Showing 69001 words to 72000 words out of 89213 words

Chapter 24 - Anya Baiwa Ce 2 Complete Hausa Novel By Aisha Adam.txt

30 Nov 2024

5333

ya rame ya lalace yace, "Ka ji abin da matarka ta ce?" Saif ya motsa baki ya fara magana, "Allah ya taimake ka ban san abin da na yi mata ba da har take son na sake ta." Nan aka ci gaba da tufkawa Abu na cewa Saif ya sake shi kuma yana faɗin bai san dalilinta na sa shi yin sakin ba. Abu duk yanda aka kaɗa aka raya ta faɗi dalilinta ta ƙi domin ta san idan ta ce tana son Maryo ta auri Saif ne za su ce mata Saif zai iya auren Maryo ko da bai sake ta ba. Bayan tafka wannan mahawarar Sarki Aminullah ya sako zancen Saif da soyayyar Maryo nan take Maryo ta tsalle ta dire ta ce sam bata ƙaunarsa. Haka aka tashi daga zaman babu daɗi kowa zuciyarsa a dagule ba tare da an cimma matsaya ba.


Bayan kwana biyu da yin maganar aka wayi gari da ɓatan Abu babu ita babu jaririnta Naufal, wannan ɓatan na Abu ba ƙaramin ɗaga hankulan mutanen cikin gidan ya yi ba, musamman Saif da abin ya runcaɓe masa goma da ashirin. Tun daga ranar cin abinci ya yi ƙaura daga wurinsa, haka daga ɓangaren Inna Habi da Maryo duk sun fita hayyacinsa, haka labarin ɓatan Abu ya karaɗe cikin Masarautar gabaɗaya. Zuciyar Fulani Maryama fari ƙal don gani take wannan shi zai bata damar ganin na ta jikan ya yi rayuwarsa a matsayin Jikan Sarki na wurin Ɗa namiji. Haka rayuwa ta ci gaba da gungurawa da matsananciyar damuwar ɓatan Abu tun basa iya ci da sha har kowa ya fauwalawa Allah lamuransu suka ci gaba da rayuwa. Bayan ɓatan Abu da wasu watanni Saif ya samu Maryo a soron farko yace, "Ina mamakin yanda aka nemi baiwar nan aka rasa ina jin tsoron kar wani abin ya cutar da su." Ido ta zura masa ta ga duk ya rame sai ƙashi, lokaci ɗaya ta ji tausayinsa ya ratsa zuciyarta ta san ko ba a faɗa ba tabbas Saif yana ƙaunar Abu domin yanayi da alamunsa sun nuna. Cikin zuciyarta take ayyana, "Ya za a yi na yarda na auri wanda ya mace a ƙaunar 'Yar uwata" Ganin shirun ya yi yasa ya katse ta da cewar, "Tunanin me kike yi?"


"Ina tunanin dalilin da ya sa 'Yar uwata za ta ɓace da ƙaramin goyo ko dai ka yi mata wani abin ne ban sani ba."


Cikin suɓutar ba ki yace, "Me zan yi mata alhalin ina ƙaunarta da abin da ta haifa..." Harshensa ne ya sarƙe bisa jin nannauyar ajiyar zuciyar da ta sauke, wani irin abu ta ji ya turniƙe mata zuciyarta ta watsa masa harara ta ce, "Dama na san kana sonta ba sai ka gaya mini ba amma ba wannan na tambayeka ina tambayarka ne ko kana da masaniyar wurin da take." Gabaɗaya sai ya ji bai ji daɗi ba don bai san maganar za ta fito daga bakinsa ba, ya wayance sa cewar, "Ba ni da masaniyar wurin da take sannan don Allah ki dawowa da Salman matarsa domin ba laifinta bane."


