Showing 87001 words to 89213 words out of 89213 words
Chapter 30 - Anya Baiwa Ce 2 Complete Hausa Novel By Aisha Adam.txt
tuhuma, cikin kuka Maryo ta gyaɗa kai tana cewa, "Mune Ammi" Da sauri ta waiga wurin Sarki Muhammad Safyan suna haɗa ido ya gyaɗa mata kai yana cewa, "Mun ɓoye miki ne ni da Ɗanki saboda na san ki da rikici sai ki ɗaga mana hankali kafin zuwansu."
Fulani Badawiyya ta rungumo su tana godewa da Allah ya bayyana mata Tagwayenta, lokaci ɗaya farinciki ya mamaye zuƙatan ahalin Fulani Maimuna ta fashe da kuka ta rarrafa gaban Mahaifiyarsu Maryo tana neman yafiya. Sarki Muhammad Safyan da kansa ya miƙe ya ƙarasa wurinta. Hannu ya sa ya riƙota sai da ya kaita har bakin ƙofa sannan yace, "Ki fice mini daga ƙasata na sake ki saki Uku. Umarnin gaggawa na baki duk wanda ya ƙara ganin ƙafarta a ƙasarta a kawo mini ita hukuncinta zaman gidan ajiya da gyaran hali na dindindin." Yana gama maganar ya janyo ƙofa ya rufe, sanin halin Zafin Sarkin Zazzau ya sa ba ta yi wata-wata ba ta fice daga Masarautar yara na binta da dutse suna jifanta.
Dillaliya cikinta ne ya kaɗa don ita bata san irin hukuncin da Sarki zai sa a yi mata ba, tana cikin tunani Sarki ya bada Umarni aka fitar da ita tare da tsula mata bulala hamsin. Shi kuwa Duna sakamakon ya yi kashen-kashen rayuka Sarki ya sa aka tura shi gidan yari ɗaurin rai da rai.
Bayan an gama jimami nan ƴan uwa da abokan arziƙi suka shiga nunawa su Maryo kulawa da soyayya, nan aka shiga nuna musu dangi na kusa dana nesa.
Matan Sarkin Zazzau huɗu, Mahaifiyar su Maryo ita ce Uwar gida sai bayan aurenta da shekara biyar da Haifi Yarima Kaleed tana cikin goyonsa Maimuna ta je ta same ta da buƙatar ta taimaka mata akan Sarki ya aureta saboda wasu ƴan Fashi sun yi mata fyaɗe lokacin da suke hanyar tafiya zuwa garinsu da ke Ƙasar Zamfara. Da ƙyar Mahaifiyarsu Maryo ta shawo kan Sarkin Zazzau ya amincewa auren Fulani Maimuna, an yi aurenta da shekara shida ta haifo ƴan biyunta duka mata.
Mahaifiyarsu Maryo da Mahaifinsu Ɗan wa da Ƴar ƙanine dukkansu gadon jinin Sarauta ne na Masarautar Zazzau, su Maryo suna da Ƙanne biyu Mace da Namiji, Nurain da Nu'aima. Gabaɗaya ƴaƴan Sarki Muhammad Safyan goma sha huɗu maza bakwai mata biyar.
Farincikin wurin ahalin Sarki Muhammad Safyna ba zai musaltu ba ririta su Maryo ake kamar tsoka ɗaya a miya, attajirai, ƴan kasuwa, ƴan uwa da abokan arziƙi sai dafifi ake yi wurin zuwa taya Sarkin Zazzau bayyanar Ƴaƴansa.
BAYAN WATA BIYAR
"Lafiya kike ta ɓata fuska waya taɓa mini ke Fulani na?" Sarki Aminullah ya faɗa cikin zolaya don da alama gimbiyar ta shi rikici take ji. Fulani Zaliha ta dube shi hawaye na ziraro mata ta ce, "Don Allah yanzu me ya fi wannan abin kunya? A ce Sirikata na da ciki ni ina laulayi." Kamar wanda aka yi wa busahara haka Sarki Aminullah ya washe baki cikin farinciki yana faɗin, "Da gaske kike?"
