Showing 21001 words to 24000 words out of 89213 words

Chapter 8 - Anya Baiwa Ce 2 Complete Hausa Novel By Aisha Adam.txt

30 Nov 2024

5351

sauri ya fara yarfe hannu saboda azaba yasa ƴan yatsu ya tsige ta, nan take wurin ya fara ɗigar da jini. Juyawa ya yi a hankali ya kalli Sarki Abdallah yace, "A samo mini ganyen tunfafiya da tsakin kuka." Tun be rufe baki ba wasu Dogari suka fice a guje, da sauri suka nemo abin da Sarkin Maharba ya buƙata. Suna kawo masa ya ce a nemo ƙwarya ƙarama a zuba ruwa kaɗan a ciki, kamar yadda ya buƙata haka suka yi. Karɓa ya yi ya zuba ganyen tunfafiyar a ciki da tsakin kukar yana murtsukawa, yana gamawa ya shiga ɗakin ya fara yarfawa akan Maryo da Maleek sai kuma wuraren da Tururuwar take bi. Suna nan tsaye suna ganin abin da yake faruwa, ɗaya bayan ɗaya tururuwar suka dinga faɗuwa suna mutuwa. Sannu a hankali Tururuwar duka ta mutu a wurin, Sarkin Maharba yace a ɗauke Maleek daga ɗakin. Da sauri Dogarawan suka ɗauki Maleek hannuwansu na zafi suka fito da shi harabar wurin aka kwantar da shi yana sauke numfashi kaɗan-kaɗan. Da sauri Fulani da taho za ta taɓa Maleek, wata razananniyar tsawa Sarkin Maharba ya buga sai kace ƴarsa domin har ya manta wacece ita a wurinsa, ba ita ba hatta Sarki Abdallah sai da ya kalle shi da mamaki. Sarkin Maharba be damu da kallon da suke yi masa ba, ya ɗebo wani garin magani ya fara barbaɗawa kan wasu daga cikin raunikan dake jikin Maleek sannan ya fara da cewar, "Kafin na barbaɗa maganin da ace wani zai taɓa shi a wajen nan to babu makawa dafin dake jikinsa zai dawo jikin wanda ya taɓa shi, tsananin da zai shiga har sai ya fi wanda shi Majinyacin yake ciki. Da ace yana cikin ɗakin haɗe da waccen." Sarkin Maharba ya nuna Maryo yace, "To da wani abu ba zai same shi ba, saboda ita ɗin FILSIFI ce. Kuma sai na baku magani wanda za ku jiƙa ku sha za ku amayar da dafin da ya taɓa ku." Jiki a sanyaye Me babban ɗaki da ta ci kuka ta godewa Allah ta ce, "Ita kuma yarinyar cen ya za a yi da ita? Domin ina ji a jikina ba ta tana buƙatar kulawa." Sarkin Maharba ya kalli Me babban ɗaki yace, "A wannan yanayin da take ciki duk abin da za a yi mata ba za ta taɓa farkawa ba." Da sauri Me babban ɗaki ta cukumi wuyansa ta ce, "Ƙarya kake me ya sa kake neman ka ɓata rawarka da tsalle?" Sarkin Maharba ya sauke hannun Me babban ɗaki yana gyara wuyan rigarsa yace, "Allah ya taimake ki, iya gaskiyar abin da na sani ita na gaya muku. Ku godewa Allah da Allah ya sa waɗannan Tururuwar ta mutu, wannan tururuwar da kuke gani a ido ba tururwa bace. Mutanenta ne suka zo ta ya alhinin halin da take ciki, Fusatattu ne za su iya halaka duk wanda ya kusance ta. Ba mutuwa tayi ba sai dai tana cikin wani irin hali na ban tausayi, wannan yarinyar da kuke gani zamu barta zuwa safiya a yadda take domin duk abin da za mu yi mata ba za mu iya dawo da ita cikin hayyacinta ba. Idan Allah ya kaimu zan dawo zuwa safiya, zan dawo da waɗansu garin magunguna wanda za a yi mata turare da wanda za ta dinga wanka da su." Sai a lokacin Me babban ɗaki ta gamsu da abin da ya gaya mata. Haka daga ɓangaren Sarki Abdallah da iyalansa. Sarkin Maharba ya tsaya a kan