karatu da Meri ba ta isa ta rika mata famkama da kudin su Mu'azzam ba, su ma ai da karatun su ke takama, ba za ta manta yadda Danjuma ya rika fama da shi akan karatu ba ya ki yi, Ita kuma ta ɗaure masa kugun yin abin da ya ga dama ga shi nan daga karshe sai buga bugan gini ga shi ya yi aure ya tara Iyalai shima fama yake yi da kansa. Saddiqu ne bai yi aure ba har yanzu ya na can garin Ikko ya na neman kuɗi amman sai ya shekara bai zo ganin gida ba sai dai a waya sai sako da ya ke yi musu wani lokacin, shima ba sosai ba tunda Auwalu ya fi shi tausayin iyaye shi kawai domin ba shi da shi ne.


Mariya ce ta rage a gabanta ita kuma ai ba ta ɗawainiyarta daga karatu har bangaren Surutu ƴaƴan Meri sun ɗauke mata wannan bangaren kuma duk abin da take so suna yi mata ko jiyan ta ganta da hijabi sabo da takalmi ta zo ta na nuna mata da cewa matar Mu'azzam ta kawo mu su ita da Walida, ta san suna kokari amman bakin cikinta ace ƴaƴan Meri ke taimaka mata to na yaushe kuma in taci ta sha su ne, tunda yanzu Ɗanjuma ba kasafai ya ke wanzanci nashi ba, ba kuma kamar a shekarun baya da ya yi suna tunda abun na su na gada ne ba haya ba.
Duk da tuntuni bala'in magajiya ya sa aka raba girkin bangaren har yau har gobe kayan abinci biyu a ke rabawa, ita rabi Meri rabi ciki har ta san ma sauran ƴaƴanta
Kuma har gobe komai in Inna Meri ta dafa sai ta aika mata da shi sai dai in taki ci, ta bar shi nan Mariya ta ɗauka ta cinye. Har ta gama jajjagen ta tunanin yadda rayuwa ta zo mata ba yadda ta yi tsammani ba da gawayi yanzu suke amfani ta fito da murhun gawayin tana kakkabewa dagacan shashen ta jiyo muryan Inna Meri na faɗin.


"Ɗan Inna ba za ka tsaya ka ci abinci ba?
Ɗanwake Walida ta yi saboda kai."


Ta na jinsa ya ce"Sai na dawo Inna, in na tsaya yamma za ta yi."


Ƙaramin tsaki taja. Tana jin wani irin takaici a kasan ranta, Mariya ta ke jira sai ta mata bugun tsiya Jummai ma tunda ta shige har yanzu bata kara lekowa ba kyafci ta yi ita kaɗai ta na girgiza jikinta daga gani za ka san Magajiya ta iya bala'i sannan cutar hassadan dake damunta ne ya sa har gobe ta kasa ganin alherin ƴaƴan Meri ne suka lulluɓe rayuwarta. Ta koma ɗaki kenan taji fitowarsu da mganarsu zuwa shashenta ta ji muryan Jummai na faɗin " Mu'azzam ka taimaka min yara nan duk ba sa zuwa makaranta daga bokon har islamiyan an kore su." Ba ta ji dai me ya ce ba ta dai ji Jummai na ta godiya kamar zata kwanta masa, baƙinciki ya kara cikata ita da ya kamata ya'yanta su ba da, su ne yau za su koma yan maula suna roko a na ba suna godiya.


Muryan Hibba taji kamar za ta shigo ɗakinta yasa zaraf ta ɗaga labule ta fito sai suka ci karo da juna cikin shirinta ga Walida rike da ƙaramar akwatinta sai Mariya dake dauke da Junoir, gabaɗayan sune har da Bintu da su Amina suma cikin shirin fita kila duk tare za su tafi ko kafin ta samu damar mgana Hibba ta rankwafa cikin ladabi tana Faɗin " Sai anjuma Magajiya yau a Tudun wada zan kwana sai jibi in sha Allahu."
Kadahan kadahan ta ce"Allah ya kaimu, ku gaida gida."


Mariya ta kallah cikin jin haushinta Mu'azzam kuma ya fice lokaci ɗaya yana fadin"Ku fito mu tafi in na kai ku daga can zan biya wani waje ne."
Amina ce ta bi shi tana faɗin" Kai Mu'azzam ka ce mu zauna kenan ba za ka dawo da mu ba?. Sun fita can waje suna magana su ma su Binta sai suka rufama musu baya, Mariya ta kallah da ke shirin bin su a fusace ta ce"Ke ina za ki je?
Cikin tura baki ta ce"Za mu raka Anty Hibba can ne, Yaya Mu'azzam zai dawo damu a motar sa."


