Showing 42001 words to 45000 words out of 89213 words

Chapter 15 - Anya Baiwa Ce 2 Complete Hausa Novel By Aisha Adam.txt

30 Nov 2024

5355

Na hallaka mijinta wato Mahaifina sannan na haike mata a wannan tarraya ta mu da ita ta samu cikinka. Ka san dalilina na yin haka?" Zulik ya dube shi da kallon tsana ya girgiza masa kai sannan Bulbutu ya ci gaba da cewa, "Laƙani aka bani na yi amfani da shi domin kasancewata Sarkin gobe a wannan masarautar. Boka na ya sanar da ni cewar matsawar na yi tarayya da Mahaifiyata za ta haifi wanda zai auri ƴar Sarki Kisumul Birmi, amma indai ban yi tarayya da ita ba har abada ni da Saruta. Bincikensa ya nuna idan muka bi da dabaru tabbas za ka aureta kuma kana aurenta Mahaifinta zai baka Sarautar ka ga sai yadda muka yi da su. Sai dai ya sanar da ni wannan yaro Ɗan wurin Waziri zai kawo maka cikas, don haka ba da gaggawa za mu bi lamarin ba. Ka yi ƙoƙari ka daina nuna jin zafinka akan Furzaan za ka ga ta fara sauraronka, kuma a yadda na lura yarinyar tana da sha'awar harbe-harbe. Don haka zan turaka horon harbi na kwari da baka in ya so idan ka dawo sai mu yaudari Sarki akan za ka dinga koya mata Harbi, a wannan lokacin za ka cusa mata soyayyarka. Kaga kana aurenta ka zama Sarki me mulkar wannan Nahiyar ta Daulatul Jinnul Sahara." Duk yadda Zulik ya kai ga jin haushin Mahaifinsa sai ya ji zuciyarsa fes baƙin cikin da ke ciki ya yaye. Kallon Mahaifin nasa ya yi yace, "A farkon labarin ji nake zuciyata na tafasa kamar na datse numfashinka, amma daga ƙarshen labarin na hango nasara da cimma buri a ciki." Daɗi Bulbutu ya ji a ranar ya shiryawa Zulik tafiya ba tare da kowa ya sani ba, ya aikata cen Nahiyar Baƙaƙe Aljanin ƙarƙashin ƙasa. (JINNUL TARABIY) Domin amsar horon Harbi yadda ya kamata.




Duk yadda Maryo ta so a raka gidan Abu Inna Habi ta ƙi yadda, a gefe ɗaya kuma tana fargabar rikicin da ka je ya zo. Suna zaune su biyu a ɗaki Inna Habi ta dubi Maryo tana cewa, "Maryo babu abin da za mu ce da Allah sai godiya. Cikin ikon Allah kina gani lokaci ɗaya idanunki da kunnuwanki sun buɗe, an ya lamarin nan babu sihiri a ciki kuwa. Ni fa ina ji a jikina tabbas akwai wani ɓoyayyen al'amari a ƙasa, amma meye haɗinki da Ɗan wurin Fulani Maryama? Sannan kuma me ya sa kika sakewa Namiji har yake iya rungumarki ke ba matarsa ba? Maryo na yi mamakin ganin haka saboda sam ban yi muku tarbiyyar son zuciya ba. Me kike tunani ga duk namiji da ya samu damar taɓa wani sashe na jikinki? Kina tsammanin zai aure ki ne?" Maryo jikinta ne ya yi sanyi ta kalli Inna Habi tana ƙarajin ƙaunar tsohuwar a zuciyarta tana faɗin, "Inna wallahi babu wani abu da yake tsakanina da Ɗanta, shi kuma Saif ba tun yanzu ba na gaya miki saurayina ne. Amma wallahi Inna ina ji a jikina shi ɗin kamar wani tsagina daga ɓangaren jikina, jikina na rayawa mini wasu al'amura musu muhimmanci dangane da rayuwata. Ciwon nan kuma yana daga Ubangiji Inna kar mu saka zargin kowa a zuciyarmu don kar a zoɓe ladan kankarar zununbin dana samu. Game da rungume ni da Saif ya yi na yi kuskure Inna amma duk hukuncin da ya dace za ki iya aiwatarwa a gare ni, na yi miki alƙwari In sha Allah hakan ba za ta sake faruwa a tsakaninmu ba. Amma wallahi ki yadda da ni Inna babu wani abu da ya taɓa haɗa ni da shi wannan ma kuskure ne." Maryo akwai iya falsafar zancen da sauke magana a inda ta dace, idan tana tsara maka magana za ka rantse da Allah wata babbar macece take yi maka magana. Inna Habi ce take mamakin yadda lokaci ɗaya kunyar Maryo ta yaye akan wannan Ɗan Sarki Saif, jiki a sanyaye ta dubi Maryo ta ce, "To ya kamata a kiyaye gaba saboda hakan baya daga tafarkin tsarin addinin musulunci." Maryo ta amsa mata cikin girmamawa, Inna Habi da har za ta tambayi Maryo game da cikin da take iƙirarin na Saif ne sai dai kuma ta fasa.


