Showing 33001 words to 36000 words out of 89213 words

Chapter 12 - Anya Baiwa Ce 2 Complete Hausa Novel By Aisha Adam.txt

30 Nov 2024

5348

musu bayani cikin harshen nasara ina fassara musu dukda nima ba kowanne turaci nake fahimta daga gare shi ba. "Ya kai wannan Shugaba ban zo domin cutar da mutanenka ba, na zo ne domin na yi bincike da aka tabbatar mini da cewar akwai wani taɓo a yankin afirka wanda bincike ya tabbatar da cewar a wannan yankin yake." Lokacin da Me gari ya ji haka kallo na ya yi da rashin fahimta yace, "Kai Yaro yanzu duk faɗin ƙasar nan a rasa inda za a yi bincken taɓo sai ƙasata an ya ba da wata manufa kuka zo ba?" Ganin yanayin da Me gari ya ke ciki ya sa John ya fahimci lalle akwai matsala don haka ya ciro wani ID kad ɗinsa ya miƙawa Me gari ya ci gaba, "Wannan kawai ya isa shedar da za ta tabbatar maka da babu wani abun cutarwa da muka zo da shi. Amma idan muka aikata muku wani abu duk hukuncin da ya dace ku ɗauka akanmu." A lokacin ban ji ko ɗar ba saboda na zaƙu na ga wanne irin bincike za a yo tun da hannunsa na ɗauke da wata ƙaramar na'ura da na lura yana zura ƙwayar idonsa a ciki. John ya ci gaba da bayani ina fassara musu, "Ba wani abu za mu yi ba da wannan na'urar zan haska domin gano shin wannan taɓon irin wanda muke buƙa ɗin ne ko kuma kamanceceniya ce." Ya ƙarasa magana yana curo wata ƴar ƙwalba yana nunawa Me gari yace, "A wannan ɗan muzubin zan ɗebi ƙasar daga nan zan koma ƙasa ta domin tabbatar da abin da muke bincike, idan har ita ce za ka ƙara ganin dawowarmu domin tattaunawa akan abin da ya kamata." Da ƙyar dai muka samu Me gari ya amince muka wuce cikin gari aka fara bincike-bincike. Duk wurin da muka wuce sai dai ka ga Fulani na faɗawa bukkokinsu suna ɓuya, wasu da suke ɗan jin hausa za ka ji suna faɗin, "Arna sun shigo" sakamakon ganin Baturen nan sanye da ƙananan kaya wanda hakan ya kasance baƙon lamari. Tun safe muke abu ɗaya tun ina marmarin abun har na ji na fara gajiya, haka Me gari tun yana biye da mu da Dogarawansa har suka ga ji suka juya suka barmu ni da John muna ta karakaina. Muna gabda ƙarasawa gidan Me gari bayan mu samu nasara ɗiban wani taɓo a wani ƙanƙanin rafi, Wata Matashiyar Bafulatana muka gani tana ganin mu taso daga rafin nan ta saki tulin hannunta a tsorace. Yarinya ce ƙarama don a lokacin ba ta fi shekara goma ba, tana shirin juyawa da gudu na ce, " 'Yan mata tsaya mana, ina za ki je?" Har lokacin ba ta gama sakin jiki da mu amma hakalinta ya ɗan kwanta da ta ji na yi hausa, cikin hausar da bata wadaci bakinta ba ta ce, "Hai gide mun banu, hai wannan rafin baƙin basa ɗiban ruwansa. Aradun Allah mun boɗare da ambaliyar ruwa. Ku yi ta kanku in ba haka ba shanye ku zai yi." Tana gama faɗa ta juya a guje ta koma ruga, ganin haka ya sa na fara tsorata na shiga yi wa John bayanin abin da ta sanar da ni. Ina gama yi masa bayani muka ji