Showing 9001 words to 12000 words out of 89213 words
Chapter 4 - Anya Baiwa Ce 2 Complete Hausa Novel By Aisha Adam.txt
yi ba, har sai da ta ji idanuwanta sun ciko da ƙwalla ta dube shi da kulawa ta ce, "Me ya sa za ka sako mana wannan kalmar bayan muna cikin farinciki." Murmushi ya yi mata yace, "Maryama kenan! Ita mutuwa babu ruwanta da lokacin walwala ko akasin haka. Fata dai Allah ya sa mu yi kyakkyawan ƙarshe." Fulani Maryama ta amsa da, "Ameen" Sannan suka ci gaba da hira.
Bayan lafawar ƙurar sannu a hankali mutane suka fara miƙewaa suna leƙen bakin hanya, gidan ya yi tsit kamar babu kowa a ciki ban da kukan tsuntsaye babu abin da yake tashi a wurin. Sarki Abdallah ne ya tashi wasu Dakaru dan su gano halin da gidan yake ciki. A ɗarare suka dinga fita suna leƙawa dan ganin abin da yake faru, sannu a hankali kowa ya watse sai kuma sautin koke-koke mutane ya fara tashi, saboda wasu an kashe musu iyaye wasu ƴaƴa ye wasu kuma matansu ne. Wannan lamari ba ƙaramin ɗaga hankalin Sarki Abdallah ya yi ba, a inda suka bar shi a zaune a nan ya jima yana nazarin makamar abin da ya dace ya yi. Lokaci-lakaci yake sauke ajiyar zuciya dan gabaɗaya kansa ya ɗau zafi, kamar wanda aka ɗanawa wuta haka ta zabura bai jira fadawansa ba ya wuce cikin gida, kai tsaye ya wuce cen turakarsa ta cikin babban sashe. Maryo na fita daga sashen ta nufi Dajin da yake bangaren wajen bishiyoyi, tana tafe tana jan dokin har suka ɗan yi nisa da jama'a. Kallonsa ta yi tana shafa shi ta ce, "Kudlifa mun gama aikinmu za ka iya tafiya" Juyowa ya yi a raunace ya kalleta, ita ji ta yi babu daɗi ta sauke kanta ƙasa ta ce, "Ba mu rabu ba ta yuwu zamu ƙara haɗuwa amma ko ba komai ya kamata ka ci gaba da bani ƙwarin gwiwa." Kamar mutum haka ya gyaɗa mata kai sannan ya kalleta ya wani irin rangaji da kai, murmushi ta yi masa ta ce, "Na gode da agajin ka mu haɗe wani lokacin." Tana gama faɗa ya zuba a guje cikin dajin be yi tafiya me nisa ba ya ɓace daga wurin. Juyowa ta yi cike da kewarsa sannan ya wuce cen sashen su inda ta bar Maleek yashe cikin wani hali.
Kamar yadda ta fito haka ta koma ta same shi yana kwance kamar gawa, murmushi ta yi ta ɗebo ruwa ta kwara masa a fuska a firgice ya tashi yana nema fita da gudu, da sauri ta buga masa tsawa nan take ya tsaya cak wuri ɗaya yana rawar jiki kamar sabon ɗan bori. Kallonta ya yi ya fashe da kuka yace, "Shukra me ya sa kike son azabartar da ni me na yi miki ne?" Takawa ta yi a hankali zuwa bakin gado ta ɗora kafa ɗaya kan ɗaya yana kallonsa ta ce, "Tun farko na gaya maka ni ba matarka bace." Maleek cikin rawar murya yace, "Wallahi na sani dan na ga alama. To wacece ke." Miƙewa ta yi ta fara takawa har ta je bakin windowa ta ce, "Sunana Maryo ni ba Shukra ba ce hasalima ni ban taɓa aure ba, ruwan ka ne ka yarda ruwan ka ne kaƙi yarda, ni na riga da na ga wuri dan haka ban ga abin da zai fitar da ni daga masarautar nan ba. Ni kaifi ɗaya ce bana magana biyu, kun zaɓi dawo dani masaurautar nan akan barina na yi rayuwa da masoyina, ni kuma naci alwashin ko da a baɗini ne dole zan kasance a masarautar na." Maleek da cikin tashin hankali yace, "Dan Allah kiyi haƙuri wallahi na yi alƙawarin sadaki da masoyinki." Kallonsa ta yi idanunta na cikowa da ƙwalla ta ce, "Babu abin da haƙurin ka zai iya yi mini ka yi sabgar ka na yi tawa domin kai din wani mallakakken sashe ne daga ɓoyayyiyar alaƙarmu."
