Showing 1 words to 3000 words out of 89213 words
Chapter 1 - Anya Baiwa Ce 2 Complete Hausa Novel By Aisha Adam.txt
[26/11/2021, 18:57] Ameera Adam🌚: 36...
Fulani Maryama turɓune fuska tayi dan ba ƙaramin haushin Jakadiya ta ji ba, gani take kamar raini ya fara shiga tsakaninsu dan haka ta ƙara ɓata fuska ta ce, "Jakadiya hawainiyarki ta kiyayi rama ta. Kar tarayyarmu da ke ta fara kaimu ga raini ki iya bakinki idan ba haka ba wallahi zan yi maganinki" Jakadiya ta saki hanci da baki tana ƙarewa Hallitar Fulani Maryama kallo dan ba ƙaramin muni tayi ba ga ranƙwalelen goshi kamar jirgi ya doso tasha ga fala-falan kunnuwa, cikin zuciyarta take mamakin yadda akayi Sarki Aminullah ya zaɓo Fulani Maryama a matsayin mata, matar tashi ma ta fari. Ganin kallon ya yi yawa yasa Fulani Maryama ta ɗan tsargu ta ce, "Lafiya kika kafe ni da idanu kamar kinga sabuwar hallita?" Jakadiya ta ce, "Yooo to Maryama me ya yi saura kuma ni da ke fa kar ta san kar ne, kinsan sirrina nasan naki babu wani isa da mallaka da zaki iya nuna mini yanzu, mu ci gaba da harkokinmu dan mu nemarwa kanmu mafita ina ganin zai fi, dan wallahi nikam na gaji da murmusasshen kannan nawa." Fulani Maryama kasaƙe tayi tana nazarin maganganun Jakadiya tabbas maganarta a hanya take amma wannan rashin bada girman da take mata yana baƙanta mata rai. Fuska ba walwala ta kalli Jakadiya ta ce, "Amma idan kina yi mini haka kina ganin mutane ba za su sa mana ido ba? Kinsan fa gidan nan komai kake yi ana ankare da kai. Matsawar kina yi mini haka wallahi za'a ɗora zarge-zarge akanmu, gara ma tun wuri ki sake tsari kuma ai koda girgiza kurna tafi magarya duk lalacewa dai ni matar Sarki ce ke kuma Jakadiya, kin ga kuwa babba, babba ne ko a gidan giya." Jakadiya da ta gaji ta zantukan Fulani Maryama a ƙagauce ta ce, "To naji amma dai ki nemo mana mafita wlh duk na shiga damuwa." Fulani Maryama ta ce, "Jakadiya bake kaɗai ba. Na ɗauka tafiyar yarinyar nan zai zame mini samun sauƙin lamura amma kina gani yadda lamarin yake kasance mana, ko dai zamu koma wurin marduska mu sanar da shi halin da muke ciki." Jakadiya ta miƙe ƙafafuwa ta ce, "Ai ni na kwana na hantse da tunanin wannan a zuciyata abin da ya fi kenan, dan Allah ya sani ba ƙaramin bankaɗar albarka ya yi mana ba" Fulani Maryama ta amsa mata sannan suka ci gaba da jajantawa a tsakaninsu.
Tsaye take a gaban mudubi tana ƙara feshe jikinta da daɗaɗan turararrika, ita kanta ta ya ba da irin kwalliyar ta da tayi hawaye ne ya ciko idanunta nan take taji zuciyarta tayi rauni tana jin tausayinta, a hankali ta fara takawa zuwa runfar ɗakinta. Jakadiya ce ta shiga ta russuna cikin girmamawa ta ce, "Allah ya taimakeki an riga da annemar miki iso wajen Takawa a kowanne lokaci yana tsammanin zuwan ki." Fulani Zaliha ta gyaɗa kai sannan ta ce, "Ina godiya Jakadiya idan Allah ya kaimu safiya ki aiko a karɓar miki alkaki da zuma." Jakadiya zube wa ta yi tana godiya, "Godiya nake sarauniyar mata mai babbar fada a fadar Mai martaba, tauraruwar taurari a cikin dubbannin mata kece zarah. Ƴar Sarki jikar saki, Matar sarki kuma da yardar Allah ke zaki zama uwar sarki." Jakadiya ta dakata da bambaɗancinta tana jan ɗankwalinta gaba da yake niyyar sulluɓewa ta ci gaba da cewa, "Madara kike ko jaririn goye ya lasa sai ya ƙara lasa, Allah ya tsare mana Yarima Saif ya ƙara masa lafiya, Takawarki lafiya farincikin Takawa duk kin dakushe su zinariya..." Fulani Zaliha ta katse Jakadiya da cewa, "Jakadiya muna godiya a turo gobe a karɓi saƙon" Tana gama faɗa ta miƙe ta wuce ɗakinta. Jakadiya taɓe baki tayi tana binta da harara cikin zuciyarta ta ce, "Wannan yarinya anyi me baƙin halin tsiya. Ita ƴar hirar nan ma bata yarda ayi da ita, ita kenan kullin a ɗaki kamar munafuka."
