Showing 51001 words to 54000 words out of 89213 words

Chapter 18 - Anya Baiwa Ce 2 Complete Hausa Novel By Aisha Adam.txt

30 Nov 2024

5357

Baiwarta shigowa a guje cikin tashin hankali ta tsaya a bakin ƙofar tana cewa, "Ranki shi daɗe kina buƙatar taimako ne?" Jin Fulani Maryama shiru ya sa Baiwarta ta faɗa ɗakin, da sauri ta matsa kusa da ita ganin halin da take ciki, a wahalce ta ɗago tana cewa, "A kwai yarinyar da ta fita ku maza ku ruƙo ta." Da mamaki Baiwarta ta ce, "Allah ya taimakeki muna zaune a rumfa (Falo) ba mu ji mostin kowa ba, babu wacce ta fita." Ɗagowa ta yi da idanu tana watsa mata mugun kallo a fusace ta ce, "Ƙarya nake miki kenan?" Matsawa baya Baiwar ta yi ta ce, "Wallahi Ranko shi daɗe babu wacce ta fita..." Cikin masifa Fulani Maryama ta ce, "Kina hauka ne yanzunan yarinyar nan Maryo ta fita ki ce mini babu wacce ta fita." Baiwar ta ce, "Bari na yi wa su Shafa'atu magana ko sun ga wucewarta." Tana gama maganar ta fice.


Tun daga ɗan yatsanta har zuwa kafaɗarta hannunta ji ta yi ya yi wani irin sanyi ya sage mata, ɗayan hannun ta saka ta tallafo hannun sai jinsa ta yi ya yi wani sharaf. Tsoro ne ya fara kamata ta yi yunƙurin sake ɗaga hannun amma ta ji ya yi mata dum! Kamar an ɗora mata Dala da gwauron dutse. Hankalin Fulani Marayama ba ƙaramin tashi ya yi ba, nan take ta fara ayyana ko dai aljanu ne suka yi mata siffar Maryo tun da, da alama sun shanye mata hannu. Tana cikin wannan yanayin su Shafa'atu suka yi sallama suna cewar, "Allah ya taimake ki wallahi..." Da sauri ta buga musu tsawa tana cewa, "Ku fice mini ba na son ganinku!" Tun bata rufe baki ba suka fice a guje ko waiwaye babu me yi. Kamar ƙaramar yarinya haka Fulani Maryama ta tallaɓo shanyayyen hannunta ta rushe da wani irin kuka be man tausayi.


A daidai lokacin da su Inna Habi za su shiga ɗakin da Abu take Saif ya diro kamar wanda aka jefo daga sama, saboda tsoron da suka ji har ja suka yi da baya. Bai kalle su ba ya faɗa ɗakin da gudu don ihun Abu jinsa yake har cikin jikinsa, a wannan yanayin da yake ciki baya jin ko ɗigon soyayyar Abu a zuciyarsa amma tabbas shi kansa ya san yana matuƙar tausaya mata, domin duk macen da ke ɗauke da Ɗa a cikin cikinta tabbas abar tausayi ce, bare macen da ke cikin mawuyacin hali irin wannan da bata ji ba bata gani ba kuma a aiwatar mata da rashin imani irin wannan. Yana shiga ɗakin a tsaye ya samu Salman da ke ɗauke da siffar Maryo, Abu ban da murƙususu babu abin da take yi, hannunta na dafe a cikinta. Saif na shiga ya ƙarasa wurinta ya rungumota jikinsa, yana ɗora hannunsa akan saitin wurin da ya ga tana dafawa. Wata irin shu'umar dariya Salman yake ƙyaƙyatawa a daidai lokacin su Inna Habi suka shiga sai kuma ya rikiɗe zuwa siffar Likita kafin su ankara da shi. Hankali a tashe Inna Habi ta ce, "Likita me yake faruwa me ya same ta." Sai a lokacin Saif ya fahimci yaudarar da Salman ya yi wa su Inna Habi, ganin yadda Saif ya yi wa Abu ya sa Inna Habi ta ja da baya ta fice daga ɗakin saboda kunya. Su Uwar Bayi ma fita suka yi tana cewa, "To bari mu basu wuri tun da mijinta na kusa duk abin da ya kamata sai ka sanar da shi." A wahalce Abu ta ɗago ta dubi Saif hawaye na zuba daga idonta, shima idanunsa ne suka ciko da ƙwalla ya sauke idonsa ƙasa yana haɗa fuskarsu wuri ɗaya. A daidai lokacin Maryo ta faɗo ɗakin bayan ta baro wurin Fulani Maryama.


