Showing 63001 words to 66000 words out of 89213 words
Chapter 22 - Anya Baiwa Ce 2 Complete Hausa Novel By Aisha Adam.txt
domin fuskarsa har haɗewa ta yi tai jawur. Ba su gama tsinkewa da mamaki ba suka riske shi ya miƙe tsaye ya fara takawa zuwa wurin da Maryo ke kwance, ba don numfashin da take yi ba za ka rantse da Allah gawa ce a wurin. Tsugunnawa ya yi a gabanta nan take Fadawa suka russunar da kansu ƙasa domin ransu gabaɗaya bai so haka ba ace Sarkin Sarakai, Sarkin da a ƙasarsa ta Najeriya (Nigeria) na alfahari da Masarauta kamar ta Kano mai cike da izzar mulki. Shugabansu da ke gefe ne ya ɗago da kai yace, "Allah ya ja ranka Ubangiji ya jiƙan Mai babban ɗaki, ina ganin a ƙara duba lamarin da maganin da za a yi mata. Muna mai roƙon alfarma ga adalin Sarki, Sarkin mai tausayin Talakawa da ya jinkirta zartar da hukun da zai gudanar yanzu.Tuba nake ranka shi daɗe idan magana ta ta yi tsauri."
Sarki Aminullah ya ɗago ya kalleshi da manyan idanuwansa masu sanyan mutum shiga nutsuwar da bai yi niyya ba yace, "Haƙƙinmu mu kula da rayuka da dukiyar al'ummarmu. Ba zan lamunci ganin yanda jinin bayin Allah yake zuba babu ƙaƙƙautawa ba. Ko a tarihin iyaye da kakanni haka bata taɓa faruwa ba, don haka zan tashe ta inma ta tashi inma na kori waɗannan azzaluman da kaina." Yana gama magana ya saka hannunsa a kan ƙafarta yana ambatar sunanta. Sai da ya yi mata kira uku sannan jikinta ya fara wata irin karkarawa. Kamar wanda aka jonawa wutar lantarki haka ya ji hannunsa ya yi wani zum! Sai kuma ƙudan zumar suka fara yanyame shi suna ƙoƙarin kai masa cizo. A hargitsa ta miƙe zaune tana buga musu wata irin gigitacciyar tsawa tana cewa, "Ku dakata!" Kamar waɗanda aka ƙamar haka ƙudan zumar suka tsaya ƙyam kowanne a inda yake a nan ya tsaya. Tafin hannunta ta buɗe lokaci ɗaya suka fara dawowa kai suna hawa kan hannunta, sai da suka gama ta ruwa tsaf a hannunta ta ce, "Na sallame ku." Da gudu suka fice buuuu! Daga cikin Fadar, hawaye ne ya fara zuba daga idanunta ta kalli Sarki Aminulla da ke tsaye gabanta ta ce, "Daraja tana ga mai babban Matsayi da girma a gare domin kai ɗin ma daban ne. Me ya sa za ka yi mini haka? Sam ban ji daɗin haka ba domin ya kai ni maƙura." Sarki Aminullah ya taka a hankali ya koma mazauninsa Fadawa suka ruɗe da cewar, "Takawarka lafiya Ɗan toron giwa! Gaba salamun baya Salamun Sikari ba kai farin banza, bangon zuma mai nason alheri kowa ya raɓe ka sai lasa. Turare kake sha ƙamshi ƙamshinka ya yi naso har ɗakunan Talakawa." Wani Bafade ne ya tashi ya je ya gyara Sarki Aminullah zaman alkyabbarsa sannan ya kalli Maryo yace, "Wanne ne shi? Ɗan gidan waye kuma mai ya aikata miki?"
"Bakin alƙami ya riga da ya bushe domin rijiyar da ke buƙatar agaji tuni da jima da ƙafewa. A baya ta nemi a gaji da tallafinka a lokacin da take ganiyar ɗaukinka amma sai ka wofantar da buƙatar hakan, alhalin bishiyar na buƙatar tallafi kafin ƙonewarta ƙurmus. Sanin wane ne shi me ya yi mini duk ba zai amfanar da mutum ɗaya daga cikin wurin nan ba domin, babu mutum ɗaya da hakanya shafa." Sai kuma ta fashe da kuka ta ci gaba da cewa. "Ka karya mini alwashina domin ba zan taɓa iya watsa maka ƙasa a ido ba domin kai ɗin mai muhimmanci ne a gare ni. Amma tabbas na ɗaukarwa kaina alwashin bai sha a banza ba." Tana gama maganar ta miƙe ta fice jiri na ɗaukanta taba tafe tana haɗa hanya kamar wacce ta aha ƙwaya. Mamaki ne ya mamaye Sarki Aminullah ya dubi Baushe yace, "Me ne ne matsalar yarinyar nan da take waɗannan maganganun marasa kan gado?"