Tana tafe kuyangunta suna take mata baya har ta ƙarasa turakar Sarki Aminullah, tana zuwa ta sallame su sannan ta ɗan zura ƙafarta ɗaya tana jin wata irin faɗuwar gaba. Ji tayi ya yi gyaran murya da alamar yaji motsin mutum a bakin ƙofar, shiga ta yi bakinta ɗauke da sallama ta nemi kan lallausar dadduma ta zauna cikin girmamawa ta gaishe shi, "Barka da hutawa Ranka ya daɗe." Kafeta ya yi da kallo yana jin kewar matarsa, cikin zuciyarsa yake faɗin, "Na rasa me yasa nake jin Zaliha na da wani irin matsayi a zuciyata? Idan aka cire laifin turen kisa da tasa ayi mini bana jin akwai wani laifin da zan iya kamata da shi." Jin ya yi shiru ya sa Zaliha ta ƙara kallonsa tana cewa, "Ina fatan na same ka lafiya?" Sarki Aminullah ya sauke ajiyar zuciya yace, "Zaliha yau kece a gari? Yaushe rabonki da nan?" murmushi ta ƙirƙiro ta ce, "Allah ya taimakeka dama wata magana na ɗan ji ana ta raɗeraɗin ta." Shima murmushi ya yi ya lura har lokacin tana fushi da shi batasan maganar da ya yi mata, a zuciyarsa ya furta, "Mata kenan! Su dai tunaninsu daban yake. Wannan shi ne a dake ka a hanaka kuka. Ni da aka yi wa laifi kuma ni ake fushi da ni." Tashi ya yi daga kishingiɗen da yake yace, "Wacce magana ce Zaliha?" Fulani Zaliha ta ce, "Na ji ana ta raɗeraɗin wai yarinya da Maleek ya tafi da ita ba matarsa bace hasalima ance bata taɓa aure ba."
Ba ƙaramin mamaki Maleek ya yi ba saboda ganin fitowar Takawa kaɗai ya isa ya tabbatar masa da lallai akwai ƙamshin gaskiya a tattare da maganar Sulaiman, cikin mamaki ya furta. "Ya ilahi wai me yake faruwa da masarautar nan ne? Ina na taɓa jin matacce ya tashi anya ba aljanu ne suke san yin wasa da hankulan al'umma ba kuwa?" A hanzarce ya ƙarasa wajen wanda ya yi dai-dai da ƙarasawar Sarki Abdallah, kutsawa ya dinga yi har ya shiga cen gaba-gaba. A zaune ya hangota tana sauke numfashi sama-sama da alama a wahalce take, waro idanunsa waje ya yi yana kallon ikon Allah, Mai babban ɗaki ya gani zaune a gabansa matar da ta shafe sama da shekara ashirin da rasuwa. Yana nan tsaye ta ɗago da kanta suna haɗa ido ta miƙa masa hannu tana cewa, " Wannan kamar Audul Maleek? Ashe zan ƙara ganinku a rayuwata?" gabansa ne ya yi mummunan faɗuwa yawun bakinsa na neman ƙafewa. Takawa ne ya ƙaraso wajen gabaɗaya matsawa suka yi suka bashi wuri, kallanta yake sosai yana jin wani yanayi a ransa, yana san ya yi mata yana fargabar kaidin magauta kar su yi amfani da wannan damar su halakar da shi. Wani tunani ya yi ya kalli Dogarawan wajen yace, "Ku ɗauke ta ku kaita ɗakin baya, a kira mini su Malam Liman yanzun nan." Kallan kallo suka fara yi a taakaninsu kowa ya