Showing 30001 words to 33000 words out of 89213 words

Chapter 11 - Anya Baiwa Ce 2 Complete Hausa Novel By Aisha Adam.txt

30 Nov 2024

5344

*Amun afuwa pls saboda na ɗan yi kuskure wurin rubuta Sarki Aminullah ya ɗaga waya ya kira Sarki Abdallah, sai daga baya na farga wallahi idan kun duba yanayin shekarun labarin a lokacin babu wayar sadarwa. Yanzu mu barshi akan Sarki Aminullahi ya aikawa da Sarki Abdallah da takarda akan yana buƙatar ganin Maryo ciki gaggawa. Amun afuwa da wannan kuskuren*🌚


Sarki Abdallah jikinsa ne ya yi sanyi lokacin da ya gama karanta wasiƙar da aka aiko masa daga masarautar Kano, Fulani Fahima a lokacin tana zaune a gefensa ta ce, "Allah ya taimake ka wata muhimmiyar magana aka faɗa?" Kallonta ya yi yana nannaɗe wasiƙar hannunsa yace, "Sirikina ya buƙaci a mayar da Yarinyar cen cikin gaggawa saboda muhimmiyar magana. Hasalima ya tabbatar mini da cewar ba matar Maleek bace. Ba mayar da ne damuwa ta ba, babbar matsalar ta yadda za mu fuskance su da yanayin da yarinyar nan take ciki, kuma shin wani abu ya taɓa shiga tsakanin Maleek da ita? Kuma wanne jawabi za mu yi wa Me babban ɗaki wanda za ta gamsu?" Fulani Fahima ba ƙaramin daɗi ta ji domin dama ta jima da son haka, saboda ta san ko ba daɗe ko ba jima dole sai kowa ya san halin da Maryo take ciki don haka take ganin babu fa'idar ɓoyewa. Gyara zama ta yi ta ce, "Allah ya taimake ka ina ganin wannan ba abin damuwa bane. Mu fito mu gaya musu gaskiyar yadda ciwon ya same ta, ita kuma Me babban ɗaki sai mu nuna mata rubutacciyar samfefar da aka aiko. Wata ƙila ma damuwar da yarinyar nan take ciki zai yi mata sauƙi idan ta koma hannun mariƙiyyarta. Amma ina fargabar Allah ya sa babu wata mu'amala da ta shiga tsakaninsu." Jinjija kai yake cikin gansuwa da jawabanta shi ya sa yake ƙara ƙaunarta saboda duk wani abu da yake neman ɗaure masa kai ita take warware masa. Ba'a ɗauki lokaci ba ya sanarwa da Me babban ɗaki halin da ake ciki, da farko fitittike musu ta yi sai daga baya da ya lallameta sannan ta amince. Amma tun a lokacin da fara hawaye na rabuwa da Maryo saboda ba ƙaramin sabo suka yi ba, gabaɗaya kayan Maryo ta shiga haɗa mata tana haɗawa tana share hawaye gwanin ban tausayi. Ita kuma Maryo da take kwance akan ƙaramin gadon ƙarfe bata san abin da yake faruwa ba.


Ɗan aiken Sarki Aminullah yana zaune yana jiran amsar da zai koma ya isarwa da shugabansa saƙon da aka ba shi, Sarki Abdallah ne ya umarci Dogari Lurwanu da ya rubuta amsar wasiƙar kamar haka.


_Assalamu alaikum Sirikina fatan alheri a gare ka da fatan kuna cikin ƙoshin lafiya. Na riski saƙonka daga hannun Dogarinka Umaru, na yi matuƙar mamakin jin yadda wannan al'amari ya kasance, amma ina me baka haƙuri babu a dadi bisa ga wata larura da ta faɗawa wannan yarinya da ka aiko da takadda akan ta. Kasan duk abin da ya samu bawa rubutacce ne daga Ubangiji, kuma ba mu ɓoye maka saboda wata manufa ba sai don muna son nema mata magani na ɗan wani lokaci. In sha Allah za mu dawo da ita hannu da hannu da yardar Allah idan Allah ya kaimu rana ita yau me zuwa._