Tana shiga ɗakin ta kalli Salman cike da tsoro don ta tabbata ganinsa a nan ba alheri bane, da sauri ta nufi gadon da Abu take don ganin halin da take ciki, nan take ta yi tozali da Saif rumgume da Abu, wani abu ta ji ya soki ƙahon zuciyarta amma sai ta kauda kai gefe tana lumshe ido, a daidai lokacin Abu ta fara zubda ƙwalla murya can ciki ta ce, "Saif!" Ɗagowa ya yi ya kalleta hatta Maryo da ke gefe sai da ta kalle ta domin yadda ta faɗi sunan za ka tabbatar da tana cikin wani irin mummunan yanayi, ta ɗan cije bakinta saboda yadda take ji ta ci gaba da cewa, "Tabbas na aikata babban kuskure, na ɗauka soyayyar ita ce farincikin komai a rayuwar nan. Ta rufe mini ido a lokacin da take buga mini gangarta, ta yadda na kasa fahimtar kuskuren da hakan ke tattare da shi. Na makance a kan soyayyarka Saif ta yadda na manta soyayyar 'yan uwantaka, amma ban yi zaton hakan har zai ka ga 'yar uwata na neman halakani ba. Duk duniya ba ni da na biyun Maryo ta ƙaunace ni kuma na tabbata soyayyarka ce ta sa ta aikata mini haka." Hankali a tashe Maryo ta kalli Abu jikinta har rawa yake ta ƙarasa wurin Salman ta cukumi wuyansa tana faɗin, "Me ka aikata mata a siffata, wallahi muddin ka cutar da ita ba zan yafe maka ba. Ina ƙara gaya maka bana son zubar jini ya wanzu a masarautar nan amma da alama kana son tarihi ya sake maimaita kansa." Sai a lokacin Abu ta waigo suna haɗa ido da Maryo ta ji tsoronta ya sake kamata, Maryo tuni hawaye ya fara wanke fuskarta domin ta lura da irin zallar tsoron dake kwance a fuskar ƴar uwarta. Sake rungume ta Saif ya yi zata sake magana ya haɗe bakinsu wuri ɗaya, da ƙarfi ya shiga hura mata iska a bakin tun tana cikin hayyacinta har ta fita daga hayyacinta idanunta suka fara lumshewa. Sannan ya ɗauke bakinsa daga nata, kamar saukar ruwan sama haka ta fara kwara wani irin baƙin amai kamar za ta amayar da hanjin cikinta. Da sauri Maryo ta ƙaraso ta riƙe ta a ɗan fusace ta ce, "Me kake yi haka ne Saif?" Ido ya zuba mata sannan yace, "Hakan shi ne mafita idan na barta da gudar da ya zuba mata tabbas zai cutar da ita da abin da yake cikinta." Idonta ne ya ci gaba da zubda ƙwalla ta sunkuyar da kai ƙasa bata furta komai ba sai kuma ta yi gaba, da sauri Saif ya riƙo hannunta don ya fahimci abin da za ta aikata, juyowa ta yi a zafafe amma kallon yake yi mata ya saukar mata da kasala, hakan ya sa ta sunkuyar da kai ƙasa ta ce, "Don Allah ka sake ni!" Shiru ya yi mata bai tanka mata.


