Showing 75001 words to 78000 words out of 89213 words
Chapter 26 - Anya Baiwa Ce 2 Complete Hausa Novel By Aisha Adam.txt
da Jakadiya tuni ta kama kanta don ta lura babu alamun wasa a tattare da shi, wasa-wasa tun ana ganin Jakadiya na abu cikin hankali tana ta tona asirinsu sai abun ya fara zarce hankali domi zance take ta saki babu hankali babu fasali.
Sarki Aminullah na shirin magana kamar saukar ruwan sama sai ganin mutum suka tsidik a gabansu cikin mummunar shiga kamar goggon biri, jikinsa gabaɗaya duk gashi. Ba ƙaramin tsorata suka yi ba don har sai da wasu suka fara ja da baya, Boka Marduska ne ya bayyana da kayan tsafinsa a fusace ya nuna Fulani Maryama yace, "Kin karya sharaɗinmu da ke dama na gaya miki duk ranar da kika fito da kayan tsafinmu a idon jama'a kashinki ya bushe, rufin asirinki shine namu asararriya domin kin tozarta aljanun suke yi miki aiki a idon jama'a dole ne su ɗauki mataki a kanki ke da ƴar korarki waccen la'anniyar, hukuncinki razanarwar fatalwa har ƙarshen rayuwarki." Boka Marduska ya faɗa yana nuna Jakadiya da wani baƙin ganye, Ihu Jakadiya ta zuba ta fara tsalle tana yagar kayan jikinta tana cewa, "Wayyo! Ku taimaka mini zai kashe ni ga shi nan da wuƙa zai yanka ni wayyo!" Ganin haka ya sa Sarki Aminullah ya yi wa wasu Fadawa magana suka kama Jakadiya suka yi gidan Turu (Gidan mahaukata) da ita, Marduska ya koma wurin Fulani Maryama yace, "Ke ma na ki hukuncin zai biyo bayanki domin ba za ki ci bulus ba." Yana shirin ɓacewa Farin tsohon nan ya yi dariya yace, "Ka ɗauka kaima za ka sha a banza ne, idan maye ya manta uwar Ɗa ba za ta manta ba. Ka tuna Boka Ƙurgen tsohon Maigidanka da ka ci amanarsa a shekarun baya? Dama na ci alwashin ba zan taɓa raga maka ba kawai na baka dama ne amma tun da ka kawo kanka ka rage mini aiki." Hankalin Marduska ba ƙaramin tashi ya yi ba, yana shirin guduwa Tsohon ya hura masa wata iska yace, "Ku bishi har can makwancinsa ku hallakashi, amma ku tabbatar da kun azabtar da shi da azaba mai tsanani kafin mutuwarsa."
Tun tsohon bai gama magana ba Marduska ya fasa uwar ƙara har sai da wasu daga cikin mutanen wurin suka toshe kunnuwansu saboda rashin daɗin sautin, nan take ya ɓace daga wurin sannan Tsohon ya mayar da kallonsa wurin Sarki Aminullah yace,
"Ba zama na zo yi ba na zo tafiya da Ɗana ne tun da kuma na bayyana maka kaina da matsayina shi kenan, idan kuma kana buƙatar taimakona zan iya taimaka maka domin ka yi mino halacci ka kula mini da Ɗana yanda ya kamata." Sarki Aminullah ya sauke ajiyar zuciya yace, "Babu inda za ka tafi da shi domin tafiyarka da shi ba alkairi bane, har yanzu ina jin Salman a matsayin Ɗana saboda duk abin da ya faru ba laifinsa bane, don haka ba za ka tafi da shi ka dilmiyar da shi kamar yanda kaima ka dulmiya."Tsohon ya ƙurawa Takawa ido yace, "Ba na son mu yi rabuwar rashin daraja ina ganin girmanka karka bari na cutar da kai..."Tun bai rufe baki ba Sarki Aminullah ya katse shi da cewar,
"Babu mai cutar da wani bawa sai abin da Allah ya nufa, don haka ƙasƙantacce da kai zai iya cutar da ni ba."Nuno Sarki Aminullah ya yi da niyyar cutar da shi kamar ya sani ya yi a'uziya ya fara karatanto masa ayoyin tsari. Duk yanda Tsohon ya so cutar da Sarki ya kasa domin duk wani siddabarunsa ya kasa aiwatarwa, Salman da ke gefe a fusace ya juyo ta sokawa Tsohon ƙaho a wuya nan take Tsohon ya fara fita hayyacinsa. A fusace Sarki Aminullah ya miƙe ya wanke Salman da mari yana cewa, "Kana da hankali kuwa Salman me yake damunka?" Salman ya wurgar da ƙahon gefe yace, "Ranka shi daɗe sauran me ya rage mutumin nan idan mun barshi matsala zai zame mana musamman ni da yake so ƙarfi da yaji ya ɗauke ni, idan na barshi baƙin dajin nan zai mayar da ni." Jikin mutanen wurin ba ƙaramin sanyi ya yi hatta Fulani Maryama sai da ta ji ba daɗi domin duk lalacewar Ubansa bata taɓa tsammanin Salman zai iya kisa ba. Tsoro ne ya kamata domin gani take ita ma kamar zai dawo kanta ya hallaka ta.