wata irin mahaukaciyar guɗa daga cikin ruwan har sai da muka ji kamar dodon kunnuwanmu za su doɗe. Hankali a tashe muka bazama da gudu kafin muje cikin gari tuni labari ya ba zu akan turawa sun taɓo baƙin rafi. Iska ce ta fara kaɗawa a garin tuni Fulanin yankin suka fara kaɗa shanayensu kowanne da ƴar jakarsa fatarsa a hannu. Haka zaman wannan rugar yake a duk lokacin da haka ta faru sai dai su bar cikin rugar, in ya so daga baya wasu fulanin su sai su yada zango a wurin, amma waɗannan idan suka tafi sun tafi kenan. Lokacin da muka zo wucewa ta wata bukka wannan matashiyar budurwar muka gani tana rungume da wata Dattijuwa, tana ta ƙoƙarin ɗora ta a kan amalanken Shanu. Da sauri na taimaka mata na cicciɓi Dattijuwar wanda da alama babu ƙoshin lafiya a tattare da ita. Muna ɗora ta muka jiyo hargowar tahowar ruwan da ya fara ambaliya da sauri muka iza shannun suka tafi da Dattijuwar na riƙe hannun yarinyar ƙam, John kuma ya riƙe hannuna muka dinga zabga gudu. Mun yi tafiya sosai sannan muka bar wannan rugar, sai dai babban tashin hankalin da muka gaza tsayar da wannan shanun wacce Tsohuwar nan take ciki. Suna gudu muna biye da su a baya cikin ikon Allah sai Shanun nan suka yi karo da wasu manyan bishiyoyi kamar wacce aka wurgo haka muka ga amalanken ya hantsila, sai ga wannan Baiwar Allahr ta faɗo kanta ya bugu da dutse har ya fashe. Da sauri muka ƙarasa wurinta na tallafota da sauri matashiyar budurwar ta ƙaraso da kuka tana fillaci haɗe da hausa tana jijjiga Matar, hawaye na ji a idanuna na ban tausayi ban yi aune ba na ji hannun Dattijuwar ta ruƙo hannuna tana faɗin, "Ka riƙe mini Shukura Amana don Allah. Ba ta da kowa a duniyar nan bayan ni, ni kuma da alama lokaci na ya zo don Allah ka riƙe mini ita da zuciya..." Maganarta ce ta maƙale lokacin da numfashinta ya ɗauke. Irin kukan da Shukra take yi duk wanda ya ga halin da take ciki sai ya zubar mata da ƙwallah. Da ƙyar na samu na lallashi Shukra shi kuma John yana gefe yana hawaye, nima hawayen nake yi don tun da nake a duniya ban taɓa shiga irin wannan tashin hankalin ba. A hankali na ƙarasa wurin amalanken na janyo wani zani na rufeta sannan na yi tafiya me ɗan nisa na ƙarasa wata ruga na sanar da su halin da muke ciki. Tare muka dawo da su suka taimaka aka ɗauki gawar Mahaifiyar Shukra muka ƙarasa da ita aka yi mata sutura. Kwananmu biyu a garin muka wuce cen Masarautarmu ya yinda acen hankalinsu ba ƙaramin tashi ya yi ba bisa ganin mun ɗebe kwanaki ba mu dawo ba, don har Takawa na shirin tura Dogarawa su bi sawunmu sai gamu mun koma musu a hargitse cikin tashin hankali, a gefe ɗaya kuma Shukra da babu abin da take yi sai kuka. Lokacin da muka je dana tambayi John kwalbar da ya ɗebi taɓo sai cewa ya yi she be ma san inda take ba, saboda gabaɗaya ya ruɗe ya shiga tashin hankali. A daddafe ya yi kwana ɗaya daga nan ya wuce ƙasarsu ta Ingila.


