Showing 27001 words to 30000 words out of 89213 words
Chapter 10 - Anya Baiwa Ce 2 Complete Hausa Novel By Aisha Adam.txt
farin ciki wurin Sarki Aminullah abun baya musaltiwa. Mutane daga garuruwa ne suka halarci taron auren, har da baƙin turawa suka zo taya shi murna daga Ƙasar Ingila. Babu jimawa aka shiga kaɗe-kaɗe da wasannin Al'adu na gargajiya abun sai wanda ya gani gwanin burgewa. Duk wani abu na kayan auren an haɗa wa Abu wanda dangin gidan maza suke yi. Haka kayan ɗaki da duk wasu kayan al'ada da ake yi wa Ƴa mace Sarki Aminullah ya yi wa Abu, daga bayan gidan Sarki aka zaɓawa Saif da Salman wasu gidaje guda biyi iri ɗaya, sai dai suma gidajen suna cikin masarautar, haka ita ma Safiya ba ƙaramar dukiya iyayenta suka narka mata ba. Duk wani shagali da ake yi Salman baya farinciki da shi. Hasalima idan ka dube shi da kyau za ka fahimci sam auren kamar baya gabansa.
Ranar da aka yi ɗaurin auren a ranar ne aka ɗauki amarya aka kaita ɗakin mijinta, Abu ta sha kuka sosai musamman da Mahaifiyarta take yi mata nasiha akan biyayyar aure, "Abu ki buɗe kunnenki da kyau ki ji ni, yanzu wani nauyi ya rataya a wuyanki me girman gaske. Igiyar aure ba abar wasa bace saboda matartabar da matar aure ke da ita ta ninka ta wacce bata da aure idan har ta riƙe mutumci, ƙima da martabarta. Ki sani ba soyayya kaɗai ita ce jigon aure ba, domin kar ki ɗauka yadda kuke soyayya a gida haka za a ɗore har cikin gida. A'a sam akwai bambamci saboda lokacin da ake waje neman fahimtar juna da samun kyakkyawar alaƙa a tsakani ake yi. Ya yinda aka yi aure kuma haƙuri da soyayya sune suke taka muhimmiyar rawa a zamatakewar aure. Yi na yi bari na bari ladabi da biyya sune jigo, haƙuri garkuwa ne kulawa ɗa'a ce godiya da girmamawa Tarbiyya ce. Duk abin da mijinki zai baki ki yi masa godiya zaman aure zo mu zauna zo mu saɓa ne, ba kodayaushe ake cikin farinciki ba. Wataran idan namiji ya guma miki sai ki ji duk duniya babu wanda ya tsaneki kamar shi, watarana kuma idan ya faranta miki ji za ki yi duk duniya babu wanda yake ƙaunarki fiye da shi."
(Gara dai mu dinga gayawa ƴanmatanmu gaskiya 😂😂😂 ba wai kullin ace yayi kissing da romance da wacce tsiyar ake a gidan aure ba, wallahi duk wacce take ɗaukar huɗubar ƙaryar novel tana ruwa, ban ce kowacce soyayyar novel ƙarya bace amma akwai soyayyar da ke kanki idan kika karanta kinsan wacce zata faru da akasin haka. Ko munƙi ko munso Aure ɗan haƙuri ne duk fallin da wasu ƴan matan suke yi ba su shiga bane, saboda suna karanta littafi su ji ance bayan ta yi sallar asuba bata tashi ba sai sha biyu kafin ta tashi mijin ya gama komai tana tashi sun faɗa banɗaki an yi awa uku a toilet ana harka da soyewa 😂😂 ban da yaudarar kai wacce uwar za a yi shafe sama da awa uku ana yi a toilet? Wallahi mazanmu babu wanda zai yadda ki miƙe kullin a gado ace ya gama miki komai kina miƙe sai dai ya ruƙo hannunki ku faɗa toilet. Amma idan da me ja wata ta gwada gobe ta bamu labari 😂😂😂😂 Billahi na san karon ba zai yi da daɗi ba.🤣🤣)
