Showing 81001 words to 84000 words out of 89213 words

Chapter 28 - Anya Baiwa Ce 2 Complete Hausa Novel By Aisha Adam.txt

30 Nov 2024

5349

yanzu nake shirin aikawa kiranki don ke na lura kamar ko a jikinki, an ya ba da gayya ba wannan zaman na ki ni fa ya fara isa ta." Zame hannunta ta yi tana bagarar da maganarsa ta hanyar cewa, "Dama na zo ɗaukan Naufal..." Bata rufe bakinta ba ta ji ya katse mata maganar ta hanyar sanya hannuwansa biyu a ƙugunta tare da faɗin, "Tun da Naufal ya yi bacci sai ki ɗauki Baban Naufal." Ɓata fuska ta yi tana kiciniyar ƙwace kanta amma ta kasa don haka ta dube shi ta ce, "Don Allah meye haka ne ka sake ni kar su ga na daɗe." Ido ya zuba mata yana kallon yanda take motsa laɓɓanta sannu a hankali, wata irin ƙaunarta ya ji ta ƙara mamaye ziciyarsa. Bai san lokacin da ya fara yawo da hannunsa cikin sassan jikinta ba, a hargitse ya fara ture hannunsa tana cewa, "Me kake yi haka Saif."


Bai kalleta ba ya ci gaba da aika mata saƙonni masu wuyar fasaltuwa tun tana yunƙurin ƙwatar kanta har ta gagara taɓuka komai. Jin lamarin nasa na neman wuce gona da iri ya sa Maryo dakatar da shi ta hanyar gantsara masa cizo. Ɗagowa ya yi cikin wata irin murya yace, "Don Allah..." Bai ƙarasa magana ba ya ji bugun ƙofa daga can bakin ƙofa Baiwar Fulani Zaliha na rafsa sallama, hankali a tashe Maryo ta fara cikiniyar kwacewa, tabatuni hawaye ya fara ambaliya a idonta ta dube shi ta ce, "Ka ga abin da nake gudu yanzu idan aka gammu fa." Wara mata hannuwa ya yi alamun ko a jikinsa ya sake rungumota jikinsa yana cewa, "Sai me idan angammun ina ce ke matata ce ko haramun ne." Jin bugun ƙofar ba ƙaramin razana Maryo ya yi ba, a hargitse ta juya za ta fita da sauri yace, "Ki tsaya ki daidaita kanki kafin ki fita." Cak ta tsaya ta kasa gaba da baya, jin takunsa ta fara yi zuwa wurinta tana juyawa ya miƙa mata Mayafinta. Kunya ce ta kamata don gabaɗaya bata san lokacin da Mayafin nata ya faɗi ba, karɓa ta yi da sauri za ta fice. Janyota ya yi ya sa hannu ya ɗago haɓarta har suna jin numfashin juna sannan yace, "Na ta ya ki murnar bayyanar Mahaifanmu!" Ɗago ta yi ta kalle shi karaf idanunsu suka haɗu bata san lokacin da ta sakar masa murmushi ba don ko babu komai kalamansa sun faranta mata zuciya. Tabbas iyaye na daban ne jin ta take wani iri don gani take abun kamar a mafarki ne ace wai ita ce yau take da Mahaifa kamar kowa dukda Inna Habi bata rage ta da komai ba. Tana cikin tunani bata yi aune ba ta ji yana ƙoƙarin kai bakinsa cikin nata, da sauri ta ƙwace kanta tana ficewa daga sashen. Dariya mai sauti ya saki yana jin wani irin farin ciki na ratsa sassan jikinsa. Takawa ya fara yi a hankali ya ƙarasa ƙofar sashensa wacce tun shigowar Maryo ya rufe ta, tana tsaye ya same ta a bakin ƙofa yana zuwa ya yi mata dariyar ƙeta yace, "An jima za ki koya mini irin gudun nan na ki, domin na ji Takawa ya yi zancen tariyarki." Lokaci ɗaya Maryo ta yi saranda har ji ta yi ƙafafuwanta na gagarar ɗaukanta. Yana buɗe mata ba ta ƙara gigin tsayawa ba ta yi gaba domin magangunsa na yunƙurun kurumtar da kunnuwanta.