Sannu a hankali tun Bayin sashen Fulani Maryama ba su san da warkewar Maryo ba, har suka hankalta. Wasu daga cikinsu sun ta ya ta murna ya yinda wasu kuma suke tsoron magana kasancewar sun fahimci Fulani Maryama ta kafa musu ƙahon zuƙa, ko gani ta yi kanfiye mu'amala da Inna Habi sai ta kira ka ta yanka maka kashedi. Lokacin da Fulani Maryama ta samu labarin faruwar wannan lamarin ba ƙaramin tashin hankali ta shiga ba, duk yadda ta so ganin Jakadiya a ranar abin ya faskara don Jakadiya na kwance maruru ya fito mata a hammata, tana kwance tana fama da hannu a sama don ko sauke shi ƙasa bata iya yi, saboda azabar da yake yi mata.


Lokacin da Saif ya koma gida Abu na zaune a kan gado ta jingina da fuskar gado da alama baccin ɗaukarta ya yi ba tare da ta sani ba, Saif na shiga ya hangi Baiwa Sahura tana surfe. Ƙare mata kallo ya yi har sai da ta tsargu take ganin kamar ya lura da ta zuba wani abu a ƙofar ɗakin matarsa. Amma sai ta hau muzurai tana faɗin, "Barka da shigowa Ranka shi daɗe." A taƙaice yace, "Barka!" Har ya wuce gaba ya juyo ya sake kallonta yana bin hannuwanta da kallo, wannan karon tsoronta ya bayyana a fili sai ya wuce cikin gida. Tun daga bakin ƙofar ɗakin ya fara bin hallitun da yake gani a fili, kansa ne ya sara masa lokaci ɗaya idanunsa suka rune jawur ya kalle su fuska babu wallahi yana faɗin, "Maza ku koma wurin da aka turo ku muddin kuka saɓa mini wallahi babu wanda zai tsira daga gare ni. Saƙo na baku duk wanda ya ƙara gigin taɓa mini gudan jinina tabbas uwarsa sai dai ta haifi wani." Tun be rufe baki ba ɗaya bayan ɗaya suka fata ɓacewa, Baiwa Sahura da take gefe tana kallonsa yana ta surutai cikin zuciyarta take ayyana ko dai wani zancen zucin yake yi har ya fara fitowa fili. Fuska a tamke ya juyo gare ta jikinta har tsuma yake amma ga mamakinta sa ta ga ya nuna ta da Ɗan yatsa ya bushe da dariya, sai da ya yi me isarsa sannan yace, "Wannan ya zama na farko kuma na ƙarshe da za a baki mugun abu domin salwantar da abin da yake cikin Matata, idan ba haka ba wallahi zan baki mamaki. Kuma karna ƙara ganin ƙafarki a sashen nan." Baiwa Sahura ban da gyaɗa kai babu abin da take yi jikinta har rawa yake ta ci gaba da abin da take yi, Saif ya faɗa ɗaki ya kwanta a kan gado ya tsunduma kogin tunanin rayuwar abin da yake faruwa da shi. Sai a wannan lokacin ya tuna cewar Maryo ƴar Uwar Abu ce ji ya yi kansa ya yi wani iri. Ɗagowa ya yi ya ga yadda take bacci a wahalce, ta shi ya yi ya ƙarasa yana gyara mata kwanciya cikin tausayawa domin kwana biui kawai duk ta zabge ta rame.


