Showing 66001 words to 69000 words out of 89213 words
Chapter 23 - Anya Baiwa Ce 2 Complete Hausa Novel By Aisha Adam.txt
hannunta suka wuce ciki Maleek ya rufa musu baya. Kamar wacce ƙwai ya fashewa a ciki haka Maryo ta bi su zuwa cikin ɗakin.
Kafin wani lokaci tuni maganar Shukra ta ƙarasa har kunnen Sarki Aminullah, Sarki Abdallah da sauran waliyan Maleek waɗanda ba su tafi ba. Maleek ba ƙaramin tausawa Shukra ya yi ba dangane da tarihin rayuwar da suka fuskanta ita da tagwayenta. Inna Habi ta goge hawayen fuskarta tana kallon Maryo da Shukra, Maryo ta share hawayenta ta ce, "Amma da kin yi haƙuri kin zauna da mijinki ya fiye miki wannan wahalar da kika sha, sai dai duk abin da ya samu bawa daga Ubangiji mai kyau ne."
"Duk abin da ya koro ɓera daga rami ya faɗa wuta to ya fi wutar zafi. Na so jure wa haka amma na ga ba zan iya ba domin neman rayuwata ake da abin da na haifa. A ranar da zan baro Masarautar Adamawa muna kwance cikin dare ni da 'yan biyu na ji katangar ɗakinmu ana rusa ta, ban yi aune ba na ji muryar da ko a mafarki ba zan manta da ita ba ƙasa-ƙasa tana cewa. Maza ku ƙone ta tana ciki da yaranta gabaɗaya. Inna jin haka da sauri na goya Hassan shi kuma Usaini na rungume shi na saka hijabi na fice da gudu a lokacin wutar har ta fara ci a ɗakinmu. A cikin daren nan haka na rinƙa gudu ko waiwaye bana yi har Allah ya sa na fice daga gidan. Na samu nasarar ficewa ne lokacin da aka tattara a bakin sahshenmu kowa na ta'ajibi. Ina ganin Sarkin ƙofa ya wuce na fice da sauri hannuna ɗaya rungume da Usaini ɗayan na toshe masa baki don lokacin wuya ta sa ya fara tsala kuka. Ina fitowa na haɗu da wasu fatake na nemi taimakonsu suna wuce da ni zuwa garin da za su yada zango. Haka na ci gaba da gwagwarmaya har Allah ya kawo ni garin Kano na rinƙa faɗi tashi har na samu gidan da zan riƙa yi musu aiki suna bani abinci muna ci nida yarana. A taƙaice kenan dalilin fitowa ta amma idan kece za ki iya ci gaba da zama kuwa." Maryo ta girgiza.
Babu jimawa Sarki Aminullah ya sa aka kai Shukra Fada, bayan an karɓo 'Yan biyunta daga wurin Iyatu. Abu tsayawa ta yi tana kallonsu lokacin da ta ƙarasa ganin abin da ake ta jita-jita a kam maganar Maryo ta rikiɗa zuwa mutum biyu.
Sarki Aminullah ido ya zuba musu yana kallo ya ɗauki lokaci mai tsayi sannan ya numfasa ya fara magana, "Dukkan yabo godiya sun tabbata ga Allah subhanahuwata'ala, wannan al'amarin ya faru ne cikin ikon Allah. Maleek ba za mu bar maka su gabaɗaya a matsayin matakan ba domin da alama akwai alaƙa mai ƙarfi a tsakanin Shukra da Maryo don haka sai dai ka zaɓi ɗaya." Takawa na gama magana Maryo ta gyara zama ta ce, "Allah ya taimake ka na haƙura na bar mata shi saboda dama rashinta ne ya sa alaƙarmu ta yi ƙarfi har da ta kai ga batun aure." Maleek da Inna Habi ba ƙaramin tausayin Maryo suka ji ba. Sarki Aminullah ya san za a yi haka domin idan bai manta ba rashinta ne ya sa aka bashi Maryo a matsayin Shukra. Wannan dalilin ya sa ya yanke wata shawara da cewar, "Bisa ga la'akari da abubuwan da ya faru idan aka warware aurenta da Maleek zan ɗaura mata aure da babban Ɗana kuma magajin wannan masarauta." Daga Maryo har Inna Habi a firgice suka kalle shi jikin Maryo har rawa yake tana tsaka da tunani ta ji Sarki Aminullah ya sallame su.