Wannan abin da Salman ya yi ne ya sanyaya jikin Sarki Aminullah don haka ya sa aka ɗauke gawar Tsohon ya bada umarnin da a haƙa rami a binneshi ba tare da wanka ko sutura ba, daga ƙarshe ya warware igiyar aurensa da Fulani Maryama, Kuka ta fashe masa da shi tana dana sani da nadama domin wannan ba ƙaramin abin kunya bane a gare ta, rarrafawa ta yi wurin Fulani Zaliha ta dafa ƙafafuwanta tana cewa, "Don Allah Zaliha ki yi masa magana ya mayar dani wallahi zai ji maganarki don Allah ki yafe mini keda Saif wallahi sharrin shaiɗan ne, kuskure ne ba zan ƙara ba." Ba ƙaramin tausayi ta bawa Fulani Zaliha ba domin saki a lokacin da baka tsammace shi ba na da matuƙar zafi, Fulani Zaliha ta dafa Fulani Maryama ta ce, "Ki yi haƙuri Yaya haka Allah ya ƙaddara miki, kuma ni da Saif mun yafe miki amma kin san ba a mayar da mace a saki uku matuƙar ba wani auren ta yi ba." Kamar Mahaukayi haka ta miƙe tsaye ta ce, "Wallahi zan yi indai zai mayar da ni ko waye zan aure shi." Yanda ta ruɗe take ruwan hawaye har sai da ta ɗan karya zuciyar mutane da yawa domin kowa ya san irin soyayyar da Fulani Maryama take yi wa Sarki Aminullah. Shi kansa Salman sai ya ji ba daɗi dukda matsanancin haushinta yake ji kasancewar ta yi masa iyaka da hayewa karagar mulki, amma ko sama da ƙasa za ta haɗe baya jin zai iya barwa Saif kujerar Masarautar Kano.
Sarki Aminullah ya kalli Fulani Maryama yace, "Za mu yi miki alfarmar ci gaba da zama a cikin ɗakinki amma muddin muka lura da hatsaniya ko tashin hankali tabbas za mu ɗauki mataki a kai. Abin da kika aikata kin cancanci zuwa gidan horo amma darajar 'ya'yan dake tsakaninmu ba za mu iya aika ki ba domin idan mun yi haka kamar mun tozarta kanmu ne." Sarki Aminullah na gama faɗar haka ya kawo ƙarshen zaman taron tare ta yin nasiha mai ratsa jiki da jan kunne akan kiyaye dokokin Ubangiji. Kafin wani lokaci tuni fadar ta yi tsit kowa ya watsa cikin gida aka samu zancen tattaunawa. Masu kwashewa Fulani Maryama na yi masu yi mata addu'a suma suna yi. Kafin tashin taron sai da Sarki Aminullah ya ƙara jaddada cewar Salman na nan a matsayin Ɗansa kuma ko da wasa ya ji wani zance na ɓilla zau ɗauki mummunan mataki a kansu.