Maleek ya ɗauko wata kwalba da wani koren ruwa a ciki ya zuba a hannunsa ya murje sannan ya shafawa Maleek, tashi tsaye ya yi yace, "Yaron nan za ku iya ɗauke shi amma sai bayan sa'o'i uku, idan ya farko ku bari ruwan ɗumi ya sha daga nan babu abin da zai faru da shi, ita kuma yarinyar cen ku janyo ƙofar ɗakin ku rufe." Yana gama faɗa ya yi wa Sarki Abdallah sallama ya fice daga gidan. Bayan sa'i uku aka ɗauke Maleek aka kaishi ɗakin Fulani Fahima, bayan ya farka kamar yadda Sarkim Maharba ya faɗa haka suka yi masa. Kallonsu ya fara gi ɗaya bayan ɗaya har ya sauke idonsa kan Mahaifiyarsa, a hankali abubuwan da suka faru suka fara dawo masa a ka. Sai a wannan lokacin ya fara jin raɗaɗin ciwukan jikinsa. Kallon mahaifiyarsa ya yi kwallah na ciko idanunsa yace, "Ummi da gaske ne Shukra ta Mutu?" Tausayin ɗanta ne ya mamaye zuciyarta tana girmama irin ƙaunar da Maleek ya yake yi wa Shukra, wani tunani ta yi sai kuma take ganin don ya nuna ƙaunarta ba wani abu bane domin Shukra ta jure abin da ba kowacce mace ce za ta iya jurewa ba, Shukra ta yi jarumtar da sai an tara dubannin mata za a iya samun mutum goma a ciki. A jiyar zuciya ta sauke ta ce masa, "Abdulmaleek!" Da sauri ya ɗago ya kalle ta domin idan ba kunnensa gizo suke masa ba yau ce rana ta farko da ya taɓa jin Mahaifiyarsa ta ambaci sunansa na yanka. Kallonta ya yi yana tattara nutsuwarsa yace, "Na'am Ummi?" Ta ruƙo hannuwansa biyu ta ce, "Tabbas ke namijin da za a nunawa duniya ne. A lokacin baya na ɗauka Shukra hauka take yi na soyayyarka sai a yanzu na tabbatar da zallar soyayyar da kuke yi wa juna. Shukra bata mutu ba sai dai a wannan lokacin tana buƙatar hutu domin Me magani yace kar abar kowa ya shiga wurinta saboda kar a dawo mata da ciwonta sabo." Hannu biyu Maleek ya sa a kumatunsa yana kafe ta da idanu, maganar Maryo ce ta dawo masa da take cewa, "Ina ƙara tuna maka da cewar ni ba Shukra bace, kayi ta gudu me yawa kamar me neman ƙarshen duniya..." Ganin kallon da yake mata ya sa ta yi tunanin kamar ya gano ba ainin gaskiyar lamarin ta sanar masa ba, tana shirin magana ta riski muryarsa a sanyaye yana cewa, "Ummi ba Shukra bace! A da ƙaunar Shukra ta sa idanuwa sun rufe nake ganin yarinyar cen kamar Shukra ce amma sam ba Shukra bace, yanzu ma na ƙara rasa Shukra wataƙila ba zan ƙara rayuwa da ita ba. Yarinyar cen Maryo ce kamar yadda koyaushe take ankarar da ni, na yarda kama da wane bata wane. A fuska ne suke kamanceceniya da Shukra amma gabaɗaya halaye da ɗabi'unsu sun bambamta." Ita kanta ta fahimci abin da yake nufi don haka ta shafa sumaraa ta ce, "Na daɗe ina zargin haka, tun farko abin da ya faru a gidan nan zuciyata ta dasa zargin haka. Amma wacece ita?" A hankali ya wara mata hannuwa alamar be sani ba sannan yace, "Dole musan wacece ita amma ko da ba Shukra bace ina jin tausayinta a raina, jikina yana bata akwai wata ɓoyayyar alaƙa da ita kaɗai ta san wannan alaƙar kamar yadda take faɗa mini, ina tausayin yarinyar saboda halin da take ciki." A sanyaye Fulani ta ce, "To Allah bata lafiya, idan ra warware maji ainihin labarinta." Maleek ya amsa da Ameen yana kwanciya saboda yadda jikinsa yake masa raɗaɗi.