Kamar sabuwar munafuka haka ta fice daga sashen Saif tana zuwa harabar gidan ta cin karo da Fulani Zaliha ta fara sunne kai ƙasa, a ɗan duburburce ta kalli Fulani Zaliha ta ga fuskarta murtuk ba fara'a ta ce, "Allah ya taimakake ki dama ɗaukan Naufal na..." Bata gama faɗar abin da yake bakinta ba Fulani Zaliha ta katse ta cewar, "Ina Naufal ɗin?" Maryo dum! Ta yi sannan ta ce, "Bacci... Yake." Fulani Zaliha ta saki murmushinsu na manya ta ce, "Idan ya tashi ki ce ya taho miki da Ɗankwalinki." A firgice Maryo ta shafa kanta don tabbatar da abin da Sirikarta ta faɗa, tana shafawa ta ji babu ɗankwali a kanta. Wata irin kunya ce ta kama ta da gudu ta fice daga sashen don tun da take bata taɓa jin irin kunyar da ta ji a wannan lokacin ba.


Tana fita Fulani Zaliha ta saki murmushi haka kawai ta ji Maryo na ƙara birgeta a zuciyarta.


Komawarta sashen su tana shiga wani irin wari ya ƙara mamaye ta saɓanin na da, da yake bugawa sama-sama. Hannuwa biyu ta sa ta fara toshe hancinta tana kallon sashen Fulani Maryama da banda warin da kukan ƙusaje babu abin da yake tashi. Tana shiga ɗakinsu ta samu Inna Habi na turara turaren wuta, ajiyar zuciya ta sauke dukda warin na doko cikin ɗakin. Abu na ganinta a hargitse ta saki murmushin ƙeta ta ce, "Ina Naufal ɗin" Nan take Maryo ta hau inda-inda daga ƙarshe dai ta ce, "Bacci yake kuma kin san ba a son tashin yara idan suna bacci." Abu ta riƙe haɓa ta ce, "To! Ko kema baccin ne ya ɗauke ki don na ji ki shiru kamar an aiki bawa garinsu." Maryo ta watsa mata harara don ta fahimci neman magana Abu take yi. Ɗauke kanta gefe ta yi ta ce, "Ni dai ban ce ba."


Abu ƙasa-ƙasa ta yi da murya ta ce, "Ummm! Idan ma haka ne meye na musu mace da mijinta." Maryo na jin haka ta wuce uwar ɗaki ko bin ta kan Abu bata yi ba. Don ta san halin Abu da zolaya tun da ta gane lagonta ta shiga uku."


Duk yanda Sarkin Zazzau ya so tafiya da Maryo Sarki Aminullah ya ƙi amincewa, akan dole yana ji yana gani haka suka juya masarautar Zazzau, sai dai kafin tafiyarsa sai da aka kira masa Maryo ya gabatar mata da Yarima a matsayin Ɗanwanta. Lokacin da za su yi sallama kamar kar ya tafi amma hakan da ya yi ya san shi ne daidai. Kafin tafiyarsa sai da aka rubutar doguwar wasiƙa aka tura Ɗan aike zuwa Masarautar Adamawa domin sanar da su halin da ake ciki.


Sarki Aminullah sai da ya haɗawa Sarki Muhammad Safyan sha tara ta arziƙi, lokaci ɗaya kunya ta kamasu domin dukkansu sun aikata abubuwa na ɓacin rai a lokacin da suke kan matsananciyar gabar da take tsakaninsu. Gabar ta samo a sani ne bayan shekaru sakamakon wani farmaki da aka kai wa Masarautar Zazzau wacce a ka yi kashe da jikkada ɗunbin mutane, da sunan Masarautar Kano. Babu ƙwaƙƙwaran bincike Masarautar Zazzau suka mayar da martani nan fa faɗa ya ci gaba da wakana a tsakani har sai da Sarkin Musulmai na na takwas Sultan Muhammad Abu Ubaid daga Sokoto ya sasanta su tukunna. Dukada haka Masarautun ba wata jituwa suke ba sakamakon kowannensu an kashe musu wani sashen na daga danginsu.


Sarkin Zazzau a wannan faɗan aka kashe masa Mahaifinsa Murabus ya yi aka naɗa Sarki Muhammad Safyan da Yayyansa mata biyu. Sarki Aminullah a wannan lokacin ne ya rasa babban Amininsa da Ƙannen Mahaifinsa biyu. Wannan rashin ba ƙaramin taɓa zuƙatan Sarakunan biyu ya yi ba. Daga ƙarshe Sarki Aminullah ya sauko har ya fauwwalawa Allah lamauransa ya watsar da dukkan makaman yaƙinsa.