"Duk wasu alamu sun gama bayyana yau wata biyu kenan rabona da baƙon wata ga alamomin cikine sun bayyana a jikina." Sarki Aminullah ya ɗaga hannuwa biyu yana godewa Ubangiji, tagumi Fulani Zaliha ta yi ta ce, "Amma kuma idan baka manta ba Maryama ta ce Boka yace ba za ka sake haihuwa ba an ya kuwa ma cikin ne?" Takawa ya ɗan ɓata fuska yace, "Kina nufin kema kin fara gasgata maganar Boka kenan, boka fa ba Allah bane da zai san gaibu. Aiki suke da aljanu suna tura su sama domin sato maganganun da Ubangiji yake yi da Mala'iku. Zancen boka zancan gaibu ne Allah shi kaɗai ya san abin da gaba za ta haifar. Kika sani duk haihuwa ku rinƙa jerawa da Matar Saif kina sauke mini tagwaye." Ai kuwa kamar ƙaramar yarinya haka Fulani Zaliha ta fashe da kuka tana girgiza kai.
Sarki Aminullah yace, "Saƙo ya same na auren yarinyar nan Safiyya (Matar Salman) Ance mini Ɗan Sarkin Nufe shi zai aureta cikin wata mai kamawa." Fulani Zaliha ta faɗaɗa murmushinta tana faɗin, "Allah sanya alheri ikon Allah ka ga lamarin Ubangiji kenan."
Tuni Abu ta riga ta gama iddarta har Yarima Kaleed ya yi maganar aurenta, da Farko ƙin amincewa ta yi sai daga baya ta amince aka ɗaura musu aure, lamarin ba ƙaramin daɗi ya yi wa Maryo ba haka ta tasa Abu tana yi mata shakiyanci kala-kala. Can Ƙasar Zazzau aka kaita cikin Masarautar Zazzau, ba ƙaramar kulawa take samu a wurin Fulani Badawiyya ta ɗauke tamkar ƴarta ta cikinta. Ba ƙaramin karamci Ina Habi take samu daga wurin Mahaifi da Mahaifiyar Maryo ba har ma da al'ummar Masarautar Zazzau bakiɗaya. Sun zama tamkar ƴan uwa sanadin ruƙon amanar da ta yi wa ƴarsu.
Watan Abu biyu da aure aka ɗaura auren Sarki Aminullah da Inna Habi, da farko fir Inna Habi ƙin amincewa ta yi don har da kukanta akan maganar aurenta da Sarki Aminullah, sai da Fulani Zaliha ta yi mata nasiha da nuna mata muhimmancin auren a yanayin shekarunta tun da ba wuce auren ta yi ba, sannan ta amince. Babu wani lokaci da aka ɗauka aka ɗaura musu aure. Fulani Zaliha da kanta ta kai Inna Habi turakar Sarki Aminullah, lokacin da ta kaita sai da ta yi musu tsiya sannan ta fice ta basu wuri. Rayuwa suke cikin farinciki, zama suke na tsakani da Allah kamar ba kishiyoyi ba don dama Fulani Maryama ita kaɗai ce mai tsananin kishi duk cikin matan Sarki Aminullah.
Cikin Maryo ya fito sosai dan har ta shiga watan haihuwarta, cikin ba ƙaramar ƙiba ya saka ba ta yi wani irin haske ta ko'ina ta yi ƙiba. Ganin haka ya sa Fulani Zalina ta sa Saif ya dawo da ita sashenta don a cewarta bai kamata Maryo ta zauna a gidanta ba saboda gudun Naƙudar dare. Ko kaɗan Saif bai ji daɗi ba amma babu yanda ya iya haka ya haɗa mata kayanta ta koma can, sai dai tun da Maryo ta koma shima ya tare a can kodayaushe yana can don wani lokacin Fulani Zaliha har kunya take ji. Sai da ta yi da gaske ta fara fatattakarsa sai ya yi kamar ya yi kuka saboda sam baya son abin da zai nesanta shi da Matarsa.
