Showing 39001 words to 42000 words out of 89213 words

Chapter 14 - Anya Baiwa Ce 2 Complete Hausa Novel By Aisha Adam.txt

30 Nov 2024

5346

na tsaka da haɗa kaya Baiwa Tine ta shiga da sallama cikin girmamawa ta miƙawa Abu akushin da Fulani Zaliha ta aikota da shi wanda ta saba aika mata da abinci, karɓa ta yi ta ajiye a gefe sai kuma ta ji jikinta ya yi sanyi, musamman da ta tuna yadda Mahaifiyar Saif take ɗawainiya da ita. Wannan dalili ya sa ta fasa tafiya gida.


Washegari Kamar daga sama Inna Habi ta ji Sallamar Maleek, bayan ya gaishe da Fulani Maryama ya ƙarasa wurin Inna Habi, sam Fulani Maryama bata so haka ba amma ta barwa kanta sai ya ta fi zata cancarewa Inna Habi. Gaisuwar mutumci suka yi da Inna Habi haka kawai ta ji tana ƙaunar Maleek saboda yadda yake bawa Maryo kulawa. Ido ya zubawa Maryo da bata san da zuwansa ba yana ji a zuciyarsa ina ma za ta iya ganinsa har ta buɗe baki ta yi masa magana. Ya jima suna hira da Inna Habi sannan ya tashi ya nufi sashen sauran Matan Sarki Aminullah. Sashen Fulani Zaliha ne ƙarshe ita ma sun jima suna hira sannan ya miƙe ya yi mata sallama. A soron tsakiya suka haɗu da Saif bayan sun gaisa Saif yace, "Ɗan uwa lallai ka miƙe da zumunci ina jin ko wata biyu ba ka yi ba rabonka da nan ya su Ummi." Maleek ya yi murmushi yace, "Kai kuwa ina da mara lafiya ai dole na zo dubiya." A ɗan hanzarce ya kalle shi yace, "Waye ba lafiya a nan?" Da mamaki Maleek ya kalle shi yace, "Maryo mana yarinyar da take kama da matata Shukra." Sunan Maryo ne ya yi masa wata irin kuɗa a kunne har sai da ɗan runtsa idanu, sai kuma ya damƙe hannun Maleek da ƙarfi yana faɗin, "Tana ina?" Maleek be yi mamaki ba ya ɗauka Saif na ta ya shi jimami ne kansa tsaye yace, "Mu ƙarasa na yi musu sallama tana wurin Babarta Inna Habi." A hankali Saif ya maimata, "Inna Habi dai Mahaifiyar Abu?" Maleek sam be ji shi ba sakamakon tuni ya yi gaba yana son ya yi musu sallama don daga nan Garin Zazzau zai wuce.


Tun shigarsu gidan gaban Saif yake faɗuwa yana jin wani iri a jikinsa, a gaggauce ya gaishe da Fulani Maryama sannan suka wuce Ɗakin Inna Habi Maryo na kwance jikin Inna Habi tana tsefe mata kai. Maleek ne ya fara shiga Saif na biye da shi. Tun shigar Saif gidan a zabure Maryo ta miƙe tana lalube-lakube tana buɗe baki alamar tana son yin magana amma ta kasa, kawai sai ta fashe da wani irin tana ci gaba da lalubawa. Hankalin Inna Habi ba ƙaramin tashi ya yi ba tana ƙoƙarin kama Maryo amma tana kwacewa. Saif na arba ta ita da sauri ya ƙarasa wurinta cikin wani irin yanayi ya sa hannu biyu rungumeta a jikinsa, Maryo na jin haka ta sauke wata irin nannanuyar ajiyar zuciya sai dai ko kaɗan bata yi yunƙurin hanashi ba. Ɗago da kanta ya yi ya hurawa idanunta iska, ya sa bakinsa a daidai kunnenta ya hura iskar da ƙarfi nan take jikinta ya fara wata irin karkarwa. Ja da baya ta fara yi tana murza idonta sai kuma ta waiga wurin Inna Habi da take tsaye kamar gunki sakamakon tozali da abin da mijin ƴarta ya yi akan idonta. Da gudu ta tafi ta rungumeta tana faɗin, "Inna kece a gabana nake ganinki." Saif ya ƙarasa ga hanyo Maryo tana faɗawa Jikinsa yace, "Ni ba ki yi maraba da ni ba?"