_LITTAFIN NAN NA KUƊI NE DA NAIRA 200 ZAKI KARANTA SHI CIKIN KWANCIYAR HANKALI, ZAKU BIYA TA WANNAN ACCOUNT ƊIN, FIRST BANK 3090957579 AISHA ADAM, ZA'A TURO DA SHAIDAR BIYA TA WANNAN LAMBAR,0706 206 2624, DAN GIRMAN ALLAH IDAN KINSAN ZAKI FITARMUN DA LITTAFI NA YAFE CINIKINKI._
[04/12/2021, 19:49] Ameera Adam🌚: 41...
Maleek cikin rauni yace, "Wacce irin alaƙa gare mu da kike ta iƙirari alhalin kin ce ke va Shukra bace, ni wallahi babu wata alaƙar da ke tsakaninmu." Murmushi Maryo ta yi ta ce, "Lokaci na nan shi zai bayyana kansa na tabbata sai ka tuno da wannan ranar." Tana gama faɗa ta kwanta kan gado ta juya masa baya zuciyarta na tafarfasa saboda tuno da masoyinta da ta yi. Maleek ficewa ya yi zuciyarsa na rawa dan gabaɗaya ya rasa makama, yana fita saƙon Mai martaba na ƙarasowa wurinsa cikin gaggawa. A gaggauce ya ƙarasa wurin mahaifinsa cikin girmamawa ya gaishe da Mahaifinsa, tun kafin ya ƙarasa Sarki Abdallah ya dakatar da shi da cewa, "Kai Maleek! Wacce irin masifa ka kwaso mana muna zaune ƙalau? Tun da na zo duniya ban taɓa ganin tashin hankalin da na yi tozali da shi ba yau, maza tun wuri ka ɗauki yarinyar cen ka fitar da ita daga cikin gidan nan, dan ni ban taɓa nufar wani da tashin hankali ba ka ga kuwa ina zaman zamana ba za ta ja mini asarar rayuwa a ƙasa ba." Maleek shiru ya yi yana nazari shi kansa lamarin yarinyar ba ƙaramin tsoro ya bashi ba, amma a gefe ɗaya ga abin da ta faɗa masa. Yana tsaka fa tunani Sarki Abdallah ya katse masa tunanin da cewar, "Idan kuma so ya rufe maka ido ba za ka iya aiwatar da abin da na umarce ka ba, ka tattara kayan ka kai da ita ku fice mini da ƙasa dan bana ƙaunar abin da zai azabtar da talakawa na. Ka duba ka gani yau jini nawa aka zubar a gidan nan? Mun yi asarar rayuka sama da ashirin ban da waɗanda suke kwance cikin jinya, dama tun farko sai da na gaya maka ina tsoron aurenka da yarinyar nan tun da babu wanda ya san asalinta, amma ka kawo mana ƙabali da ba'adi ka ga abin da hakan ya haifar." Maleek jiki a sanyaye yace, "Allah ya taimake ka ta ce ita ba Shukra bace, hasalima ta ce mini ko aure bata taɓa yi ba." Sarki Abdallah baƙin ciki ya kama shi, yana ganin kamar Maleek na neman yi masa yawo da hankali, cikin tsawa yace masa, "Ba wannan na tambaye ka ba! Matarka ce ba matarka bace ba ni da matsala, dan haka na baku nan minti goma ko ta fice mini daga gida ko kuma ku fice mini gabaɗaya." Maleek ya marairace murya ya fara zayyanewa Sarki Abdallah yadda suka yi da Maryo, yana ci gaba da hawabi Takawa ya ɗaga masa hannu yana cewa, "Bana buƙatar ƙara jin wara magana daga gare ka, dan haka ku fice mini ko na sa a fitar da ku." Kamar kazar da ƙwai ya fashewa a ciki haka Maleek ya fice daga turakar mahaifinsa ya nufi sashensa gabansa na dukan uku-uku.
