Showing 87001 words to 90000 words out of 103785 words
da itama za ta iya rantsuwa ta ba da shaidan har gobe ya na son Binta kuma dalilinta ne yaki ba ma rayuwarsa haske ko kaɗan sai dai in ina ita ina taran Baban inna da wannan maganar? Ai wannan bakar zuciyar tasa kamar ta kafuran farko ba za ta barshi ya baiwa zuciyarsa abin da take so ba.
"Kin yi shuru Meri, ko kina ganin da matsala ne?
Hajiya ta faɗa ta na kallon Inna Meri, ita kuma sai ta rausayar da kai kafin Ta ce" Hajiya da gaske nake yi da nace komai ya wuce kuma har abada bazan ƙi Binta a matsayin Surukata ba, sai dai abu ɗaya ne matsalan Baban Inna a gaban ku ya yi rantsuwan ko zai mutu bai yi aure ba ba zai iya auranta ba, Hajiya kin san wasu daga cikin hallayarsa kafiya da naci ga zuciya da riko har gobe Baban Inna ya kasa manta abunda ya faru tun daga lokacin rayuwarsa ta sauya ya daina shiga mutane ya koma rayuwa shi kaɗai, ya daina nuna ya na jin daɗin duniyar nan ma Hajiya mun yi mun yi akan ya daina tuna baya ya fuskanci gaba amman har gobe ya kasa gina ma kansa wata rayuwar, kina ganin a wannan halin da ya ke ciki zai karɓi maganar Binta a karo na biyu.?
Inna Meri ta karishe faɗa tana kallon Hajiya itama sai ta kalleta cikin tunani da nazari, Inna Meri ta yi ajiyar zuciya kafin ta ce"Shi ne hanzarina Hajiya, da kamar wuya gurguwa da auren nesa wannan zuciyar ta Baban Inna ni kaina ta na bani tsoro bansan adadin sallar daren da na yi a kan sa ba, ina rokon Allah ya ya ye masa wannan bakar zuciyar ko ya samu shima ya yi rayuwa irin ta kowa" Yadda Inna Meri ta karishe a raunane ya sa Hajiya taji itama jikinta ya yi sanyi sai ta kasa mgana.
Illah kai da ta kaɗa tana faɗin "Kafin rasuwar Kabiru Murja ta jaddaddamin ya ce a yi ma Binta duk abunda ta ke so, ni kuma nan duniya ban ga abunda Binta ta jima ta na so da kauna tare da bege irin Mansoor ba."
inna Meri ta ce"Ikon Allah! A cikin ranta kuma sai tace ai shima har gobe bai daina begenta ba, Hajiya duk sai gwiwanta ya yi sanyi sai dai ta cigaba da gaya ma Inna Meri irin wasiyar da Kabiru ya bari kafin ya rasu har acikin ran Inna Meri ta tausaya kuma ita ba ta da matsala mai yin shine matsalan da kansa. Sai ga Inna Meri sai a'asar su ka bar gidan Hajiya shima Baban Inna ke ta faman kiran wayar Inna Walida ta ɗauka cikin muryansa ta koda yaushe ya ce"Ina Innar ? Lokacin tana ɗakin Hajiya sai ta yi masa ƙaryan tana sallah.
Cikin yanayin maganarsa Ya ce"Ina kuka je na zo bakwa nan gabaɗaya.?
Sai Walida ta rasa bakin mgana Binta na yi mata raɗan ta ce sun je gaisuwa dakyar ta iya ce masa suna cikin gari sun raka Inna gaisuwa amman ga su nan zuwa.
Lokacin Mimi na ɗakin amman hankalinta na kan waya ne, Walida na sauke wayar Bintu ta ce"Da kin sake kin gaya masa in da mu ka je da yau sai yayi biji biji dake."
Walida tace"Ina sane shi ya sa na rasa abin da zan ce."
Allah ya taimaka sai ga Inna Merin ta ce su zo su tafi, Hajiya ta ji daɗi ita da Mimi har bakin get suka rakasu Hajiya na jadaddama Inna Meri sai ta zo da kanta har gida in sha Allahu. Sai a hanya ne suke faɗama Inna Meri Baban Inna ya kira.