Abu ta ci kuka sosai haka ita ma Inna Habi har da share hawaye saboda rabuwar da za su yi da Abu. A ranar da aka kai Abu tare da wasu tsirarun ƙawayenta suka kwana saboda bisa ga al'ada hakan ake yi ga duk amaryar da aka kaita ɗakin mijin. Washegari aka yi buɗar kai tare wasu shagulgulan tsakanin ƙawayen amarya da ƴan tsirarun abokin Ango Saif saboda abokanansa biyu jal Huzaif da Haris, sune suka gayyato nasu abokan suka rufa musu baya. Washe garin buɗar kai Ango Salman ya shiga ɗakin amaryarsa Safiya haka daga ɓangaren Saif shima ya shiga ɗakin Amaryarsa tare da rakiyar abokansa. Shi kuwa Salman dama ba shi abokai shi kaɗai yake yawo kamar maye. Yana shiga ɗakin Bayin da ke zaune da Safiyya suka tashi suka fice, Salman gadan-gadan ya ƙarasa kan gadon ya janye hular alkyabbar jikin Safiyya. Dukda baya wani farinciki da auren amma ganin yadda Safiya ta sha kwalliya ba ƙaramin tafiya ta yi da shi ba, rungumota ya yi jikinsa yana shaƙar ƙamshin jikinta da aka wanketa cikin azababbun turarruka masu matuƙar ƙamshi. Ganin lamarin Salman na neman wuce gona da iri ya sa Safiya ta tattara ƙarfinta ta ɗan ture shi ta ce, "Yarima me ye haka?" Cikin kasalalliyar murya yace, "Me kika gani da idonki? Haƙƙina zan karɓa" Haushi ne ya kama ta ta ce, "Ko za ka karɓi haƙƙinka ai ka bi komai a sannu." Salman be jira cewarta ya fisge alkyabbar jikinta ya shiga neman ƙwatar haƙƙinsa.
Da sallama ɗauke a bakinsa ya shiga ɗakin, daga bakin ƙofa ya tsaya ya harɗe hannuwansa yana kallonta cikin farinciki. Jin shiru babu alamun takowar mutum ya sa ta ɗago kai karaf suka haɗa ido. A kunyace ta sunkuyar da kai ƙasa tana wasa da ƴan yatsunta. A hankali ya fara takowa har ya zauna kusa da ita sannan ya zame hular alkyabbarta. Hannu ya sa ya ɗago haɓarta cikin tausasa murya yace, "Kunyar me ake ji." Abu shiru ta yi tana murmushi, goshinsu ya faɗa ya yi mata raɗa ƙasa-ƙasa sai gani nayi ta sunne kai ƙasa tana dariya, ɗago da kanta ya yi tana ƙoƙarin sunkuyarwa ta ji hannuwansa biyu ya tallafo fuskarta, yana goga hancinsu wuri ɗaya. kamar almara haka suka fara jin shassheƙar kuka daga waje Abu ce ta fara ɗagowa suka haɗa ido, tana shirin magana ya sa ɗan yatsansa akan bakinta yace, "Shiiii bari na duba na gani." Yana gama faɗa be jira cewarta ba ya ɗauki fitilar ƙwansu da ta kasance sabuwa dal da ita ya fita waje yana haske-haske.
🙄🙄🙄🙄🙄 Uban iya a dawo lafiya garin leƙe-leƙen idan ka kai kanka cen kai ka sani, ka fita ka bar Amarya Allah sa kar a gwada muku ɗiban albarka ba😂
Barkanmu da Juma'a🥰
_LITTAFIN NAN NA KUƊI NE DA NAIRA 200 ZAKI KARANTA SHI CIKIN KWANCIYAR HANKALI, ZAKU BIYA TA WANNAN ACCOUNT ƊIN, FIRST BANK 3090957579 AISHA ADAM, ZA'A TURO DA SHAIDAR BIYA TA WANNAN LAMBAR,0706 206 2624, DAN GIRMAN ALLAH IDAN KINSAN ZAKI FITARMUN DA LITTAFI NA YAFE CINIKINKI._
[18/12/2021, 19:47] Ameera Adam🌚: 51...