Duk inda nutsuwa take ta yi gabas Maryo ta yi yamma domin tun da Sarki Aminullah ya furta haka shi kenan ta rasa nutsuwarta. A ranar labarin duk abin da ya faru ya karaɗe cikin masarautar. A ranar ne Saif ya kwanta rashin lafiya banda amai babu abin da yake yi yana ambatar sunan Maryo. Tun suna ɗaukan lamarin da wasa har abin ya fara gagarar Kundila. Kwanan su Maleek guda suka tattara zuwa garin Adamawa.
A wannan karon SarkinAminullah ba ƙaramin damuwa ya yi dangane da ciwon Saif ba, da kansa ya aika aka kira masa Fulani Zaliha ya tambayeta abin da yake damunsa. Da farko ta yi niyyar ɓoye masa ganin ɓoyewar bashi da amfani ya sa ta sanar da abin da yake damunsa.
Kwana biyu da yin maganar Sarki Aminullah ya sa aka kira masa Inna Habi, Maryo, Abu, Saif da sauran matansa gabaɗaya. Bayan ya gabatar da maƙasudin zaman na su ya kalli Maryo zai yi magana Abu ta yi karaf ta ce, "Allah ya taimakeka don Allah ka yi mini wannan alfarmar domin kai kaɗai ne za ka iya tabbatar da ita." Maryo ta dubi Abu ta ce, "Karma ki wahalar da bakinki domin hakan ba zai taɓa yuwuwa ba."
_LITTAFIN NAN NA KUƊI NE DA NAIRA 200 ZAKI KARANTA SHI CIKIN KWANCIYAR HANKALI, ZAKU BIYA TA WANNAN ACCOUNT ƊIN, FIRST BANK 3090957579 AISHA ADAM, ZA'A TURO DA SHAIDAR BIYA TA WANNAN LAMBAR,0706 206 2624, DAN GIRMAN ALLAH IDAN KINSAN ZAKI FITARMUN DA LITTAFI NA YAFE CINIKINKI._
[22/01, 16:55] Ameera Adam🌚: 66....
Waiwaye...
Kafin wani lokaci tuni ɓatan Rayzuta da Farratu ya karaɗe ciki da wajen masarautar Daulatul Jinnul Sahara, hankalin Sarki Kisumu ba ƙaramin tashi ya yi ba. Nan take ya baza masu tsaron cikin Masarautar aka shiga bincike a tunaninsa bincike suke yi a baɗini kuma ninke shi suke yi domin kusan kaso casa'in da tara sun san yanda aka yi Rayzuta ta ɓace. Yana nan zaune Labari ya ishe masa a sirrance na tafiyar da aka yi da Rayzuta da mai ɗakinsa, wannan labarin ya same shi daga bakin Mahaifin Furzaan sakamakon wani amintaccen dogari da ya sanar masa. Lokacin da Furzaan ya ji labarin ji ya yi kamar ya yi hauka, nan take Sarki Kisumu ya bada umarnin zama na gaggawa a cikin fada. Ransa ba ƙaramin ɓaci ya yi ba ganin yawan Dogarawa masu tsaron Masarautar ace wai har a ta fi da matarsa da 'yarsa ba tare da sun yi ƙoƙarin dakatarwa ba. Suna nan zaune yana tsaka da jawabi Furzaan ya miƙe jikinsa har rawa yake yace, "Ranka ya daɗe a yi mini izini na tafi Masarautar Sarki Buzaag na sare kanshi dana Bulbuta da ɗansa Zulik domin sun munafinci Masarautar nan dole ne a yi musu hukunci mai tsanani. Ka bani dama na je na taho da Rayzuta da Mahaifiyarta domin na yi rantsuwa sai sun girbi abin da suka shuka da hannunsu." Sarki Kisumu ba ƙaramin daɗi ya ji ba domin ya tabbata bai zaɓawa 'yarsa zaɓon tumun dare ba. Cikin ƙarfafa masa gwiwa yace, "Tabbas kai Ɗan halak ne kuma na ƙara tabbatarwa daga tsatson jinin Aminina ka fito. Amma ka sani kai kaɗai ba za ka iya karawa da su ba domin na san wane ne Sarki Buzaag ba tun yanzu ba. Ba za mu farmake su yaƙi ba matuƙar ba su suka fara kawo mana hari ba, don haka zamu zuba musu ido don ganin abin da suke da niyyar yi. Amma matuƙar suka cutar mini da iyali sai na yi mummunan ɓata musu..." Bai rufe baki ba wani Bawansa ya faɗo fadar jina-jina yana haki yana nuna ƙofa yana cewa, "Ranka ya daɗe ga Bulbutu can da rundunar Sarki Buzaag sun kawo mana hari sun kashe dubbannan mutane nima da ƙyar na..." Harbin kibiyar da aka sakar masa a baya ne ya katse maganar da yake yi nan take ya faɗi ya mutu. Hankalin Sarki Kisumu ya kai matuƙar ƙolokuwar tashi da sauri ya mike yana ɗaukan kayan yakinsa. Haka suma sauran mazauna wurin kowa ya fice a guje yana neman kayan yaƙinsa. Sanƙira tuni ya yi shelar ɗaura ɗamarar yin yaƙi saboda kowa ya kasance cikin shiri.