Cikin faɗuwar gaba ta ce"Allah ya sa dai ba ku ga ya ma sa in da mu ka zo ba ko?.
Bintu ta ce"Wa zai je ya yi karo da Kura? Ce ma sa walida ta yi muna cikin gari gaisuwa."
Inna Meri ta ce"To gwara hakan, ba na son fitinarsa da yamman nan."
Adaidaita suka hau saboda su Hassan suna zuwa Kofar gidan Wanzamai suka ci karo da shi tare da Baba Danjuma sun fito sallah. Suna ko ƙarisowa wajen su su Bintu na rige rigen gaishe da Mansoor ita da Walida sau ɗaya ya amsa, yana sanye da riga da wando baki da fari a jikinsa. Kansa da Pcap kamar ko da yaushe.
Shi Baba Danjuma bai san Mansoor bai san inda su Inna suka je ba kawai sai ya kalli Inna yana faɗin"Na ga kun jima ne? Ko Hajiyar ce ta tsaida ku? Inna Meri ba ta kawo zai iya cewa wani abu ba kawai sai ta ce"Eh wlh shiyasa mu ka jima." Mansoor ke yi ma Inna barka da zuwa, Sai kawai Baba Ɗanjuma ya kallesa yana faɗin"Daga gidan Marigayi sulaiman Dabo su ke, da yake Mu'azzamu ya yi waya da ita Innar taku ya ce sun dawo shi ne ta ce za ta je ta yi musu gaisuwa na ce hakan na da kyau an yi zaman amana a baya Allah dai ya jikan sa."
Ba su Bintu kaɗai suka tsure ba har Inna Meri, shi ko tun kafin Baba Ɗanjuma ya gama mgana sauran rahaman dake saman fuskarsa ta gushe bai kara mgana ba.
Inna Meri ta tasa jikokinta gaba za su shiga gida da sauri Bintu ta ce"Inna bari kawai mu wuce yamma ta yi"
Sai da dariya ta kusa kama walida wato ta san abin a zai biyo baya dole ta gudu in gari banza ne Bintu sai Inna ta yi mata jan ido take tafiya.
Ita kanta Inna Merin a sanyaye ta shiga gidan suna shiga da Magajiya suka fara cin karo, Mariya ba ta nan ta na gidan Zuwaira, Inna na yi mata sannu da gida dakyar ta amsa Ita walida ma wucewarta ta yi, ita kanta Innar yau ba tsaya bin Magajiyar kamar uwarta ba ta biyo bayan Walida.
Suna shiga ɗakin Walida ta juyo tana faɗin"Inna yau mun shige su mun yi ma Baban ki laifi"
Inna Meri na rataye hijabinta saman Kofa ta ce"An yi masa laifin sai ya zo ya dake ni."
Innar ta faɗa a kufule sai Walida ta ja bakinta ta yi shuru ta yi ciki ita kuma Inna sai ta fara zuba ruwa a buta ta shiga ta kama ruwa daman Hajiya ta yi ta yi su tsaya su yi sallar la'asar Inna Meri ta ce sun sai sun isa gida. Ta fito kenan ta fara alwala sai gashi ya shigo da gif gif da ɗin tafiyarsa kafin ma ta ɗago kanta ta ji maganarsa a masifan ce a saman kanta.
"Inna fisabillahi me kuka je yi gidan nan?
Tana shafan kai ta ce"Gaisuwar mutuwa."
Ta faɗa itama kai tsaye, wani abu ne ya ji ya taso mai cikin kokarin danne abun ya ce"Inna har za ki iya zuwa gaisuwar wannan mutumin?
Inna ta ce"Eh mana ai musulmi ne ɗan uwana ko?
Ta katse shi cikin gajiya da maganarsa zai kara mgana ta ɗaga masa hannu cikin kosawa kafin ta ce"Ka ga na je gaisuwa gidan maƙiyanka sai ka dakeni Mansoor haba don Allah, kai kenan shigen bakar zuciya ko a baya da ka ga na daina hulɗa da Hajiya wlh ba saboda abin da ya faru ba ne, saboda kai ne ba na so in dawo maka da abin da ya wuce ne amman ba domin tsoron fininarka ba."