Washegari kamar yadda Sarkin Maharba ya faɗa haka ya cika alƙawari, safiya na yi ya dawo Masarautar Sarki Abdallah kamar masu jiransa haka ya same su cikim shiri, lokacin da suka dunfari ɗakin Maryo take haka Bayi suka dinga leƙe kowa yana son kashe ƙwarƙwatar idanunsa, Sarki Maharba na tura ƙofar ya same ta a cen ƙuryar ɗaki ta zauna ta haɗa kai da gwiwa ta cusa kanta a ciki. Takawa ya dinga har ya je gabanta ya tsaya ya fara cewa, "Yarinya ɗago da kanki." Maryo shiru ta yi bata ɗago da kanta ba, sai da ya yi mata magana sau uku bata ɗago ta kalle shi. Hannu ya sa ya taɓa ta a tsorace ta miƙe tana lalube-lalube, da sauri ya sa hannu biyu ya riƙe sosai jin haka ya sa Maryo ta fara tattaɓa shi har ta kai ga fuskarsa, jin gashi a fuskarsa ya sa ta janye jikinta da sauri a ɗan tsorace. Sarkin Maharba jiki a sanyaye ya saketa ya juya a raunace, ganin haka ya sa Maleek ya saurin cewa, "Baba lafiya menene?" Sarkin Maharba yace, "Tabbas zanen ƙaddarar bawa baya taɓa gujewa ruhin me shi, ita ƙaddara tamkar yadda jini yake gudana a jikin ɗan adama haka ita ma take zaga sassan jikinsa. Wannan yana ɗaya daga cikin shafin ƙaddararta, gujewa ƙaddara kuwa kamar ƙoƙarin gujewa mutuwa ne. A yadda ƙaddara ta samu bawa mafi kyautuwa ya amsheta hannu bibbiyu, domin bijirewa ƙaddarar shi zai kai ga afkawa cikin ƙaddarar da baka yi tsammani ba. Wannan yarinyar da kuke gani ta riga da kurumce kuma ta makance wannan ma yana daga cikin shafin ƙaddararta."


MARYO FANS! I FILL UR PAIN 😢


KWANA BIYU COMMENTS ƊINMA SHIRU🌚


_LITTAFIN NAN NA KUƊI NE DA NAIRA 200 ZAKI KARANTA SHI CIKIN KWANCIYAR HANKALI, ZAKU BIYA TA WANNAN ACCOUNT ƊIN, FIRST BANK 3090957579 AISHA ADAM, ZA'A TURO DA SHAIDAR BIYA TA WANNAN LAMBAR,0706 206 2624, DAN GIRMAN ALLAH IDAN KINSAN ZAKI FITARMUN DA LITTAFI NA YAFE CINIKINKI._
[14/12/2021, 18:47] Ameera Adam🌚: 49...




