Showing 15001 words to 18000 words out of 89213 words

Chapter 6 - Anya Baiwa Ce 2 Complete Hausa Novel By Aisha Adam.txt

30 Nov 2024

5343

tsaf ya yi mata yace, "Maryama na aika a zo da Sarkin Wanzamai a sirrance ya baki magani don gaskiya na damu da ganin kanki haka babu gashi, wannan ba ƙaramar matsala bace ace haka kawai ka wayi gari babu gashi ko silli ɗaya, ko ma'askin dare fa ba haka yake yi ba." Fulani Maryama yaƙe ta yi ta amsa masa don kada ta yi gardama ta tonawa kanta asiri ana zaune ƙalau, gara ta zuba ido masu maganin su zo su gama abin da za su yi su tafi. Ta tabbata makarin komai yana hannun Marduska don Marduska ya wuce tunanin me tunani.


Salman ya yi mamakin yadda ya sanarwa da Abuh amma babu ko ɗigon farinciki a tattare da fuskarta, amma kafin wannan lokacin ya tabbata ko mahaukaci ya san Abuh ta fara ƙaunarsa, be tursasa mata ba sai ma nuna mata ya yi da be fahimci abin da take nufi ba. Don haka ko da ya ga ta yi shiru ya kau da kai gefe don ƴan muskilancin ne akansa yace mata, "Zainab ki yi nazari akan abin da na sanar da ke amma ba zan tilasta miki ba, ina sauraronki zuwa nan da kwana biyu." Yana gama faɗa ya wuce, Abuh zama ta yi sai ga hawaye na bin fuskarta wannan shi ake kira da gaba kura baya siyaƙi. Idan har ta ce bata ƙaunar Saif ta yi ƙarya hasalima da shi take kwana take tashi a ranta, amma ta san hakan ba me yuwu bane. Ya za ayi ta auri mutumin da ƴar uwarta take begen shi babu dare babu rana. Girgiza kai ta fara yi tana faɗin, "Inaa sam wannan ba zai taɓa yuwuwa ba." Miƙewa ta yi da niyyar shiga sashen Fulani Maryama don ta sanar da mahaifiyarta halin da ake ciki amma tana gabda shiga ƙofa wasu dogarawa suka dakatar da ita, da mamaki ta kalle su da niyyar buɗe baki ta yi magana taji ɗaya yace, "Umarni ne daga Fulani Maryama ta ce kar a ƙara barinki ki shiga sashenta." Babu yadda Abuh ta iya haka ta juya tana jin zuciyarta babu daɗi, sashen su ta nifa zuciyarta da tunane-tunane, ta ɗaga labulen ɗakinta ta ji Fulani Zaliha ta ƙwala mata kira wanda ya yi daidai da faɗuwar gabanta, kamar mara jini a jiki haka ta juya jiki a sanyaye ta nufi turakar Fulani Zaliha ta russuna cikin girmamawa ta gaishe ta, "Barka da hutawa ranki shi daɗe" Murmushi Fulani Zaliha ta yi ta ce, "Barka dai ƴata ya ganki duk wani iri me yake damunki?" Abuh da sauri ta ɗago sai kuma ta ga sam ba za ta iya sanar mata da halin da take ciki ba don ta tabbata uwa uwa ce dole idon ta ce bata son Saif dole ba za ta ji daɗi. Don haka ta sunkuyar da kai ta ce, "Na je ganin Inna ta ne Dogarawa suka hanani shiga." Fulani Zaliha ta ce, "Kamar ya? Waye ya isa ya hanaki shiga ko Maryaman ce ta bada umarni?" A hankali ta gyaɗa mata kai. Ajiyar zuciya ta sauke ta ce, "Wannan ba hurumi na bane amma zan yi wa Takawa magana." Da sauri Abuh ta ce, "A'a don Allah karki gaya masa kar na yi wa Fulani Laifi." Murmushi Fulani Zaliha ta yi ta ce, "Zainab me ya sa kin fiye tsoro ne, yauwa ɗazu mun yi magana da Saif. Takawa yace su fito da matan aure shi dai yace kece zaɓinsa, ba ƙaramin daɗi na ji ba saboda ƴar gida za muyi amma ban sani ba za ki amince da shi?" Gabaɗaya Abuh dabaibayewa ta yi gumi ya fara tsattsafo mata, shiru ta yi ta faɗa duniyar tunani a duniya dai ta san Fulani Zaliha tana matuƙar ƙaunarta, bata taɓa ƙyamarta ba tana yi mata abin da uwa za ta yi wa ƴar ta. Jin shirun ne yasa Fulani Zaliha ta dafa kafaɗarta wanda shi ne silar dawowarta daga duniyar tunanin da ta faɗa, ɗagowa ta yi suka haɗa ido ta sauke kanta ƙasa, Fulani Zaliha ta ce, "Zainba! Na ɗauke ki tamkar ƴata idon bakya son Saif ki gaya mini ba zan miki dole ba, sai na sashi ya nemi wata." A hankali Abu ta ce, "Ba haka bane Ranki shi daɗe na amince." murmushin jindaɗi Fulani Zaliha ta ce, "Masha Allah, Tashi ki je Allah ya tabbatar da Alheri." Abuh bata iya amsawa ba ta miƙe a kunyace ta fice ta nufi ɗakinta, tana shiga ta fara zarya har lokacin gumi ne yake karyo mata.