_SAƘO DAGA MASARAUTAR ADAMAWA_


Tambarin Masarautar Adamawa aka buga a jiki tare da naɗe farar takardar samfefar wacce aka yi rubutun ajami, aka bawa Dogarin da ya kawo takardar tare da guzurin da zai yi a hanya. Maleek tun da ya ji labarin tafiyar Maryo hankalinsa ba ƙaramin ta shi ya yi ba, dukda ya san ba matarsa bace amma idan ya kalle ta tana rage masa kewar Shukransa. Yana zaune a ɗakin Me babban ɗaki ita kuma tana lallaɓewa Maryo kanta, ya zuba mata ido yana tuna irin rayuwar da suka yi da ita da abubuwan al'ajabin da ta dinga yi kafin faruwar lalurarta, murmushin yaƙe ne ya suɓuce masa yana jin kewarta a zuciyarsa. Kallon ɗan bakinta da take cunowa gaba ya yi wanda da alama zafin kitson ne ya sa take ɗan tura baki don dai babu bakin magana ne, ta shi ya yi tsam ya ƙarasa wurin Me babban ɗaki yace, "Tsohuwa wannan kitson fa takura mata yake dubi yadda goshinta duk ya fito a bari sai an jima a ci gaba." Ya faɗa yana ƙoƙarin janye Maryo. Duka ta kai masa a baya ta ce, "Matsa mini daga gabana sakarkaru idan na biye ta yarinyar nan kanta a haka zai lalace dubi don Allah yadda fuskarta ta yi kyau amma da ta bar kai kamar na maza. Dududu kitson ƙwaya nawa ne ƙwaya takwas ne fa, na ƙi na sake ta ba zan saki kannan ba sai na gama." Maleek ficewa ya yi daga ɗakin yana mita don ya ga gaban goshin ta ya yi jawur.


Lokacin da Saƙon Masarautar Adamawa ya samu Sarki Aminullah duk sai ya ji babu daɗi, dukda ya san komai muƙaddari ne amma yana jin kunyar a dawo da ita ga mariƙiyarta domin ta sha yi masa zarya amma ya ƙi bata dama. Lokaci ɗaya ya ji be kyauta ba a gefe ɗaya kuma yana fargabar irin larurar da za su yi tozali da ita wacce aka ce Maryo na ɗauke da ita.


Kwanci tashi babu wuya a wurin Allah, kwanakin da Sarki Abdallah ya ɗiba sun cika. Sun shirya tsaf daga Me babban ɗaki, Maleek, Fulani Fahima, Maryo da Sarki Abdallah su kaɗai suka shirya tafiya don Fulani Fahima cewa ta yi ba za ta tafi da autarta ba ta zauna a wurin su Fulani. Duk budurin da ake Maryo bata sani ba sai dai jikinta yana bata akwai wani wuri da suke haramar tafiya. Maleek ne ya taimaka mata ta shi ga rumfar keken dokinsu wanda aka tanadarwa Me babban ɗaki amma ta ce fur ita da Maryo za su shiga, ganin haka ya sa Maleek shima ya shiga keken dokin na su Maryo. Fulani Fahima da Sarki Abdallah a wani keken dokin daban. Keken dokin Dogarai ne a gaba da suke ɗauke ba bindigogin farauta na sassaƙen itace, saboda koda za a samu farmakin wata dabbar, sai na su Me babban ɗaki yake bin su sannan na Sarki Abdallah yake biye da na su Maryo sai kuma keken dawakai biyu a baya da suke gadin su Fulani Fahima. Tafiya suka yi me nisan gaske sai da suka shafe wuni guda da rabin rana sannan suka ƙarasa Masarautar Kano me ɗumbin albarka. Maryo tun da ta ji tafiyar ta ƙi ƙarewa jikinta ya bata wataƙila Masarautar Kano suka nufa idan kuma ba cen bane to wani wurin ne me nisan gaske.


