Showing 3001 words to 6000 words out of 89213 words
Chapter 2 - Anya Baiwa Ce 2 Complete Hausa Novel By Aisha Adam.txt
yi kamar me bacci lakadan. Zama ya yi ya ɗago ta dukda yadda hannuwansa suke raɗaɗi, amma har lokacin bata buɗe ido ba, ruwa ya ɗebo ya fara yayyafa mata kamar wanda yake zubawa dutse haka ya ƙare zuba mata ruwa ba tare da ta motsa ba.
Hankali a tashe ya nufi sashen mahaifiyarsa domin ya sanar da ita halin da ake ciki, yana zuwa ya samu ana ta kokawa da Fulani Babba ta yage kayan jikinta tsaf, sai wawurar mutane take tana kai musu cizo, Mahaifiyarsa ce da sauran matan mahaifinsa ne suke ta ƙoƙarin ganin sun tura Fulani Babba ɗaki sun rufe amma abin ya ci tura. A haukace take bin su tana cewa, "Wallahi shukura ko ni ko ke sai dai mu illata juna" tana faɗin haka tana yagar naman jikinta haɗe da kaiwa mutane warta. Maleek na zuwa ba ƙaramin tashin hankali ya shiga ba mantawa ya yi da tasa damuwar da yazo da ita, cikin dabara ya samu suka hankaɗata cikin ɗaki suka rufe kowa na mayar da ajiyar zuciya. Maleek na shirin jan mahaifiyarsa domin ya tambayeta abin da yake faruwa, daga cen filin Masarautar suka ji iface-iface da koke-koken mutane wasu daga ciki suna guje-guje, ban da kururuwar mutane babu abin da yake tashi a wajen. Gaɓaɗaya suka ari na kare suka fita a guje har ragowar matan Sarki Abdallah dake tsaye carko-carko, suna fita suka yi tozali da babban tashin hankalin da ya fi wanda suka ciki a cikin gidan, da gudu kowa ya fara gudun neman ceton rai. Maleek saboda firgici bai tsaya ko ina ba sai cen ƙuryar ɗakinsu, ya maƙale a cen bayan Maryo yana sauke ajiyar zuciya. Duk wannan abin da yake faruwa Maryo na kwance tana bacci hankali kwance.
Maleek anya ka nemi maɓoye me kyau kuwa😂
Barka da hutun ƙarshen mako🥰
_LITTAFIN NAN NA KUƊI NE DA NAIRA 200 ZAKI KARANTA SHI CIKIN KWANCIYAR HANKALI, ZAKU BIYA TA WANNAN ACCOUNT ƊIN, FIRST BANK 3090957579 AISHA ADAM, ZA'A TURO DA SHAIDAR BIYA TA WANNAN LAMBAR,0706 206 2624, DAN GIRMAN ALLAH IDAN KINSAN ZAKI FITARMUN DA LITTAFI NA YAFE CINIKINKI._
[01/12/2021, 17:12] Ameera Adam🌚: ANYA BAIWA CE?
BONUS🌚
38...
Ɗan shiru ne ya biyo baya babu abin da yake ta shi sai kukan ƙananan tsuntsaye, a hankali ta ɗago da kai ta kalleshi jin shirun da ya yi yana nazari. Idan idanunta ba ƙarya suke yi mata ba tabbas ta lura da matsananciyar damuwar da ke kwance a saman fuskarsa, suna haɗa ido ya tattaro murmushin ƙarfin hali ya ɗora akan fuskarsa wanda ake kira da yaƙe kafi kuka ciwo. Murya a sanyaye ta furta, "Allah ya taimake ka dama abin da ya kawo ni kenan. Ina me roƙo da ataimaka a dubi wannan roƙon da na zo da shi." Ta ƙarasa faɗa tana gyara zaman alkyabbar da ke jikinta. Ƙura mata ido ya yi yana jin kewar matarsa sai dai ya lura a yanzu idan ya tanka mata ta samu guri kenan dan ya lura da rashin walwalar da ke kwance a saman fuskarta. Shirun da ta ji ya yi ne yasa ta ɗago ta kalleshi sai kuma ta sunkuyar da kai ƙasa dan ba za ta iya jurewa kallon sa ba, a hankali ya motsa bakinsa kamar me ciwon haƙori yace, "Babu damuwa zamu duba mu gani, in sha Allah zan kira Fahima na ji halin da ake ciki tsakaninsu da yatinyar." Miƙewa ta yi cikin girmamawa tana faɗin, "Na barka lafiya Ranka shi daɗe." Tana gama faɗa ta yi gaba ya bita da kallo har ta fice daga turakarsa, lumshe ido ya yi dan ji yake yana matukar kewar Zaliha kawai dai ya rasa dalilin da yasa ya kasa yafe mata dukda kasancewarsa mutum mai sauƙin kai da rashin riƙo.