"Tun jiya suka dawo da ita sai dai an sami matsala domin ta rasa cikin jikinta. Bana tunanin tana cikin hayyacinta saboda firgitar da ta yi." Maryo ta faɗa tana neman wucewa, da sauri ya riƙo hannunta ta tura jikin bango yana kallonta yace, "Don Allah ki taimaka min ki amshi soyayyata. Me ya sa ba za ki yi haƙuri ba ko dan kin ga na mutu a kanki?" Matsawa ta yi gefe ta ce, "Me ka yi mini da za ka ba ni haƙuri? A gaskiya ka yi haƙuri amma ni ba zan aureka ba..." Wata gigitacciyar tsawa ya buga mata yana cewa. "Wallahi sai kin aure ni." A razane ta ƙanƙame jikinta a gefe don ta gama tsorata da yanayinsa, tsugunnawa ya yi ƙasa kamar ƙaramin yaro yana rusa kuka yace, "Shi ke nan tun da ba za ki aure ni ba amma ki sani ba zan taɓa yafe miki ba matuƙar na mutu kika yi mini kuka, ki je kawai nima zan je ban taɓa tsammanin soyayya na riɗewa zuwa ƙiyayya ba. Babu komai wataƙila wannan ita ce kalar tawa jarrabawar." Yana gama maganar ya miƙe ya wuce cikin gida, a hankali ta bi bayansa jiki a sanyaye tana runtse idonta wasu shuɗaɗɗun abubuwan baya suka sake dawo mata a cikin dodon kunnenta ta ji maganganunsa na baya na yi mata amsa kuwwa.


"Wanda ya san mutumcin ƙauna baya yi mata riƙon sakainar kashi! Jikina yana bani wannan lokacin shine ƙarƙarewar numfashina! A duk bugun numfashi yana sauka tare da tsantsar ƙaunarki, iya zayyana kalaman da suke zuciyata ɓata lokaci ne. Amma Ƙaddara ta gindaye jindaɗinmu tabbas fitar ƙaddara tamkar fitar numfashi ce. Ki kula min da ajiyar da na yi a cikinka domin tabbas ina ji a jikina watarana zan dawo na karɓi a bata. Kaicon ragowar numfashina da ba zai iya aiwatar da jindaɗin rayuwarmu ba, amma na yi miki alƙawari tabbas sai na dawo na cimma sauran burina. Amma ki sani matsawar ban cimma burina ba shi kenan rayuwata babu sauran amfanin da za ta iya aiwatarwa don haka dole a koma 'yar gidan jiya." Jikinta har wani irin rawa yake sai dai tana shiga cikin gidan ta samu Fulani Zaliha ta fasa kuka Sauran Bayi na tayata a gefe guda Saif na kwance a ƙasa.






Littafi ya taho gangara har na fara missing ɗinsu😢


_LITTAFIN NAN NA KUƊI NE DA NAIRA 200 ZAKI KARANTA SHI CIKIN KWANCIYAR HANKALI, ZAKU BIYA TA WANNAN ACCOUNT ƊIN, FIRST BANK 3090957579 AISHA ADAM, ZA'A TURO DA SHAIDAR BIYA TA WANNAN LAMBAR,0706 206 2624, DAN GIRMAN ALLAH IDAN KINSAN ZAKI FITARMUN DA LITTAFI NA YAFE CINIKINKI._
[23/01, 19:35] Ameera Adam🌚: 67...




Maryo na shiga ta samu Fulani Zaliha na Jijijjiga Saifa, kafin wani lokaci tuni labarin rashin lafiyarsa ya je kunnen Sarki Aminullah. Ba a ɗauki lokaci ba ya sa aka wuce da shi asibiti.


Tuna baya...


Furzaan bai tsaya a ko'ina ba sai da ya yi tafiya mai nisan gaske sannan ya sauke a cikin kogon dutse mai ɗauke da koriyar ƙorama da ƙananan tsuntsaye, a gefe ya kwantar da Rayzuta ya ɗebi ruwa yana shafa mata a fuska. Sai bayan wani lokaci ta buɗe idonta ta sauke su a kansa, hannu ta sa ta shafo fuskarsa idonta na zubar fa hawaye. A hankali ya fara lallashinta yana goge mata hawaye har ta tsagaita da kukan, ta yunƙura a hankali ta tashi zaune. Kallonsa ta yi ta kalli wurin da suke ta ce, "Yanzu shi kenan mu biyu muka rage? Ya kashe mini matar da nake yi mata kallon Mahaifiyata, sannan shima Mahaifina na rasa shi gatana ya riga da ya ƙara..."


"Matsawar ina numfashi ba za ki yi kukan maraici ba domin ni zan maye miki gurbin Uwa da Uba. Addu'a za mu yi musu domin ta su ta riga da ta ƙare, na zaɓi mu yi rayuwa a nan ne domin na san waye Zulik ba zai taɓa barinki ba, ni kuma ina tsoron a samu akasi ya illata ki domin ke mace ce ƙarfinsa da naki ba zai taɓa zuwa ɗaya ba." Furzaan ya faɗa yana goge mata hawaye. Hancinta ne ya fara ɗigar da jini kanta na sarawa, da sauri ya sa abu ya tare yana tambayarta, "Lafiya me yake daminki? Dama kina yin haka ne ko yanzu ne abin ya same ki."