Furzaan kamar jira yake tuni ta ɗauki kayan yaƙinsa ya fita ya fara ragargazar maza yana kai su ƙasa. Kafin
wani lokaci tuni wuri ya hautasine da ƙura ban da ƙarar ƙasusuwan jikinsu da manyan miyagun ƙarafuna babu abin da yake tashi a wurin. Sai dai sarkin yawa ya fi Sarkin ƙarfi, munafukan Masarautar Sarki Kisumu tuni suka rikiɗa zuwa kaiwa tsagin Sarki Kisumi farmaki. Lokacin da Mahaifin Furzaan, Furzaan da Sarki Kisumu suka lura da haka sai yaƙin ya fara sauya salo. Ganin ana neman kai tawagar Sarki Buzaag ƙasa ya fusata su suka fara buɗe musu wuta wani Barde ne ya kawowa Sarki Kisumu suka Mahaifin Furzaan na ganin haka ya tare sukar ta huda cikinsa har zuwa bayansa. Nan take jini ya yi tsartuwa idanunsa suka fara kafewa, Sarki Kisumu ya wurgar da takobinsa ya ƙwalla ƙara ya rungumo abokinsa yana ci gaba da kuka kamar ƙaramin yaro yana cewa, "Me ya sa za ki mini haka? me ya sa ba za ka bari mu tafi tare ba." Wannan kukan da Sarki yake yi ne ya ja hankalin Furzaan ganin Mahaifinsa a ƙasa cikin jini ba ƙaramin ɗaga masa hankali ya yi ba. Da sauri ya ƙarasa ya rungume shi yana kiran sunansa. Daga cen gefe a fusace Babban Barden ya ɗauke Barden da ya kai wa Sarki suka mari yana cewa, "Baka da hankali ne ba ka ji sharaɗin da Mai gida ya kafa mana ba yace duk rintse kada mu kashe mutanen da ya lissafa mana yanzu da shi ka samu da ya kenan?" Furzaan na jin haka ya miƙe a fusace ya ɗau takobinsa ya fille kan Barden da ya kashe mahaifinsa nan fa faɗa ya ƙara ɗaukan zafi, Mahaifinsa yana gabda mutuwa ya kalli Sarki murya a shaƙr yace, "Kabar faɗin haka domin ba komai bane don Amini ya sadaukar da ransa ga amininsa. Na ji daɗi ƙwarai da ni zan fara tafiya na barka, amma ina me jadadda maka ko bayan raina ban yarje Furzaan ya auri wata ba bayan Rayzuta kuma ko zai mutu na fi son ya mutu a tafarkin jarumta ba jarumin da aka ci shi da yaƙi ba." Ya saki murmushin ƙarfin hali ya ci gaba da cewa, "Dama na gaya maka na girmeka tsaurin ido ne ya sa kake abota da ni amma na girmeka na riga ka aure, na riga ka haihuwa kuma yanzu ma sai na riga ka mutuwa. Yaro matsa gefe me gidanka na magana." Waɗannan kalaman tun suna yara ƙanana Mahaifin Furzaan yake gayawa Sarki Kisumu, tun ba su yi hankali ba har suka fara zama samari. Wani lokacin idan suna tsokamar junansu Mahaifin Furzaan na faɗin haka yake kashe bakin Sarki Kisumu. Don haka a wannan lokacin da mutuwarsa ta zo ya ƙara jajjada masa. Sarki Kisumu na jin ƙarashen zancensa ya rungume shi ya fashe da wani irin matsanancin kuka, duk wanda yake wurin idan ya ga irin gursheƙen kukan da yake yi sai ya tausaya masa. Tuno rayuwarsu ta yarinta ya rinƙayi da barkwancin Amininsa tare da sauƙin kai irin nasa. Kasa taɓuka komai ya yi ya rungume gawar Amininsa yana ci gaba da kuka.