A wata ziyara da Sarki Aminullah ya kaiwa Sarkin Zazzau har lokacin bai wani tarbe shi da ƙima ba hakan ba ƙaramin ɓata ran Sarki Aminullah ya yi ba, a lokacin da zai yi masa sallama ya dube shi ya saki murmushin takaici yace, "Wannan gabar ta mu na tabbata watarana sai ta koma alkairi da ikon Allah sai mun haɗa zuri'a da kai domin Allah ya dubi zuciyata da ƙudurina." A hassalle Sarki Muhammad Safyan yace, "Allah ya tsare ni da haɗa zuri'a da kai idan ka ga haka ta faru sai dai idan bana numfashi, ko bana bumfashi duk wanda ya aurawa Ɗana ko Ƴata ahalinka sai mun yi shari'a da shi ranar gobe ƙiyama don ba da yawuna ba." Tun ranar da suka yi wannan rabuwar babu wani abu da ya sake haɗa su har aka shafe shekara sama da Ashirin, duk wani taro da zai haɗa su kowanne yana bakin ƙoƙari wurin ganin bai hallata ba ko ya saɓa lokaci don kar ya haɗu da abokin hamayyarsa.


Wannan dalilin ya sa lokacin da Sarki Aminullah ya yi masa rakiya da Sarkin Zazzau ya nemi yafiyarsa gabaɗaya kunya ta kamata su. A ɓangaren Maryo kuwa tun da Inna Habi ta sanar mata da maganar tariyarta ban da kuka babu abin da take yi, lokaci ɗaya zazzaɓi ya rufe ta ruf ban da rawar ɗari babu abin da take yi.


Lokacin da Sarkin Zazzau ya koma Masarautarsu da Farko ya so sanarwa da Mahaifiyar Maryo abin da yake faruwa, amma gudun kar ya tayar mata da hankali ya sa ya kwaɓi Yarima akan kar ya sanar mata har sai zuwa sati biyu masu zuwa wato ranar da za a kai su Maryo Masarautar da ƴar uwarta. Kamar tana da masaniya akan tafiyarsu haka Fulani Badawiyya ta yi ta tambayar Takawa abin da suka tattauna a Masarautar Kano amma fir ya ƙi sanar da ita.


Mutumin da Yarima ya kama ya je kashe Abu ba ƙaramin duka ya ci ba, tun ana tambayarsa yana iya magana har sai da ta kai ga da ƙyar yake iya amsawa. Yarima ya yi wannan dabarar ne don ya kama Fulani Maimuna hannu bibbiyu domin ya jima yana zarginta akan miyagun abubuwa da dama, ya san wacece ita don haka ya san hujjar Abu kaɗai ba za ta fitar da shi ba. Lokacin da Mutumin ya ga mutuwa ido biyu nan take ya zayyana musu wacce ta tura shi da ƙwangilolin da take ba shi a baya har zuwa wannan lokacin da asirinsa ya tonu.


Masarautar Kano


Kimanin ƙarfe Takwas na dare Sarki Aminullah ya bada umarni aka ɗauki Amarya Maryo zuwa ɗakin mijinta Ango Saif, ba ƙarmin kuka Maryo ta sha ba haka Inna Habi tun tana dakewa har ta gagara ta fashe da matsanancin kuka, yanda take jin Maryo a zuciyarta tamkar ƴarta ta cikinta. Abu ce ta rinƙa lallashinta sannan ta yi shiru, ita ma ta wuce a ka kai Maryo da ita sai dai ba sashen da Saif ya zauna da Abu aka kai Maryo ba. Wani sashen daban Sarki Aminullah ya sa ka gyara mata tare da zuba mata dukiya tamkar ƴarsa ta cikinsa.

Lokacin da aka kai Maryo wani irin abu ne ya tokare zuciyar Abu a hankali ta rinƙa furta, "Innalillahi'wa'inna'ilahirra'ji'un" Sannan ta ji salama a zuciyarta. Allah ya sani ita kanta ta san har lokacin a kwai ragowar soyayyar Saif a zuciyarta amma alwashi ta ɗaukarta kanta koda soyayyar Saif za ta kashe ta ba za ta sake zaman aure da shi. Jin hawaye na niyyar yin galaba a idanunta ya sa Abu saurin ficewa daga ɗakin ta koma sashensu domin ba ta burin wani ya yi tozali ta fuskarta har wani ya fahimci halin da take ciki.