Salman da ke gefe ya saki dariya me sauti yana tafi da hannunsa yace, "Ka bar murna karenka ya kama Kura." Saif ya ɗaga masa gira ɗaya yace, "Ka san ko kura ta rame ta fi ƙarfin gawurtattun karnuka." Maryo ta nuna shi da ɗan yatsa fuska babu walwala ta ce, "Duk a kaina kake wannan haukan ko? Ka ɗauka zan ƙaunace ka ne bayan kana barazanar halakar da ƴar uwata. Ka buɗe kunnenka ka saurareni da kyau ka ji, wallahi baka ci bulus ba na rantse da Allah sai na baƙanta maka da baƙin ciki me tsanani. Idan ma saboda Saif kake yi wannan haukan daga kai har shi babu wanda zan aura, na faɗa na ƙara wallahi babu mutum ɗaya daga cikinku da zan aura. Ka taɓa mini 'Yar uwata ni kuma na ɗaura ɗambar taɓaka tun daga yau har ƙarshen rayuwata." Abu ce ta jiyo ta kalli Maryo tana miƙa mata hannu, a hankali Maryo ta ƙarasa ta riƙe hannunta tana sunkuyar da kai ƙasa ta fara cewa,


"Don Allah ki gafarce ni ƴar uwata ba ni na cutar da ke ba, kuma ba ni da burin cutar da ke daidai da ƙwayar zarra a zuciyata, duk wannan abin ya faru da ke ta sanadina ne don Allah ki yafe mini." Maryo ta faɗa tana kallon ƙwayar idon Abu, Saif ne ya taimaka mata ta tashi daga gadon da take kai zuwa wani gadon ya nannaɗe zanin gadon da ya ɓaci, a hankali Maryo ta bi ta kan sabon gadon ta sake zuba mata idanu don jin amsar da Abu za ta bata.


Abu ce ta kalli Saif da ke hidima da kayan wurin ta ce, "Ba zan taɓa yafe miki ba har sai Saif ya yi mini alƙawarin duk abin da na buƙata a wurinsa zai aiwatar mini." Gaban Maryo ne ya yi mummuna faɗuwa, Saif ya tsaya cak sannan ya waigo ya zubawa Abu ido yana juya maganganunta. Gyaɗa masa kai ta yi, a hankali Saif ya furta, "In dai za ki yafe mata na yi miki alƙwarin biya miki buƙatarki matuƙar bata saɓawa addinin musulunci ba." Abu ta gyara kwanciyarta tana cewa, "Don girman Allah ka sauwaƙe mini ka auri 'yar uwata Maryo, wallahi ko baka sauwaƙe mini ba na yi alƙawarin ba zan koma gidanka ba." Jin maganarta ya yi dum! ya zuba mata idanu ya kasa furta koda kalma ɗaya ce. Da ƙarfi Maryo ta daki gadon da Abu take kai ta ce, "Yaushe kika fara hauka Abu ban sani ba? Kina cikin hayyacinki kuwa?" Abu ta saki murmushi ta ce, "Tun da muke baki taɓa gaya mini magana ta rashin girmamawa irin wannan ba, me ya sa don na faɗi abin da yake raina zamu fara haka da ke.?" Idanun Maryo ya kaɗa jawur ta ce, "Wa muke bautawa?" Abu ta ce, "Allah!" Maryo ta jinjina kai ta ce, "Na rantse da girmansa idan har Saif ya sake ki saboda wannan buƙatar taki babu ni babu ke, kin sanni farin sani idan ba bar abu na bar shi har abada kar ki janyo abin da zai rabani da ke. Karki manta komai rubutacce ne a wurin Ubangiji, kina tunanin bawa zai iya gujewa rubutacciyar ƙaddararsa? Kenan Allah ba zai jarabcemu ba ko mun fi Ubangiji sanin abin da ya kama? Ko kina gidan Saif ko bakya gidansa wallahi ba zan aure shi ba don haka idan kina son na ci gaba da ɗaukanki kamar yadda muke da ki bar wannan maganar."


Abu ta lumshe ido ta ce, "Ina burin ganin farincikinki Maryo amma ki sani wannan ciwon nawa ba na tashi bane don Allah ki bari na ga aurenki da Saif kar sai lokacin da ƙasa ta rufe mini ido a yi babu ni, domin ina ji a jikin wannan cikin abokin tafiyata ne..." Da sauri Saif ya rufe mata baki idanunsa sun yi jawur saboda tashin hankali, Maryo jikinta na rawa ta ƙarasa wurim Abu ta ce, "Ya isa ki bari ki samu lafiya duk abin da kike so haka za a yi ba dai so kike na aure shi ba. To Allah ya baki lafiya." Kamar me shirin ta shi sama haka Salman ya fice fuuuu daga cikin ɗakin. Gabaɗaya suka bi shi da kallo babu wanda ya tanka masa.