BILLAHI AKWAI ƘURA GIDAN SARKI AMINULLAH YA KUSA KAMAWA DA WUTA😂




_LITTAFIN NAN NA KUƊI NE DA NAIRA 200 ZAKI KARANTA SHI CIKIN KWANCIYAR HANKALI, ZAKU BIYA TA WANNAN ACCOUNT ƊIN, FIRST BANK 3090957579 AISHA ADAM, ZA'A TURO DA SHAIDAR BIYA TA WANNAN LAMBAR,0706 206 2624, DAN GIRMAN ALLAH IDAN KINSAN ZAKI FITARMUN DA LITTAFI NA YAFE CINIKINKI_
[30/12/2021, 17:38] Ameera Adam🌚: 57....




A kunyace Maryo ta sunne kai ƙasa don sai yanzu take jin nauyin abin da ta yi a gaban Inna Habi, kiciniyar kwace kanta take Saif ya haɗa goshinsu wuri ɗaya har yana jin yadda sautin ƙirjinta yake bugawa da sauri-sauri, kamar me yi mata raɗa a kunne haka muryarsa ta fara sauka tana ratsa sassan jikinta yana faɗin, "Ba dai guduwa za ki yi ba?" Kallon gefen da Inna Habi take ta yi ta mayar masa da amsa cikin sigar da ya yi mata magana, "Inna tana kallonmu fa." Sassauta riƙon da ya yi mata ya yi ai kuwa kamar me jira da sauri ta ƙwace kanta tana murmushi ta koma cen bayan Inna Habi ta rungomata ta baya tana ɗora kanta a gefen kafaɗarta. Ilahirin jikin Inna Habi ya yi sanyi saboda abu ne da bata taɓa tsammaninsa ba, a yadda ta lura babu wata damuwa a tattare da Maryo sai ma ta lura shauƙin da suke nuna juya kamar mata da mijin da suka yi shekaru ba tare da juna ba. Maleek da ke gefe gabaɓaya annurinsa ya ɗauke sai furzar da iska yake me zafi yana wurgawa Saif mugun kallo, takawa ya fara yi a hankali zai ƙarasa wurin Maryo a hargitse Maleek ya buga masa wata uwar tsawa yana faɗin, "Dakata! Wane irin shirme kake yi haka?" Nan take annurin da ke fuskar Maryo da Saif ya ɗauke kamar waɗanda aka isar musu da saƙon mutuwa. Saif ne ya zuba masa idanu sai da ya lumshe su ya sake buɗewa sannan ya kuma watsa masa manyan idanuwansa da suka fara sauya launi, da wata irin murya ya kalle shi yana faɗin, "Ina matukar ganin mutumcinka Ɗan uwa karka bari ya zube, domin na tabbata idan ya ɓare ko ƙwayar zarra ba za ka iya ɗiba daga gare ni ba. A wannan karon na yi alƙwarin duk wanda ya yi niyyar katange ni da ita na rantse da Allah sai na datse numfashinsa." Kamar wanda aka jefo daga sama haka ya faɗo musu ɗakin yana haki tamkar wanda ya wuni ya kwana yana tseren gudu. Fuskarsa a murtuke take babu ɗigon fara'a ya kalli Saif yana jin wata irin tsanarsa na mamaye masa zuciyarsa, sai da ya haɗiyi yawu me ɗaci sannan ya dube shi yana nuna shi da ɗan yatsa yana cewa, "A wannan karon ka kaini maƙurar bango amma zan nuna bakin rijiya ba wurin wasan makaho bane, kuma ko Kura ta rame ta fi ƙarfin gawurtaccen karen farauta. Na tabbata wannan karon idan aka ce ka dube ta da kallon rahama sai ka faɗi ka suma saboda irin izayar da zan wanzar maka..." A hassale Maryo ta katse shi da faɗin, "Ganin gida yake sa kare zagin Kura amma ba a daji ba. Kada ka manta kowa ya aikata son ransa zai ga ba daidai ba. Amma kuma zan ƙara tunatar da kai ko cikin tumaki rago ke zuwa fada. Ka yi yaƙi da dukkan jarumtarka ba da kaifin tsafi ba, idan baka manta ba a baya ina gaya maka kai ba me sa'a bane kuma ba za ka taɓa zama me sa'a ba." Wani malalacin murmushi Salman ya saki yace, "Zan rangwanta masa albarkacin soyayyar da kike yi masa, saboda azabtar da masoyi a gaban masoyi yana da matuƙar ciwo. Amma na yi rantsuwa na ƙara sai na nusar da ku Abubuwa da yawa suna ɓata a fada ba sai Takalmi ba." Maryo za ta sake magana Saif ya ɗaga mata hannu nan take idonta ya ciko da ƙwalla ta ce, "Don Allah a wannan karon karka dakatar da ni, ka fi kowa sanin wanene shi bana son ya ƙara nasara akanmu."Cikin sigar lallashi Saif ya dube ta ya sa hannu yana goge mata zirin hawayen da ya zubo mata sannan yace, "Wuƙar fiɗar giwa ba girma gare ta ba sai dai kaifi. Alƙawari na ɗaukarwa kaina duk rintsi ba zan bar me shirin yi mini iyaka da ke ba. Ki kwantar da hankalinki hargagin damusa baya firgita Namijin Zaki. Kamar baki san shi da hargagi ba ban son ki sawa kanki damuwa kin ji." Maryo gyaɗa masa kai ta yi tana watsawa Salman harara. Maleek da Inna Habi zama suka yi kamar mutum mutimi suna kallon ikon Allah, don yawancin wannan zaurancen nasu ba fahimta suke ba. Salman ne ya taka gaban Saif yana gyaɗa kai kamar na ƙadangare yace, "Wuya makarantar kare haka zalika wuya ita ke sa gawa sakin tusa. Amma ka sani alamar rago tana ga ɗaurin bante don haka idan kere na yawo zabo na yawo watarana za su haɗu." Yana gama faɗar haka ya fice daga ɗakin yana huci zuciyarsa na ƙuna. Bayan fitarsa babu jimawa Saif ya mara masa baya kowa ya yi hanyar gidansa.


