Showing 78001 words to 81000 words out of 89213 words
Chapter 27 - Anya Baiwa Ce 2 Complete Hausa Novel By Aisha Adam.txt
yanda muka lafiya a rabu lafiya."
Fatan alheri 🥰
_LITTAFIN NAN NA KUƊI NE DA NAIRA 200 ZAKI KARANTA SHI CIKIN KWANCIYAR HANKALI, ZAKU BIYA TA WANNAN ACCOUNT ƊIN, FIRST BANK 3090957579 AISHA ADAM, ZA'A TURO DA SHAIDAR BIYA TA WANNAN LAMBAR,0706 206 2624, DAN GIRMAN ALLAH IDAN KINSAN ZAKI FITARMUN DA LITTAFI NA YAFE CINIKINKI._
[31/01, 21:41] Ameera Adam🌚: 72...
Sarki Aminullah tattara hankalinsa ya yi wurin Sarki Muhammad Safyan sannan yace, "Wannan wace maganace ina fatan ba za ta ƙetare iyaka ba." Ya yi maganar cike isa irin ta goggun Sarakunan da sarauta ta zame musu jinin jikinsu. Sarki Muhammad Safyan ya saki murmushin taici yana ƙoƙarin danne ɓacin ran da yake taso masa, mayar da kallonsa ya yi wurin Abu dake gefe sannan ya zaro sarƙar hannunsa wacce Yarima ya karɓa yace, "Wannan Sarƙar kince baki ita aka yi, yarinyar da take cikin Masarautar nan ce ta baki, Ina 'yar uwar Sarƙar da mai sarƙar suke? Me ya sa ka killace mini 'ya'ya tsawon shekaru? Me ya sa za ka ɗau fansa ta wannan sigar. Tabbas wannan Sarƙar ta Hasana ce ina ta Usaina da Usainar suke?" Sarki Aminullah ya dube shi cikin rashin Fahimta yace,
"Ya kamata ka fito a mutum ka yi mini bayanin da zan gane abin kake nufi."
Sarki Muhammad Safyan ya tamke fuska kamar ta fusataccen bijimin Sa yace, "An sace mini 'Ya'ya shekara goma sha Takwas baya! Wannan sarƙar da kake gani ba guda ɗaya bace guda uku rak aka sassaƙar mini su masu ɗauke da tambarin Masarautar Zazzau." Sarki Aminullah ya yi murmushin yaƙe yace, "Ta wannan sigar ka ɓullo? Muhammad Safyan!" Sarki Aminullah ya kirashi da wata irin kausasshiyar murya wacce take nuna tabbas maganarsa babu alamun wasa a ciki. Ya ci gaba da cewa, "A yanzu shekaru sun ƙaru girma ya ƙara kama mu bana tunanin abin da ya faru a baya zamu ƙara maimaita shi domin jiya ba yau bane. Wacce riba zan samu idan na rabaka da 'ya'yanka bayan nima na haifa, don Allah idan akwai abin da ya kawo ka ya kamata mu tattauna ba wannan ba." Sarki Muhammad Safyan ya harzuƙa cikin ɓacin rai yace, "Aminullah wannan karon a Uba na zo gare ka ba Sarkin Zazzau ba! Ina tsaye a matsayin Uban da zai tsaya kai da fata domin ƙwato haƙƙin ƴaƴansa. Ka gaya mini ina ka kai mini ƴaƴana?" Sarki Muhammad Safyan ya yi maganar a tsawace har sai da Abu ta tsora.
Sarki Aminullah Ya jinjina kai yace, "Lallai da alama tura za ta fara kai bango amma da alama wankin hula zai iya kaika dare..." Da sauri Sarki Safyan ya katse Sarki Aminullah. Ganin lamarin na nema yamutsa hazo ya sa Saif ya tausasa harshe cikin kwantar da murya yace, "Allah ya taimake ka har yanzu bamu fahimci maganar da kake yi ba, mai zai hana ka yi wa Mai martaba..."
Sarki Muhammad Safyan ya bugawa Saif tsawa yana cewa, "Dakata yaro! Wannan ba maganarka bace karka sake ka ƙara saka mana baki." Saif babu yanda ya iya haka ya ja bakinsa ya tsuke saboda da alama iyayen nasu biyu sun ɗauki zafi.