Wani irin harara magajiya ta sakar mata kafin ta ce"To ki fita ki gani,wlh sai na yi kasa kasa dake acikin gidan nan"
Daga haka ta duka tana zuba gawayi acikin murhun dake gabanta lokaci ɗaya tana kara sakin tsaki, Mariya ba ta da yadda za ta yi dole ta fita waje ta mika ma Bintu Junior ta ce Magajiya ta hana ta zuwa, ba wanda ya damu sanin halin Magajiya duk wanda ke rayuwa a gidan wanzamai ba ma acikin gidan ba har makota su san wacece ita a haka ma ta rage a shekarun baya in ta fara bala'i da masifa sai makota sun ji acikin gida kuma sai su Gaje sun cika tsakar gida suna bata hakuri, abin da ba a taɓa ji ba shine nuryan Inna Meri tana tanka mata daga ita har Baba Danjuma masu hakuri ne da kau da kai daga sha'aninta.


Da Mariya ta dawo haka ta rika jaraba tana zaginta, Inna Mari na cikin bangarenta ita da Jikokinta ƴaƴansu Amina tunda za su dawo ta nan kafin su wuce gida sai suka bar mata yara a wajen ta, sai ta yi kamar ta leka ta yi mgana sai kuma ta fasa sanin Halin Magajiya yanzu nan sai cibi ya za ma kari, ta kuma san ta na zagin mariyan ne saboda ta zo bangaranta to ta isa ta raba ta da yan'uwanta ne? har ƴaƴan Jummai ta jii an zagi ubansu an ce su da uwarsu marasa zuciya, daga nan Jummai ta tarkata ya'yanta zuwa gida. Sai ta koma kan Mariya har su Mu'azzam suka dawo tana jarabarta.


Inna Meri na bangarenta t na ba ma yan biyun Bintu da suka saka rigiman koko da za su sha, sai da ta mike ta dama musu sannan ta zauna ta a zaman ba su, sauran ma suna gani suka ce suma sai sun sha, gabaɗaya yaran sun zagayeta Sanda suka shigo Bintu da mgana a bakinta faɗi take yi.
"Innarmu wai me aka yi ma magajiya take ta bala'i haka?
Inna Meri ta ce" Ina zan sani? Tun fitan ku ta ke ta yi ta gama zagin Jummai da Jummai ta tafi gida ta koma kan Mariya ina ga bai wuce dai yinin da ta yi a bangarena tare da ku." Mu'azzam ya samu waje ya zauna yana Faɗin"Har yau dai Magajiya ba ta sauya ba? Wai bakin ta baya ciwo ne?
Walida tace"Inna mariyan ma ta so bin mu Magajiyar ta hana ta zuwa."
Inna Meri ta ce"Bakomai wata rana sai labari, zata daina." Yaya Halima ta zauna a kasa kusa da Inna Mari ta bangaren dama Amina ta zauna a bangaren hagu, Bintu kuma ta zauna kusa da Mu'azzam Walida kuma na kofar daki ta yi tsaye ba ta zauna ba. Yaya Amina ce ke faɗin"Inna ai ban tunanin akwai ranar da Magajiya zata sauya. Har Baba dai ya gaji da halinta ya saka mata ido."


Bintu ta taɓe baki kafin ta ce"Dan dai ta samu daga Baban har Innan salausalau ne da irin mu ne da tuni ta raina kanta"
Inna Mari ta aika mata da dakuwa tana Faɗin"Mungode ja'ira, ai Annabi cewa ya yi duk wawaye ya gani a Aljannah ba masu wayau ba, kum rayuwar nan duka nawa ta ke? hakuri ribar zaman duniya da na biye mata ai ba ta taɓa biyo ni bangarena ta yi min wani abu ba, ai hausawa suka ce kulawa yabawa ni dai Allahu shi ne shaida na tunda aure ya kawo ni gidanan nake zaune da kowa lafiya, Alheri ne tsakanina da kowa acikin zuciya ta ba ni da niyar cutar da kowa, kuma ina so ku saka ranku a duk in da kuke ku rike gaskiya da amana sannan ku nufi wanda ma ya nufe ku da sharri ku saka masa da Alheri, ku ma sai ku cigaba da ganin Alheri a rayuwar ku har bayan ran ku."
A yadda suka zagayeta za ka fahimci akwai kauna ta uwa da abin da ta haifa a tsakaninsu, Mu'azzam ya yi mirmishi kafin ya ce" Shi ya sa har gobe ba ni da kamar ki Inna ta, Allah ya kara miki lafiya da tsawon kwana."