daƙire yana tsoron tafiya. Jin muryarsa yasa Mai babban ɗaki ta ɗago da kai ta kalli Sarki Abdallah ta ce, "Audullahi baka yi murna da gani na bane? Nice fa kasan waye ya mayar dani haka? Matarka ita ta cutar dani na tsawon shekaru wata yarinya ce ta kuɓuto dani ta ce mini sunanta Muhaibish" Tari ta yi tana kare bakinta da busasshen hannunta mai tsananin dauɗa ta ci gaba da cewa, "Tsakanina da Matarka sai dai Allah ya isa, kuma umarni nake baka kayi mata saki uku rass idan ba haka ba wallahi sai na tsine maka" Gaban Sarki Abdallah ne ya faɗi musamman da yaji ta ambaci sunan Muhaibish, azuciyarsa yake maimaita sunan sannan yake ayyana anya ba aljanu ne suke neman wasa da hankulansu ba, kallan Dogarawan ya yi a ɗan fusace ya buga musu yace, "Ina magana kuna tsaye" Jiki na rawa suka fara kinkimarta suka wuce da ita cen ɗakin baya. Sarki Abdallah ya juya zai koma ciki saura kaɗan ya yi tuntuɓe da Hansatu matar Waziri tana kuka da birgima a gabansa tana cewa, "Wayyo ni wayyo gata na ya ƙare shikenan rayuwarmu ta zo ƙarshe Takawa, shikenan sun kashe mini shi ɗazu-ɗazu muka gama fita da shi amma wai babu shi sun kashe kai jama'a wallahi Allah ya isa tsakaninmu da duk wanda ya yi masa wannan mugun abun."
Wani Dogari ne ya buga mata tsawa yana shirin magana Takawa ya dakatar da shi ya kalli Hansatu yace, "Me yake faruwa Hansatu?" Hansatu ta goge hawayenta da gefen rigarta cikin kuka ta fara magana, "Allah ya taimake ka lafiya ƙalau muna zaune muna hira da Babansu Rafi'u kawai sai ji nayi yana cewa ƙafarsa kamar almara haka naga jini na tsartuwa ta tsakankanin ƙafafuwansa, daga haka naji yana cewa Muhaibish ta gafarce shi ruɗin zuciya ne amma ta bashi dama zai gyara kuskurenshi, daga haka bai ƙara magana ba sai gani nayi bakinsa na talewa kafin wani lokaci anɓare bakinsa kamar na yankakkiyar tinkiya, wannan ban da aikin asiri ya za'ayi haka ta faru?" Tana gama faɗa ta sake rushewa da kuka tana buga ƙasa. Sarki Abdallah ji ya yi kansa ya yi nauyi duk dakiya irin tashi sai da ƙwallah ta zubo masa, cikin tausaya ya kalli wasu Bayi mata yace, "Ku ƙarasa gida da ita ku kwantar mata da hankali" Tun bai rufe baki ba suka ƙarasa wurin Hansatu suka kamata suka wuce da ita, har zuwa lokacin kuka take me tsuma zuciya. Kallan wani dogarinsa ya yi yace, "Aje a samu Galadima suyi masa sutura idan ankammala ayi mini magana." Yana gama magana ya fara takawa a hankali kamar Kazar da ƙwai ya fashewa a ciki. Maleek daskarewa ya yi a wuri shima a hankali ya fara takawa ya wuce har ya nufi hanyar sashensu ya tuna da masallaci zashi wanda tuni har an idar da sallahr yana tsaye ganin al'ajabi.