"Salman wannan maganar da na kawo maka na san dalilin da ya sa na kawo maka ita, haba ɗan arziƙi karka watsa mini ƙasa a ido mana." Fulani Maryama ta ƙarasa maganar tana fargabar abin da zai gaya mata. Ɗagowa ya yi ya kalle yana cije baki yace, "Wai kina cikin hankalinki kuwa da zaki ce na nemi wata matar na aura? Kin san dai ni Maryo ce zaɓina." Fulani Maryama yanyo shi ta yi tana masa raɗa a kunne ɗagowa ya yi da Kansa ya cikin farinciki yace, "Lallai matar nan kanki yana wuta ya zama dole na nemo aure ko da acikin ƴan shilolin cen ne, shima wancen kwantaccen dole na hura wuta a ɗaure shi da wata."
FATAN ALHERI🥰🥰
_LITTAFIN NAN NA KUƊI NE DA NAIRA 200 ZAKI KARANTA SHI CIKIN KWANCIYAR HANKALI, ZAKU BIYA TA WANNAN ACCOUNT ƊIN, FIRST BANK 3090957579 AISHA ADAM, ZA'A TURO DA SHAIDAR BIYA TA WANNAN LAMBAR,0706 206 2624, DAN GIRMAN ALLAH IDAN KINSAN ZAKI FITARMUN DA LITTAFI NA YAFE CINIKINKI._
[05/12/2021, 18:08] Ameera Adam🌚: 42...
Wani yalwataccen murmushi Fulani Maryama ta yi tana kallon Salman har ta bayyana farincikinta a fili, saboda ko kaɗan bata taɓa tsammanin zai amince da buƙatarta cikin sauƙi ba, amma da ta tuna irin huɗubar da tayi masa sai ta ji tabbas dole ma ya amince, yana daga tsaye ya kalleta yace, "To wai ma ni wacce tsabar za a nema mini ne? Gaskiya ya kamata a nema mini auren ƴar babban gida dukda ba ita bace muradina ba." Fulani Maryama ta miƙe tsaye ta dafa shi tana cewa, "Wannan ba damuwa bace, zan yi wa Mai martaba magana ya nema maka a cikin ƴaƴan abokanansa, amma na fi son ya nema maka ƴar Sarkin Masarautar Gumel dam suna ɗauke da ɓoyayyar dukiya ne yawa ka san fa Mahaifinta ita kaɗai ya mallaka." Cikin rashin ladabi da ɗa'a yace, "Ke wannan ya dama dan da alama ke zalamammiya ce, ni mulki da mallakar Rayzuta ne a gabana. Wai wancen tsohon yaishe zai matsa ya bani wurina? Gaskiya idan na yi a aure a satin na biyu ko da tsiya dole na haye karagar mulki, ko lokacin tafiyarsa ya yi ko ma be yi ba dole na ƙara masa burki..." Da sauri Fulani Maryama ta rufe masa baki tun bai ƙarasa faɗar abin da yake furtawa ba a firgice ta ce, "Kai Salman me kake faɗa haka?" Takawa ya yi har ya je bakin ƙofa be tanka masa ba, ya juyo yace, "Ba zan iya zama na jira har sai ya mutu ba, zan datse numfashinsa ko na samu na haye mazaunina" Jikin Fulani Maryama har rawa yake ta ce, "Ka daina faɗin irin haka Salma. Ba na san mutane su dasa zargi a kanka dan Allah." Cikin halin ko inkula ya ɗaga kafaɗa yace, "Be dame ni ba ko kaɗan amma wallahi kinji na rantse miki muddin na yi aure ba zan rufa makwanni uku ban ɗare karagar mulki ba." Yana gama faɗa ya fice daga ɗakin. Wani irin gumi ne ya shiga ketowa Fulani Maryama dan har ga Allah tana matuƙar ƙaunar Takawa, soyayyarsa ce ma ta sa take bin bokaye dan ganin ta mallake shi ita kaɗai. Jiki a sanyaye kamar wacce aka zare wa laka haka Fulani Maryama ta zauna daɓas, bata damu da irin zafin da ta ji ba. Wani nazari ta yi sai kuma ta saki murmushi tana cewa a fili, "Dole na na karkatar da hankalinsa Salman, yaro man kaza." Daga cen bakin ƙofa ta ji sallamar Inna Habi, sai da ta mula ta mule sannan ta amsa mata a daƙile kamar me ciwon maƙogaro. Sai da ya shafe sama da minto biyar bata bawa Inna Habi umarnin shiga ba sannan ta ce, "Kya iya shigowa kin yi mini sandandan a tsaye kamar gungumen icce, uwar me kika zo yi mini yanzu?" Hawaye ne ɗigowa Inna Habi da sauri ta goge ta shiga cikin girmamawa ta russuna tana faɗin, "Allah ya taimake ki dama zuwa na yi na ji ko zan yi miki matsar ƙafar, saboda rannan na ji kin ce bakya buƙatar ɓata lokaci."Shiru ne ya biyo baya ba tare da ta tanka mata ba ta bi ta da wani wulaƙantaccen kallo ta ce, "Amma dai yau ba ki yi wanka ba ko? Daga shigowar ki tsami duk ya cika mini ɗaki." A raunane Inna Habi ta ce, "Allah ya taimake ki wallahi na yi wanka." Wurga mata harara ta yi ta ce, "Au ƙarya nake yi miki kenan? Tashi ki fice miki daga ɗaki kar ki kumburar mini da ciki maza fita sai na neme ki." Haka Inna Habi ta fita tana shayar ƙwalla saboda takaici har ta ƙarasa ɗakinta.