Ganin an kara samun saɓanin rashin fahimta ya sa Sarki Muhammad Safyan ya kalli Abu ya buga mata tsawa yana faɗin, "Ke wa kika ce ya baki sarƙar nan?" A firgice Abu ta ce, "Wallahi Maryo ce kuma da kanta ta bani ana gobe zan tafi." Ƙirjin Saif ne ya buga da wani irin bugu mai tsanani. Sarki Aminullah ya kalleta cikin damuwa a zuciyarsa yana ayyanawa wannan wacce yarinyar ce da tun zuwanta gidansa ake ta samun matsaloli.
Sarki Aminullah kallon Saif ya yi yace,"Maza ka je ka kira mini Matarka da Mahaifiyarta."
Kamar jira Saif yake da sauri ya fita ya nufi sashen Fulani Maryama hannunsa ɗauke da Naufal, yana shiga wani irin wari ya fara dukan hancinsa da sauri ya tsartar da yawu yana rufe hanci. A gaggauce ya isarwa da Inna Habi saƙon Maimartaba ya fita yana waigen ɗakin fulani Maryama da tsirarun ƙuɗaje suka fara yanyame ɗakin.
Inna Habi tun da suka samu saƙon kiran Sarki Aminullah suka yi hamdala domin warin da suka wayi gari da samunsa ba ƙaramin cika musu ciki ya yi ba. Ba su kawo komai ba amma kuma jin kiran ya basu mamaki domin a iya saninsu Sarki idan ya yi baƙi baya kiran wasu daga cikin gida zuwa Fada. Suna shiga tun daga nesa Maryo ta hango Abu a zaune sai dai duk ta yi baƙi ta rame. Kuka ta fashe da shi ta ƙarasa ta rungume Abu tana ci gaba da rusa kuka. Za ta fara magana Sarki Aminullah ya katse ta cewar,
"Ya isa haka domin akwai muhimmiyar maganar da ke tafe da mu." Fadar ce ta tsit Maryo ta hau wara ido domin ba ƙaramin tsorata ta yi ba tana tsoron kada a ce mata Abu bata dawo da Naufal ba.
Sarki Muhammad Safyan ƙurawa Maryo ido ya yi gabansa na faɗuwa, ita kanta Abu sai yanzu ta lura da wani abu. Tun ranar da ta fara tozali da Yarima ta rasa a inda ta san mai yanayin kamarsa, tsoro da fargabarsa ya hanata zama ta ƙare masa kallo.
Sarki Aminullah ya miƙawa Maryo sarƙar da ya karɓa ya gani daga hannun Sarkin Zazzau. Da sauri ta karɓa tana murmushi ta ce, "Abu yanzu sai da kika cire sarƙar nan da kin ɓatar min fa kinsan ko Inna ba ta san na baki ba." Sarki Muhammad Safyan ya zuba mata ido yana ganin yanda take magana, amma gudin kar ya yi hanzari ya yi shiru. Sarki Aminullah ya katse Maryo da cewar, "Bama son sakarci a wurin nan." Shiru Maryo ta yi Sarki Aminullah ya ci gaba da cewa, "A ina kika samo sarƙar nan." Maryo ta yi shiru ta kalli Inna Habi domin ita kanta ba za ta ce ga inda ta samo ta ba abu ɗaya ta sani Inna na bawa wannan sarƙar muhimminci. Maryo ta sunkuyar da kai ta ce, "Allah ya taimake ka Inna ce ta siya mini tun ina yarinya."
Kallon da Sarki Aminullah ya yi wa Inna Habi shi ya tabbatar mata da yana buƙatar ƙarin bayani daga gare ta don haka ta russunar da kai ƙasa ta ce, "Allah ya taimake ka kamar yanda na gaya maka a baya na tsinci yarinyar nan, a ranar da na tsince ta tare da wannan sarƙar na tsince ta sai wani murjani." Sarki Muhammad Safyan ya yi karaf yace, "Kika tsinceta ita kaɗai ko kika tsince su."
Inna Habi ta ce, "Allah ya taimake ka Ita kaɗai na tsinta tana jaririya." Sarki Muhammad Safyan ya yi kabbara yana cewa, "Tabbas Allah shi ne abin godiya amma ya tabbata wannan yarinyar jinina ce, zo mu ga idonki matuƙar kina da tawadar Allah a idonki tabbas kece Hasana." Maryo da kanta ya gama ɗaurewa da waɗannan mutane masu dajara sai wurga idanu take tana neman da wacce yake magana.