Takawa yake a hankali yana haskawa musamman wuraren da ya fi jin tashin sautin muryar me kukan, sashen hanyar banɗaki ya nufa daga cen bayan bishiyar Tsamiya yake jin tashin kukan mace, kukan ba ƙaramin taɓa zuciyarsa ya yi ba dukda be san wacce take kukan ba amma ya tabbata kukan na fitowa daga ƙaraƙashin zuciyarta ne. Abu da tun bayan fitowarsa ta fara jin tsoro na neman mamaye zuciyarta. Fitowar ta ya yi daidai ta hango shi da ta yi ya lula cen, da sauri ta ƙwala masa kira amma be waiwayota ba har sai da ya zagaya wurin bishiyar. Zuwansa ke da wuya ya ji ɗiff kamar an yi ruwa an ɗauke ya nemi kukan da yake ji ya rasa, sai ma kukan tsuntsaye da ƙananan ƙwari da ke tashi a wurin, juyowa ya yi yana daɗa haskawa daga cen jikin bango ya hango kamar inuwar mace a zaune ta cusa kanta cikin ƙafafuwanta. Yana ƙarasawa ya nemi inuwar ya rasa. Ganin haka ya sa Abu ta ƙara ƙwala masa kira a karo na biyi don haka ya juya da sauri ya nufi wurinta. Yana zuwa ta ja hannunsa cikin ɗaki a ɗan tsorace take kallonsa ta ce, "Ya Saif yanzu fa dare ne wallahi tsoro nake ji, a daren nan za ka je wurin bishiyar tsamiya ana zaune ƙalau." Jinjina kai ya yi yace, "Na leƙa in gani ko yara masu ganin ɗaki ne aka bar wata daga ciki." Abu ta kwaɓe fuska ta ce, "Gaskiya ni tsoro nake ji wallahi." Aljihunsa ya shiga lalube zuwa cen ya zaro wani ƙullin magani yace, "Bari na aika a kawo mana garwashi dama Ammi ce ta bani garin maganin nan na turare ne." Yana juyawa zai fita zaraf Abu ta bishi saboda ta gama razana da kukan da suka ji da farko. Babu yadda ya iya haka ya wuce yana gaba tana biye da shi, wani Dogari ya kira ɗaya daga cikin Dogarawan ƙofa ya aika aka ɗebo masa wuta suna zuwa ɗaki ya turara musu sannan ya ɗauko kazar da ya kawo musu ta amarci, a hankali ya fara bawa Abu amma saboda kunya ta kasa karɓa ta ci. Sai da ƙyar ta iya gutsira ta ci gutsire biyu daga haka ta ce ta ƙoshi. Saif ɓata fuska ya yi sai da ta ga ransa ya ɓaci sannan ta saki jiki ta suka ci gaba da ci. Bayan gama ciye-ciyensu suka gabatar da sallar nafila tare da addu'o'i sannan suka wuce kan gado suka ya da zanzo. Saboda gajiya Abu tana kwanciya bacci ya yi gaba da ita, Saif kwanciya ya yi a gefenta ya fara ƴan juye-juye. Abu cikin bacci ta fara jin baƙon lamari daga wurin Saif, da farko yi ta yi kamar ba ta ji shi ba amma daga baya da ta ji lamarin na neman gagar kundila ta shiga neman alfarmar ya ɗaga mata ƙafa. Gabaɗaya Saif birkice mata ya yi tun tana magiya har bakin ta ya yi laƙwas.
(Bari mu wuce wurin kar na je na aiwatar da ɗiban albarka😂🤣)
Washegari Salman tun farar safiya ya miƙe ya faɗa banɗaki ya tsarkake jikinsa, be bi ta kan Safiyya ba dukda yadda ta galabaita ko motsin kirki bata yi saboda ko kaɗan Salman be bi da ita ta lallami ba. Kai tsaye cikin gidansu ya nufa yana zuwa aka fara jansa da tsokanar ango-ango. Fulani Maryama na ɗakinta ta jiyo su ba ta kai ga miƙewa ba ta ji Salman ya shi ga wurinta, da mamaki ta kalleshi don gari ma be gama wayewa ba ta ce, "Salman lafiya da farar safiya haka? Ko Jakadiya sammako ta yi muku?" Yana daga tsaye yace, "Zuwa na yi na gaya muku a tura a gyara waccen yarinyar, gaskiya fa yarinya ta yi ƙoƙari don lokacin da nake tuki sai da na so wuce ƙofar mazugal..." A hassale ta katse cikin ɓacin rai ta ce, "Kai baka da hankali ne Salman ni Mahaifiyarka kake gayawa haka? Saboda rashin mutumci."
Saif tun asuba ya taimakawa Abu ta gyara jikinta, ba ƙaramin tausaya mata ya yi ba, guntun tsaki ya ja ganin yadda zanin gadon ya yi da ya tuna dole sai ya ciro shi an shiga da shi cikin gida domin a tabbatar da amarya ta kai ƙimarta ko bata kai ba. Janye zanin gadon ya yi ya shimfiɗa wani sannan Abu ta hau ta kwanta ta koma bacci jikinta da ɗan ɗumi alamun zazzaɓi.