Saif buri ya ciki 😛 Amarya ta tare ina muku fatan alheri kuma ina neman afuwarku na jina shiru da kuka yi, sakamakon uzururruka da suka hanani typing.


Na ga hirarrakinku wasu da alama sun ɗan tikice na ji suna ba su gane Mahaifin Maryo ba domin sun ji ance Sarki Aminullah Mahaifinta ne kuma aka ce Sarkin zazzau ma Mahaifinta ne.


Idan kun tuna labarin tun a baya boka yace akwai yarinyar da bai san ya take ba mutumce ko aljan sihirinsa ya gagara nuna masa. Amma idan kun tuna yace za ta tashi da ruhi uku ta farko ƴar fararen aljanun ƙarƙashin ƙasa, ta biyu ya Sarkin baƙaƙen doron Ƙasa sai ta ukunsu da za ta zo a wannan zamanin wato Rayzuta. Idan ba ku manta na baku labari lokacin da Maryo take Masarautar Adamawa na Mahaifiyar Muhaibish wacce aka azabtar wacce ta kasance bil'adam to a wancen ƙarnin Wazirin Sarkin Adamawa ko Wambai ne na manta shine mahaifinta. idan ba ku manta ba shi ne har ta yi kashe-kashen nan a zuwan ɗaukan fansa tun da ruhikan azaaluman da suka zalinceta suma sun dawo.


A masarautar Kano kuma Sarki Aminullah shi ne mahaifinta a wancen ƙarnin wanda ta kasance Ƴar Sarkin Baƙaƙen doron ƙasa, Ku fahimta Sarki Aminullah yana ɗauke da siffar Mahaifinta na wancen ƙarnin shi ya sa take yi masa kallon Mahaifinta, kuma abin da ya sa take kallonsa da ruhin Mahaifnta saboda ruhin Aljanu Biyu ne a jikinta. Tun da idan kun lura tana wasu abubuwa irin na jinnu. Sarkin Zazzau kuma shine ainihin Mahaifinta na zahiri wato Maryo wacce Boka ya kira da Rayzuta, to kunga ai ruhi uku kenan ina fatan babu sauran ruɗani amma idan da mai tambaya zai iya yi akan abin da ya shige masa dubu don ko ni labarin ya cakar da ni da yawa.🤣




_LITTAFIN NAN NA KUƊI NE DA NAIRA 200 ZAKI KARANTA SHI CIKIN KWANCIYAR HANKALI, ZAKU BIYA TA WANNAN ACCOUNT ƊIN, FIRST BANK 3090957579 AISHA ADAM, ZA'A TURO DA SHAIDAR BIYA TA WANNAN LAMBAR,0706 206 2624, DAN GIRMAN ALLAH IDAN KINSAN ZAKI FITARMUN DA LITTAFI NA YAFE CINIKINKI._
[11/02, 17:52] Ameera Adam🌚: 74...






A ranar da ka kai Maryo a ranar labarin warin da ke fita daga sashen Fulani Maryama ya riski Sarki Aminullah, da farko Bayinta ya fara tambaya take a ka sanar masa da gabaɗaya sun tafi babu wacce take bata kulawa sakamakon warin ya wuce misali. Da aka tambayi Inna Habi ita cewa ta yi ta shiga da safiyar ranar ta rinƙa buga ƙofar amma da Fulani Maryama ta amsa ƙin buɗewa ta yi sai ma zagin ɗiban albarka da ta rinƙa wurgo mata. A daren ranar aka mayar da Inna Habi da Abu sashen Fulani Zaliha Takawa ya aika Wasu Bayi sashen Fulani Maryama suka yi juyin duniya ta buɗe musu ƙofa ta ƙi. Lokacin da saƙon haka ya isa ga Sarki Aminullah ba ƙaramin fusata ya yi ba don haka yace a rabu da ita zuwa safiya.