_LITTAFIN NAN NA KUƊI NE DA NAIRA 200 ZAKI KARANTA SHI CIKIN KWANCIYAR HANKALI, ZAKU BIYA TA WANNAN ACCOUNT ƊIN, FIRST BANK 3090957579 AISHA ADAM, ZA'A TURO DA SHAIDAR BIYA TA WANNAN LAMBAR,0706 206 2624, DAN GIRMAN ALLAH IDAN KINSAN ZAKI FITARMUN DA LITTAFI NA YAFE CINIKINKI_
[30/01, 10:57] Ameera Adam🌚: 71...
Masarauatar Kano.
Abin duniya goma da ashirin ne ya haɗewa Sarki Aminullah domin idan yace ba ya son Maryama ya yi ƙarya, ita ce matarsa ta fari uwar 'ya'yansa ya bata dukkan yarda amma ta rasa da me za ta saka masa sai wannan miyagun ayyukan, tabbas lamarin akwai cin zuciya, juwa ce ta fara ɗaukansa don haka ya nemi wuri ya zauna. A yanayin da yake yana buƙatar mai tausarsa ta bashi baki amma wa zai kira? Gani yake duk wacce ya kira za ta ga ya yi kiranta ne saboda abin da ya faru. Yana nan zaune Fulani Zaliha da sauran matansa suka shiga kamar sun san abin da yake ransa. Fulani Bilkisu ce ta fara magana kasancewar ita ce matarsa ta biyu ita ce babba tun da babu Fulani Maryama.
Ruwa mai sanyi ta ɗebo masa na cikin randa ta miƙa masa, bai musa mata ba ya karɓa yasha sannan ta fara da cewa,"Allah ya taimake ka ya baka yawan rai Sarki mai adalci Sarkin talakawa Sarki mai karamci da mutumci." Sai da ya sauke ajiyar zuciya sannan ya gyaɗa mata kai ta ci gaba da magana, "Allah ya taimake ka a madadina da na iyalanka baki ɗaya muna ƙara jajanta maka da baka haƙuri bisa abin da ya faru." Kamar jira yake murya a shaƙe yace, "Me na yi wa Maryama da za ta saka mini da haka?" Fulani Zaliha ta karɓe zance da cewar, "Baka yi mata komai ba! Haka zalika karka ɗora damuwa da tashin hankali a zuciyarka. Ina me bawa Sarki haƙuri domin wannan yana daga cikin shafin jarrabawarka. Allah ya gwada kai ne domin ya jarabci imaninka." Sarki Aminullah ya miƙe tsaye sai da ya yi taku biyu yace, "Tabbas haka ne kuma muna godiya ga Allah (S.W.T) akan abin da ya jarabce mu da shi." Nan suka ci gaba da bashi baki sai da suka ga ya huce sosai sannan suka yi masa sallama suka fice kowacce ta wuce sashenta.
Kwana biyu a tsakani sai ga saƙo daga Masarautar Zazzau lamarin ba ƙaramin girgiza shi ya yi ba domin banza bata kai zoma kasuwa. Bayan da Sanƙira ya gama karantawa Sarki Aminulla numfasawa ya yi ya kalli Ɗan aiken yace, "Ku bashi kyakkyawan Masauki zuwa wayewar gari." Ɗan aiken ya ɗago ya russhnar da kai ƙasa yace, "Allah ya taimake ka umarnine daga ubangidana cewar kar na kai wayewar a gari a Masarautar nan." Ƙura masa ido Sarki Aminullah ya yi yana son gano wani abu daga Bafaden amma ya gaza ganowa, Sarki Amullah ya ya kalli Sanƙira yace, "A rubutu martanin amincewa zuwansa sannan a bawa Bafaden guzuri kafin tafiyarsa." Gabaɗaya fadawa suka ruɗe da cewar, "Godiya yake Sarkin Musulunci, godiya yake Ɗantoron giwa, sikari ba ka yi farin banza ba, Sanƙira ya amsa shi ma ya yi godiya."
"Ka kwantar da hankalinka Ranka shi daɗe in sha Allahu babu abin da zai faru sai alheri, wataƙila akwai muhimmin abin da zai kawo shi amma na tabbata ba tashin hankali bane, da tashin hankali ba zai aiko da ɗan aike ba." Sarki Aminulla ya jinjina kai domin yana jin daɗin yanda kodayaushe Fulani Zaliha take ƙarfafa masa gwiwa akan abubuwa da dama, kallonta ya yi ya ji kunyar ta duk ta kamashi. Dafa kafaɗarta ya yi da hannu biyu yace, "Zaliha!" Yanda ya kira ta shi zai tabbatar maka da muhimmancin maganar da zai furta mata.