Ta faɗa kai tsaye kafin ta juya ta cigaba da wanke kafarta, shi kuma takaici ya hana shi mgana. Kirjinsa ke wani suya yana jin hucinsa na fita ta bakin hancinsa.
Sai kawai ya juya yana faɗin"Shike nan Inna ai shike nan kawai."
Gif Gif kamar wani damisa haka ya juya ya fice Inna ta rakasa da harara Ina dalili da sanyin la'asar zai zo ya tada mata da hankali. Ta kuma san tunda ya fusata ya fita an yi yaji sai ranar da kuma aka huce.
Tsab ta idar da alolanta ta shiga ɗaki tana kiran sunan Walida wacce ta leko tana faɗin "Ya ta fi ne Inna?
Ƙaramin tsaki ta ja kafin ta ce" Lokacin sallah ya kure Walida ki fita zuwa alola."
Daga haka ta shimfiɗa sallaya nan tsakar falon ta tada sallah.
*Janafty*
*IDAN AN CIZA..!*
*Wattpad:Jamilaumar315*
*Arewabooks:Jamilaumarjanafty*
*Mallakar:Janafty*
*SADAUKARWA GA HAJIYA AISHA AHMAD IYA*
Ina iyayem yara kuke kuzo MAIDALILI LACE AND THRIFT takawomuku ingantattun overralls bodysuit da longsleeves domin inganfa lapia dakuma kawara suturun yaranku.kamar yanda kuka sani damuna saida overall kisaqa bebynki ki sinkumeshi bakinki alaikum baruwansa da kamuwa da sanyi.akwai na yammadatan yara kamar yan 3yrs dabasan lulluba da sanyinnan kiyuta rufe yaro yana budewa tokizo kisaya musu overrall kawai dare nayi kizura yaro ciki kisamasa sock da saf wannan shi ake kira blanket huta🥰kiyi kokari ki killace yaranki awannan damunar dan gujewa kamuwarsu da damshi.inanan kano unguwar sharada ina tyra kayana ko ina a nigeria.08033627255
*Page 18*
Huci kawai ya ke saki shi kaɗai ransa in ya kai dubu ya ɓaci Inna ba ta kyauta masa ba, ba domin Baba Ɗanjuma ya ga fitowarsa ba, da anguwan zai bari dole ya yi alwala suka tafi masallaci tare ana idarwa saboda kada ma su Baba Sani su tare shi ya yi saurin tashi yana kara waya a kunne kamar yana waya Baba Ɗanjuma yana can yana musabaha da mutane Baba Sani da Baba Ɗanlami kuma ganinsa ya sa suke Allah Allah su fito domin su haɗu amman ko da suka fito ya bar haraban masallacin ma gabaɗaya.
Baba Sani ya jinjina kai kafin Ya ce
"Ɗanlami wai ka lura yaro nan yana gudun mu ne yanzu? Baba Danlami ya yi kayfci kafin ya ce"Wlh nima na lura, ka bar mutum kawai saboda kuɗin da yake ba mu ne duk wata sai ɗan taimako in ya taso, ba dole ya ganmu ya yi wucewarsa ba tunda ga yan maula." Baba sani ya yi shuru kafin ya ce"Laifin duk na Yaya Ɗanjuma ne, in da amana muma fa muna da hakki akan dukiyar yaron nan tunda ai gidan uban mu aka riƙe shi, amma ya tattare komai ko nuna masa matsayin mu ba ya yi yadda ake ba ni labarin kuɗin yan ƙwallon kafa wlh zai iya kai mu saudiya ma sannan ya siya mana manyan gidaje a garin Abuja da motoci."
Baba Ɗanlami sai da ya yi wata yar dariya kafin ya ce"Haba! to ai naga shi ma Yaya Ɗanjuma bai kai shi Saudiyan ba ma sannan bao sai siya masa mota ba, ya dai gyara gidan ya siya masa mashin itama tunda aka sace ai bai kara siya masa ba, kai ko uwarsa Meri ai ba kai saudiya ba mu kuma a suwa? Karan kaɗa miya."