SHA BIYAR GA WATAN SATUMBA A SHERAR DUBU ƊAYA DARI TARA DA HAMSIN DA ƊAYA
(15/09/1951)


Wanda ya yi daidai da ranar Laraba a ranar ne Sarki Aminullah da Abokinsa Sarkin Gumel, suka sanya ranar auren Salman Aminullah Muhammad da Safiyya Yusuf Kabir sai Saifullah Aminullah Muhammad da Zainab Ya'u Me Nagge. An saka ranar aure wata uku farinciki wurin waɗanan iyalan abin ya ƙi misaltuwa.


MARYO NA CEN AN YI WUFF DA MASOYINTA😢
_LITTAFIN NAN NA KUƊI NE DA NAIRA 200 ZAKI KARANTA SHI CIKIN KWANCIYAR HANKALI, ZAKU BIYA TA WANNAN ACCOUNT ƊIN, FIRST BANK 3090957579 AISHA ADAM, ZA'A TURO DA SHAIDAR BIYA TA WANNAN LAMBAR,0706 206 2624, DAN GIRMAN ALLAH IDAN KINSAN ZAKI FITARMUN DA LITTAFI NA YAFE CINIKINKI._
[10/12/2021, 19:46] Ameera Adam🌚: 45...






Lokacin da labarin sanya aurensu ya isa kunnuwan Abuh haka kawai ta ji gabanta ya yanke ya faɗi, tana daga ɗakinta a kwance ta ji Jakadiya tana ta zabga bambaɗanci da fadanci. Kasancewar Fulani Zaliha na cikin farinciki yasa ta kalli Jakadiya da murmushi ɗauke a saman fuskarta ta ce, "Jakadiya anjima a aiko a karɓi tukwici." Jakadiya sakin baki ta yi tana kallon Fulani Zaliha don Allah ya sani tun da take da ita sai da irga adadin murmushin da ta taɓa gani a saman fuskar Fulani Zaliha, hasalima tun da take bata taɓa daɗewa a sashenta kamar daɗewar da ta yi yau ba. A zuciyarta ta fara godia don ta tabbata tun da ta samu arziƙin sakin fuska, ba ƙaramar kyauta za ta samu ba. Wannan ya bata damar yashe baki ta ci gaba da bambaɗanci har Fulani Zaliha ta sallame ta. Jakadiya na fita bata zarce ko ina ba sai sashen Fulani Maryama, kanta tsaye ta yi sallama ta shiga. Tun daga tsakar gida Jakadiya ta fara rangaɗa guda, tana juyi a tsakar gida. Inna Habi dake ɗaura lalle daga ɗakinta tana hangota ta girgiza kai, don gabaɗaya ta gama fahimtar Jakadiya munfuka ce ajin farko. Kasancewar Fulani Maryama na cikin farin ciki yasa ta bawa Bayin ta damar kowa ya tafi sabgar gabansa na tsawon wunin. Jakadiya na shiga ta tsugunna nan ma ta fara bambaɗanci kamar yadda ta yi wurin Fulani Zaliha, sai da ta gama ta gyara zama ta ce, "Allah ya taimake ki wai ni kam don Allah wace tsiya ce ta ƙarewa Zaliha da Ɗanta, su rasa wacce zai aura sai ƴantacciyar Baiwa. Kai wallahi ni kam ba ƙaramin takaici na ji ba wannan ai salon ya ja wa Masarautar nan zagi ne saboda Allah, duk ƴaƴan Sarakunan ƙasar nan amma ya rasa wa zai so sai waccen figaggiyar ƴar Fulanin." Fulani Maryama da tun shigar Jakadiya Murmushi ne kwance a saman fuskar, ta kuma washe baki tana dariya me sauti ta ce, "Im muguwar kaza ta fara shiga akurki duk wacce ta zo sai ta tare ta. Don haka ni fes a gareni." Jakadiya ta yi murmushi ta ce, "Fulani Maryama kenan. Ba a sanin murnar karen da bashi da wutsiya." Fulani Maryama ta ɗora ƙafa ɗaya kan ɗaya cikin izza da isa ta ce, "Jakadiya duk Karen da bashi da wutsiya dube shi da kyau ƙwayar idonsa za ta gaya miki amsar halin da yake ciki." Jakadiya ta saki shewa ta ce, "Amma kin fi kowa sanin Zaliha Miskila ce cikin mata ba kamar sauran kishiyoyinku take ba, na tabbata wannan karen kallon ƙwayar idonsa za yi miki wahala." Fulani Maryama ta buɗe