Maleek na gabda ƙarasawa sashensu ta hango Maryo ta fito fuskarta ba yabo babu fallasa, tana tafe tana motsa ƴan yatsu kamar me lissafi. Ɗaga hannu ya yi kamar zai yi mata magana amma gabaɗaya tsoro ya hana shi furta ko da kalma ɗaya ce, Yana kallonta har ta nufi sashen Mahaifiyarsa. Gabansa ne ya yi mummunan faɗuwa jikinsa har rawa yake be san lokacin da ya bita a guje ba, don yana tsoron abin da za ta aiwatar a cen ba. Duk yadda yake sauri amma be cimmata ba kafin yaje tuni ta daɗe da shiga, tana shiga kai tsaye ta nufi ɗakin da aka rufe Fulani Babba. Da ƙafa ta hankaɗa ƙofar nan take ƙofar ta buɗe fuska a ɗaure ta damƙi hannun Fulani babba ta fisgota da ƙarfi suka fito daga ɗakin, Maleek na tsaye da sauri ya bi bayansu yana tambayarta amma ko waiwayonsa ba ta yi ba bare ya sa ran zata amsa masa. Fulani Babban ta fara cewa, "Don Allah ki..." Kallon da Maryo ta yi mata ne yasa ta ja bakinta ta rufe, tana tafiya kai tsaye ta wuce cen ɗakin da aka ajiye Me Babban ɗaki.
Barka da hutun ƙarshen mako🥰
_LITTAFIN NAN NA KUƊI NE DA NAIRA 200 ZAKI KARANTA SHI CIKIN KWANCIYAR HANKALI, ZAKU BIYA TA WANNAN ACCOUNT ƊIN, FIRST BANK 3090957579 AISHA ADAM, ZA'A TURO DA SHAIDAR BIYA TA WANNAN LAMBAR,0706 206 2624, DAN GIRMAN ALLAH IDAN KINSAN ZAKI FITARMUN DA LITTAFI NA YAFE CINIKINKI._
[06/12/2021, 19:46] Ameera Adam🌚: 43...