Bayan kwana biyu da warkewar Maryo ta gama tabbatarwa kanta dai suna zaune ne a sashen Fulani Maryama, ko kaɗan ba ta so hakan ba saboda gabaɗaya ta tsani matar don tun da take bata taɓa jin wani mutum da ta tsane shi farat ɗaya ba kamar Fulani maryama. Kamar kullin yauma ta saka Inna Habi da magiyar zuwa gidan Abu amma sai hanya-hanya Inna Habi take yi mata, babu yadda ta iya haka ta haƙura. Misalin sha biyun rana Inna Habi ta kwanta tana jan carbi har bacci ya yi awon gaba da ita. Hamdala Maryo ta yi don haka ta ja ɗauko mayafinta a hankali ta fito harabar gidan. Baiwa Sahura ta ga ni da sauri ta ƙarasa wurinta tana ƙasa-ƙasa da murya ta ce, "Sahura don Allah ina ne gidan Yayata Abu ki raka ni?" Sahura ta gwalo ido waje saboda kashedin da Saif ya yi mata, ganin haka ya sa Maryo ta ce, "Lafiya Sahura?" Sahura ta wanyance da cewa, "Fulani Maryama ce ta sani aiki sai dai in nuna miki gidan ba zan shiga ciki ba kar na daɗe na yi laifi a wurinta." Hannu bibbiyu Maryo ta sa ta riƙo hannun Sahura ta ce, "Na gode Sahura Mu je."


Sahura tana gaba Maryo na biye da ita har suka ƙarasa ƙofar gidan su Abu, daga bakin ƙofa ta tsaya Maryo ta shiga tana rafka sallama. Tana shiga tsakar gidan haka kawai ta ji gabanta na faɗuwa amma sai ta yi tsammanin ko dan ta kwana biyu ba ta yi tozali da ƴar uwar tata bane. Bayin Abu ne suka amsa mata nan take tambayarsu Abu suka nuna mata ɗaki kasancewar duk sun san Maryo ƴar uwar Abu ce ya sa basu tsaya yi mata iso ba. Maryo sai da ta yi sallama a bakin ƙofa sannan ta ji Abu ta amsa mata sama-sama, ɗaga labulen ta yi ta shiga a zaune ta hangi Abu akan filo da turtsetsen cikinta. Jin yadda Abu ta amsa mata ya sa Maryo ta ɗauka ko don bata gane ta ba, amma lokacin da ta shiga da murnar ta ƙarasa gaban ƴar uwarta tana faɗin, "Abu kece haka yeeehh na kusa Ɗaukan Ɗana na kaina." Maryo har da ɗan tsallenta kamar wata ƙaramar yarinya, Abu dukda tana jin haushin Maryo a ƙasan zuciyarta ba ƙaramin daɗin ganin Maryo ta ji ba, sai dai kishin mijinta da take ji akan Maryo ya hanata amsarta hannu bibbiyu. Ɗauke kai gefe ta yi ta ce, "Maryo ke ce?" Maryo zama ta yi a sanyaye tana mamakin sauyin halin ƴar Uwarta don ta yi tunanin za ta yi farinciki da ganinta, basarwa Maryo ta yi ta ce, "Abu ya jikin ya Yayan namu?" Ras gaban Abu ya buga wani haushi ya sake turniƙe ta, sai da ta furzar da iska me zafi ta ce, "Duk muna lafiya." Maryo ta jinjina kai da yanayin mamaki ta ce, "Abu hala cikin nan yana takura miki ko bakya jin daɗi ne?" Abu ta watsawa Maryo wani Kallo tana shafa cikin jikinta ta ce, "Cikin da Masoyina ya yi mini har zan ce yana takura mini, sai kace wacce aka yi wa dole." Wannan karon mamakin Maryo be ɓoyi ba a hankali ta miƙe jiki ba ƙwari ta ce, "Abu ni bari na wuce gida Inna ba ta san na fito ba." Abu tana daga zaune ta ce, "Ki gaishe su." Maryo ta amsa tana ɗaga labulen za ta fita suka kusa gware da Saif hannunsa ɗauke da ledar kwakwar manjar da Abu ta ce masa tana buƙata, be lura da ita ba saboda da sauri Maryo ta yi baya tana faɗin, "Subhanallah ashe da mutum a hanya." Muryarta ce ta karaɗe dodon kunnensa da sauri ya saki ledar hannunsa bakinsa na rawa yace, "Ke... ke ce?" Mamakinta ƙarara ya bayyana ta ce, "Me ka zo yi gidan Abu." Abu da ke cen gefe ta yunƙura da ƙyar ta miƙe tsaye ta ce, "Kamar ya me ya zo yi mutum da gidansa, Maryo ko baki san Wannan ne Mijina ba." A hargitse Saif ya buga mata tsawa yana faɗin, "Lafiyarki Abu?" Kafin Abu ta yi wani yunƙuri Maryo da take jin jiri-jiri na nema ɗibanta ta ce, "Wai abin da ta faɗa haka ne kaine Mijinta?" Saif ya sunkuyar da kai ƙasa Abu da gayya ta ce, "Maryo na taɓa yi miki irim wannan wasan ne, idan ba ni ce matarsa ba kin san dai babu yadda za a yi Namiji kamarsa ya shigo mini ɗaki." A hankali Maryo ta fara jan kafarta ba tare ta lura da inda take jefa ta ba ta fita, da sauri Saif ya sha gabanta yana faɗin, "Don Allah ki tsaya ki ji yadda lamarin ya kasance wallahi..." Hannu ta ɗaga masa tana dubansa da rinannun idanunta ta sai kuma ta saki murmushin yaƙe da ya fi kuka ciwo ta ce, "Ba sai ka ce mini komai ba, don Allah ka bani hanya na wuce saboda ina yi maka kallon Yayana ba zan iya yi maka ranshin kunya ba kamar yadda bana taɓa yi wa Adda Abu." Tana kaiwa nan ta fice daga ɗakin tana tafe wani abu na dunƙule a zuciyarta hatta ƙafarta bata san inda take jefa ta ba.