Lokacin da suka sauka a ɓangaren Fulani Maryma suka sauka saboda duk abun Fulani Maryama tana matuƙar karrama duk wanda aka ce mata ya fito daga ɓangaren Sarki Aminullah ne, a wani ɓangaren kuma saboda ace ta fi sauran matan Sarki haba-haba da mutane ya sa take washe baki kamar wacce aka yi wa kyautar kujerar hajji. Me babban ɗaki tana riƙe da hannun Maryo har suka shiga ɗakin Fulani Maryama, shigarta ɗakin ke da wuya ta ji kanta ya yi wani irin sarawa, har sai da ta hannu ta ɗan dafe gefen kanta. Alamun zirarowar jini ta ji a hancinta, da sauri ta ɗauko ƙyallen wurin Saif ta fara gogewa. Fulani Maryama sai umarni take bayarwa ana jido kayan ciye-ciye da shaye-shaye ana direwa a gabansu. Tun da ta ƙyalla ido ta ga Maryo haka kawai ta ji gabanta na dukan uku-uku, suna haɗa ido da Maryo ta ji cikinta ya hautsine ita kuwa Maryo bata san ma me take yi ba. Ga wanda ya ga Maryo ba zai taɓa tsammanin tana da matsalar ido ba, saboda idanunta a buɗe suke tar za ta yi ta ɗan waige-waigenta kamar tana ganin abin da yake faruwa. Fulani Maryama bayan sun gaisa da su Me babban ɗaki tana son ta yi maganar Maryo tana jin tsoro ga shi ta ga sai kallonta take suna haɗa ido. Wani tsoron Maryo ne ya ɗarsu a zuciyarta haka dai ta ja bakinta ta tsuke. Inna Habi tun da ta ji shigowarsu Fulani Fahima ta kasa zaune ta kasa tsaye, daga cikin labulenta ta hango wucewar Maryo. Ta ga ta daɗa haske sosai sai dai ta ɗan rame hakan ne ya sa tsayinta ya ƙara fitowa sosai. Dabara ce ta faɗo mata don tana san ta shiga wurin Maryo ta san da zamanta a gidan tun da lokacin da Maryo ta tafi ba su koma sashen matan Sarki ba. Nakiyar da ta yi wa Fulani Maryama ta ɗauka ta nufi ɗakin bakinta ɗauke da sallama ta shiga, sai da ta ajiye musu a gabansu ta koma gefe ta fara gaishe da Me babban ɗaki. Tana shirin gaishe da Fulani Fahima suka ji an aiko da kiransu daga Fadar Sarki Aminullah. Inna Habi kallon Maryo take da mamaki duk sai ta ji ta muzanta don sun haɗa ido da Maryo ya fi a irga amma ba ta ga alamun za ta yi mata magana ba bare ta nuna ta santa. Jiki a sanyaye ta miƙe za ta fita Baiwar da ta isar da saƙon kiran ta tabbatar da ana nemansu har Inna Habi. Amsa mata suka yi sannan suka ta fice domin sanarwa da Dogarin da Sarki Aminullah ya aiko. Fulani Maryama ba ta so yadda aka ware ta ba amma ta tabbata koma meye akwai wani muhimmin abin da ya kawo su. Saboda da gama bikinsu Salman ko wata guda ba a yi ba kuma daga Fulani Fahima har Sarki Abdallah sun halarci bikin.