Baba Sani zai yi mgana kenan sai ga Baba Ɗanjuma ya zo wajen sai ya yi shuru hannu ya ba suka yi yi musabaha daman tunda ya gan su yasan da wata mgana.
Baba Ɗanlami ne ya fara faɗin.
"Yaya Danjuma gaskiya ka yi ma yaron nan Mansoor mgana, kamar mu zai gani ya rika wulakantawa? Baba Ɗanjuma ya yi saurin cewa"Anya? Ko dai bai gan ku ba ne?
Baba Sani ya ce" Zencen kake so, ya fa ganmu amma sai ya ɗauke kai ya yi wucewarsa in ma saboda ɗan abin da yake ba mu ne ya ke ganin kamar ya na yi mana alfarma gwara ka gaya masa gaskiya muma muna da hakki a kansa tunda ya tashi a ƙarkashin mu, duk tsiya dai a gidan Wanzamai ya tashi kuma da gidan zai yi tutiya yau ko saudiya ya kaimu bai biyamu rikon da mu ka yi masa ba ahto."
Baba Ɗanlami ya ƙarishe da faɗin"Ka ji zencen gaskiya." Baba Ɗanjuma bai yi mamaki ba sanin halin ƴan uwan nashi kamar waɗanda suka taɓa tsinana ma Mansoor ɗin wani abu suna ta kumfar baki, baya son nana ta mgana ɗaya ya sa ya ba su hakuri yace zai yi masa mgana.
Ashe korafin na su ba ɗaya ba ne nan take Baba Ɗanlami ya kalli Yayan na shi yana faɗin" Shi kuma Mu'azzamu dai ya manta damu? Ko wancan zuwa ma bai bari mun haɗu ba, ina ga ko ya yi saƙo iya kai da Meri saƙon ke zuwa gare ku, domin ba na jin ko Magajiya tana samun wani abu aciki."
Sai alokacin ya buɗe musu ido cikin gargaɗi ya ce"Ko ni da na haifesu ban kwanta a gida na dogara da su ba, suma ai suna da na su uzurin rayuwar duk abin da kuka ga ba'a baku ba ba'a kawo ba ne, wani abun ma ba na sanin da shi ake ɗauka a baku ba yaran nan duka biyu daga Mu'azzamu har Mansoor ɗin ba sa yi min abu ba su yi muku ba ko da ɗinki ne na kaya domin ɗaya suke ɗaukan mu, kune da shigen zarge zarge da tsegumin ku da ya sa kuka kasa fahimtar komai ballantana ku godema Allah Bisa ni'imar da ubangiji ya yi muku."
Yana gama faɗin haka ya yi wucewarsa ya bar su su na raka shi da harara Baba Sani har ya na kwaikwayon maganar Yayan na shi Baba Ɗanlami ya ce"Dankari! Mgana fa ya faɗa mana wato ba ma gode ma Allah kuma sannan mu zuciyarmu ta mutu sannan har da gorim mu ƴaƴanmu su yi mana ɗin " Baba Sani ya yi tsaki kafin ya ce. "Kyaleshi akwai ranar maida martani."
Suna tafe suna ta faɗin mganganu.Suna zagin ɗan uwansu uwa ɗaya uba ɗaya da suke tunanin ya samu duniya zai wulakantasu Ahalin duk tarin alherin da sanadin su Mu'azzam suke samu har gobe ba su gani ba Ƴaƴan na su kowa na fama da rayuwa wasu ma ga iyalai ba aikin yi, shi fa babban yaron Baba Sani Direba ne yau ya na da mota gobe bai da shi, bai da ma takamammen mai gidan da zai ba shi mota saboda tsabar rigime rigimensa, sauran mazan na shi kuma duk ba wani mai ƙwakwaran Sana'a sai Hayatu kaɗai da ya ke sana'ar fenti amman kuma shi kanshi ya sani da iyalansa ko kaɗan ba shi da zuciyan taimakon iyayayensa da ga shi sai matar shi sai ƴaƴansa dangin matarsa kawai da ita suke shanawarsu.