"Don Allah ki yafe mini ke da Saif domin na cutar da ku na zalince ku. Har yanzu zargin kaina nake kamar ban cancanci zama shugaban Al'umma ba tun da a tsakanin iyalina ma ban kwatanta adal..." Hannu ta sa ta rufe masa baki sai kuma ya sakar masa murmushi da cewar.
"Hakan bai kyautu daga gare ka ba domin da a ce magauta za su ji wannan kalaman naka da abin da suke buƙata ne ya samu, wani ya yi rawa ballantana Ɗan makaɗi." Waro ido waje ya yi yace, "Waye haka?"
"Wacce ta yi mini iyaka da farincikina ma yafe mata ballanta kai? Dama tun can bamu riƙe ka ba. Ɗan'adam ajizi ne ko kana nufin Allah ba zai jarrabce ka ba?" Matse mata baki ya yi yace, "Ni dai ban ce ba kar haɗani da Ubangiji." Gabaɗaya suka saka dariya Fulani Zaliha ta ce, "Ka san mene ne babban abin da ya fi faranta mini?" Sarki Aminullah ya girgiza mata kai ta ci gaba da cewa, "Da Allah ya bayyana gaskiya ina da ƙarashen numfashi, na ji daɗi da Maryama ta wanke mu dangane da kisan da ake zargin na tura Maryo ta yi maka. Tabbas wannan babban farinciki ne mun godewa Allah." Rungumota ya yi yana cewa, "Mu ajiye wannan maganar saboda kunyarta nake ji."
"Mun barta, amma fa dole a nemi maganin lalurarka domin ko ba a faɗa ba Maryama ta yi mana jirwaye mai kamar wanka, don haka tun da lalurar ta cuta bace ba za mu ci gaba da zura maka ido ba." Haɓarta ya tallaɓo da hannu biyu yace, " Fillo wai yaushe kika fitsare idonki? Mamaki nake wai yaushe Zalihata ta zama haka." Fulani Zaliha ta yi dariya ta ce, "Tun ranar da ka fitsarar da ni." Yana shirin magana Fulani Zaliha ta ci gaba da yi masa magana.
"Allah da gaske na ke a da mun ɗauka lalaurar daga Allah ce tun da har magunguna an nema ba a dace ba amma yanzu tun da mun fahimci sihiri ne mai zai hana a nemi magani tun da ai mun yi haƙuri shekara nawa muna tare a haka tun ba ma ni ba da aka cuceni, tun da ƙuruciyata ina jin na haifi Saif ko shekara uku bai yi ba ka haɗu da matsalar. Ni an ya ma ban fasa yafiyar da na yi wa Maryama ba." Ta faɗa cikin zolawa ai kuwa Sarki Aminullah mai zai yi ba dariya ba. Idan ka ga yanda yake yi wa iyalaninsa sai ka rantse ba wani mai sarauta bane. Ya dube ta yana riƙe kunnuwa sa biyu yace, "Kaina bisa wuya zan sa a nemar mini magani ko dan na wuce gori, ita kuma Maryama ba zan ce komai ba sai yanda kika ce."
Fulani Zaliha ta ce, "To a hanzarta gaskiya tun kafin na yi maka bore! Yauwa Ranka shi daɗe na ke ganin mai zai hana yaron nan akai masa matarsa ina ganin take-takensa sai hanya-hanya yake yi mini da alama wallahi matarsa yake son akai masa kawai don bai fito ya faɗa bane." Sarki Aminullah gabaɗaya ya shafa'a da zancen Saif saboda ruguntsimin da aka yi, jinjina kai ya yi yace, "Haka ne tun da yau talata mu bari ranar Juma'a ranar albarka a kai masa matarsa ina ga haka ya fi." Fulani Zalina ta amsa masa sannan ta sauya murya zuwa damuwa idonta na cikowa da hawaye ta ce, "Allah Sarki Abu ko suna wacce duniyar oho? Allah ya tsare su a duk inda suke." Gabaɗaya suka amsa da Amin, shi kansa Sarki Aminulla duk sai ya ji babu daɗi.