"Babu wani abu da yake damunta sai dai maganganunta cike suke da ɗaukan fansa. A fusace take da fushi mai tsanani amma tabbas yanda ta faɗa ɗin haka ne kai mai muhimmanci ne a wurinta Allah ya ƙara maka lafiya." Baushe ya faɗa yana kallon Sarki Aminullah.
"A nema mata magani domin nan da kwanaki ƙalilan za a ɗaura mata aure. Don haka dole a san abin yi."
Baushe ya yi jim yana nazari domin yana ganin da kamar wuya gurguwa da auren nesa, don haka ya ɗago yace, "Allah ya taimakeka a iya sani da laluben magunguna na har yau Allah bai sanar da ni irin maganin da zan bata..." Tun bai rufe baki ba Fadawa suka buga masa tsawa suna cewa, "Hattara! Hattara dai Baushe." Baushe ya russunar da kai ƙasa yace, "Allah ya taimake ka a gafarce ni amma maganar yanda take haka na faɗa. Domin bansan abin da zan yi mata ta warware ba." Yana gama maganar Sarki Aminullah ya sallame shi ƙarshe ya sallami zaman fadar gabaɗaya.
Maryo na zuwa gida da sauri Inna Habi ta rungumo tana shafata jikinta da ya yi furu-furu da ƙasa tana cewa, "Maryo in ce dai babu wani abu da yake damunki wani labari ya ishe mini wai kin cen fada a kwance haka ne? Ina fatan dai ƙwarin nan ba su cutar da ke ba?" Maryo ta dafe kanta tana lumshe idanu ta ce, "Ba abin da ya same ni Inna kaina ciwo yake." Hannu Inna Habi ta kai ta dafa ta ji kanta ya yi rau saboda zafi da sauri ta kaita ɗaki tana fitowa ta samu mutane sun fara taruwa har da masu leƙe. Mamaki ne ya kamata amma bata furta musu komai ba saboda bata san abin da suke yi wa leƙe ba.
"Ka tafka babban kuskure da ka tsaya, a tunaninka za ka iya tarar aradu da ka ne? Karka manta tasirinta ya rinjaye naka da ninki biyu. Ba ƙarfinku ɗaya ba domin da ka tsaya ja da bayinta na tabbata sai ta ƙone ka da ƙarfinta domin ta fusata fushi mai tsanani. Na aiko Gurubu ya ɗauke ka domin niyyarta ta hallaka ka gabaɗaya, saboda ka taɓa mata 'yar uwa da Ɗan da take jinsa tamkar nata." Tsohon ya faɗa ransa a ɓace. Salman ban da haki babu abin da yake yi don haka ya ɗago da rinannun idanunsa yace, "Wallahi sai na koya mata hankali saboda waccen abar za ta azabtar da ni haka?"
"Bari ba shegiya bace da Ubanta. Amma idan ka shegantata akwai lokacin da za ka nemo mata uba ka saƙala mata. Yaƙi dan zamba ne domin ba a shigarsa sai da shiri don haka ina baka shawara da karka tunkareta gaba da gaba saboda za ka tunatar da ita babban ɓacin ran da idan ta ganka a gabanta sai ta cinyeka ɗanye." Salman ya dube shi yace, "Yanzu haka zan zura mata ido kenan ta ci bulus?"
"Bata ci bulus ba sai dai bana san ka da yawan gaggawa domin wata ra zai kai ga danasani. Yanzu ka zauna a nan ka ƙarasa jinyar idan kuwa ka koma na tabbata sai ta illata ka. Haka zalika ka yi sake ɗan zaki ya girma domin tuni ta jima da kwaye maka baya, domin ta fahimci shirinmu tun da ɗauke maka matarka a yau ɗin nan. Maganar da nake yo maka a yanzu cikin da ke jikin matarka tuni babu shi saboda tsananin firgitar da ta yi. Sai dai mu bi ta wata hanyar ba wannan ba, domin wannan tuni da babu ita."