Lokacin da suka isa ɗakin Me babban ɗaki tana kwance da alama hutun gajiya take fanshewa wanda ta manta rabonta da runtsawa a lallausan makwanci irin wannan. Maryo na shiga ta durƙusa gaban Me babban ɗaki ta ce, "Babah ta so muje fadar Sarki." Ba musu Me babban ɗaki ta miƙe ta bi Maryo na gaba riƙe da hannun Fulani Babba, Me babban ɗaki na biye da ita kamar jela. Lokacin da suka ƙarasa fadar babu kowa a ciki sai Dogarawan bakin ƙofa, lokacin da Maryo ta je shiga babu wanda ya yi gigin hanata shiga, sai ma ja da baya da suka yi a ruɗe saboda kowa shakkar Maryo yake. Sai da ta ƙarasa ta zaunar da Me babban ɗaki sannan ta juyo bakin ƙofar ta kalli wani Dogari fuska a haɗe ta ce, "Maza ka je ka kira mini Sarki Abdallah." A firgice ya kalle ta yace, "Shi Ranka shi daɗe ɗin za a kira miki?" Tsawa ta buga masa ta ci gaba da cewa, "Kace masa ya zo yanzu idan ba haka ba abin da ya faru ɗazu zai ƙara faruwa har na yanzu ya fi na ɗazu muni." Jiki na rawa Dogarin ya wuce cen sashen Sarki Abdallah." Yana zuwa ya ne mi iso da ƙyar ya samu aka barshi ya shiga sakamakon idan yana sashen iyalinsa ba a cika neman iso ba, sai da ya sanar da su abin da yake tafe da shi sannan suka bari ya shiga. Yana shiga ya fara inda-inda, ganin haka yasa Sarki Abdallah ya buga masa tsawa bakin sa na karkawa ya fara magana sai kuma wayar Sarki Abdallah ta fara ruri. Shiru ya yi har Takawa ya ɗauka bakinsa ɗauke da sallama, murmushin ƙarfin hali ya aro ya yafa a saman fuskarsa bayan sun gaisa Sarki Abdallah yace, "Siriki ina niyyar kiranka ka riga ni." Daga cen ɓangaren Sarki Aminullah ya yi dariya yace, "Na ji a jikina ai Siriki da fatan duk kuna lafiya?" Sarki Abdallah kamar wanda aka soso masa inda yake masa ƙaiƙayi har ya manta da Dogarinsa da ke tsugunne yace, "Ehto Siriki lafiyar fa da sauƙi." Gaban Sarki Aminullah ne ya faɗi a ɗan razane yace, "Ko shi yasa na kira Fahima ban same ta ba?" Sarki Abdallah ya sauke gwauruwar ajiyar zuciya yace, "Ko kana da labarin Me babban ɗaki ta dawo?" Sarki Aminullah yace, "Kamar ya Me Babaan ɗaki ta dawo kamar wacce ta yi tafiya? Siriki wannan wacce irin magana ce? Dama wanda ya mutu yana dawowa ne?" Nan take Sarki Abdallah ya zayyane masa duk abin da yake faruwa yana gabda ƙarƙare maganar, Maryo ta ban ko ƙofar ta yi tsaye a kansa tana faɗin, "Sarki Abdallah na aiko kiran ka na ji shiru ka wuce muje ina da magana me muhimmanci." Shiru ya yi yana kallonta ya ga babu alamun tsoro a tattare da ita, tarin da Sarki Aminullah ya yi ne yasa shi tunawa da wayar da ke kare a kunnensa. Gyaran murya ya yi yace, "Sirikina ina fatan ka ji muryar yarinyar da take magana?" Sarki Aminullah da mamaki ya gama cika shi murya a sanyaye yace, "Wai me yake faruwa ne?" Sarki Abdallah da ya gama ƙagauta yace, "Ina na sani. Maganar gaskiya yarinyar nan dole ta bar mana masarautar nan wallahi, ba zan iya ba yau Allah ne kaɗai yasan adadin rayukan da muka yi asara. Ina dalili shi kansa Maleek ɗin na gaya masa idan ba zai iya sallamarta ba ya bi ta su tafi cen, amma nidai su bar mini ƙasata ta zauna lafiya tare da talakawa ba tare da wata tarzoma ba babu gaira babu dalili." Sarki Aminullah shiru ya yi don har ga Allah shi ba sauraron sauran jawabin Sirikin nasa yake ba, fargabarsa ɗaya idan ta dawo tashi masarauta wanne irin tashin hankalin za su shiga. Yana tsaka da tunani ya ji Sarki Abdallah yace, "Ina matsanancin tausayin talakawa na saboda ba su ji ba basu gani ba babu yadda za a yi a dinga salwantar da rayuwarsu suna mutuwar wulaƙanci." Sarki Aminullah ya haɗiyi yawu da ƙyar yace, "To Allah ya rufa asiri." Daga haka suka yi sallama ya mayar da kallonsa ga Maryo da take tsaye fuska a murtuke babu walwala.
Cikin izza da isa irin ta tsatson jinin sarauta ya kalleta ya saki murmushi yace, "Zan bi ki ne kawai saboda ina gudun zalincin da zaki aiwatarwa talakawa na, ko kaza bana fatan ƙara rashinta bare bil Adam." Yana gana faɗa ya miƙe tsaye yana gyara zaman rawaninsa sannan ya wuce, da sauri Maryo ta yi gaba fuuuuu har mamakin saurinta suke yi saboda wata irin tafiya take yi kamar za ta