Fulani Zaliha da kanta ta rinƙa gyaran amarya, Maryo ba ƙaramin kunya take ji ba domin ba wani sabo ta yi da ita ba. Ba kamar Abu da take 'yar ɗakinta ba, ita kuwa Fulani Zaliha nunawa ta yi kamar ba ta lura da abin da Maryo take yi ba, Inna Habi ba ƙaramin daɗi take ji ba domin duk wanda ya ƙaunaci na ka kaima abin ka ƙaunace shi ne tana jin daɗi yanda Fulani Zaliha take ƙaunar 'yanmatan nata biyu.
Saif tun da ya ga Maryo a sashen Mahaifiyar yaje zarya shine shiga ɗauko wannan mayar da wannan, yanzu ma Fulani Zaliha na zaune tana shafawa Maryo lalle a jiki ya shiga, lallan ba ƙaramin kyau ya yi mata a jiki ba abinka da farar fata jikinta sai sheƙi yake, daga ita sai ɗaurin ƙirji saboda gyaran da take yi mata kar ya ɓata kayan jikinta. Duk zaryar da Saif yake a tsakanin sauran ɗakunan yake yi wannan karon ne ya yi shahadar kutsa kai cikin ɗakin ya wayance da ɗaukan abu. Saif yana shiga har tuntuɓe yake yi yana waigen Maryo. Gabaɗaya kunya ce ta kamata ta sunkuyar da kai ƙasa, yana shiga ɗakin ya maƙale a bango yana leƙensu jin shirun ya yi yawa ya sa Fulani Zaliha ta ce, "Idan ka ga leƙen ka zo ka wuce tun ranka bai ɓaci ba." Kamar sabon munafuki haka Saif ya wuce sumi-sumi yana sunne kai ƙasa. Yana fita Fulani Zaliha ta saki murmushi tana mamakin wai yau Saifullahinta ne zai yi mata dabara.
RANAR JUMA'A
Duk abin da ya kamata a yi na gyaran ɗaki da duk wanda ake yi wa amarya an riga da an yi wa Maryo dare kawai ake jira ya yi akai amayar ɗakin mijinta.
Tarba mai kyau Sarki Aminullah ya sa aka shiryawa baƙinsa matafiya daga ƙasar Zazzau, abinciccika aka yi kala-kala tare da tanadar kayan ciye-ciye da shaye-shaye. Sarki Muhammad Safyan shi da Yarima suka taho da ɗan wurin Fulani Zannira mai suna Umar, sai fadawansa da masu tsaronsa da masu yi masa hidima.
A fadar Sarki Aminullah aka yi musu masauki sai da suka ci suka sha kamar wani abu bai taɓa shiga tsakanin Sarakunan biyu ba, sannan Sarki Muhammad Safyan ya bada umarnin a fito da Abu da take cen cikin keken doki hannunta ɗauke da Naufal, tun da ta ji sun sauka a Masarautar Kano take jin kamar ta yi tsuntsuwa amma ina babu wannan halin saboda yanda masu tsaronta suka kafa suka tsare.
Saif yana zaune a a gefe bayan sun gaisa da su Yarima yana shirin tashi ya ga an shigo da Abu cikin wulaƙantacciyar shigar kayan Bayi. Wata irin saranda ya yi bakinsa na rawa yace, "Abu ke ce." Abu na jin haka ta fashe da wani irin kuka ta miƙa masa Naufa tana cewa, "Don Allah ka yafe mini Saif wallahi ban tabbatar da na aikata kuskure ba sai na masifu suka fara afka mini." Jikinsa na rawa ya sa hannu ya karɓi Naufal yana kallon yanda yaron ya yi wayo sosai kammaninsa dana Mahaifinsa sun ƙara fitowa.
Sarki Muhammad Safyan ne ya katse musu magana sannan suka nemi wuri suka zauna, Sarki Muhamma d Safyan ya kalli Sarki Aminullah cikin wata irin murya yace, "Aminullah ta fe na ke da muhimmiyar magana ba da wasa na zo, a baya ka san irin abin da yake tsakaninmu amma ba wannan ne a gabana ba ina san ina. Ina tafe da tuhuma a gare ka kuma ina fatan zaka bani haɗin kai domin na fi som