Sauran matan kuma suna gidajen mazajensu suna ji da kansu, wasu ma suna nema ne, shi ko Baba Ɗanlami duk wannan Kumfar bakin da ya ke yi ya na da ya'yan amman ba su iya taimakonsa da komai, tunda Abdurrahim ɗinsa ya na sana'ar sai da kayan wuta, sannan ƴarsa Bara'atu tana auran mai kuɗi sai dai irin makokan nan ne, ita kanta ba ta ci ba ballatana ta kawo gida. Amman ba'a taɓa jin suna mgana kan ƴa'ƴansu ko samu suka yi ba su taɓa nunawa a gani bar su dai ko da yaushe idanuwansu na kan Mu'azzam da Mansoor gani su ke yi kamar suna kawo ma Baba Ɗanjuma wani duniyar ne su ba ya ba su, ko kuma suna ware su ba sa ba su kuɗi tunda su gani suke yi wani duniya Mansoor da Mu'azzam suka tara.
*******
Da bacin rai ya isa gidansa, daman kuma a mashin ɗin haya ya zo, motarsa ya kunna ta sai ta fara wani hayaki sai kawai ya barta sai ya kira bakanike mashin ɗin sa kuma ta yi kura sai ya kai wanki kuma yana jin kasalar zuwa sai kawai ya hau mashi ɗin haya zuwa can anguwar. Sai ga shi ya je ya ji abin da ya kusa saka shi kamar ya mutu saboda Haushi shiyasa ko jimawar da ya so ya yi bai yi ba ya yi tafiyarsa dalilin da yasa yana ganin su Baba Sani suna jiran sa kuma in ya tsaya a yadda ya ke jin ɓacin rai zai iya yi musu ba dai dai ba, in kuma ya yi musu mgana yana cikin fushi ya faɗi abunda bai dace ba sai su ji haushin shi shi ya sa ya yi tafiyarsa kawai.
Takaicinsa ɗaya wai Inna har da gayya ta yi na zuwa gidan to ina abun zuwa Allah ya jiƙan rai ga wanda ya kusa kashe miki ɗa Mu'azzam ya faɗo masa a rai daman ya san duk yana sane da duk abunda ke faruwa aiko sai ya ci masa mutumci. Sallar Isha'a a gida ma ya yi yunwa ya ke ji amman ɓacin ran da yake ciki ya hana shi ya sama ma kansa mafita. Mu'azzam ya doka ma kira ya na faman huci fushinsa tsab yake son ya huce a kansa.
Mu'azzam na tare da Matarsa Hibba suna yin Dinner sai ga kiran Mansoor ya ɗauka da zumuɗin sa sai dai zumuɗin ya koma ciki domin cikin faɗa da masifa Mansoor ya fara faɗin" Mu'azzam !Mu'azzam! Mu'azzam! Sau nawa na kira ka?
Yana jin haka ya san yau shi kuma sai ya sha masifa. Cikin sanyin murya ya ce.
"Sau uku."
"To ka kiyayeni wlh in ba haka ba sai na ɓata maka rai, bar ganin kana da kaki, kakin ka banza ne ni awajena ba ka wuce ƙanina da nake yi ma hukunci in ya yi ba dai dai ba."
Mu'azzam na shafa keyarsa yace"Me na yi ne yau kuma? Cikin kufuluwa Aji ya ce"Abunda ka san ka aikata ashe ba ka da kishin kai ban sani ba? Kai ne ka kira Inna ka na gaya mata wai su Mimi sun dawo ka sakata ta ɗauki su Walida suka tafi gidan wai sun je gaisuwa me ye haka? Me ye alaqar mu da su da har kake wani yaɗa sun dawo? Ba na son wawanci fa Mu'azzam ka sanni sarai." Mu'azzam ya yi shuru ya rasa na cewa in ya yi mgana sai maganarsa ta yi zafi sai kawai ya zaɓi da ya yi shuru haka ya zauna sai da Mansoor ya gama masa masifa da faɗa sannan cikin ladabi ya ce"Allah ya baka hakuri ba da wata manufa na faɗa ma Innar ba, kuma har ga Allah ni ban ma san za ta je ba domin ba ta faɗa min ba."
Mansoor ya yi ƙaramin tsaki kafin ya ce"Ni fa na daina yarda da kai, kai ma ka koma layinsu Nasir, nan ba har lambata ka