Fulani Babba ban da zarya babu abin da take yi a tsakiyar ɗakinta sakamakon mugun labarin da ya iso mata, wanda ba ta taɓa tsammanin makamancinsa ba ko a mafarkinta. A fili ta furta, "Anya wannan Shukran da na sani ce? Me yasa zuwanta ya zame mini masifa da bayyanar al'amurana, tabbas akwai wani ɓoyayyan al'amari a game da ita koma menene dole na dakatar da ita kota halin ƙaƙa." Wani abu taji yana ɗan yi mata yawo a jiki da sauri ta kai hannu tana ƙoƙarin cire shi amma babu komai, haka taji ya fara mamaye jikinta ta ko'ina kamar tafiyar ƙadangare. Tun tana daga zaune harta miƙe tsaye tana karkaɗe-karkaɗe, kamar saukar aradu haka ta ji muryar wani Dattijo yana cewa, "Kin karya mana alƙawari karki zargi kowa game da abin da zai biyo bayanki idan kin tuna da yarjejeniyarmu a shekarun baya da suka wuce." Shiru taji kamar anyi ruwan sama an ɗauke haka taji mai maganar ya yi ɗiff komai ya ɗauke, daga ƙasanta ji ta yi kamar abu na zuba tana dubawa ta ga wani farin ruwa na ɗan tsiyaya me wari-wari. Tana nan tsaye ta ji wannan tafiyar ƙadangaren tana ci gaba da yi a jikinta ga fatar jikinta na mata wani irin tauna kamar ana yagar naman jikinta, cikin fitar hayyaci ta fice a guje tana kururuwar neman taimako. Bayinta da suka ga haka suma suka rufa mata baya suna ƙoƙarin kamota dan gudu take kanta ba dankwali ga zanin jikinta ta fara yagewa tana cewa, "Wace ce ke da zaki dagula mini lissafi?" Cak ta tsaya waje ɗaya tana ja da baya sai kuma ta ce, "Kika ce sunanki Muhaibish? Ba ke ce Shukura ba?" Zubawa ta ƙara yi a guje kamar zautacciya tana cewa, " Dan Allah ki yi haƙuri Shukura wallahi kuskure ne na tuba ki yafe ni, wayyo Allahna!" Tana faɗar haka tana ƙoƙarin tsige zanin jikinta har ta nufi fadar Sarki Abdallah daga ita sai fatarinta tana ƙoƙarin yage rigar jikinta.
Sarki Aminullahi shiru ya yi yana nazari saboda shi kansa tun da su Maleek suka tafi da yarinyar kullin sai ya yi mafarki da ita kala-kala, mafarkai yake ba fasali shi kaɗai ƴan kwanakin nan ban da tunaninta babu abin da yake yi. Har mamaki yake akan me zai zauna yana tunani akanta bayan babu wani abu da ya haɗa da ita, sautari mafi yawan mafarkinsa yana mafarki yana cikin hatsari tana ƙoƙarin cetonsa. Sai dai duka mafarkinsa zai yi tare da Salman da ita amma Salman na ƙoƙarin cutar da shi ita tana yunƙurin ceton sa. Numfasawa ya yi kalli Fulani Zaliha da ta zuba masa idanu yace, "Zaliha kin san dai baza mu aikata abin da ba haka yake ba kuma idan ance haka yana nufin mun aikata haramci kenan?" Fulani Zaliha ta ce, "Allah ya huci zuciyarka a dai duba tambayata, ko a mafarki bana tunanin zaka iya aikata makamancin haka sai dai ko a cikin halin rashin sani, Allah ya baka yawan rai a bincika da kyau ina fatan ban ɓata maka rai ba" Shiru Sarki Aminullah ya yi yace, "Shikenan! Amma bama tunanin haka zata iya kasancewa tun da yarinyar da Mariƙiyarta sun amince. Amma zan kira Fahima naji halin halin da ake ciki."
Ku kawo ɗauki Masarautar Adamawa tana cikin wani yanayi😂
_LITTAFIN NAN NA KUÆŠI NE DA NAIRA 200 ZAKI KARANTA SHI CIKIN KWANCIYAR HANKALI, ZAKU BIYA TA WANNAN ACCOUNT ÆŠIN, FIRST BANK 3090957579 AISHA ADAM, ZA'A TURO DA SHAIDAR BIYA TA WANNAN LAMBAR,0706 206 2624, DAN GIRMAN ALLAH IDAN KINSAN ZAKI FITARMUN DA LITTAFI NA YAFE CINIKINKI._
[27/11/2021, 17:56] Ameera Adam🌚: 37...