Yau na san Abu ta shiga uku🥺🥺




_LITTAFIN NAN NA KUƊI NE DA NAIRA 200 ZAKI KARANTA SHI CIKIN KWANCIYAR HANKALI, ZAKU BIYA TA WANNAN ACCOUNT ƊIN, FIRST BANK 3090957579 AISHA ADAM, ZA'A TURO DA SHAIDAR BIYA TA WANNAN LAMBAR,0706 206 2624, DAN GIRMAN ALLAH IDAN KINSAN ZAKI FITARMUN DA LITTAFI NA YAFE CINIKINKI._
[07/01, 19:39] Ameera Adam🌚: 58...



Lokacin da ta koma Inna Habi bacci take hankali kwance bata tashi ba, Maryo na shiga ta zube a ƙasa tana sakin kuka me tsuma zuciya. Sama-sama Inna Habi ta fara jiyo kukan Maryo a firgice ta tashi tana tambayarta abin da yake faruwa, Maryo ban da kuka babu abin da take yi hatta magana ta kasa iya furtawa. Inna Habi jikinta na rawa ta miƙe ta fita daga ɗakin tana dube-dube sai dai tsakar gidan shiru ma yake babu Bayin da ta bari suna aiki kafin ta kwanta bacci. Komawa ta yi ta zauna ta zubawa Maryo idanu don bata san me za ta yi ba, tun da ta yi mata tambayar duniya amma amsa ɗaya ce kukan da take rusawa. Sai da ta ci kuka ta gode Allah fuskarta jawur sannan Inna Habi ta sake tambayarta tana ƙasa da murya kamar me raɗa, "Maryo me aka yi miki? Ko yaron nan Ɗan wurin Maryama ne ya yi miki wani abu?" Maryo girgiza mata kai ta yi ta ce, "A'a ba shi bane." Kanta ne ya ci gaba da sara mata saboda tsananin ciwon kai ko idanunta bata iya ɗagawa, a hankali jini ya fara ɗiga daga hancinta tana shirin gogewa Inna Habi ta ruƙota cikin tashin hankali tana faɗin, "Me aka yi miki Maryo haka da har yake neman tayar miki da ciwonki?" Sai a lokacin Maryo ta iya faɗawa jikin Inna Habi ta fashe da wani irin kuka me tsuma zuciya. Inna Habi jin kukan Maryo take har cikin ranta tana ayyana wannan karan ta kai maƙurar tiƙiwa, ba Salman ba ko Fulani Maryama ce ba za ta iya ci gaba da ɗauka ba.