Ko a girgiza kurna ta fi magarya domin duk lokacin da ka daidai Giwa da ɗantsako banbancin a bayyane yake, Sarkin yawa ko cikin maye yake ya fi Sarkin Ƙarfi. Duk yanda Furzaan ya kai ga ƙoƙarin kashe Dakarun Sarki Buzaag sai da suka yi masa ƙawanya sannan suka ɗaure shi da wata murtukekiyar igiya. Kan Sarki Kisumu suka koma shima da ƙyar suka yakice shi daga jikin gawar Amininsa suka ɗaure shi, sanann suka yi ƙoƙarin tafiya da shi. Furzaan na gaba Sarki Kisumu na biye da shi, Masarautar ta yi tsit sai gawarwakin mutane da kukan mata da ƙananan yara.
Daga bakin ƙofa ya hango Mahaifiyarsa a kwace cikin jini bata ƙarasa mutuwa ba tana ɗaga hannu alamar neman taimaka. Juyawa ya yi wurinta da sauri suka fisgeshi da ƙarfin tsiya kansa ya bugu da wani ƙarfe take ya faɗi sumamme. Suna ficewa daga masarautar ba su tsaya ko ina ba sai Masarautar Sarki Buzaag .
Lokacin da Zulik ya shiga da Rayzuta ɗaki kallonta ya rinƙa yi yana lasar baki, sannan ya cire kayansa yana niyyar haike mata gadangadan. Kukan kura ta yi tare da jin wani irin ƙarfi ya zo mata ta hankaɗa shi da bango gefe ta kalla ta hango wani mulmulallan farin ƙarfe ta ɗauka tana nishi saboda nauyinsa ta buga masa. Dukda ya goce amma sai da ta same shi. Nan take ya fasa wata ƙara ya zube a wurin sumamme sai Dogarawan Sarki Buzaag ne suka shiga suka kai masa ɗauki. Ajiyar zuciya Rayzuta ta yi tana lumshe idanu, ta ci gaba da addu'ar Allah ya kawo mata mafita a cikin halin da take ciki.
Har lokacin Sarki Kisumu bai daina hawayen rashin Amininsa ba, suna zuwa Sarki Buzaag ya kalle su ya bushe da dariya yana nuna Sarki Kisumu da ke cikin jini, Sai da ya tsagaita da dariya sannan Bulbutu ya shiga fuskarsa kwance da murmushi. Sarki Buzaag ya kalli Sarki Kisumu yace, "Dube ka abin tausayi, Sarki mai ji da izzar mulki amma yau ya koma ƙasƙantaccen mutum wanda Bawan Masarautar nan ya fi shi daraja. Mai zai hana ka taugunna na ɗora ƙafata a kafaɗarka ka nemu yafiyata na mayar da kai maɗaukaki koda ba ka kai matsayin da kake da shi a baya ba." Sarki Kisumu ya yi murmushin takaici yace,"Izza tamkar numfashi take, numfashi kuma a kodayushe shine ruhi kai ne ƙasƙantace ba ni ba domin ni na tsaya domin kare dukiya da talakawana ko a yanzu na mutu tabbas ban mutu a banza ba." Daga ɗakin da take ta fara jiyo muryar Mahaifinta da sauri ta fito tana zuwa ta faɗa jikinsa tana kuka. Sautin Kukan da take yi ni ya doko dodon kunnensa, wata gauruwar ajiyar zuciya ya sauke yana buɗe lumsasun idanuwansa. Tarwai ya ɗora su a kan fuskar Rayzuta, suna haɗa ido ta yunƙura za ta wurinsa da sauri Dogarawan suka riƙe shi suna dankwafar da kansa ƙasa. Bulbutu ne ya sa a ka janye Rayzuta gefe sai Zulik ya shigo yana ɗingisawa, wurin da Rayzuta take ya nufa ya dafa kafaɗarta yana murmushi. Wani irin abu ne ya tokare zuciyar Mahaifinta da Furzaan da sauri ta sa hannu ta ture Zulik tana matsawa gefe.