Suka amsa da Amin gabaɗayan su, Itama ta amsa da Amin tana faɗin" Nima ai bani da kamar ka ɗan Inna Allah ya cigaba da tsare min kai a duk inda ka sanya kafa Allah ya yi maka jagoranci.' Cikin bayyana farinciki ya amsa da Amin lokaci ɗaya yana kara faɗin " Inna in na samu kuɗi zan kai ki Makka kafin ki mutu ke da Baba za ku je ziyara dakin Allah in sha Allahu."
Gabaɗayansu suka amsa da In sha Allahu Allahu ya sha.


Inna Meri kamar ta yi kuka ta ce"Amin Amin Allah yasa muna da rabon zuwa, Baban Inna shima kullum zencen sa kenan Allah ya cika muku burin ku na Alheri"
Mu'azzam ya ce"Mun fara magana da shi, Inna suprice za mu ba ku in sha Allahu."
Yan'uwan suka taya Inna da amsawa da cewa Allah ya nuna mana lokacin.
Hira suka cigaba da yi suna hirar su Walida ta je ta zubo ma Mu'azzam ɗanwake ya zauna yana ci lokaci bayan lokaci yana tsoma bakinsa cikin mganar ƴan'uwansa mata. Inna ya kallah sai faman wahala take yi da yara iyayensu na gefe suna hiran su ko ajikinsu.


Cikin faɗa ya kalle su yana faɗin " Wai don Allah Nanny mai reno kuka mai da inna? tunda kuka zo gida nan ina lura da ku kowacce ta sauke ƴa'yanta sai Inna ke ta faman wahala da su."
Bintu ta ce"Ai sun fi son renin Innan ne ni fa ba domin Bashir ya ce a'a ba da tuni na dawo da su Hassan wajen Innanmu na gaji wlh." Hararanta ya yi kafin ya ce"Dole ki kwaso ki kawo mata mana tunda kin samu jaka ko ita ta ce ki je ki haihu."
rufe baki Bintu ta yi tana dariya Yaya Amina na gefe ta ce" Inna fa ke son kiriniyan yara nan, ko zuwa mu ka yi ba mu zo da su ba sai ka ji ta ce kuka bar ɗiyan ga a gida ba ku zo min da su ba"
Inna na yar dariya ta ce"Kyale su Ɗan Inna rai ne ya kaini, yau in da ba na raye wajen za su je? Wata rana ba za su ganni ba gwara su mori kakar ta su tun yanzu."
Har suna haɗaa bakin wajen faɗin"Ba yanzu zaki mutu ba Inna."
Yaya Halima ta karɓe da faɗin"Ita Inna daman akwai kiran mutuwa ana zaune lafiya."


Mu'azzam kuma ya ce"Inna sai kin ɗauki ɗan Yaya Mansoor ko ƴarsain sha Allahu."
Inna ta ce"Allah yasa, amman na cire rai da ganin Auran Baban Inna, ganin auransa da ya'yansa ai sai mai yawan rai tunda na ga ba shi da niyyan auran kwata kwata."
Mu'azzam ya ce"In sha Allahu zai yi Inna mu ta ya sa da addu'a don Allah."
Inna ta sauke numfashi kafin ta ce"Addua'armu kullum ba ta yankewa a gare ku, Allah ya sausasauta masa wannan zuciyar ya sanya masa salama acikinta."
Suka amsa da Amin gabaɗayan su Yaya Amina tace"Nifa ina tunanin yarinyar nan ce har yau ya kasa cire ta acikin ransa."
Yaya Halima ta ce" kike gani? Yarinyar da ya zo ya tsani jin sunanta. Ranar Babansu Khairi na kallon labarai nake gaya masa Mansoor ya sota tun tana matashiyarta a zamanta hannun kakarta sai dai sun rabu da jimawa, itama fa ba ta yi aure ba har yanzu"


Bintu ta ce"Ba ta yi aure ba mana, amman fa tana da kyau ga iya kwalliya ni dai wlh Saboda ita nake kallon tashar su har ga Allah tana burgeni kuma sun bala'in dacewa da Baban Inna."
Inna na jin su duk

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login