Kamar wacce a tsikara haka ta mike ta nufi sashen Fulani Zaliha, bata kula kowa ba ciki har da Fulani Zaliha, tana shiga ta samu Abu a kwance cikin wani yanayi. Jaririnta yana gefe idanunsa a kakkafe suna kallon sama. Gabaɗaya ido suka zuba mata suna kallo abin da za ta yi. Kan Abu ta fara zuwa ta sa hannuwanta biyu ta dafe kanta da ƙarfi sai ta saka bakinta a saitin kunnenta ta hura mata wata irin iska, firgigit ta miƙe tana kalle-kalle kamar me matasalar ƙwaƙwalarwa. Sai kuma ta wata uwar ƙara ta ƙara zubewa a wurin. Hannuwa biyu Maryo ta ɗaga tana godewa Allah domin bata taɓa tsammanin haka ba. Ɗaukan jaririn ta yi ta ɗora shi a ƙafarta ta fara matsa masa ciki take wani farin ruwa ya fara fita daga bakinsa, zuwan can ya tsanyare da kuka sai da kyar Maryo ta lallashe shi bayan ya yi shiru ta miƙe za ta fita har ta je bakin ƙofa ta waigo ta ce, "Kar wanda ya taɓa ta zata warware ta farka da kanta, amma yaron za ku iya ba shi kulawa. Tana gama maganar ta furzo wasu duwatsu guda biyu daga bakinta ta murmushe su a wurin sannan ta fice.
Tana fita ta ci karo da Saif kamar ita yake nema suna haɗuwa ya wurgo mata tambaya. "Me ya sa kika musu haka?"
"Ta yaya zan barsu bayan kowannensu yana buƙatar jin ɗumin ɗan uwansu, idan ka yi haka kamar ka tsorata da lamarinsa ne. Kowacce Uwa ya fi kyautuwa gare ta da ta bawa Ɗanta kulawa." Ta karkaɗe hannuwanta sannan ta bi ta gefe ta wuce.
Bayan wani lokaci Abu garau ta miƙe kamar ba ita, haka ta rungumi Ɗanta tana mamakin kwanciyarta a wurin sai dai babu wanda ya sanar da ita komai. Salman na wurin Dattijo yana ci gana da samun sauƙi, sai dai fir tsohon ya hana shi tafiya a cewarsa sai ya ƙara samun lafiya ya kintsa shi. Sarki Aminullah haka ya rinƙa kiran masu magana ana bawa Maryo don ganin ta warke ta samu lafiya garau. Marasa lafiyar da suka jikkata sakamakon ƙudan zuma suna samun sauƙi waɗanda suka mutu haka Sarki Aminullah ya aika aka yi musu sutura aka binne su tare da bawa iyalansu tallafin kuɗi da kayan abinci.
Kwanci ta shi babu wuya an yi suna Yaro ya ci sunan Sarki Aminullah suna kiranshi da Naufal, ranar suna an sha shagali 'yan uwa da abokan arziƙi daga sassan garuruwa haka suka zo bikin taya murna. Fulani Zaliha farinciki a wurinta baya musaltuwa haka daga wurin 'yan uwanta na nesa da suka zo. Fulani Maryama saboda baƙin ciki ɗaki ta shige ta fashe da kuka Jakadiya na lallashinta tana bata baki, domin wannan shine ga ƙoshi ga kwanan yunwa saboda gabaɗaya ta rasa ta yanda za ta yi ta cutar da yaron. Kamar wanɗanda aka shafewa tunani da tunanin Salman haka kowa ya manta ta shafinsa, kuma tun daga wannan lokacin babu abin da ya sake faruwa akan Abu da Jaririnta ba. Lokacin da Maleek ya zo bayan suna duk wasu abubuwa na shirin biki da ya tambayi Maryo ce masa kawai ta yi ya yi duk abin da ya dace, saboda wani abin na shi ba ƙaramin kunya yake bata ba. Don yanda yake zumuɗin bikin yanda ka san bai taɓa aure ba.
Sannu-sannu bata hana zuwa...