hannuwa alamar rashin damuwa ta ce, "Jakadiya kin manta da ko anci birnin Kura ba a ba kare dillanci, Maryama nake ginshiƙin dutse kowa karo da ni za shi ƙasa. Sam ban damu da wacce Saif zai aura ba ko da kuwa mahaukaciya ce burina na dai kawai ya yi aure shi da Salman, idan na fara cimma wannan matsayar sai na san yadda zan ɓullowa sauran lamura, domin shan tabar kwaɗo da baki da hanci yake." Jakadiya ta kalli Fulani Maryama tana jinjina kai ta saki murmushi ta ce, "Maryama ƙarfin gwiwarki da izzar ki yana matuƙar birge ni, ba kowa yake gane murmushin jaki ba wani idan ya gani ɗauka zai kuka yake wani kuma ya yi tsammanin cizo zai kai." Fulani Maryama ta gyaɗa kai kamar ƙadangaruwa ta ce, "Tabbas kuwa, domin kwana a gado daban da sabon kabari." Jakadiya ta sauya fuska zuwa yanayin jimami ta ce, "Oh! Sabon kabari me sa a tuna Allah. Maryama yaushe za mu tuba ne?" Fulani Maryama ta ce, "Lokacin da na gama biyan buƙatar rayuwata." Jakadiya ta kalleta a kaikace ta ce, "Ai kuwa buƙatar me rai bata cika sai kwana ya ƙare." Ɗaure fuska Fulani Maryama ta yi ta ce, "Wani me ran ya kan cika buƙatunsa sai kuma rai ya yi halinsa. Jakadiya idan muna raha ki bar sako mini zancen mutuwa." Jakadiya cikin zuciyarta take mamakin baƙi hali irin na Fulani Maryama da bushewar zuciya, da mamaki ƙarara asaman fuskarta ta ce, "Sarautar Allah kare a bakin kura. Maryama wacce irin zuciya gare ki." Kai tsaye Fulani Maryama ta bata amsa, "Wacce aka ciro daga jikinki aka liƙa mini." Jakadiya ta shi ta yi ta ce, "To Allah ya ƙwato ki don na lura kin yi nisa bakya jin kira." Fulani Maryama ba ta tanka mata ba, saboda ta lura idan ta biyewa Jakadiya sai ta ɓata mata rai alhalin tana cikin farin ciki. Jakadiya na fita bata zame ko ina ba sai ɗakin Inna Habi. Rangaɗa uwar sallama ta yi Inna Habi ta amsa mata ba yabo ba fallasa. Zama ta yi a gefe dokin ƙofa ta ce, "Uwar amarya sai kuma nake jin abun alheri." Inna Habi ta ɗauka murnar Salman take yi mata, murmushi ta yi ta ce, "Eh wallahi Yarima ya kusa girma, Allah ya nuna mana lokacin." Ganin kamar Inna Habi bata fahimci inda zancen ya dosa ba Jakadiya ta ce, "Ban da abin ki Habi na san dai Abu ai ba ta fari bace a wurinki, to karar me za ki yi?" Inna Habi ta yi murmushi ta ce, "Jakadiya karar me zan yi kuma?" Jakadiya ta ce, "Yooo na ga ina yi miki Allah sanya alherin Abu kina kaucewa, Allah na tuba ai farinciki za kiyi Namiji kamar Saif me nasaba da tushe har aka yi masa baiko da Abu ai abin nunawa duniya ne." Cikin rashin Fahimta Inna Habi ta ce, "Wace Abun aka yi wa baiko da Saif?" Jakadiya gulma na cinta ta ce, "Abuh ƴar wurinka mana ai duk tare aka yi musu baiko da Salman. Kuma ance yana mutuwar son Abuh ita ma tana ƙaunarsa, wai ke baki sani bane." Inna Habi ta fahimci bugun cikinta Jakadiya take don haka ta ce, "Na yi mamaki da Abuh ta zaɓi Saif ne, mun yi magana da ita ta ce akwai wani Yaro da suke taɗi. Kin san yaran yanzu baka gane alƙibilarsu." Jakadiya sam ba haka ta so ba ta miƙe tsaye tana faɗin, "Yooo ke kuwa ga wurin da za a haɗu da babban rabo, ko ba komai ai ta auri jinin Aminullahi."tana gama faɗa ta fice daga gidan.