Shukra duk gidan nan babu wanda take yadda da shi sai ni, saboda gabaɗaya a tsorace take da kowa kasancewar bata saba mu'amala a irin yanayin Masarautarmu ba. Sannu a hankali na fara fuskantar yadda mutanen gidanmu suke ƙyamarta, hasalima da farko komai tayi dariya suke yi mata saboda rashin wayewarta. Ko kaɗan haka baya mini daɗi kuma na fara nuna musu hakan, sai kuma suka fara chamfata wai tun ranar da muka dawo da Shukra baƙin al'amura suke faruwa marasa daɗi. Haka nake tausarta idan na ga tana kuka na yi ta bata haƙuri, tun abun yana damunta har ya zame mata jiki. Kuma wannan tsangwamar ba wai iya Mata da ƴaƴan Sarki ba har Mahaifiyata ba a barta a baya ba wurin nuna ƙyamarta ba. Shekararta biyu a masarautarmu tuni na faɗa soyayyar Shukra wanda ita ma tuni na lura da yanayinta. Ban sha wahalar bayyana mata sirrin zuciyata ba domin ita ma ta yi zurfi a soyayyata. Ban gayawa Mahaifiyata ba saboda na san ba ƙaunar Shukra take ba bare ta bani goyon baya. Mahaifina na sanarwa da buƙatata be yi wata-wata ba ya haɗa matansa ya sanar musu tare da hukuncin juma'a me zuwa zai sa a ɗaura mana aure. Kafin ranar kuwa ba ƙaramim ƙwarbai aka yi da Mahaifiyata ga Fulani Babba na ƙara zuga ta. Juma'a me zuwa aka ɗaura aurena da Shukra kuma wani ikon Allah a ranar da aka ɗaura aurenmu ranar muka samu takarda akan rasuwar Kakata wato Mahaifiyar Mahaifiyata, kafin Mahaifiyata su gama shiri Allah ya saukar mini da wata larura wanda na yanke jiki nan take ba tare da na san abin da yake faruwa ba. A wannan lokacin tsanani a ƙaru a wurin Shukra kowa ya tashi mayya yake kiranta saboda banda maita wai babu yadda za a yi ana ɗaur aure ango ya faɗi. Haka Shukra ta ci gaba da jinyata memakon rayuwar amarci amma wannan amaryar haka ta ƙare kwanakin amarcinta wurin wanke mini fitsari da kashi tare da wani irin amai na nake yi me warin gaske. Sai da na shafe shekara guda a haka sannan Allah ya kawo mini makarin ciwon a lokacin kowa ya gaza da ni babu me zuwa wurina sai Mahaifiyata da Mahaifina, ita ma takaicin ganin Shukra na bani kulawa ya sa ta ke kwashe kwanaki ba tare da ta waiwayo ni ba, saboda duk yadda ta so a raba aurena da Shukra Takawa cewa ya yi zai tambayi Shukra idan tana son a raba auren zai raba idan kuma bata so za mu ci gaba da zama a haka har zuwa wani lokaci idan anga ciwon babu ranar warkewa sai a raba auren, kuma ana tambayar Shukra ta fashe da kuka ta ce ita abarta tana sona a haka. Lokacin da na samu Lafiya Shukra ta fi kowa farinciki a gidanmu Amma warkewata be sa ta samu sa'ida daga wurin Mutanen gidanmu ba. A cikin kwanakin nan Takawa ya sa a ka hau yi mana ƴan gyara-gyare, ba a ɗauki kwanaki ba muka tare muka ci gaba rayuwarmu cikin farinciki.