Cikin Shammata Sarki Kisumu ya miƙe ya faɗa kan Sarki Buzaag ya damƙi maƙogaronsa iya ƙarfinsa ya matse da hannuwansa biyu. Kafin Dogarawan su yi wani yunƙuri tuni Sarki Buzaag ya mace har lahira. Da sauri suka janye shi suna kai masa duka ta ko'ina, ganin haka ya sa Furzaan ya yi kukan kura ya kwarma ihu ya yage igiyar da a ka ɗaure shi da ita. Nan take sabon faɗa ya rikice a cikin fadar. Furzaan sai da ya rufe duk wata ƙofa da yake da tabbacin wasu za su fahimci halin da suke ci sannan suka fara azababben yaƙi. Zulik na ganin haka ya fisgi hannun Rayzuta ya shige wani ɗaki da ita ya datse ƙofar. Bulbutu da ke cikin fargaba ganin za a iya cinsu da yaƙi ya sa ya zage damtse ya fara ƙoƙarin kare kansa. Anan cikin haka suka fara faɗa shi da Sarki cikin nasara Sarki Kisumu ya soka masara takobi a ciki har sai da ta huda bayansa. Amma ga mamakinsa sai gani ya yi Bulbutu ya fashe da dariya kallon cinyar Sarki yake wacce ya sara da wani sihirtaccen shu'umin gatarinsa saboda tsananin faɗa bai san da saran ba sai da ya ga Bulbutu na kallon wurin. Bulbuta ya fara shaƙuwa yana faɗin, "Ni da kai duk babu mai rayuwa domin wannan gatarin sunanshi Gaɓar mutuwa, tun da na sareka zai fara fitar da gaɓɓon jikinka, ka ga an yi ba a yi..." Bai ƙarasa maganar ba ya ji Sarki Kisumu ya ƙwallah ƙara sakamakon cinyarsa da ta fita daga gangar jikinsa, Bulbutu murmushi ya yi nan take rai ya yi halinsa. Haka gaɓɓan jikin Sarki Kisumu suka ci gaba da fita yana ƙwala ihu saboda tsananin azaba. Da sauri Furzan ya ƙarasa gare shi sakamakon ya gama da duk sauran Baraden da ke wurin. Zuwan sa ke da wuya Sarki Kisumu yace ga garinku nan.
Cikin zafin nama ya tashi ya doka ƙofar ɗakin da Zulik da Rayzuta lokacin da ya shiga yana ta kiciniyar guduwa da ita ta ƙofar sirri. Ganin Furzan da takobi ba ƙaramin ɗaga masa hankali ya yi ba, Rayzuta na ganin haka ta fisge ta koma bayansa tana kaka. Ƙofar ɗakin ya rufe da ƙarfi sannan ya zaunar da ita a gefe nan suka shiga karawa cikin azabbaen yaƙi mai raunatar da zuciyar ƙananan jarumai. Zulik na ganin Furzaan ya tasamma halaka shi ya fice ta ƙofar sirri da gudu nan take ya ɓace cikin tsafin da Mahaifinsa ya yi masa kafin ya mutu. Furzaan bin bayansa ya yi da gudu amma ya neme shi sama da ƙasa ya rasa. Rayzuta ce ta biyo shi sakamakon jin bugun ƙofar da wasu dakaru suke yi. Kama hanunta ya yi za su gudu ta ja ta tirje tana cewa, "Furzaan ina za mu ta fi mu bar Mahaifina." Furzaan ya sunkiyar da kai ƙasa yace, "Ki yi haƙuri amma mun rasa Baba." Wata uwar ƙara ta ƙwalla ta zube ƙasa a sume. Ganin lokaci na ƙurewa ya sa Furzaan ya ɗauke ta cas ya rufe ƙofar da ƙarfi ya fara falfala gudu da ita cikin sararin samaniya.
Wannan kenan!
Sarki Aminullah ya tatattara hankalinsa kan Abu yace, " 'Yata ina jin ki." Maryo ban da harara babu abin da take wurgawa Abu, Abu ta russunar da kai ƙasa ta ce, "Allah ya taimakeka ina son ka sa Saif ya sauwaƙe mini." Da sauri Fulani Zaliha ta ɗago ta kalli Abu da ta sunkuyar da kai ƙasa don ta san wannan hukuncin ba zai taɓa yi wa Fulani Zaliha daɗi ba domin ta nuna mata ƙauna kamar ita ce ta haifeta. Sarki Aminullah ya kalli Saif da ke gefe duk