Ranar wata juma'a bayan gudanar da sallar Juma'a aka gabatar da ɗaurin auren Maryo da Maleek a babban masallacin juma'a na gidan Sarkin Kano da ke cikin ƙwaryar garin Kano. Dubbannin mutane ne suka halarci ɗaurin auren wanda ya tara manyan mutane, attajira, 'yan siyasa da dai sauransu. Kafin ranar an gabatar da bukukuwa na al'ada kamar yanda yake wanda ya haɗar da kamu saka lalle da du abin da ya danganci shagalin bikin aure.
Murna wurin Maleek abin baya musaltuwa, haka daga wurin Maryo dukda ta san ba wata zazzafar soyayyar take mata ba amma sai ta tsinci kanta cikin farinciki da annushuwa. Saɓanin Abu da take taya mijinta kishi, don Abu fushi take da Maryo sosai ko magana ta yi mata sama-sama take amsawa. Saif duk wanda ya kalle shi ya san yana cikin matsananciyar damuwa saboda yanda ya rame ya ƙanjame ya lalace. Da Fulani Zaliha ta takura da abin da yake damunsa ƙin gaya mata ya yi. Sai Abu ce ta sanar da ita abin da yake faruwa tun daga farko har ƙarshe, tausayin Ɗanta ne ya kama ta domin ta san idan ta ce za ta yi magana ita kanta ta san bata yi wa kanta adalci ba, kuma Fulani Fahima da wane ido za ta kalle ta? Wannan dalili ya sa ta kira Saif ta rinƙa tausarsa tana ba shi baki.
Ranar ɗaurin aure da yamma Maleek ya aika kiran Maryo, da farko ƙin zuwa ta yi amma Inna Habi ta matsa mata. Tana zuwa ta same shi a babban zaure, mutane sai kallonta suke saboda yanda ta yi shar da ita sai zuba ƙamshi take. A kunyace ta ce, "Barka da yamma!" Shauƙin ƙaunarta yake ji har a zuvciyarsa, ya riƙo hannunta yace, "Da baza ki zo bane?" Ɗagowa ta yi tana shirin ƙwace hannunta ta ce, "Mutane suna kallonmu" Kashe mata ido ɗaya ya yi yace, "Sai me?" Shagwaɓe fuska ta yi ta ce, "Amma ai..." Wata murya ce ta katse ta sakamakon jin yanda ta ratsa gaɓɓan jikinsu gabaɗaya sautin muryar na faɗin, "Don Allah ku taimaka mini azzalumai ne wallahi cutar mu suke son yi." Saif da tsaye a bakin ƙofar ya kalle su yana sakin wani shu'umin murmushi. Jiki na rawa Maryo ta fisgota da ƙarfin tsiya ta maƙureta a bango tana cewa, "Wace ce ke?"
🌚Na baku gari kowa wace oho
_LITTAFIN NAN NA KUƊI NE DA NAIRA 200 ZAKI KARANTA SHI CIKIN KWANCIYAR HANKALI, ZAKU BIYA TA WANNAN ACCOUNT ƊIN, FIRST BANK 3090957579 AISHA ADAM, ZA'A TURO DA SHAIDAR BIYA TA WANNAN LAMBAR,0706 206 2624, DAN GIRMAN ALLAH IDAN KINSAN ZAKI FITARMUN DA LITTAFI NA YAFE CINIKINKI._
[19/01, 19:22] Ameera Adam🌚: 65...