Shukra mace ce me haƙurin gaske duk irin abin da ake yi mata a gabana da bayan idona ba za ta taɓa nuna mini a fuskarta ba, muna cikin wannan yanayin da daɗi babu daɗi Shukra ta samu ciki. Nan tsanani ya ƙaru a wurinta daga wurin Mahaifiyata har wurin Fulani babba don dama a yadda na fahimta Fulani Babba ta fi tsananta mata fiye da Ummi. lokacin cikinta na da wata uku, Ummi da Fulani Babba suka sakata kwalemar ɗakunansu dukda bayin da suke cikin gidan nan amma Shukra bata gaza ba haka ta gama da ɗakin Ummi ta koma ɗakin Fulani Babba. Tana gama wannan aikin jini ya ɓalle mata a ranar ta yi ɓarin wannan cikin, shine ɓarin da ta yi har ta wuni ta kwana a sume." Maleek na zuwa nan a zancensa Sarki Abdallah ya saki salati ya kalli Fulani Fahima ta da take zabda ƙwalla yace, "Fahima ina yi miki kallon me hankali ashe kanki da saura, yanzu saboda Allah da yarinyar mutane ta mutu me za ku gayawa Ubangijinku?" Fulani Fahima ta share hawaye ta ce, "Wallahi sharrin sheɗan ne da muguwar huɗubar da Fulani Babba take yi mini." Cikin takaici Sarki Abdallah yace, "Ai shi ke nan ga shi ta bar muku duniyar sai ku ci karen ku babu babbaka. Wallahi na fara ɗora ɗan zargi akan mutuwar yarinyar saboda mutuwarta na ƙunshe da al'ajabi." Fulani Fahima ba ta tanka masa ba saboda ta san ko za ta haɗiyi Qur'ani ba za ta fita ba idan ta ce ba ita ta haddasa mutuwar ba." Maleek ya jingina da bango yana lumshe ido ya ci gaba da cewa, "Hutun da Shukra ta samu na ɗan lokacin da ta yi jinya ne amma ko sati ba ta yi da yin ɓarin ba aka koma ƴar gidan jiya. A wannan karan ne na magantu akan izayar da ake yi mata ta yi yawa, saboda tana auren ɗan Sarki amma ko wacce take auren Bawan gidanmu ta fita kwanciyar hankali. Ba'a ɗaɗe da yin ɓarinta ba ta kuma samun ciki shima cikin me matuƙar wahalarwa, don ko cikin da ta yi ɓarinsa be bata wahala kamar wannan ba. Da yake Allah ya yi cikin jikinta sai ya taka ƙasa a wannan rayuwar Allah ya sauke ta lafiya ta haifo Tagwayen ƴan biyu duk maza. Tun daga wannan lokacin Ummi ta fara sauke ƙiyayyar da take yi mata. Ganin haka ya sa na same ta a ɗaki na dinga yi mata nasiha a nan take ta nuna mini nadamarta, ba ƙaramin daɗi na ji ba don a lokacin ba ƙaramin kulawa take bawa Shukra da abin da ta haifa ba. Tun daga ranar suka fara raba gari da Fulani Babba don ba haka ta so ba. Haka rayuwa ta ci gaba da tafiya har Allah ya kaimu ranar da ba zan manta da ita ba. Kasancewata ɗaya daga cikin Jami'in Ɗan Sanda ya sa ba ko yaushe nake zaune a cikin Masarautarmu ba, don bayan haihuwar Shukra da wata biyu aka yi mini canjin aiki zuwa Ƙasar zariya. A ranar da lamarin zai kasance haka kawai jikina ya bani na koma don ganin halin da iyalina suke ciki, sai dai wani babban tashin hankali dana ruska ina zuwa na samu sashen Shukra ya ƙone ƙurmus babu abin da aka iya fitarwa a ciki. Na shiga tashin hankalin da tun da na zo duniya ban taɓa shiga ba..." Maganar Maleek ce ta maƙale sakamakon kukan da ya ci ƙarfinsa. Jikin mutanen wurin ne ya yi sanyi, Sarki Abdallah ya zubawa Fulani Fahima idanu yace, "Fahima ki gaya mini tsakaninki da Ubangijinki me kike sani game da mutuwar matar yaron nan." Fulani Fahima da hankalinta ya gama tashi ta ce, "Ranka shi daɗe wallahi ko Qur'ani zan iya dafawa akan ban da masaniya dangane da mutuwar Shukra, abin da na sani gabannin asuba ƙaurin hayaƙi ne ya farkar da ni ina fita na samu Dogarai da Bayi carko-carko a tsaye wurin ruguzajjen kuma ƙonannan ginin da su Shukra suke ciki yana ci da wuta. Wallahi wannan ne gaskiyar abin da na sani." Sarki Aminullah ya numfasa ya kalli Maleek cikin tausayawa yace, "Maleek ina fatan za ka rungumi ƙaddarar da Ubangiji ya saukar maka. Addu'a za ka yi mata Ubangiji ya jiƙansu ya gafarta musu." Fulani Fahima ta kalli yayanta ta ce, "Allah ya taimakeka don Allah idan babu damuwa a aura masa Maryo don na san hankalinsa zai kwanta da ita." Sarki Aminullah ya yi wani irin murmushi da ta kasa gane manufarsa yace, "Fahima kenan, ƙarfin mulkinmu ba shi zai bamu lasisin zartar abin da muka ga dama ba. Yarinyar nan mutum ce kamar kowa babu yadda za a yi mu aurar da ita tana cikin lalura ba tare da mun ji ra'ayinta ba. A baya mun yi kuskure kuma wannan karon ba za mu maimaita ba, za mu ci gaba da kula da ita har Allah ya bata lafiya idan ta warware sai Maleek ya nemi soyayyarta, idan ta amince da shi falillahil hamdihi idan kuma ba ta amince da shi ba, ba za mu yi mata dole ba." A firgice Inna Habi ta ɗago ta kalli Sarki Aminullah ta ce, "Allah ya taimake ka wani abun ne ya samu Maryo?" Yanayin yadda ta yi maganar za ka fahimci tana cikin tashin hankali. Nana take Me babban ɗaki ta zayyanewa Inna Habi duk abin da ya faru da Maryo. Inna Habi bata san lokacin da ta matsa da sauri ta rungume Maryo tana fashewa da wani irin kuka ba. Kamar wacce ta fahimci Inna Habi ce a jikin nan hawaye fara bin idanun Maryo tana yi tana laluben hannun Inna Habi, aikiwa tana taɓo cindon da ke gefen ƙaramin ɗan yatsan Inna Habi Maryo ta saki wani irin kuka me ban tausayi don da alama ta fahimci a jikin wacce take yanzu.