"Ban taɓa yi ba, wannan ne karo na biyu karon farko Zulik ne ya buga mini kansa nan take jini ya fara ɗiga ta hancina, sai kuma yanzu da haka kawai na wayi gari da shi." Wanke mata ya yi sannan ya ci gaba da rarrashinta har ta fara sakewa. Haka suka ci gaba da rayuwa a wurin cikin soyayya da kwanciyar hankali, satinsu guda a kogon wani lamari ya gindaya a tsakaninsu kasancewarsu Mace da Namiji. Zaune suke kowa ya yi shiru fuska ɗauke da damuwa Furzaan yace, "Don Allah ki gafarceni wallahi na rasa yanda aka yi na kasa riƙe kaina?" Hawaye ta goge ta ce, "Babu komai domin na san ba za ka taɓa cutar da ni ba." Tun daga wannan lokacin babu wani abu da ya ƙara shiga tsakaninsu, haka suka ci gaba da gudanar da rayuwarsa. Sai dai babban abin da yake damunsu lalurar fitar jini daga hancin Rayzuta (Haɓo) da yake son zame mata jiki, ganin lamarin na ƙara ci gaba ya sa ya fara yanke shawarar nema mata magani.


Bayan wata huɗu da faruwar lamarin, Rayzuta ta fahimci sauyin da take samu daga jikinta daga ƙarshe sula tabbatarwa kansu da cikin gare ta na tsawon watanni Huɗu. Ba ƙaramin murna suka yi ba haka Furzaan ya ci gaba da bata kulawa kasancewarta yau da lafiya gobe babu.


Wata rana suna zaune Furzaan yace, "Idan Allah ya sauke ki lafiya zamu fita daga kogon nan muje a ɗaura mana aure." Murmushi ta yi masa ta ce, "Allah ya kaimu amma ni mace nake son haifa." Daga can gefe suka ji an ce, "Idan har kin haife shi ko? Alƙwari na ɗaukarwa kaina ba za ki haife cikin wannan abin ba, yana gama maganar ya fara hura iska ta ko'ina daga bakinsa, nan take sai ga masu siffar Rayzuta babu adadi kowacce ɗauke da ciki kamar, kowacce daga cikinsu jiran sunansa take tana kuka, Furzaan dafe kansa ya yi cikim damuwa, wata dabara kallon ƙasa ya fara yi, inuwar muce ɗaya ya gani wannan ne ya bashi tabbacin cewar ita ce Rayzutansa, da sauri ya ruƙota jikinsa ya kalli wurin da Zulik yake yace, "Me ya sa kake koƙarin..." Maganarsa ce ta maƙale masa jin wuƙa ta huda kayan cikin, ajiyar zuciya ya sauke ya ɗago yana kallonta daga can gefe ya ji wata ta fasa ƙara tana ta taho wurinsa, wacce ta soke shi da wuƙar ce ta ja baya ta riƙiɗa zuwa siffar Zulik, sannu a hankali waɗancan suk suka ɓace, Kuka Rayzuta take tana tallafe da shi a hankali ya dafa bango hannunsa ɗaya na kan cikinsa ya zare wuƙar ya dunfari Zulik suka fara faɗa. Sai dai zubar jinin da yake yi ne ya sa ƙarfinsa ya fara jin ƙasa jini na ɗaukansa. Babu yanda ya iya yana ji yana gani ya faɗi a ƙasa, sai dai duk da haka bai ƙaraya ba yana ƙoƙarin kai wa Zulik suka da wuƙa.


Zulik na ganin haka ya fisgo Rayzuta ya maƙureta da bango, ya fara kiciniyar haike mata. Ganin haka ya sa Furzaan yunƙurawa a hankali zai tashi daga baya ya ga wasu masu siffar Zulik sun danne shi, suna soka masa makamai yana ji yana gani Zulik ya haikewa Rayzuta ban da kuka da kuruwar kiran sunansa babu abin da take yi.