Al'ummar da ke zaune a masarautar Adamawa ba ƙaramin mamakin mugun halin Fulani Babba suka yi ba, saboda su dai a iya zamansu da ita basu taɓa kawo za ta aikata makamancin abin da ta furta da bakinta ba. A iya saninsu dai ita mace ce me son girma da son shugabanci, amma ba su yi zatan son matsayin nata har ya kai ga haka ba. Wunin ranar haka kowa ya wuni da ta'ajibinta, wasu na tsine mata wasu kuma suna ganin kuskurene da kowanne ɗan Adam yake iya aikatawa. Amma mafi yawa daga ciki sun fi danganta hakan da son zuciya, zalinci da rashin imani. Maryo na komawa ɗaki ta zauna ita kaɗai a ɗaki ta haɗa kai da gwiwa tana zubda wani irin hawaye me ƙuna, zuciyarta za fi take ga wani irin raɗaɗin ƙaunar Saif da yake ƙara nuƙurƙusar zuciyarta. Hannu ta sa ta dafe saitin zuciyarta ta kuma fashewa da kuka, nan take wani irin tari ya turniƙeta tun tana yi daga zaune har ta fara galabaita tana dafa bango tana ƙoƙarin miƙewa, feshin jini bakinta yake yi har ta fara fita daga hayyacinta. Dafa bango ta fara yi tana tafe tana labuben hanya hannunta ɗaya na kan ƙirjinta, hannu ɗaya tana laluben ƙofar fita. Tana zuwa bakin ƙofa ƙarfinta ya ƙare nan ta yanke jiki ta faɗi hancinta da bakinta na zubar da Jini. Lokacin da fadar ta watse jiki babu ƙwari Maleek ya miƙe kallon Mahaifinsa ya yi yana jin tausayinsa na mamaye zuciyarsa, musamman yadda ya ga har zuwa wannan lokacin yana rungume da Mahaifiyarsa yana zubda hawaye, ita ma hawayen take yi tana shafa kansa da rawanin kansa yake ƙoƙarin zamewa. Ganin hakan ne yasa Dogarawa suka sallami kowa harda su suka fita zuwa bakin ƙofa, ya zama ɗakin daga Sarki Abdallah, Me babban ɗaki sai ƴaƴansa maza guda Uku. Maleek ga ni ya yi ba zai iya ci gaba da gani ba don zuciyarsa ta fara karyewa, don kukan da Muhsin yake ba na farinciki bane. Yana kukan halin da Mahaifiyarsa take ciki da abin da ta aikata, don gabaɗaya ji yake ya tsani kansa yana kunyar fita ya haɗa ido da sauran al'umma. Lokacin da Maleek ya nufi sashensu gabansa ne ya ci gaba da faɗuwa don be san abin da zai je ya tarar, jiki babu ƙwari ya kamar marar laka a jiki haka ya fara takawa har zuwa bakin ƙofa, sama-sama yake jiyo nishinta tsoro ne ya fara kamashi don gani yake idan ya leƙa kamar zai iya ganin abin da zai kuma sumar da shi, kamar marar gaskiya haka ya fara tafiya saɗaf-saɗaf har ya zura kansa ya leƙa don ganin abin da yake faruwa. Zaro ido waje ya yi lokacin da ya yi tozali da halin da take ciki, da sauri ya ƙarasa hankali a tashe ya fara ƙwala mata kira amma bata iya buɗe idonta ba bare ya sa ran za ta kula shi ba. Hankali tashe ya ɗauke ta yana ƙwalawa Bayin da ke harabar sashen amma sakamakon abin da ya faru babu kowa a wurin, da sauri ya fice daga wurin ya nufi sashen Mahaifiyarsa da ita. Yana shiga ya same su jigun-jigun sam hankalinsa be kai ga yanayin da suke ciki ba, cikin