Gabaɗaya suka hallara a cikin fadar Sarki Aminullah, Sarki Aminullah tare da Sarki Abdallah suna kan mazauni ɗaya. Cikin fadar iya waɗannan mutanen ne kawai sai Dogarawan da suke tsaron bakin ƙofar. Sarki Aminullah ne ya buɗe zaman nasu da Addu'a sannan ya gaishe da Me babban ɗakin cikin girmamawa. Kallon Inna Habi ya yi ya kalli jama'ar wurin ɗaya bayan ɗaya yace, "Maƙasudun wannan taron kusan za mu iya cewa ke ce kika jagorance shi, shin za ki iya sanar da mu gabaɗaya domin jin ta bakinki don sauran su tabbatar daga gare ki maganarnan ta fito." Inna Habi ta share ƙwallar idonta ta ƙara sanar musu da cewar Maryo dai ba matar Maleek bace hasalima budurwa ce ko auren fari bata taɓa yi mata ba. Jinjina kai gabaɗaya suka yi saboda labarin ba sabo bane a wurinsu tun da tuni an sanar da su a baya. Sarki Abdallah ya numfasa ya kalli Inna Habi yace, "Baiwar Allah amma kin san da haka me ya sa kika bari har muka tafi da ita, yanzu da wani abu ya shiga tsakaninta da yaron nan ya kike gani lamarin zai kasance, tun da mu gabaɓaya mun san matarsa Shukra kuma duk wanda ya san Shukra idan ya ga Maryo ba zai ce ba ita bace." Inna Habi jiki a sanyaye ta gaya musu dalilinta a lokacin iƙirarin cikin jikinta da Maryo take yi na Saif da kuma yadda ta ga Maleek ya dage akan Matarsa ce, ita a ganinta idan Maleek ya tafi da Maryo ba za a fahimci cikin jikinta ba shege bane. Gabaɗaya jikinsu sanyi ya yi musamman Sarki Aminullah, Sarki Abdallah ya kuma kallonta yace, "Ma sha Allah da kika fahimci kuskurenki kuma ba ki ji tsoron komai ba kika faɗi gaskiya, don kuskure kam an yi shi amma hamdalar da za mu yi da babu wani abu da ya haɗa Maleek da Maryo tun da na tuntuɓe shi tun a gida. Amma a yanzu muna so ki sanar da mu tsakaninki da Allah ya ya Maryo take a wurinki shin ke kika haifeta ko kuma ƴar riƙo ce?" Inna Habi ta kalli Maryo ta ji soyayyar yarinyar na ƙara shiga jikinta ci gaba da cewa,




"Maryo dai ba ƴata bace hasalima babu wani dangi na Uwa ko Uba da muka haɗa da ita, sai dai Allah ya sani ina jin Maryo a cikin raina kamar ƴar da na haifa. Kamar yadda na sanar da Sarki Aminullah a baya mu fulani ne kuma fulanin tashi. Shekara goma sha biyar da suka wuce wata rana mun tafi kiwon awakai da shanun mun cikin daji, mun yi kiwo mun dawo kamar yadda muka saba a hanyar mu ta dawowa mukan tsaya a bakin wani rafi mu shayar da dabbobinmu ruwa. Mu kuma mu kan wanke jikinmu mu ɗebi wani mu zubawa jakkai su wuce mana da su gida. A ranar ma haka ina goye da Abu wacce a lokacin bata fi wata tara ba na ji fitsari ya matseni. Abu na miƙawa Goggota ta riƙe mini ita ni kuma na kewa na tsugunna domin kama ruwa, ina hanyata ta dawowa na ji kukan jaririya a bakin wata ƙatuwar bishiyar Kuka. Allah ya sani a lokacin na yi matuƙar tsorata sai dai kukan da yarinyar take yi ya sa nake ganin ba zan iya wucewa na barta a wurin ba. Jikina na rawa saboda tsoro ba ƙarasa wurin da addu'a a bakina na ɗauko ta tana ci gaba da tsanyara kuka. Na yi tsammanin ina ɗaukanta wani abun zai same ni amma sai na ji shiru, ina ɗaukata ta sa hannu a baki tana tsotsa. Da sauri na ƙarasa wurin su Goggo na nuna musu Maryo, suma ba ƙaramin tsorata suka yi ba don a nan take Goggota tace sai na mayar da ita ko ƴar aljanu ce na ɗauko. Baffa shi hana yace wannan ƴar mutane ce ta yuwu wata mara tsoron Allahn ce ta jefar da ita, kuma idan ma ƴar aljanu ce muna zuwa zai yi mata turare. Haka na rungumi Maryo muka tafi gida muka ci gaba da rayuwa na haɗa ta da Abu ina kula da su." Inna Habi ta ɗago ta kalli Maryo ta ci gaba da cewa.


"Tun ranar da na tsinci Maryo Allah ya dasa mini ƙaunarta daidai da rana ɗaya ban taɓa bambamta ta da Abu ba, hatta su kansu ba su taɓa sanin ba ciki ɗaya suka fito ba sai lokacin da wannan maganar ta Maleek da cikin Saif ta tashi. Ni na riƙe Maryo tun tana tsumma har kawo girmanta, ban da tafiyarta Adamawa Maryo taba taɓa tafiyar kwana biyu ta bar gabana ba ita da ƴar uwarta."Sarki Aminullah ya jinjina kai cikin yabawa da kyawawan haki irin na wannan baiwar Allahr, a yanzu ya daina ganin laifinta saboda dama ɗan adam tara yake be cika goma ba don haka kowanne ɗan Adam yana kuskure. Maleek jikinsa ne ya gama sanyi yanzu ya ƙara tabbatarwa da Maryo ba Shukransa bace. Inna Habi kamar ta san abin da yake ransa ta ce, "Yaro bansan wacece Shukranka ba amma da alama kana matsanancin sonta. Don Allah idan ba za ka damu ba zan so na ji a wane gari Shukranka take ka ga idan aka bincika wataƙila a gano wurin da take."