Sarki Aminullah duk yadda ya kai ga dauriya sai da ya zubar da ƙwalla, ganin suna ƙara karyar masa da zuciya yasa ya sallame su tare da Jaddada zaman Maryo a hannun Inna Habi kuma a ɓangaren Fulani Maryama.


Fulani Fahima, Me babban ɗaki, Maleek da Sarki Aminullah kwanansu ɗaya suna juya Masarautar Adamawa. Maleek da Me babban ɗaki ba ƙaramin kuka suka ci ba don duk wanda ya kalli Maleek zai ɗauka mutuwa aka yi masa, Me babban ɗaki kuwa da ƙyar aka raba su da Maryo don a lokaci ɗaya duk ta fige ta fita hayyacinta. A haka suka yi sallama suka juya masarautarsu. Labarin dawowar Maryo da lalurarta lokaci ɗaya ya karaɗe Masarautar Kano, Fulani Maryama da Jakadiya farinciki a wurinsu kamar waɗanda aka yi wa albishir da gidan aljanna. Tsafi gaskiyar me shi. Fulani Maryama haka ta dinga hurawa Jakadiya hanci tana faɗin surukullenta ne ya kama Maryo har ta na nakashe.


BAYAN WATA BAKWAI


Abu ce zaune da tulelen cikinta ta marairaicewa Saif a shagwaɓe tana faɗin, "Don Allah Abu Nouf ka taimaka ka barni na je na gano ƴar uwata, dukda ina matuƙar jin kunyarta amma tun da na ji labarin dawowarta jiya a wurin Baiwa Nafi ko baccin kirki na kasa. Wallahi ban da sukuni tun da aka ce mini ga a halin da take ciki. Ina fargabar tozali da halin da take ciki, na san Maryo ita kanta ina na a ranta don Allah ka barni na je na gano ta ko na ji daɗi." Ta ƙarasa faɗa tana zubda hawaye don Allah ya sani duk duniya mutane uku ne masu muhimmanci a rayuwarta, daga Inna Habi, Saif sai Maryo. Jiya tana kwance a ɗaki ta ji Baiwa Nafi ita da Sahu suna hirar Maryo, karaf ta tambaye su anan suka ƙara mata haske. Ranar kuwa ta sha kuka kamar me haka ta kwana tana juyi tun Saif na lallashinta har ya gaji. Kallonta Saif ya yi yace, "Ba na ce miki kar na ƙara jin maganarta a bakinki ba? Idan kin ga kin fita daga gidan sai dai idan wanka za ki je gida."




_LITTAFIN NAN NA KUƊI NE DA NAIRA 200 ZAKI KARANTA SHI CIKIN KWANCIYAR HANKALI, ZAKU BIYA TA WANNAN ACCOUNT ƊIN, FIRST BANK 3090957579 AISHA ADAM, ZA'A TURO DA SHAIDAR BIYA TA WANNAN LAMBAR,0706 206 2624, DAN GIRMAN ALLAH IDAN KINSAN ZAKI FITARMUN DA LITTAFI NA YAFE CINIKINKI._
[22/12/2021, 18:29] Ameera Adam🌚: 55...






Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login