Sai a lokacin Maryo ta ɗan sha jinin jikinta yadda ta ga Inna Habi ta yi laƙwas tana binta da kallo. Abu ce ta faɗo mata a rai da sauri ta kalli Inna Habi ta ce, "Inna ina Abu take?" Ras gaban Inna Habi ta buga saboda kullin da wannan tunanin take kwana tana tashi, babban damuwarta ace idan Maryo ta samu lafiya ta wace sigar za ta fara sanar mata da mijin da ƴar uwarta take aure. Jin ta yi shiru ya sa Maryo ta ƙara cewa, "Ba dai har yanzu tana sashen Fulani Zaliha ba?" Jiki a sanyaye kamar kazar da aka jefa da gishiri ta ce, "Kin san fa ƴar uwarki ta yi aure tana gidan mijinta." Wani uban tsalle Maryo ta buga ta ɗane Inna Habi tana faɗin, "Don Allah Inna? Ina ne gidanta a rakani?" Maleek kallonta yake cikin birgewa yana mamakin wannan baiwa da ikon Allah, abu ɗaya zai rabata da Shukransa ita wannan ya lura tana da hatsaniya saɓanin Shukra da ko hira bata cika yi da mutane ba. Inna Habi ta yi mata hararar wasa ta ce, "Tun ba ki gama warware ba yau-yau fa kika samu lafiya, babu inda za ki sai kin ƙara warwarewa."


Ɗan turo baki gaba ta yi ta ce, "Don Allah Inna ki sa a raka ni na kwana biyu ban ganta ba." Maleek ne ya yi gyaran murya yace, "Maryo babu magana kuma?" Kunya ce ta kama ta don sun haɗa ido da shi ya fi a ƙirga amma da yake a cikin shauƙi take ba su gaisa ba, a ɗan kunyace ta ce, "Ina Wuni!" Gyara tsayuwa ya yi, sai da zuba hannu a aljihu yace, "Lafiya ƙalau ya jikin" Ta bashi amsa, "Da sauƙi." ya mayar da akalar kallonsa ga Inna Habi yace, "To Allah ƙara sauki Inna ni zan wuce sai an kwana biyu." Ina ta ce, "Har tafiya Audulmaleek? To a gaida gida Allah ya tsare a gaishe da Fulani da Mai Babban ɗaki." Ya amsa mata tare ta yin gaba, zunguro Maryo ta yi a hankali tana ƙasa-ƙasa da murya ta ce, "Maza rakashi ko bakin ƙofa ne." Maryo ta yi gaba taba tura baki gaba ba don ta so hakan ba. Suna zuwa bakin ƙofa a gurguwa ta yi masa sallama ta dawo wurin Inna Habi.


Waiwaye...