Abu ta ce, "Maryo meye alaƙarki da Likitan can har kuke musayar yawu." Nan take Saif ya sanar da ita abin da yake faruwa, Maryo ta kora mata bayanin burin Saif a kanta. Ganin ta shiga damuwa ya sa suka kwantar mata da hankali da nuna mata hanyoyin da za su shawo kan matsara. Maryo ta sanar da Abu za ta auri Saif ne domin ta lura idan ta biye mata sai jikinta ya sake rikicewa fiye da na baya, don ta lura da nadamar aurensa da ƴar uwar tata ta yi.


Fulani Maryama ta gana tabbatarwa da kanta hannunta ya riga da ya shanye, ba a ɗauki lokaci ba ta sanarwa da Takawa duk abin da yake faruwa, lokacin da take yi masa bayani kuka ne a fuskarta shaɓe-shaɓe. Ba ƙaramin tausaya mata ya yi ba, amma abin da ya fi daminsa da ta ce Maryo ce ta shanye mata hannu sai dai an tabbatar da cewar tun da aka tafi da Abu asibiti babu wanda ya ga gilmawar Maryo, ganin yadda ta rikice ya sa Sarki Aminullah ya tabbatar da cewar tabbas aljanu ne suka shafe ta domin babu yadda za a yi ace mutum ɗan uwanka ya shanye maka hannu. A ranar ya aika ka fara gayyato masu magungunan gargajiya domin sun bata magani ko hannun ya miƙe. Kafin wani lokaci tuni shanyewar hannun Fulani Maryama ya karaɗe cikin Masarautar, wannan gayawa wancan gayawa wancan. Sauran kishiyoyinta sam maganar bata yi musu daɗi ba haka daga ɓangaren Jakadiya lokacin da labarin ya je mata sai da ta shiga banɗaki sau biyu sannan ta lallaɓa ta nufi sashen Fulani Maryama domin tabbatar da abin da kunnuwanta suka jiye mata dukda ita ma ba maruru na ci gaba da rarake hammatarta.


Abu satinta Biyu a asibiti aka sallamota jikinta ya yi kyau sosai ta warware, cikinta ya ƙara tsufa da ƙyar take iya ɗaga ƙafarta, wannan dalilin ya sa Fulani Zaliha ta dakatar da komen Abu ta umarci a mayar da ita sashenta domin ta ci gaba da bata kulawar da Uwa take bawa ƴarta. Inna Habi na jin daɗin yadda Fulani Zaliha take ƙaunar Abu, Maryo ku san kullin tana wurin Abu domin idan damuwa ta yi mata yawa in taje can tana samun sauƙin halin da take ciki. Hakan yana yi wa Inna Habi daɗi domin damuwar da Maryo take shiga na raguwa, ana cikin haka Maleek ya kawo mata ƙoƙon barar soyayyarsa. Da farko ta so ta bijire masa amma sai ta yi tunani idan ba amince masa ta yi ba ba zata samu kwanciyar hankali a wurin Saif da Salman ba, domin ta san ita kanta Abu ta yi mata shiru amma ta jadadda mata baza ta koma gidan Saif ba ya fi a irga. Wannan labari ba ƙaramin daɗi ya yi wa Inna Habi ba dama kuma duk wanda ya ga yadda Maleek yake yi wa Maryo zai tabbatar da irin ƙaunar da yake yi mata.


Ba a ɗauko lokaci ba Manya suka suka shiga magana, Mahaifin Maleek ya zo Masarautar Kano ya nemar Ɗansa auren Maryo a wurin Sarki Aminullah. Takawa sai da ya ji ta bakin Maryo domin yace wannan karan sai an ji daga gare ta, a kunyace ta amsa dukda za ta auri Maleek ne ba don tana sonsa ba sai don kyawun halinsa da kulawar da yake bata. Nan take Sarki Aminullah ya sanya musu rana wata biyu masu zuwa. Lokacin da Saif da Salman suka samu wannan labarin ba ƙaramin girgiza su ya yi ba, amma ga mamakin Maryo sai ta ga Salman bai nuna wata damuwa ba sai dai Saif da ya rikice mata yana nuna mata tsananin damuwarsa.