Satin Maryo biyu a gida Allah ya sauke ta lafiya ta haifo santaleliyar Jaririyarta Mai kama da ita sak, Yarinyar babu inda ta baro Maryo a kammi sai dai ɗan duhun Mahaifinta da ta ɗauko. Farinciki wurin mutanen Masarautar Kano abun baya musaltuwa, lokacin da labarin haihuwar Maryo ya isa Masarautar Zazzau ba ƙaramin farinciki suka yi ba, saboda Murna Abu har ji ta yi kamar ta yi tsuntsuwa. Kwana biyar da haihuwa su Abu suka dira Masarautar Kano tare da kayan barka sha tara ta arziƙi. Abu saboda farinciki rungume Jaririyar ta yi kamar wani zai ƙwace mata. A lokacin da Maryo ta haihu Abu na da cikin wata uku, da daddare suna zaune su biyu a ɗaki Maryo ta dubi Abu ta ce, "Hajiyata ina ce kina kula mini da Ɗan uwa don ke dai na ga alamun yana baki kulawar da ta kamata, kin ga yanda kika zama uwar mata kuwa, don ni har gani na yi kamar da ajiyar mu a wurinki." Abu ta yi dariya ta ce, "Ƴar iska wai yaushe kika yi baki ban sani ba? Wallahi kin bani mamaki wai yau Maryo ke faɗin wannan maganar." Maryo ta kishingiɗa tana faɗin, "Sanin da kika yi mini amma yanzu kafin ki koma yarinyar sai na ƙara kintsaki yanda za ki bawa Ɗan uwana kulawa." Abu ta rafka salati tana tafa hannuwa ta ce, "A'uzubillah yasin kinfi ƙarfina bari na baki wuri, amma duk iskancin mutum sai ya yi arba'in biyu ko uku a gida." Maryo ta yi ƙasa da murya ta ce, "Wallahi da na bi mijina sahunmu a likafa mun wuce gida don an shiga haƙƙin masoya." Daidai lokacin Fulani Zaliha ta shiga ɗakin, Maryo ba ƙaramin kunya ta ji ba amma Fulani Zaliha ta yi kamar ba ta ji su ba ta kwantar da Naufal, kasancewar tun lokacin da Abu za ta yi aure ya koma wurin Maryo lokacin da cikinta ya fara girma sai Fulani Zaliha ta sa Saif ya kai mata shi.
Ranar Suna Jaririya ta ci sunan Mahaifiyar Maryo aka saka mata Rabi'atul Badawiyya, a lokacin Shukra tana goyon Ɗanta Namiji Mai sunan Sarki Muhammad Safyan, an yi shagali na ban mamaki. Mawaƙa da makaɗa sun baje kolinsu suna ta wasanni haka aka yi taron suna aka gama lafiya.
BAYAN KWANA HAMSIN
"Fulani maganar gaskiya yaron nan matarsa yake yi wa jelan nan saboda kina gani da kaɗan-kaɗan ya kwaso kayansa ya dawo gidan nan, ya yi mana zuru ya ji shiru kin ga yace idan ya dawo ai a bashi matarsa su tafi." Ina Habi wacce ta koma Fulani Habiba ta yi maganar cikin ƙasaitacciyar shiga ta alfarma. Fulani Zaliha da cikinta ya fara fitowa ta ce, "Fulani rabu da shi so nake na gyarata sosai don sai ta ƙara sati biyu nan gaba." Inna Habi ta zaro ido waje ta ce, "Sati biyu! Tabdi lallai zan kai ƙararki wurin Takawa don wallahi wannan shiga haƙƙin ba za a yi wa Ɗana ba." Fulani Zaliha ta daidaita nutsuwarta sannan ta ce, "Wai don Allah da gaske yaron nan dalilin dawowarsa kenan?" Inna Habi ta saki murmushi ta ce, "Kina mamaki wallahi idan ba so kike a samo mana da cikin gida ba ki tattara matarsa ki kai masa, yau fa kwananta Hamsin da bakwai." Fulani Zaliha ta yi jim sannan ta ce, "Ai kuwa ba da ni za a yi wannan abun kunyar ba."
"To kuwa gara ki mayar masa da matarsa tun wuri." Gabaɗaya suka saka dariya.