damuwa yake faɗin. "Ummi! Shukra don Allah karta mutu aman jini take yi." Hankalinta ne ya tashi da sauri ta aika aka kira baushe nan take ɗan aiken ya dawo tare da Baushe. Kwantar da Maryo aka yi tana numfashi sama-sama, ƙura mata ido ya yi sanann ya jiƙa wani garin magani ya shafa mata a jiki ya ɗura mata sauran a bakinta. Numfashinta ne ya ci gaba da kaiwa da kawowa yana sama yana ƙasa, tarin ne ya ƙara rufeta ta fara yi babu ƙaƙƙautawa. Baushe ba ƙaramin tsorata ya yi ba, don be taɓa ganin ciwo irin wannan ba. A hankali Maryo ta buɗe idanunta da suka rune jawur, kallonsu take ɗaya bayan ɗaya hawaye na ƙwarara daga idanunta ta fara motsa bakinta a hankali tana cewa, " kowanne lokaci kowanne ɗan adam yana tafiya da yadda ƙaddararsa ta faro tun daga tsiron nufashinsa, ni tawa rubutacciyar ƙaddarar kenan. Allah ya ƙaddara ba zan sake cika burinmu na kasancewa ababen farantawa zuƙata ba, tafiyar ƙaddarata tafe yake da sauran ƙalubalen baya. Wataƙila tarayyata da shi bata da alheri shi yasa inuwar junanmu take ƙara nesa da juna." Tari ta ƙara yi jini na bin gefen bakinta ta ɗago ta kalli Maleek da ke gefe yana zubda ƙwallah, ta sakar masa murmushi ta ce, "Tabbas na aminta da yadda ka jiɓanci wani tsagi na daga sashena, haka tamu ƙaddarar take samun muradin abokin rayuwarmu na tafe da ƙalubale. Ka riƙe maganar da nake gaya maka har kullin, ni ba Shukra bace ka yi ta gudu me yawa kamar wanda yake laluben bangon duniya, tabbas za ka cinma muradinka idan har ka kasance baka wuri ɗaya a zaune. A duk lokacin da ka haɗu da Shukra ka bata wannan zoben na hannuna, wataƙila zata fahimci zanen ƙaddarata wanda yake tattare da ƙalubale." Hannu ta ɗaga da kyar jikin ta na karkarwa ta damƙi hannunsa da ɗan yatsenta yake ɗauke da wata azurfa, kuka na neman cin ƙarfinta ta ce, "Don Allah zan baka saƙo ka kaiwa Saif!" Hannu ta sa ta dafe zuciyarta da take barzanar faso ƙirjinta hawaye na zuba ta ci gaba da cewa, "Ka gaya masa ina ƙaunarsa fiye da tunanin ne tunani kuma ba zan fasa ƙaunarsa domin ƙaddararsa tafe take da tawa ƙaddara. Ka gaya masa na ci albarkar ƙaunar da nake masa ya sakawa ƴarsa sunana, sai ƴar uwa ta Abuh ka gaya mata ta tayani kishinsa saboda ta san yadda nake mutuwar sonsa, da zan iya da na shawarci ta zame masa mata sai dai banajin zan iya haɗiye wannan ƙaddarar. A dacen ma ban juri ganinsa da wata mace ba bare yanzu, ka isar da saƙona gare su na fatan aleri. Sai Inna Habi..." nan take tari ya sarƙe ta amai ya ci gaba da zuba daga bakinta. Numfashinta ne ya shiga yin sama da ƙasa ta fara wata irin shaƙuwa, da sauri Maleek ya ɗau ruwa ya fara ƙoƙarin bata amma sai ji ya yi numfashinta ya ɗauke, jikinta ya yi wani irin nauyi kanta ya langaɓe gefe ɗaya. Cikin tashin hankali ya fara ƙwallah mata kira amma babu alamun

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login