Bayan fitar Maryo a hassale Saif ya ƙarasa wurin Abu ya fisgota da iya ƙarfinsa, gani ya yi ta kafe shi da idanu sai kuma ta bushe da wata irin dariya. Sunkuyar da kai ƙasa ya yi saboda baƙin ciki ya rasa wanne irin hukunci zai yi mata. Be ƙarasa tunanin da yake yi ba ya riski muryar da bata zame masa baƙuwa ba a cikin dodon kunnensa ana faɗin, "Wannan shi ne karonmu na farko da kai a taƙaice za mu iya kiran wannan da wasa farin girki." Yana gama maganar Abu ta sulale ta faɗi ta rubda ciki. A zabure Saif ya yi kanta yana kiransa sunanta, daga saman kansa ya sake jin bushewa da dariya yana ana faɗin, "Wannan karon za ka tashi biyu babu." Be saurara masa ba ya fara jijjiga Abu da lokacin tuni jini ya fara zuba daga jikinta. Ganin wannan ba zai kai shi ba ya sa shi fita da sauri gudu-gudu, kai tsaye ya wuce sashen Mahaifiyarsa. Da gudu ya faɗa ɗakinsa yana ƙwala mata kira, kai da ka ji irin kiran da yake yi mata za ka tabbatar ba na lafiya bane, kamar yadda sauran Bayi suka riski shigowarsa cikin tashin hankali." Hankali tashe Fulani Zaliha ta tare shi tana tambayarsa, ban da haki babu abin da yake saukewa yana faɗin, "Abu ce ta faɗi har ta fara zubar da jini." Ba ƙaramin tashin hankali Fulani Zaliha ta shiga ba da sauri ta aika aka kira mata Uwar Bayi da Uwar tuwo. Lokacin da suka ƙarasa gidan Abu ta fara fita daga hayyacinta, Saif sai kaiwa da kawowa yake yi yana nazarin irin hukuncin da ya dace ya ɗauka akan Salman. Kafin wani lokacin tuni unguwar zoman da aka kira ta ƙarasa ta fara duba Abu sannan ta jiƙa magani da turare aka bata na sha da shafawa sannan ka turara turare. Jikinsa ne ya bashi akwai abin da yake faruwa a ɗaki wurin da Abu take kwance yana shiga akin Uwar Bayi ta miƙe zumbur tana faɗin, "Ranka shi daɗe wannan ciwon mata ne ka fita duk abin da ya dace za mu yi..." Tun bata rufe baki ba ya ɗaga hannu ya maka mata a fuska Unguwar zoma na ganin haka jikinta ya fara karkarwa tun bata gama haɗa kayan magungunanta ta ɗauki jakarta ta fice daga ɗakin.


Shaƙar wuyanta Saif ya yi da ƙarfin tsiya yana huci kamanninsa sun fara canja launi idanunsa sun fito sun yi jawur gashin jikinsa ya miƙe yana huci yace, "Ka kasar mini matata ko na illata ka, wallahi daga ita har abin cikinta idan ya samu matsala sai na kassara rayuwarka." Salman dake ɗauke da siffar Uwar bayi ya bushe da wata mahaukaciyar dariya yace, "Na yi tsammanin kanka baya ja ashe yana ɗaukan al'amura. Na gaya maka wallahi ba za ka iya ja da ni ba, sai na kashe ka da ranka kana kallo. A tashin farko ka ga na rabaka da Masoyiyarka na tabbata babu yadda za a yi ta ci gaba da ƙaunarka bayan tana muku kallon maciya amana kai da matarka. Sannan ka kwantar da hankalinka ba zan halaka matarka ba domin idan na halaka ta zan baku damar da za ku iya ɗinkewa har maganar aure ta shiga tsakani. Sai kuma abin cikinta bana tsammanin za ku same shi a yadda kuke da buƙata. Zan iya baka zaɓi idan ita ka zaɓa ko Mahaifiyarka, Mahaifinka, Matarka da abin da yake cikinta fansarta ne duk zan

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login