Lamarin Fulani Maryama ya munana, duk mutum mai imani idan ya ga hakin da take ciki sai ya tausaya mata. A cikin wannan watannin gabaɗaya ta ciccizge jikinta, wasu rauninkan sun warke wasu kuwa guraren duk sun ruɓe, tsutsa duk ta fara cin ɓargonta ta rarake naman jikinta. Idan ka bi ta wurin ɗakinta ban da wari babu abin da yake tashi a wurin, lokacin da ciwon nata ya motsa da ta rasa wurin da za ta gaya ta ci, hannunta ta zura ta ƙwaƙwalo ƙwayar idonta tun bata kai ga cirowa ba ta fasa ƙara saboda azaba tana ihu, haka ta gama matagugunta babu wanda ya bi ta kanta, haka ta ci gaba da rayuwa cikin wulaƙanta da tagayyara.
A ɓangaren Jakadiya kuwa hauka take tuburan sai dai abin da yake ƙara haukata ta, tsirowar gashin kanta a duk lokacin da gashin kantabya tsiro sai wani aljani ya zo ya kafa bakinsa a kanta har sai ya zuƙe duk wani silin ga shi.
Ba a ɗauki lokaci ba Fulani Zaliha da kanta ta ƙara shirya Maryo da magungunan gyara, ba ƙaramun kyau ta yi ba jego ya amshe ita da ƴarta sun yi matuƙar kyau. Wata rana da daddare su Fulani Bilkisu suka mayar da Maryo ɗakin mijinta.
"Wai wata sabuwar kunyata kike ji?" Ta cikin mayafi Maryo ta zuro kai tana leƙensa, da sauri ya fisgo mayafin yana janyota jikinsa yana cewa, "Kunnuwana basa amsar sarewar duk wani sauti face na zinariyar macen da babu kamarta, idanuwa na yi mini gizo a duk lokacin da na buɗe su matuƙar ban sauke su a kanki ba. Jikina ya yi maraicin rashinki domin a kowanne sakan gangar jikina na ambaton sunanki, na yi matuƙar kewarki matata amma sai nake ganin kamar ba ki damu da ni. " Kashe masa ido ɗaya ta yi ta ɗora kanta a jikin kafaɗarsa tana cewa, "Harshe na furta kalmomi ne domin bayyana saƙon abin da yake cikin zuciya, sai dai tawa zuciyar na bayyanawa ƴar uwarta saƙonta ne a kodayaushe domin zuciyata da taka a haɗe suke basa taɓa rabuwa. A duk bugun numfashina yana sauka ne da ɗumbin begenka! Mai zai sa na yi rashinka bayan ni da kai abu ɗaya ne? Tabbas so daban yake haka ma ƙauna! Ina ƙaunarka mijina farincikina mai faranta zuciyata." Maryo na gama faɗa ta lumshe masa ido tana kanne masa ido ɗaya, Saif ku san mutuwar tsaye ya yi ƙaunarta na ƙara fisgarsa, rasa abin yi ya yi kawai ya janyota ita da Rabi'a (Nimra) ya rungume su cikin farinciki.
Tammat Bihamdullilah
Komai ya yi farko zai yi ƙarshe a nan na kawo ƙarshen wannan labarin, masoya ina godiya da nuna kulawarku ta hanyar siyan littafina bani da bakin gode muku, sai na ce Allah ya bar ƙauna domin yabon gwani ya zama dole. Tabbas kuɗin ƴan amana ne wallahi na yi matuƙar alfahari da ku saboda ban taɓa ganin labarin nan a kowanne group ba. Na gode da yanda kuka riƙe mini amana Allah ya bar ƙauna.❤️❤️🥰🥰
_LITTAFIN NAN NA KUƊI NE DA NAIRA 200 ZAKI KARANTA SHI CIKIN KWANCIYAR HANKALI, ZAKU BIYA TA WANNAN ACCOUNT ƊIN, FIRST BANK 3090957579 AISHA ADAM, ZA'A TURO DA SHAIDAR BIYA TA WANNAN LAMBAR,0706 206 2624, DAN GIRMAN ALLAH IDAN KINSAN ZAKI FITARMUN DA LITTAFI NA YAFE CINIKINKI._