Sarki Muhammad Safyan da kansa ya tako wurin Maryo ya ɗago da kanta yana kallon ƙwayar idonta, Maryo sai gani ta yi ya rungumeta yana furta, "Alhamdullah Allah na gode maka da ka bayyana mini ɗaya daga cikin ƴaƴana da na rasa." Sai kuma ya raunana murya yace, "Ko a ina zan samu Usaina? Ina ma Allah zai bayyana mini ita kamar yanda nake ganinki a gabana." Daga bayansa ya ji ance.
"Ita ma ka same ta domin ita ma tana nan da ranta." Sarki Aminullah ya faɗa murya ɗauke da ƙwarin gwiwa. Da sauri Sarki Muhamma Safyan ya miƙe ya ƙarasa wurin Sarki Aminullah yace, "Don Allah tana ina a wane wurin take." Sarki Aminullah yace, "Idan har wannna Hasana ce to babu ko tantama Matar Maleek ita ce Usaina."
"Waye Maleek don Allah gaya mini shi, tabbas wannan Hasana ce wallahi Usaina tana da cindo a ƙafarta." Sarkin Zazzau ya yi maganar cikin ɗoki. Sarki Aminullah ya yi murmushi yace, "Ɗan ƙanwata ne yake aurenta." Sarkin Zazzau cikin farinciki yace, "Masha Allah yanzu yau ni nake jin daddaɗan labari akan tagwayena, Allah me iko yanzu Usaina har ta yi aure?" Sarki Aminullah ya yi dariya mai sauti yace, "Kana mamaki ne? Ita ma ta gabanka ga mijinta nan." Kunya ce ta kama Maryo da sauri ta sunne kai ƙasa tana murnushi. Haka kawai ta fara jin wani irin farinciki na ziyartarta ganin abin take kamar a mafarki wai yau ita ce take gaban Mahaifinta. Sarki Muhammad Safyan yace, "Ikon Allah ka ce da na yi abin kunya a gaban Siriki." Cikin zolaya Sarki Aminullah yace, "Idan baka yi a gaban wannan sirikin ba ka yi ai a gabana." Kallon rashin fahimta Sarkin Zazzau ya yi masa, Sarki Aminullah da ya fahimci haka sai yace, "Ina nufin ka yi abin kunya a gabana tun da ni sirikinka ne Ɗan wurina ne yake aurenta."
Sarkin Zazzau ya saki baki da mamaki yace, "An ya Aminullah babu lauje cikin naɗi kuwa?" Sarki Aminullah sai yanzu maganarsa ta tsawon shekaru ta faɗo masa da ya taɓa gayawa Sarkin Zazzau lokacin da suka rabu baram-baram dutse a hannun riga. Murmushi ya yi ya kallin Sarkin Zazzau yace, "Dama na gaya maka cikin ikon Allah auratayya sai ta haɗa zuri'armu ta yanda duk wani rashin jituwa ya kau daga gare mu. Allah ne ya yi wannan haɗin kuma shi ya barwa kansa sanin alherin da ke tattare da haka."
Abu da ke gefe wani irin daɗi ta ji domin ta san ko babu komai ta goge tabon ɓacin ran da ta dasawa Maryo a zuciyarta. Ko ba komai tafiyarta ta kawo abubuwan alheri da dama, silar tafiyarta ya sa Saif ya auri Maryo. Uwa Uba kuma ta sanadinta Maryo ta sadu da iyayenta.
Har lokacin Sarkin Zazzau bai gama amincewa da a rashin sani aka yi auren Maryo da Saif ba, gani yake kamar yana da sa hannu wurin sace masa ƴaƴansa. Sai da aka bashi labarin Maryo tun daga ranar da Inna Habi ta tsinceta har zuwanta Masarautar Adamawa da abubuwan da ya faru. Ya matuƙar jinjinawa Inna Habi akan namijin ƙoƙarin da ta yi wurin rainon Maryo da yanda ta bata kulawar da ta dace. Nan take hira ta ɓarke aka ci gaba da ciye-ciye da shaye-shaye. Maryo na hannun Mahaifinta kamar wani zai ƙwace masa ita. Anan ya fahimci irin tsantsar shaƙuwar da ke tsakani Abu da Maryo abin ba ƙaramin birgeshi ya yi ba.