BAYAN SATI UKU


Ranar Laraba da daddare naƙuda ta kama Abu tun tana ɓoyewa har ta ji ciwon ya tsananta ta fara sintiri a ɗaki, Fulani Zaliha ce ta farka saboda jin motsin Abu da ta yi. Ku san kwana ta yi tana abu ɗaya sai bayan Asuba Allah ya sauke ta lafiya ta haifo santalelan Ɗanta namiji kyakkyawa kamarsa ɗaya sak da Saif. Fulani Zaliha ba ƙaramin farinciki ta yi bata jima tana kallon yaron sai take tuna lokacin da haifi Saif, rumgume shi ta yi tana godiya ga Allah bisa wannan kyautar da ya yi musu.


Da kanta ta gyara Mai jego ta da jariri sannan ta mayar da su kan shimfiɗa Abu ta rungume Ɗanta suka koma bacci, sai a lokacin Fulani Zaliha ta aika Bayi da ta kira Unguwar zoma, nan take ta ƙaraso ta gyara wurin sannan aka fara sanarwa da mutanen kyakkyawan albishir.




_LITTAFIN NAN NA KUƊI NE DA NAIRA 200 ZAKI KARANTA SHI CIKIN KWANCIYAR HANKALI, ZAKU BIYA TA WANNAN ACCOUNT ƊIN, FIRST BANK 3090957579 AISHA ADAM, ZA'A TURO DA SHAIDAR BIYA TA WANNAN LAMBAR,0706 206 2624, DAN GIRMAN ALLAH IDAN KINSAN ZAKI FITARMUN DA LITTAFI NA YAFE CINIKINKI._




[12/01, 18:55] Ameera Adam🌚: 61...


Waiwaye...


Duk yadda Zulik zai yi ya janyo hankalin Rayzuta ya yi amma sam abin ya faskara, hasali ma 'yar gaisuwar mutumcin da suke yi ma ta yanke ta don ko ya zo cikin fadarsu idan tana zaune, ko ta tashi ko ta nemi wani uzurin da zai tashe ta daga wurin, abin sam baya yi wa Furzaan daɗi sakamakon Zulik abokinsa ne makusanci ba shi da na biyunsa. Hasali shi ba mai sha'awar tara abokai bane, wannan dalilin ya sa kodayaushe yana cikin masarauta idan baya sashen su to yana wurin ƙawarsa wacce ta rikiɗe zuwa masoyiyarsa. Wata ranar Juma'a suna zaune cikin lambum Mahaifinta suna hira Furzaan ya zuba mata ido lokacin da take ba shi labarin mafarkin da ta yi,


Bari mu ɗan taɓa yaren nasu🌚


"Wurbankis guna bila kalbistu kinmansu walbisu fatgurin zakbistu..."


(Ka bani goron albishir na baka labarin mafarkin da na yi, ka san mai ya faru...)


Sai kuma ta katse maganar bakinta tana zuba masa ido har ta sa hannu a saitim fuskarsa, har sai da ta ɗan tafa hannunta a kan fuskarsa sannan ta ɗan ɓata fuska ta ce, "Wai dama ba saurarena kake yi ba."


Shagwaɓe fuska ya yi yace, "A kodayaushe sauraron muryarki na sanya ni faɗawa cikin wani yanayi, har yanzu gani nake ina ta bilayi ban sani ba ko waiwayen da nake yi za a fahimci ƙishirwata. Sai dai a koyaushe idan na yi tuno da giwa ta yi wa barewa nauyi na kan ji karaya a zuciyata, sai dai bana jin zan iya jure kishirwar da nake ji ba tare da na kawar da ita ba." sai kuma ya marairaice murya kamar mai shirin yin kuka ya ci gaba da cewa, "Ba ta yi mini adalci ba kuma da zan iya tozali da na hukuntata da hukunci mai tsanani saboda bata shawarce ni ba. Na faɗa kogin soyayya ba tare da shiri ba sai dai bana jin zan samu gurbi domin bakin rijiya ba wurin wasa makaho bane. Wannan dalilin

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login