SHAFIN DAI NA SAN BA ZAI MUKU DAƊI BA😢😢😢 AMMA KUYI HAƘURI HAKA YANAYIN LABARI YAKE GABA ZA KU FAHIMCI DALILIN HAKA, KAR KU MANTA A DUNIYA BA KOMAI MUTUM YAKE NEMA KUMA YA SAMU BA.😢
_LITTAFIN NAN NA KUƊI NE DA NAIRA 200 ZAKI KARANTA SHI CIKIN KWANCIYAR HANKALI, ZAKU BIYA TA WANNAN ACCOUNT ƊIN, FIRST BANK 3090957579 AISHA ADAM, ZA'A TURO DA SHAIDAR BIYA TA WANNAN LAMBAR,0706 206 2624, DAN GIRMAN ALLAH IDAN KINSAN ZAKI FITARMUN DA LITTAFI NA YAFE CINIKINKI._
[19/12/2021, 12:46] Ameera Adam🌚: 52
Jakadiya da zumuɗi ta nufi gidan Amaren don tabbatarwa idonta tsegumin abin da aka umarce ta, da sallama ta samu shiga ɗakin Safiyya. Da fululluka ta fara cin karo da alkyabbar Safiyya, da ƙafa ta shure su ta fara kyaɓe baki ta ce, "Ƴar nan sannu kin ji. Girman kenan muma duk da haka muka zo nan. Yoo Allah na tuba ku ai da girmanku tun da ga alama daga ke har Abu kun kai sha biyar-biyar. Mu kuwa fa mu da sha bibbiyu aka haɗa mu da ƙaratan mazaje ai ba muyi ma langwaɓewarku ba. Tashi mu gani." Safiyya miƙewa ta yi a hankali da sauri Jakadiya ta ja gefe tana dafe ƙirji, Safiyya sai rangwaɗar da kai gefe take saboda azaba. Jakadiya ta sauke ajiyar zuciya ta ce, "A'a lallai Salman gara da Takawa ya hanzarta aka yi auren nan. Allah na tuba da an ƙara wani lokaci wataƙila muma ya fara kawo mana farmaki, dubi yadda ya yi wa yar mutane tambaɗar rashin imani. Kai Amma dai Maryama ta haifi Jarababbe, ko dan ai be yar a ƙasa ba saboda lokacin Maryama da Takawa har guduwa yake tana nemansa saboda Jaraba." Safiyya ta gaji da surutan Jakadiya a ɗan fusace ta ce, "Kin zo taimaka mini ne ko surutu kika zo yi mini, ko kuma in sa a kira wacce za ta taimaka mini." Jadiya ta harareta a fakaice ta ce, "A'a wa kuma za ki kira a wannan yanayin da kike ciki wacce ta wuce ni." Jakadiya na surutu tana gyara gadon, sannan ta taimakawa Safiyya ta gyara jikinta. Tana gama gyarawa ta shimfiɗa wani zanin gadon, jikinta zafi zau da zazzaɓi ta koma kan gadon ta kwanta saboda ba ƙaramin jin jiki take ba.
Jakadiya na gamawa ta wuce wurinsu Saif tana shiga ta tsaya a bakin ƙofa tana rangaɗa sallama, kasancewar ta ga takalmansa a bakin ƙofar. Saif ne ya fito yana ɗan murza idanu don shima baccin ya koma. Washe baki Jakadiya ta yi ta ce, "Allah ya taimaki Yarima, dama na zo ne domin na taimakawa Abu ta gyara jikinta sai kuma zanin gado da zan ɗauka, ka ga na matar Salman kai amma dai Salman an yi jarumin namiji, dubi yadda zanin gadonsu ya yi kaca-kaca da..." Cikin ɗaure fuska Saif ya ɗaga mata hannu yana faɗin, "Ban tambaye ki ba." Juyawa ya yi ya ɗauko mata zanin gadonsu ya miƙa mata yana jan guntun tsaki, yana shirin komawa ta ce, "Ai zan gyara Abu." Be juyo ya kalle ta yace, "Na gyara matata." Jakadiya ba haka ta so ba don ta so ta ga yadda Abu ta yi don ta ji daɗin isar da labari. Don haka ta ɗan tsuke fuska ta ce, "Amma ai ka san a ƙa'ida ni nake gyara duk wata sabuwar amarya." Saif ya kuma tamke fuska yace, "Ni na ɓata abata kuma na gyara ta." Yana gama faɗa ya shige ɗaki. Jakadiya haushi ya kuma turniƙeta ta juya ta mita da ƙunƙuni. "Eh ai ya nuna mini idonsa ya buɗe wai shi ya yi sabon aure, ai wallahi kamar kumbo kamar kayanta yaron nan babu abin da ya bari na Zaliha. Duk mugun halinta ya kwashe tsaf.