Maleek ya goge zufar da ke goshinsa yana zubar da hawaye yace, "Shukra bata da kowa sai ni, nine na zame mata Uwa da Ubanta. Kowa ya juya mata baya a lokacin da ni na kasa guje mata, Shukra ta karramani ta ceci rayuwata da ba don ita ba ta tuni ko gawata ba za a samu labarinta ba. Amma duk wannan karamcin da ta yi mini be sai da samu ko da kallon rahama ba daga ahalina. An azabtar mini da matata an baƙanta mata fiye da tunanin me tunani. Sai ga shi yanzu kowa nemanta yake a lokacin da ta yi mana nisa, wataƙila ma ta yi mana nisan da har abada ba za mu ƙara riskarta ba. Fulani Fahima ita ma hawaye take saboda tabbas sun nuna ƙyama ga Shukra sai ga shi suna nemanta ido rufe.


Maleek sai da ya sha kukansa kuma babu wanda ya hana shi saboda a lokacin da yake wannan maganar ji yake kamar an kuma soso masa da tsohon gyambon da ke cikin zuciyarsa. Share hawayensa ya yi ya ci gaba da cewa, "Shekara biyar da suka gabata a cikin garin Shanono cikin wani ƙauye me suna Rigar Arɗo..."




_LITTAFIN NAN NA KUƊI NE DA NAIRA 200 ZAKI KARANTA SHI CIKIN KWANCIYAR HANKALI, ZAKU BIYA TA WANNAN ACCOUNT ƊIN, FIRST BANK 3090957579 AISHA ADAM, ZA'A TURO DA SHAIDAR BIYA TA WANNAN LAMBAR,0706 206 2624, DAN GIRMAN ALLAH IDAN KINSAN ZAKI FITARMUN DA LITTAFI NA YAFE CINIKINKI._
[21/12/2021, 19:32] Ameera Adam🌚: 54...





"Shekara biyar baya da suka gabata a cikin garin Shanono cikin wata ruga me suna Rigar Arɗo. Rigar Arɗo riga ce me ɗauke da fulani wacce take cike da yalwar dabbobi da daga dangin shanu, awakai da tsirarun tsuntsaye. A wannan rugar muka yada zango ni da wani Baturen ingila me suna John da zo ƙasar Najeriya ya sauka a masarautarmu kasamakon akwai kyakkyawar alaƙa tsakanin Mahaifina da ɗan Sarkin ingila wanda ya kasance mahaifi a wurin John. Ya zo ƙasar akan binciken wata turɓaya wacce bincike ya nuna kasantuwarta a wancen yankin. Duk cikin masarautarmu nine wanda na bawa fannin ilimin boko muhimmanci, hasalima ni cikakken Jami'in Ɗan Sanda ne. Saɓanin ƴan uwana da suka fi karkata a harkokin da suka shafi sarauta. Zuwansa da bayyana manufar zuwansa ba ƙaramin daɗi na ji don ni mutum ne me yawan son binciken harkokin da ya shafi ilimin boko har ma da na addini. Lokacin da zai tafi wannan gari tare da shi muka tafi duk wani abu da yake yi ina ankare da shi. Lokacin da muka sauka a wannan rugar sai da muka nemi izini a wurin me garin wannan yankin, da farko Me gari be fahimci manufar John ba kuma duk cikinsu babu me jin turanci sai ni. Haka ya dinga bayani ina fassara musu, amma dukda haka be saki jiki da mu ba sai da na nuna masa tambarin masarautarmu sannan hankalinsa ya ɗan kwanta, don yana gudun abin da zai cutar da al'ummarsa. John ne ya fara yi

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login