Rayzuta ta taso cikin kulawa da soyayyar iyaye gaba da baya, tun bayan haihuwarta da wata uku Mahaifiyarta ta fara ciwo sama-sama. Tun ana ganin abin da wasa har lamarin ya fara ba su tsoro, saboda yanzu riƙon Rayzuta ya dawo hannun Farratu da zama, ba ƙaramin tausayin yarinyar take ji ba musamman ga ƙarancin watanninta ace Mahaifiyarta babu lafiya. Haka daga wurin Mahaifinta hankalinsa ba ƙaramin ta shi ya yi ba. Lokaci ɗaya labarin rashin lafiyar Wurshil Ba'is ya karaɗe cikin wannan Daula ta masarauta me ɗauke da ɗubin Aljanun a ciki. Ba a ɗauki lokaci ba aka fantsama neman magani cikin da wajen wannan nahiya. Koyaushe a cikin haɗa mata magani ake amma kullin ciwonta kamar ƙara gaba yake yi. Sarki Kisumul Birmi tun yana sa ran warkewarta har ya fara sare wa sakamakon yadda jikin nata yake ƙara rikicewa. Farratu ita take jinyar Wurshil Ba'is domin ta ce babu wanda za ta lamuncewa ya yi jinyarta, saboda jikinta yana bata akwai lauje cikin naɗi dangane da ciwon kishiyar tata. Wannan haɗin kai na Matan Sarki Kismul Birmi ba ƙaramin daɗi yake yi masa ba, a ɓangare ɗaya yana ƙara jin ƙaunar Uwar gidansa na ƙara mamaye zuciyarsa, yana jinjina karamci da kyawun hali irin nata. Burdamu Ita ce Mahaifiyar Furzaan, amintakar mazajensu ya sa ta su ta zo ɗaya da Farratu suka ɗinke saboda kusan halinsu ɗaya, wannan ta sa zumuncin su ya ci gaba da tafiya gwanin birgewa. Furzaan da Zulik tun suna yara suka taso da abotarsu sai dai bambamcin ɗabi'u da halaye da suke da shi tun suna ƙanana.


Furzaan Yarone me nutsuwa ladabi da biyayya Uwa Uba girmama na gaba da shi, yana da saurin fahimtar abu. Yana da barkwanci sosai ta jin tausayin Mahaifiyarsa da ma sauran duk wani me buƙatar taimako. Saɓanin Zulik da ya ta so da haɗama, handama da babakere. Tun be yi wayon ba yake da hangen abin da wani yake da shi, sai dai da ya ɗora ido akanka muddin ya ga ka zarta shi da wani matsayi zai kawo hassada, ƙyashi da baƙin ciki ya ɗora akanka. Duk waɗannan ɗabi'u na Zulik Furzaan ya fahimce su saboda yana da saurin karantar yanayin da ƴan uwansa Jinsin Aljanu suke ciki. Don haka tun suna ƙanana kowa ya san halin kowa a cikinsu, saboda haka Furzaan yake cin maganin zama da Zulik don a zauna lafiya.


Lokacin da Rayzuta ta kai shekara biyar a duniya lokacin ne ciwon Mahaifiyarta ya warke wato a ranar ne ta koma ga mahalicci, Farratu ta yi kuka ranar kamar ranta zai fita. Sarki Kismul Birmi sai shi ya dinga lallashinta yana bata haƙuri. Shiru ta yi ta faɗa duniyar tunanin irin wasiyar da Wurshil Ba'is ta bar mata a lokacin da take gabda da mutuwarta.


(Bari mu taɓo yarensu🤪)


"Jaskinbat minfartif basu kutminba Farratu banakul ginsatu lalbisfahu warga su minzanu kalmunsiban hurumi Rayzuta minzat falsibuhu zadigul basfu walkin."


(Haƙiƙa ke ta daban ce Farratu ban taɓa jin kishiya me karamci kamar ki ba ko a tarihi, Allah ya yi ni ba me yawancin kwana bace don haka ga amanar Rayzuta nan ki riƙe kamar ƴarki ta cikinki.)