Me babban ɗaki gabaɗaya ta shiga damuwa sakamakon ciwon Maryo da ta tashi da shi, wannan karanma ranga-ranga aka ɗauke ta zuwa asibiti. Sai da ƙyar Allah ya bada iko aka samu damar shawo kam ciwon nata. Ba ƙaramin faɗa likitan ya yi musu ba saboda yace tana cikin matsananciyar damuwa shi ya sa ciwon nata yake yawan ta shi akai-akai. Babu yadda suka iya a wannan karanma amsawa Likitan suka yi sannan suka ci gaba da bata kulawar da ta kamata. Ko kaɗan Sarki Abdallah be sanarwa da Fulani Fahima halin da Maryo take ciki ba, don ya san za ta shiga cikin matsananciyar damuwa.
Lokacin da aka kai zannuwan gadon su Abu Inna Habi ba ƙaramin farinciki ta yi ba don ko ba komai, Abu ta kankaro mata daraja da ƙima a idon mutane. Sai dai tun daren ranar idanunta ya gagara bacci saboda miyagun mafarkan da ta dinga yi Maryo, wanda abun ba ƙaramin tsoro ya bata ba. Haka kawai zuciyarta take raya mata akwai damuwa saboda wannan mafarkan da take yi har sun fi na kwanakin baya muni. A daddafe take cinye kwanakin don ganin ƴan biki da sauran ƴan uwa da suka halarci bikin sun watse domin ta je ta tunkari Sarki Aminullah da maganar bakinta ayi wacce za a yi a ƙare, don ta ga ji da dakon zunubin da take yi ba dare babu rana.
Bayan sati biyu da biki amare da angwaye ba ƙaramin murzar amarci suke yi ba cikin so da ƙauna. Safiyya babu yadda ta iya har ta fara sabawa da halin Salman saboda tuni zuciyarta ta afkawa soyayyarsa. A ɓangarensa shima ya ɗan rage wasu abubuwan yana ɗan lallaɓata wurin mu'amala ba kamar baya ba da yake yi mata ta ƙarfi da yaji. Sai dai babu wata hira me daɗi da take shiga tsakaninsu. Tsayawa gayawa me karatun soyayyar da ake ɓarza a gidan su Saif ɓata lokaci ne, amma a wannan lokacin ne Abu ta tabbatarwa zuciyarta babu wata ƴa mace da za ta iya samun gurbi a zuciyar Saif. Wani abun idan ya yi mata ita take jin kunya ba shi ba, saboda Saif gawurtaccen namiji ne a fagen iya soyayya, har mamaki take idan ya yi wani abun domin a baya ta ɗauka yadda yake shiru-shiru ta za ci babu wata duniyar gajimare da ya sani.
(Maryo fans 😂 na san ji kuke kamar ku ɗebe mini albarka😂)
Sarki Aminullah ba ƙaramin ɓacin rai ya shiga ba lokacin da ya gama jin zantukan da Inna Habi take gaya masa, kallonta ya yi ya ga yadda take zubda hawaye sai kuma ya ji ta bashi tausayi musamman da ya tuna yadda Maleek ya kafe kai da fata akan Maryo matarsa ce. Wayar salularsa ya sa wani Dogari ya ɗauko masa nan take aka danna lambar Sarki Abdallah, yana ɗagawa murya babu walwala Sarki Aminullah yace, "Sirikina ina buƙatar ganin yarinyar nan Maryo wacce Maleek yace matarsa ce, ina buƙatar ganinta cikin gaggawa daga yai zuwa gobe." Yana gama faɗar haka ya datse kiran.
_LITTAFIN NAN NA KUƊI NE DA NAIRA 200 ZAKI KARANTA SHI CIKIN KWANCIYAR HANKALI, ZAKU BIYA TA WANNAN ACCOUNT ƊIN, FIRST BANK 3090957579 AISHA ADAM, ZA'A TURO DA SHAIDAR BIYA TA WANNAN LAMBAR,0706 206 2624, DAN GIRMAN ALLAH IDAN KINSAN ZAKI FITARMUN DA LITTAFI NA YAFE CINIKINKI._
[20/12/2021, 13:01] Ameera Adam🌚: 53...