Cikin ɗimauta Maleek ya buga masa tsawa yana faɗin, "Ƙarya kake yi. Maryo bata kurumce ba, Malam ka fito ka faɗa mana abin da ka yi mata, Idan ba haka ba wallahi sai na hukunta ka." Murmushin Dattijon ya yi ya ƙara taku biyu zuwa gaban Maleek yace, "Yaro man kaza. Kana tunanin akwai wani abu na mugun abu da zan iya aiwatarwa wannan yarinyar? Ka san da wacce kake tare kuwa? Ita ɗin me matuƙar muhimmanci ce ba ɗaya take da sauran mutane ba. Bana tunanin akwai Ɗan adam mutum da zai iya sarrafa wani abu domin ya cutar da ita. A gabanku na buɗe ƙofa na shiga wurinta wannan ya isheku alƙalanci idan ma na yi mata wani abu, sannan kai musulmi ne na tabbata ka yi imani da ƙaddara me kyau da marar kyau. Ka sawa zuciyarka ƙaddarar da ta haɗaku ita ce ta jefa ta cikin wannan halin da take ciki." Jikin Maleek ne ya yi sanyi wani irin tausayin Maryo yake ji, kasancewarsa Jarumin gaske ba kowannen abu yake iya zubdawa ƙwallah ba sai ga shi a wannan lokacin idanunsa na shatatar da hawaye. A hankali ya zame ya zauna daɓas kamar wanda ya samu saƙon mutuwa, ban da hawaye babu abin da yake yi. Fulani Fahima da sauran mutanen wurin jigun-jigun suka yi saboda gabaɗaya jikinsu ya yi sanyi. Me babban ɗaki ce ta nufi ɗakin da Maryo take da sauri don tabbatar da abin da Sarkin Maharba ya faɗa. Tana shiga ita ma Maryo tana yunƙunrin juyowa hannunta na lalube-lalube, da sauri Me babban ɗaki ta riƙota tana cewa. "Ke yarinya kalle ni nan kina jina." Maryo laluba jikin Me babban ɗaki ta fara yi tana jin alamun mace ce ta faɗa jikinta tana rushewa da wani irin kuka. Duk yadda Fulani Fahima ta so daurewa sai da idanunta suka dinga zubda ƙwalla. Me babban ɗaki kuka take sosai tana faɗin, "Yarinya yanzu wai abin da mutumin nan yake faɗa mana gaskiya ne? Kaico rayuwa yau wane irin tashin hankali ne wannan muke ciki." Maryo da bata san me take faɗa ba ban da kuka babu abin da take yi, sai da ta yi kuka me isarta sannan ta ɗago ta lalubo hannun Me babban ɗaki ta kai saman fuskarta daidai kan manyan dara-daran idanunta, ta ɗora akai sai kuma ta sake fashewa da kuka tana ja da baya har ta jingina da bango ta zauna ta sake haɗa kai da bango tana ci gaba da ruskar kuka. Jiki a sanyaye Me babban ɗaki ta juyo ta fito ta same su carko-carko cikin alhini, cen bakin ƙofa ta nufa ta samu wani Dogari ta kira shi, da sauri ya ƙarasa ya russuna cikin girmamawa kamar me neman gafara. Me babban ɗaki ta dube shi fuska ɗauke da damuwa ta ce, "Maza ka je ka kira mini Audullahi." A zabure ya miƙe ya fice daga wurin. Ba a ɗauki lokaci ba Sarki Abdallah ya fito cikin takun ƙasaita yana tafe yana barbaɗar da izzar mulki, yana ƙarasawa Russunawa ya yi a gabanta cikin girmamawa. Me babban ɗaki ta ci gaba da sharce ƙwallah sannan ta sanar masa da abin da Sarkin Maharba ya sanar musu, Sarki Abdallah na gama jin bayaninta ya ɗago ya kalli Sarkim Maharba dake tsaye da jaka rataye a kafaɗarsa, sai wani zabgegen kwari da baka da yake rataye a wuyansa. Sarki Abdallah ya miƙe tsaye zuciyarsa babu daɗi ya leƙa ɗakin da Maryo take ya ji yadda take raira kuka, jin kukanta yake har cikin jikinsa. Kallon Sarkin Maharba ya yi yace, "Babu wani abi da za a iya domin taimakon halin da take ciki, idan da hali ko da idanunta ne a taimaka a bata maganinsu. Menene silar wannan kurumcewar ta ta?" Sarkin Maharba ya gyara zaman kwari da bakarsa yace, "Haihuwarta na tattare da ɓoyayyun lamura a zahirin gaskiya babu wani abu da zan iya aiwatarwa akanta saboda ita ba kamar sauran mutane bace. Tun lokacin da ta zo duniya ƙaddara ke bibiyar rayuwarta, ƙaddara da ta dawo da ita na fi tsammanin ita ta jefa ta cikin wannan yanayin. Daga ni har sauran masu maganin duniya babu wanda zai iya warkar da ita saboda wannan ciwon na ta ba irin ciwon da wani zai iya taimaka mata bane. Amma za ku iya jarraba neman masu magunguna ko za a dace domin ba a san inda rabo yake ba. Ina fatan za a yi mini afuwa ranka shi daɗe idan kalamaina sunyi kaushi" Me babban ɗaki na jin haka ta kuma rushewa da kuka. Babu wanda ya hanata sai da tayi me isarta sannan ta kalli Sarki Abdallah ta ce, "A ɗauke ta akaita sashena ta ci gaba da zama acen a turo mini Bayi uku waɗanda za su dinga yi mana hidima." Sarki Abdallah ya amsawa Mahaifiyarsa sannan ya juya ya sa a sanarwa da uwar Bayi buƙatar Me babban ɗaki. Maleek yana zaune a gefe kamar wani sakarai haka yake bin su da idanu, yana kallo wasu
Bayi suka riƙo Maryo suka wuce Me babba ɗaki na gaba suna biye da ita a baya kamar jela, a lokacin fuskar Maryo ta yi jawur idanuwanta duk sun kumbura saboda kuka. Babu jimawa mutanen wurin kowa ya watse nan fa ƙananan maganganu suka fara zaga cikin gidan masarautar kowa na tofa albarkacin bakinsa, wasu na ganin alhakin waɗanda suka mutu da waɗanda suka jirkata ne ya kama Maryo, ya yinda wasu suke tausayin ta matuƙa. Musamman idan suka tuna yadda makanta ta same ta sama ta ka da girmanta.