Kuka ne ya kwacewa Farratu tana jin maganganun Wurshil Ba'is har cikin zuciyarta, share hawayenta ta yi ta ce, "Ki daina faɗin haka cuta ba mutuwa ba sai kwana ya ƙare." Murmushi Wurshil Ba'is ta yi ta ce, "Wannan karon ciwon haɗe yake da ƙarar kwana. Dama Kakana ya taɓa gaya mini tun ina budurwa cewa ƙaddarata za ta kawo ni Masarautar Jinnul Sahara, ya sanar da ni komai amma ba zan iya sanar da ku ba saboda gudun tayar da tarzoma, amma abu ɗaya zan sanar miki da shi akan Rayzuta ba don tana matsayim ƴata ba, ina baki shawara ne dangen da goben Ƴar Rayzuta. Don Allah idan yadda kina ɗauke ni har zuciyarki haka nake kada ki Aurawa ɗaya daga cikin zuri'ar Bulbutu, idan kuka yi wannan kuskuren na tabbata ƙasƙantattun Bayin cikin masarautar nan sai sun fi ku ƴanci a cikin Masarautar nan." Farratu ta kalli Wurshil Ba'is da mamaki ta ce, "Me zai haɗa zuri'ar Sarki Kisumul Birmi da zuri'ar Bawa Bulbutu, karki manta Rayzuta jinin sarauta ce su kuwa dangin Bayi ne." Murmushin yake Wurshil Ba'is ta yi ta ce, "A kwana a tashi ko bayan babu raina za ki tuna da wannan maganar. Ki sanarwa da Sarki wannan huɗubar tawa na tabbata ba zai watsa miki ƙasa a ido ba. Idan kika cire wannan zuri'ar na yarje duk wanda Rayzuta ta nuna tana so matsawar ba shi da wani aibu ku aura mata shi. Amma ina fargabar abin da Kakana Bundur ya sanar da ni dangane rubtacciyar ƙaddararta, wataƙila yin hakan ya dakatar da tasirin ƙaddararta sai dai..." Bata ƙarasa maganar ba numfashinta ya ɗauke nan take rai ya yi halinsa.


Haka rayuwa ta ci gaba da tafiya Rayzuta na hannun Farratu tana bata kulawa tamkar ita ta haifeta har Rayzuta ta fara zama budurwa, a wannan lokacin duk wasu al'amuran da ya shafi harkar Mulki Mahaifinta yana koya mata. Rayzuta nutsatssiyar yarinya ce sai dai ta taso da farin jinin duk kuwa da yadda Mahaifinta ya yi farin jini lokacin da yana matashi ta dame shi ta wannan fannin. Wata irin shaƙuwace ta shiga tsakaninta da Furzaan, a fannin iyayensu hakan ba ƙaramin daɗi ya yi musu ba. Ga wanda ya fahimci wannan alaƙa tasu zai fahimci shaƙuwar ta su ta rikiɗe zuwa soyayya. Zulik tun da Allah ya sa ya zama saurayi ya ji duk duniya babu yarinyar da yake ƙauna sama da ita. Babban burinsa ya ga an aura masa ita ya mori gangar jikinta, saboda Allah ya yi mata kyakkyawar sura cikin jinsinsu na Aljanu. Ganin hankalinta ya fi karkata ga Furzaan ya sa ya fara neman cusa soyayyarsa ƙarfi da yaji a zuciyar Rayzuta, wanda a lokacin har saɓani suka fara samu tsakaninsa da ita, don har sawa take Dogarawan ƙofa su dakatar da shi. Watarana yana zaune Mahaifinsa ya same shi a ɗaki ya ƙarewa Zulik kallo duk ya rame ya fara lalacewa, dama kuma ya daɗe da fahimtar halin da Ɗan nasa yake ciki kuma hakan ba ƙaramin daɗi ya yi masa ba. Zama ya yi a kusa da shi ya ambaci sunansa cikin wata irin murya da take tabbatar masa Mahaifin nasa yana son yin magana me muhimmanci da shi.


"Zulik na fahimci ka faɗa tarkon soyayyar Rayzuta ƴar Sarki Kisumul Barmi, amma ka sani soyayya da ita kamar dawo da wanda ya mutu ne. Na san za ka yi mamakin jin haka daga gare ni kuma wannan ba abin mamakii bane idan ka duba matsayinka da nata." Bulbutu ya dakata da maganar yana kallon yanayin da Zulik ya shiga, cikin rashin ladabi Zulik yace, "Wacece Mahaifiyata? Ka fara sanar da ni wannan in yaso duk wani bayani sai ya biyo baya." Murmushi Bulbutu ya yi yace, "Mahaifiyarka ta rasu tun bayan da ta haife ka, Mahaifiyarka ita ce Mahaifiyata.

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login