Maryo tana son ta karɓi Naufal amma ta rasa ya zata yi saboda wata irin kunyar Saif da take ji, shi kuwa da sun haɗa ido zai kashe mata ido ya sakar mata murmushi. A wannan zaman ma sai da Abu ta jaddada maganarta na saki a wurin Saif don har ga Allah ta cirewa zuciyarta son ci gaba da zama da shi. Shiru Saif ya yi yana nazari ya riski muryar Sarki Aminullah yana cewa,
"Saif ina gani ka sauwaƙewa yarinyar nan zai fi domin kana gani ta sanadin rashin sakin da baka yi mata bane har ta guje mana ta yi tafiya mai nisa, shi zaman aure na mutum biyu ne idan ɗaya ya nuna ba ya yi shi kenan." Saif ya gyaɗa kai sannan yace, "A yi mini afuwa ranka shi daɗe zan aiwatar da abin da take buƙata amma ba zan iya aiwatarwa yanzu ba." Hakan ba ƙaramin daɗi ya yi wa Sarakunan biyu ba, Sarkin Zazzau har a zuciyarsa ya ji ya aminta da nutsuwar Saif. Daga haka Sarki Aminullah ya sallami yaran ya rage sai sarakunan biyu.
"Lallai Fulani Badawiyya a kwai murna a lokacin da ta yi tozali da ƴaƴanta. Don haka da Hasana za mu tafi kafin saƙo ya isa Ƙasar Adamawa." Cewar Mahaifin Maryo.
"Ai kuwa ba za ta bika yai ba domin yau za a kaita ɗakin mijinta amarya ce ko tarewa bata taɓa yi ba." Ɓata fuska Sarkin Zazzau ya yi ai kuwa Sarki Aminullah yace, "Bar cika kana batsewa duk abinka, Maryo ba za ta bika ba domin yau za mu kaiwa Ango amaryarsa idan ba so kake mu yi masa ta leƙo ta koma ba. Ka bari lokacin da ƴan Adamawa suka ƙaraso sai a haɗasu gabaɗaya a tafi da su ita ma Mahaifiyarsh ta fi gasgatawa." Da wannan shawarar Sarkin zazzau ya amince akan bayan sati guda za su ƙara dawowa. Da farko ya nuna a bari ya kawo Mahaifiyar yarinyar kafin tariyar Maryo amma Sarki Aminullah ya ƙi amincewa domin ya nuna masa an jima da ɗaurin auren tariya ce ba ta tare da wuri ba.
_LITTAFIN NAN NA KUƊI NE DA NAIRA 200 ZAKI KARANTA SHI CIKIN KWANCIYAR HANKALI, ZAKU BIYA TA WANNAN ACCOUNT ƊIN, FIRST BANK 3090957579 AISHA ADAM, ZA'A TURO DA SHAIDAR BIYA TA WANNAN LAMBAR,0706 206 2624, DAN GIRMAN ALLAH IDAN KINSAN ZAKI FITARMUN DA LITTAFI NA YAFE CINIKINKI._
[10/02, 20:04] Ameera Adam🌚: 73...