Bayan da Zulik ya gama abin da zai yi ya ƙarasa gaban Furzaan yace shafa fuskarsa yace, "Ashe haka kake kwasar gara shi ya sa ka killace ta a wurin na? Abin da baka sani ba lokacin da kuka shigo wurin nan ina biye da ku. Na baku wuri ne na koma wurin boka na dominnya tsumani da kayan tsafinsa kuma ga shi buƙatata ta biya, don haka zan ɗauke na kaita a cire cikin jikinta na killace ta domin biyan buƙatar kaina." Yana gama magana Furzaan ya hamɓare shi da ƙafa har sai da ya yi baya, Rayzuta ce ta taso ta bayansa ta ɗaba masa wuƙa a kafaɗa a gigice ya ƙwallah ƙara. A fusace ya koma wurinta ya kifeta da mari ta faɗa kan cikinta. Fita ta fara yi daga hayyacinta saboda azaba Furzaan na niyyar miƙewa Zulik ya burma masa ƙaho a ciki, nan take ya faɗi fuskarsa na kallon Rayzuta, Fisgota Zulik ya yi ya sake ƙoƙarij haike mata cikin rauni Furzaan ya fara magana, "Wanda ya san mutumcin ƙauna baya yi mata riƙon sakainar kashi! Jikina yana bani wannan lokacin shine ƙarƙarewar numfashina! A duk bugun numfashi yana sauka tare da tsantsar ƙaunarki, iya zayyana kalaman da suke zuciyata ɓata lokaci ne. Amma Ƙaddara ta gindaye jindaɗinmu tabbas fitar ƙaddara tamkar fitar numfashi ce. Ki kula min da ajiyar da na yi a cikinka domin tabbas ina ji a jikina watarana zan dawo na karɓi a bata. Kaicon ragowar numfashina da ba zai iya aiwatar da jindaɗin rayuwarmu ba, amma na yi miki alƙawari tabbas sai na dawo na cimma sauran burina. Amma ki sani matsawar ban cimma burina ba shi kenan rayuwata babu sauran amfanin da za ta iya aiwatarwa don haka dole a koma 'yar gidan jiya." Rayzuta ta fashe da kuka ta fisge ta ƙarasa ta rungomo shi jikinta tana kuka sai dai tuni alƙami ya riga da ya bushe rai ya yi halinsa. Jikinta na rawa ta miƙe zuwa wurin Zulik a fusace ta cire ƙahon da ya soka wa Furzaan ta shammace shi ta soka masa a ciki, kafin ta yi wani yunƙuri ta shigar wani abu ta bayanta har sai da ya ɓullo da cikinta, nan take suka faɗi gabaɗaya kowa rai ya yi halinsa, kamar tashin iska haka masu siffar Zulik kowanne ya ɓace daga wurin, wurin ya zama sai gawarwakin Zulik, Rayzuta da Furzaan.


Wannan ne ƙarshen tarihin rayuwar su Rayzuta ta baya.


Saif sai da ya yi ku san sati guda a asibiti sannan aka sallame shi, babu laifi jikinsa ya yi kyau sai dai har wannan lolacin baya iya cin abin, ci gaban da aka samu da ya farfaɗo amma yanda yake kullin haka yake. Satinsu uku da komawa gida wata ranar laraba a ka wayi gari da matsanancin ciwon Saif, wannan karon Fulani Zaliha ta ci alwashin duk yanda za ta yi za ta taimakawa Ɗanta domin ya samu Maryo ta aure shi. Wannan karon kafin su je asibiti abin na sa ya lafa. Inna Habi na zaune a ɗaki Fulani Zaliha ta shiga, Inna Habi na shirun gaida ta Fulani Zaliha ta zube mata a kan gwiwoyinta tana roƙonta.


"Don Allah Inna ki taimaka ki shawo kan Maryo ta amince masa, shi kaɗai na mallaka shi kaɗai Ɗana Jikina ɗaya tilo shima kin ga yanda Ubangiji ya jarabce mu, Na san babu wani abu da zan iya aiwatar bayan in roƙi alfamarki na san idan kika yi mata magana za ta iya amincewa da buƙatata Don Allah ki taimaka mini kada na rasa shi." Tausayinta ba ƙaramin ratsa Inna Habi ya yi ba, ta wani fannin har kunyarta sai da ta kamata ace mace mai izza da mulki yau ita ce take russuna mata akan buƙatarta, tabbas Fulani Zaliha ta cancanci a yi mata halarci domin duk inda Ɗan halak yake Fulani Zaliha ta je wurin. Inna Habi ta ɗaga Fulani Zaliha zaune ta ce, "Ranki ya daɗe ki daina roƙona insha Allah Maryo za ta auri Saif zan yi magana da ita." Fulani Zaliha haka ta durƙasa sai zabga godiya take tana fita Inna Habi ta samu Maryo da maganar, da farko Maryo ƙin amincewa ta yi sai da Inna Habi ta yi mata nasiha mai ratsa zuciya sannan ta amince.