Fulani Babba na shiga fadar tun daga bakin ƙofa ta fara soshe-soshe tana ɗaga rigarta sama, a zabure Sarki Abdallah ya miƙe duk da kasancewar fadar babu mutane sosai bai fi mutum huɗu bane a ciki. Fulani Babba tunkarar Takawa ta fara yi tana cewa, "Dan Allah ka dakatar da ita zata kashe wallahi illatani take son yi, wayyo Allah jikina! Wayyo shukura zata kashe ni" tana nan tsaye Bayin ta suka shigo da gudu sai kuma suka yi carko-carko, Sarki Abdallah ya buga musu tsawa yana cewa, "Baku da hankali ne da kuna ganinta ba za ku iya mayar da ita cikin gida ba a wannan halin?" Da sauri suka matsa suna son kama Fulani Babba suna jin tsoro, dake wa kawai suka yi suka rirriƙeta suka fara kiciniyar wucewa da ita nan ta fara ihu tana faɗin, "Ku ƙyaleni na kaiwa mijina kuka shi kaɗai zai share mini hawaye na..." bata ƙarasa faɗa ba suka fice da ita. Sarki Abdallah komawa ya yi daɓass ya zauna ya dafe kansa yana nazari hankali a tashe, gabaɗaya baya cikin hayyacinsa saboda damuwa. Miƙe wa ya yi zai fice sai ga Dogarin da ya aika kiran Malam liman ya shiga yana cewa, "Allah ya taimakeka ya baka yawan rai Malam Liman yana cen ɗakin da aka kai Mai babban ɗaki" sai a lokacin ya tuno da aiken da ya yi bai iya tanka masa ba sai gyaɗa kai da ya yi sannan dogari ya fice daga fadar. Bayan wani lokaci jiki a sanyaye Sarki Abdallah ya fice zuwa ɗakin da Liman yake tare da rakiyar dogarawansa da suke take masa baya. Lokacin da ya shiga Malam Liman har ya gabatar da alwala ya fara yi wa Mai babban daƙi ruƙiyya, Sarki Abdallah gefe ɗaya ya ja ya zauna yana kallonsu, tana zaune cikin kojalallun kayanta jikinta futu-futu kamar wacce aka tono daga cikin rami. Malam Liman ya jima yana abu ɗaya sanann ya sallame ya kalli Sarki Abdallah ya ce, "Allah ya taimake ka ba na tunanin akwai shafar jinnu a jikin baiwar Allahr nan, sai dai tabbas akwai ɓoyayyan al'amari." Mai babban ɗaki ta ƙurawa Malam Liman ido ta ce, "Tabbas akwai ɓoyayyan al'amari domin kuwa matarsa ita ce silar shiga ta cikin wannan halin. Da saninta aka killace ni a kogon dutsen bokanta, na tabbata ba ta taɓa zaton haka za ta iya faruwa ba, ba ta yi tsammanin zan iya dawowa cikin ahalina ba" tana zuwa nan a zancenta ta rushe da kuka. Jikinsu ne ya yi sanyi Sarki Abdallah ya gyara zaman yace, "Amma sama da shekaru ashirin kenan da muka wayi gari da gawarki a ɗaki wannan lamari akwai rikitarwa." Mai babban ɗaki ta ce, "Idan kun tsaya kun fahimceni lamarin ba zai rikitar da ku ba, ka je ka duba matarka na san yanzu haka idan bata fara hauka da fisge-fisge ba tana kan hanya domin sharaɗin da bokanta ya gindaya mata kenan matuƙar na dawo masarautar nan" A firgice ya ɗago yana kallonta tabbas maganar da ta faɗa ta tabbata amma ya za a yi ace matacce ya tashi, gaskiya lamarin akwai rufa ido. Miƙe wa Sarki Abdallah ya yi yace, "Malam Liman anya lamarin nan babu shafar jinnu kuwa ina ganin rufa ido suke san yi mana" yana gama faɗa ya juya zai fice da sauri Malam Liman yace, "Allah ya taimake ka na tabbata ka san ƙur'ani zancen Allah ne, kuma idan har jinnu ne zasu bayyana kansu gaskiya ina ji a jiki akwai ƙamshin gaskiya a maganarta. Shi kansa a wannan lokacin ya fara gasgatawa amma abin da yake mamaki da shi ya za a yi matacce ya tashi, juyowa ya yi ya kalli dogarawan da ke tsaye yace, " A kira bayi mata su tafi da ita su gyara mata jikinta." yana gama faɗa ya fice daga ɗakin, bayan fitarsa Mai babban ɗaki ta fashe da kuka ta ɗago ta kalli Liman ta ce, "Wai yanzu ni Audullahi yake tuhuma da rashin gaskiya anya matar cen bata juya masa ƙwaƙwalwa ba?" Malam Liman cikin tausayawa ya fara lallashinta har tayi shiru babu jimawa Bayi suka ɗauketa suka tafi da ita.
Da mamaki yake kallonta yana daɗa mamakin irin wannan ɗogon baccin da take yi kamar na rashin lafiya, bubbuga fulonta ya fara yi yana kiran sunanta jin ta yi shiru tana bacci lamarin da ya fara bashi tsoro. Hannu yasa ya fara ɗan dukan ƙafarta amma har wannan lokacin ko motsi bata yi ga kuma munshari nan tana