Da sauri Maleek ya ƙarasa yana ƙoƙarin cire Maryo da sauri ta waigo gare shi tana cewa, "Don Allah karka dakatar da ni bansani ba ko an turota ta illata ni, wataƙila kaidin Salman ne." Maleek ne ya sauke idanunsa a kan Matar kusan numfashinsa ne ya ƙafe ya shiga nuna ta da hannu bakinsa na rawa. Daga can ɓangaren matar ta zuba masa ido jikinta na rawa numfashinta na niyyar ɗaukewa ta ce, "Kai... Kai ne?" Tana faɗin haka ta zube a wurin. Da sauri Maleek ya ƙarasa ya tarota ta faɗa jikinsa yana jijjiga ta. Maryo ta kalli Saif da yake kokarin barin wurin tana son ta tambaye shi game da wannan macen da ta gani mai siffarta sai kuma ta haƙura. Kallon Maleek ta yi tana shirin tambayarsa ta ga ya saɓi matar ya ɗauke ta kamar jaririya ya wuce cikin gida. Can sashen Fulani Maryama ya wuce ta ita haka ya tafi ya bar Maryo a soro cikin tunane-tunane iri-iri, saboda gabaɗaya kanta ya gama kullewa. Kafin wani lokaci tuni gidan ya karaɗe da zancen Maleek ya ɗauko Amarya babu lafiya. Babban abin da ya ɗaure wa mutanen gidan kai bayan sun ga ankwantar da Maryo sai ga wata ta shigo. Sai da Maryo ta shigo suka tabbatar da ba ta farkon bace domin waccen sanye take da yagaggun kaya kuma Maryo ta fi ta haske da gogewar fata.Wannan maganganun da ake yi ne suka ƙarasa kunnen Inna Habi tana zuwa jikinta ya yi wani irin sanyi domin tun da take bata taɓa ganin matsananciyar kama irin wannan ba. Ita kanta Maryo abin ya matuƙar bata mamaki, sai dai tana tsaye ta kasa koda motsa ɗan yatsanta ne. Inna Habi ce ta sauke ajiyar zuciya ta ɗebo ruwa ta yayyafa mata domin ji take tamkar Maryonta ce kwance a wurin. Tana tashi ta fara bin mutanen wurin da kallo a hankali ta furta, "A ina nake nan." Tana tuno wanda ta gani ta zabura zata fice daga gidan da sauri Maleek ya kama ta ya riƙe ta gam, ido ta zuba masa ta hau kiciniyar kwacewa tana cewa, "Ina fatan wannan mafarkin kar ya zame mini gaskiya, Ya Allah ka farkar da ni." Maleek ya hura mata iska a fuska lokaci ɗaya ta sauke ajiyar zuciya ta ci gaba da kallonsa kamar ta samu sabuwar hallita.
"A ina kika ɓoye mini tsahon shekaru kin barni ina bulayi?"
"Waye kai?" Ta faɗa tana ƙoƙarin ƙwacewa.
"Na san an cutar da ke amma don Allah ki karki watsawa soyayya ƙasa a ido, ki taimaka ki yi mata hallaci domin ta wahalar da ni fiye da tunaninki." Maleek ya faɗa mata a shagwaɓe kamar zai yi kuka. Idanun mutane yana kallonsu kowa na kashe ƙwarƙwatar idonsa. Maryo da ke gefe ta tsuke fuska ta ce, "Wace ce ita." Don ita gabaɗaya ta manta da cewar ya taɓa iƙirarin ita matarsa ce. Sai a lokacin ta juya ta kalli Maryo, zaro idanunta waje ta yi a tsorace domin ko a mafarki bata taɓa yin tozali da hallita mai matsananciyar kama da ita ba sai yau.
"Shukra ce! Ita ce wacce soyayyarta ta haukata ni har ta makanta mini ido na ce ke ce matata." Inna Habi da ke gefe ta ce, "Wannan ba maganar tsaiwa bace ya kamata mu nemi wuri a yi zancen a zaune." Maleek ƙin sakin Shukra ya yi domin gani yake kamar za ta kwace ta gudu ya sake rasa ta, hannu ya ɗora a kan fuskarta yace, "Inna 'yan biyu suke?" Sunkuyar da kai ƙasa ta yi ta ce, "Suna can wurin Iyatu a bakin kasuwa."
"Wace ce ita?" Maleek ya tambaya a ruɗe.
"Wata tsohuwa ce da nake bar mata yara na tafi aikatau idan na dawo sai na karɓe su." Shukra ta faɗa tana ƙoƙarin kwacewa ta ce, "Lokacin tashinta ya kusa bari na je na karɓo su don idan banje ba sai na ƙara mata kuɗi."
"Aikatau Shukra? Kece kike aikatau? Me ya sa haka me ya sa za ki yi aikatau alhalin kuna da gata?" Maleek ya yi maganar hankali a tashe. Shukra ta saki murmushin takaici ta ce, "Zamana a wurin nan ya fiye mini kwanciyar hankali Maleek, domin rayuwa nake yi mai cike da 'yanci saɓanin rayuwar da na yi a ba..." Tun bata rufe baki ba ya saka hannu ya rufe mata yana girgiza mata kai. Inna Habi ce ta riƙe