Maryo tun da aka kaita ban da kuka babu abin da take yi musamman da ta lura Abu tuni ta yi ficewarta, bayan kowa ya watse Ango shi kaɗai ya shiga ɗakin Amaryarsa bakinsa ɗauke da Sallama. A hankali ta iya amsa masa tana ci gaba da kuka mara sauti, ledojin hannunsa da wani ƙaton akushi ya ajiye a gefe sannan ya zauna a kusa da Maryo ya ɗaga mata mayafin da ke a kanta, yana ƙarewa fuskarta kallo ta kumbura suntum. Abin ka da farar mace tuni fuskarta ta yi Ja sai sauke ajiyar zuciya take.


Farin kyalle ya ciro ya fara goge mata fuska lokaci ɗaya ta ji ƙamshin turarensa ya cika hancinta, lumshe ido ta yi ba tare da ta sani ba har sai ta bashi dariya. Jin shiru ya daina gogewa ya sa ta buɗe ido karaf suka haɗa ido ta ga yanda ya zuba mata idanu. Ba ƙaramin kunya ta ji ba da sauri ta ja mayafinta ta sinne kai ciki tana murmushi.


Janyo ta ya yi yana faɗin, "Kunyar wai ta meye yanzu da kike ji? Ko kin manta lokacin da kike tsayawa kina yi mini tsiwa." Ɗago haɓarta ya yi yace, "Wannan bakin tsiwar ko hmmm" Miƙewa ya yi yace, "Ta so mu yi alwala mu gabatar da Sallah. A kunyace Maryo ta miƙe suka ɗauro alwala sannan suka gabatar da sallar Nafila. Akushin da Mahaifiyarsa ta bashi ya buɗe don shi kansa bai san meye a ciki ba, yana buɗewa ƙamshin farfesun kaji ya ciki ɗakin. Kunce ledar da ya zo da ita ya yi wacce ya siyo gasassun Kaji ya turawa Maryo gabanta yace, "Bismillah" Waro ido waje ta yi sai kuma ta girgiza masa kai. Ɓata fuska ya yi don dama ya san za a rina domin bahaushe yace "Alamar ƙarfi tana ga mai ƙiba" Hannun riga ya tattare ya gutsuro ƙatuwar cinya yace, "Buɗe bakin!"

Da sauri da sunne kai ƙasa ta ce, "A'a zan ci da kaina" Murmushi ya yi yace, "To ko ki ci ko kuma na baki da kaina har sai kin cinye komai na wurin nan." Ganin da gaske yake ya sa Maryo ta zage don dole ta rinƙa ci. Kasancewar wunin ranar bata ci wani abincin kirki ba tun na safe ya sa ta ci farfesun sosai domin ba ƙaramin daɗi ya yi ba, kayan ƙamshi sai tashin ƙamshi suke yi. Sai da Saif ya ga ta ci ta ƙoshi sannan shima ya ɗan ci ba wani na kirki ba, kayan marmari suka sha Maryo ce ta fara ta shi sannan Saif ya ƙarasa.


Bayan ta wanke hannunta can gefen gado ta koma, ta zauna sakamakon dare ya fara tsalawa, tattara kayan ya fara yi Maryo tana jikin gado a hankali bacci ya fara ɗaukanta. Jin baccin na neman cin ƙarfinta ya sa ta haura saman gado ta yi kwanciyarta ta duƙunƙune kamar mage, cikin baccinta ta fara jin Saif na aikamata da saƙonnin da suka girmewa tunaninta, tun tana yunƙurin dakatar da shi har ta haƙura.


Asuba ta gari ban iya ɗiban albarka 🏃🏻‍♀️


Wani irin farinciki ne ya mamaye zuciyarsa har aka yi assalatu Maryo na rungume a jikinsa. Kiran assalatu ne ya tashe shi a hankali ya zame jikinsa ya je tsarkarke jikinsa ya gabatar da alwala sannan ya tashi Maryo, da kansa ya taimaka mata ta gyara jikinta. Ba ƙaramin tausayi ta ba shi ba saboda yanda ya ga yanayinta, tana idar da sallah ta koma ta kwanta bayan ya dawo daga Masallaci ya bi gefenta ya kwanta. Juye-juye yake saboda yanayin da yake ciki amma ganin irin wahallan baccin da take yi, ya sa akan dole ya haƙura, ga jikinta ya ɗauki wani irin za fi da alama zazzaɓi ne ya rufe ta ruf.


Bayan gari ya yi haske

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login