Duk irin baƙar wahalar da Abu ta sha sai da ta bawa su Maryo labari tun daga farko har ƙarshe, Inna Habi ba ƙaramin tausayawa 'yarta ta yi ba sakamakon yanda ta sanar da su da irin azabar da ta sha kafin zuwanta Masarautar Zazzau har zuwa miyagun ayyukan da Fulani Maimuna take saka ta akan Yariman Masarautar. Maryo ban da kuka babu abin da take yi don ƴar uwar tata ba ƙaramin rama ta yi ba ta lalace ta yi wani irin baƙi kamar wacce ta yi shekara da shekaru tana jinya. Maryo ce ta kalleta fuskar shaɓe-sheɓe da hawaye ta ce,
"Abu me ya sa kika aikata wannan kuskuren? Yanzu da mutuwa ta riske ki me za ki gayawa Ubangiji dangane da haƙƙin mijinki da dana Yarona?" Abu ta goge hawayen idonta ta ce, "Maryo ba zan iya ci gaba da zama da Saif ba kin san yanda nake tun ina ƙarama, ada ma na ɗauki aurena da shi a matsayin ƙaddara da rabo wanda dole babu yanda zan yi har sai Naufal ya fito a tsakanina da shi. Babu yanda ban yi da ke ba akan ki amince da aurensa shi ya sauwaƙe mini amma gabaɗayanku kuka shafawa idonku toka, alhalin ko makaho ya san irin tsantsar ƙaunar da kuke yi wa junanku. Maryo!" Abu ta ambata da wata irin murya har sai da Inna Habi ta ɗago ta kalleta ta ci gaba da cewa, "Fitar da na yi, na yi ne bisa tsautsauyi sai ga shi Allah ya kawo alheri a cikinta. Tabbas na san na aikata kuskure wanda har abada ba zan sake aikata makamancinsa ba, Maryo ashe ba banza ba miskilancinki da son girmanki ba, duk sun samo asali ne sakamakon ku jinin Masarauatar Zazzaune!" Da sauri Maryo ta ɗaka mata duka a cinya tana wurga mata hararar wasa ta ce, "Bana son iskanci fa idan ba haka ba yasin na sa mayar da ke Baiwata." Abu ta saki dariya ta ce, "Idan ke baki mayar da ni ba ai wancen sanganrtaccen yayan naki ya mayar da ni, wallahi karki ga baƙar wahalar da ya bani hatta tsawa idan ya yi sai hanjin cikina ya kaɗa mugu kawai yana yawo tsalo-tsalo kamar tazuge." Maryo ta ƙunshe dariyarta ta ce, "Ɗan uwan nawa ne mugu a gabana Abu."
Abu ta watsa mata harara ta ce, "Yoo meye idan ba mugun ba, wai ma tsaya kina nufin ƴan ubancin za ki gwada mini?" Maryo ta riƙe kunnuwanta biyu ta ce, "Ni na isa na ce wadon Sarki ba tazuge." Abu ta saki dariya ta ce, "Kin isa mana idan aka naɗa mijinki ya zama Sarki abin da ya fi tazuge ma za ki iya cewa babu. Meye a ciki kai da kaya ai duk mallakar wuya ne..." Maryo ta bige bakin Abu saboda kunyar da ta ji don Inna Habi na gefe tana jin su, ta harari Abu ta ce, "Wallahi ke dai bakinki ba shi da linzami ashe dai mai hali baya fasa halinsa." Gabaɗaya suka saka dariya.
A hankali Abu ta fara tambayar su Inna Habi bayan tafiyarta abubuan da suka faru, nan take suka bata labari tun daga farko har ƙarshe har zuwa auren Maleek da Maryo da za a yi da kuma aurenta da Saif. Anan ta fahimci Maryo Amaryace shakaf ko tare wa bata yi ba. Sun jima suna hira Sannan Abu ta dubi Maryo ta ce, "Maryo maza je ki karɓo mini yarona a wurin Mijinki na san yanzu ya fara jin yunwa." Duk yanda Maryo ta so ƙin zuwa fir Abu ta ƙi bata dama babu yanda ta iya ta fita suwa sashen Fulani Zaliha. Bayan ta gaida Fulani kai tsaye ta ce,
"Allah ya taimake ki dama Abu ce ta aiko a duba ko Naufal ya tashi daga bacci." Maryo ta faɗi haka ne don kar Fulani Zaliha ta yi zaton ko ta zo wurin Saif ne haka kawai. Tuni Fulani Zaliha ta harbo jirgin Maryo. Can sashen Saif ta nuna mata ta ce, "Shiga ciki tun ɗazu suna ciki." A kunyace Maryo ta miƙe ta wuce sashen Saif.
Tun da ta shiga ta fara rafka sallama amma shiru kake ji babu amsa, a tunaninta ko gabaɗaya sun yi bacci tun da ta ji shiru ta san Naufal ya yi bacci. Ɗakinsa ta shiga tana sallama ta leƙa uwar ɗaki a cen kan katifa ta hango Naufal yana ta bacci hankali kwance. Murmushi ta saki ta ƙara ta yi masa kiss a goshi ta janyo zani ta rufa masa a jikinsa sannan ta taso ta fito zuwa rumfa, (Falo) kamar daga sama haka ta ci karo da mutum da sauri ta fara ja da baya.
Murmushi ya sakar mata ya ƙarasa wurinta ta ƙara ja da baya har ta tokare da bango. Janyo ta ya yi da sauri yana cewa, "Dama