Lokacin da Inna Habi ta sanarwa da Fulani Zaliha ba ƙaramin farinciki suka yi ba nan take Saif ya miƙe ya take ƙafafuwansa, Wata ranar juma'a da ta zagayo aka ɗaura auren Maryo Saif a bisa sadaki dubu biyar.


(Ku san shekarun baya kuɗi daraja gare shi, dubu biyar ma sai gidan wane da wane.)


Masarautar Zazzau ɗaya ce daga cikin muhimman Masarautun gargajiya na ƙasar hausa da ma yankin Afirka ta yamma. Tarihi irin na kunne ya girmi kaka ya yi nuni cewa, Zazzau wata daɗaɗɗiyar Masarauta ce wadda ta samo asali tun ɗaruruwan shekaru da suka gabata, wato daga lokacin Jahiliyya ko kuma kafin zuwan addinin Musulinci. Tana ɗauke da manyan jarumai masana fannin ilimin addini daban-daban.


Yau typing sai da na gama ya goge wallahi sai dai ku karanta da hakuri

_LITTAFIN NAN NA KUƊI NE DA NAIRA 200 ZAKI KARANTA SHI CIKIN KWANCIYAR HANKALI, ZAKU BIYA TA WANNAN ACCOUNT ƊIN, FIRST BANK 3090957579 AISHA ADAM, ZA'A TURO DA SHAIDAR BIYA TA WANNAN LAMBAR,0706 206 2624, DAN GIRMAN ALLAH IDAN KINSAN ZAKI FITARMUN DA LITTAFI NA YAFE CINIKINKI_
[28/01, 16:01] Ameera Adam🌚: 69...




Masarautar Zazzau.


Ganin Mutumin na neman ɓata musu lokaci ya sa Saif kiran Dogarawan bakin ƙofa, jikinsu na rawa suka shiga su biyu da bulali a hannunsu, russunawa suka yi cikin girmamawa suna faɗin, "Allah ya taimaki Yarima Allah ƙarawa mai jiran gado lafiya." Saif ya dakarar da su da cewa, "Kuna ina kuka bar wannan Mahaukacin ya shigo?" Sai a lokacin suka ɗaga kai suka mayar da kansu wurin Farin Tsohon da ke tsaye, da mamaki suke kallonsa sannan ɗaya daga cikinsu yace, "Allah ya huci zuciyarka Ranka ya daɗe wallahi ba bu wanda ya wuce mu a bakin ƙofa." Tsohon na jin haka ya bushe da dariya, ba ƙaramin tsoro ya basu ba don gabaɗaya yanayinsa kamar bana ainihin bil'adam ba. Sarki Aminullah ya kallesu fuska a ɗaure yace, "Maza a fice da shi tun kafin hukunci ya sauka a kansu." Tun bai rufe baki ba suka yunƙura za su kama tsohon da sauri ya nuna su da wani mushen muzuru nan take suka yanke jiki suka faɗi jikinsu na wani irin karkarwa. Ganin haka ba ƙaramin ɗaga hankalin Sarkin Aminullah da Saif ya yi ba, Sarki Aminullah na shirin magana Tsohon ya taka gabansa yana faɗin, "Ina son ka tara mini dukkan mutanen gidan nan domin ina tafe da muhimmiyar magana amma muddin ka ƙi amincewa haka na rantse maka yanda na halakar da waɗannan bayin naka sai na halakar da mutanen gidan nan gabaɗaya."


Ganin da gaske yake ya sa Sarki Aminullah ya aika aka fara shela, ba a ɗauki lokaci ba sai ga jama'a damƙam sun cika faɗa. Sarki Aminullah fargaba ce ta kama shi domin tsohon ya fara ba shi mamaki, Tsohon na riƙe da hannun Salman kamar wani zai ƙwace shi, can

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login