Bayan wasu kwanaki Fulani Fahima na zaune a turakar Sarki Abdallah suna hira, ya dube ta yana mata kallon tsaf yace, "Fahima akwai abin da yake daminki amma ban sani ba ko yanzu kin fara ɓoye mini damuwarki ne?" Kanta ta ɗora akan ƙafafuwansa ta ce, "Tabbas ina cikin damuwa matuƙa amma ban san ta ina zan fara ba. Ban san yadda za ka ɗauki maganar ba, bana jin ɗar dangane da amincewa buƙatar sai dai ban sani ba ko Me babban ɗaki za ta amince." Murmushi ya yi yace, "Hala akan yarinyar cen Maryo za ki yi magana?." Yunƙurawa ta yi ta tashi zaune tana gyara kallabinta ta kalle shi da kulawa ta ce, "A kan Maryo ne Ranka shi daɗe. Allah ya taimake ka gani nake ɓoyewa Yaya da Mariƙiyar yarinyar kamar be kamata ba, saboda Me maganin nan da bakinsa yace babu abun da zai warkar da ita, kuma ka ga an saka lokacin auren su Salman. Yanzu kana gani idan lokacin bikin ya zo ba zamu da ita ba, ko kuma su, su zo mana wata rana. Me zai hana kawai a sanar musu da halin da take ciki, ai su musulma ne dole su yarda da ƙaddara." Sarki Abdallah ya dube ta da yanayin damuwa yace, "Ban ƙi ta taki ba Fahima amma mu bari nan da ɗan wani lokaci mu ga ni, za mu ci gaba da neman magani don ba mu san inda za a dace ba." Jinjina kai ta yi ta ce, "To Allah ya datar da mu ya bata lafiya." Sarki Abdallah ya amsa da ameen, sannan ya kuma kallon ta yace, "Bayan wannan maganar sai wacce kuma don har yanzu bakinki da motsi." Kame-kame ta fara yi ya dafa kafaɗarta yace, "Fahima! Me kike son faɗa ki gaya mini." Fulani Fahima ta sunkuyar da kai ƙasa gabanta na bugawa ta ce, "Dama am akan Fulani Babb..." Wata razannaniyar tsawa ya buga mata jikinta na rawa ta ja bakinta ta tsuke, ganin yadda ranshi ya yi mugun ɓaci ya sa ta kalle shi ta ce, "Ina neman afuwa ranka shi daɗe tuba nake." Be kalli wurin da take ba yace, "Ba damuwa amma ki kula." Ta amsa masa sannan ta fara sako masa wata hirar tun yana ɓata fuska har ya sake suka ci gaba da hira.


A kwana a tashi babu wuya haka rayuwa ta ci gaba da gangarawa Maryo ba ƙaramin kulawa take samu a wurin Me babban ɗaki ba, wani irin so take mata da ko sauran jikokinta bata jin su a ranta kamar ita. Ita kanta Maryo ta fahimci a wurin da wacce take, haka suke zaune koyaushe zaman kurame wani lokacin Me babban ɗaki har magana take gwada yi wa Maryo ta ga ko za ta kulata amma sai dai ta ji shiru. Tun Maryo na yawan koke-koke har ta fauwalawa Allah lamuranta, sai dai ta yi wata irin rama ta zabge fuskarta ta yi fayau. Kuma har wannan lokacin sau biyu ciwonta yana motsawa idan ya tayar mata kamar ba za ta yi raina ta dinga aman jini kenan. Sauƙin lamarin da suka samu da ake haɗa mata dana asibiti dukda da farko basu ɗauke shi da wani muhimmanci ba.


(Note: ku tuna shekara saba'in baya Al'ummar hausawa ba kasafai idan ciwo ya samu suke yarda

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login