"Maganar gaskiya Marduska na gaji wannan marmasasshen kan nawa. Ka duba ka gani fa yanzu da abin da zaka saka mana da shi kenan? Kawai daga ka buƙaci gashi sai ka aske mana kai. Ni wannan duk ba shi ya fi ɗaga mini hankali ba, tun bayan fitar gashin nan nake saka ran naji alamar wani sabo ya fara tofowa amma shiru kake ji kamar an shuka dusa. Gaskiya ka cuce mu wallahi baka taɓa ɓata mini rai kamar yau ba, duk fa saboda yarinyar nan nake wahalar banza amma ka duba ka gani na wayi gari da kai a sutale kamar bayan ludayi." Jakadiya da ke gefe sai gyaɗa kai take kamar ƙadangaruwa, ita kanta dan dai tana shakkun Marduska da tuni ta rufeshi da masifar ɗiban albarka. Marduska ƙuri ya yi da idanu yana kallon Fulani Maryama har ta gama masifar da take yi, miƙe busassun ƙafafuwansa ya yi masu kama da fusasshen itace ya ɗago ya dube ta da ƙwala-ƙwalan idanunsa masu matukar muni yace, "Maryama idan ban halakaki a nan take ba Allah ya tsine mini." Jakadiya ta dube shi a kaikace cikin zuciyarta ta ce, "Yoo dama me ya rage meye kai idan ba tsinannan ba." Ya ci gaba da cewa, "Har kya yi maganar cuta ke mutane nawa kika cuta a rayuwarki? Kuma mutane nawa kike kan cuta yanzu haka? Ko kin manta Salman ba jinin Takawa bane kike zaune da shi a matsayin ɗansa wanda a yanzu haka yana ƙudirin hallaka shi ta kowanne hali. Da kin ɗauka zan yi miki aiki a sadaka ne babu tukwici? Ahir ɗin ki da gaya mini maganar da ta zo bakinki idan ba haka ba wallahi ina iya mayar da gabanki ya koma bayanki, anan wurin da kike ina iya tsaface ki na ɓatar da ke kuma a manta da ke har tashin duniya. Idan za ki yi iskancinki ki san a inda ya dace ki yi amma ki tabbatar da kin yi na farko kin yi na ƙarshe a nan. Tun ranar da kika fara zuwa wajenmu muka sanar dake dokokinmu kika amince dan haka ki kama kanki, duk abin da kika ga ya biyo bayanki sakamakonki ne." Fulani Maryama tsoro ne ya kamata dan sai a lolacin ta fahimci wautar abin da ta aikata. Cikin nadama ta russunar da kai ta ce, "Tuba nake Marduska na yi kuskure ayi mini afuwa, ka san duk wani mai rai ajizi ne." Murmushin jindaɗi ya yi ya kalli Fulani Maryama yana hura boɗareren hancinsa kamar na botorami yace, "Fulani Maryama kenan kedai zuma ce sai da wuta. Babu komai an yafe miki amma ki kiyaye gaba, Kuma ki bar murna karenki ya kama zomo billahilazi a kodayaushe komai yana iya tashi kwaɓarki na iya yin ruwa. Bar ganin yarinyar nan ta bar masarautarku ki ɗauka zaki miƙe ƙafafuwa yadda kike so a kodayaushe nayi bincike ina ganin bala'i haɗe da tashin hankali a cikin masarautarku. Na gaya miki a wannan karan me sha da rayuwarsa sai wanda Allah ya tseratar, ina tunanin tarihi ne zai ƙara maimaita kansa sai dai wannan karan abun zai fi ƙamari da muni fiye da tunanin me tunani, ina matuƙar tausayawa Sarki Aminullah domin shi mutum ne me sanyin hali amma wani dalili daban kan iya tabbatar da wani yanayi a masarautarsa. Tabbas ƙaddara dole idan har Allah ya rubuta saukarta akan mutum, guje mata kamar gujewa mutuwa ne sai dai wataƙila tazo da sauƙi ko akasin haka. Amma bana ganin wannan ƙaddarar zata iya zuwa cikin sanyin hali ba tare da ta girgiza mazauna da wajen cikin masarautar ba. Abin da yake ƙara ɗaure mini kai ta yadda na kasa ganin daga ina wannan ƙaddarar zata soma shin Zulik ne zai fara taso da ita ko Rayzuta ko kuma mai dannaniyyar zuciya Furzaan. Lamarin tattare yake da sarƙaƙiya me ɗauke da ɓacewar tunani, ina ƙara haska miki hanya ne domin ki kwana da sanin tashin hankalin ba zai zo miki da sauƙi ba, zama bai ganki ba domin su tanadi suka yi na dubbanin shekaru ke kuma daga yanzu naki tanadin zai soma. Ki yi ƙoƙari kija Zulik a jikinki asirin bil adam a yanzu baya taɓa tasiri a jikinsu sai dai ki haɗa da kissa nafi tunanin wannan ce hanya mafi sauƙi a gare ki. Ki cusa masa soyayyar mulki da zaƙin da ke cikinsa dukda shima a haukace yake ta wannan fannin, amma hakan da zaki yi zai iya sa ki samu wani matsayi a wurinsa kamar wancen karnin. Ni da kika ganni ƙarƙari na yi miki bincike na kuma sanar da ke halin da ake ciki, domin su Rayzuta sun fi ƙarfina ba zan iya ja da su ba idan kuwa na zaƙewa lamarin halaka ni a wurinsu ba abu ne mai wuya ba." Ya ƙarasa maganar yana kafe Fulani Maryama da idanu. Jikinta ba ƙaramin sanyi ya yi ba duk tayi fiƙi-fiƙi kamar sabuwar munafuka, kamar wacce take da gyambo a baki haka ta ɗaga laɓɓanta a hankali ta ce, "Marduska a duk lokacin da na ziyarce ka maimakon ka kwantar mini da hankali sai dai akasin haka, na zo ne dan ka bani mafita amma koyaushe sai dai ka dilmiyar dani cikin tashin hankali. Ka sare mini gwiwa ta yadda nake ganin ba zan iya aiwatar da komai ba dukda zuciyata tayi tsayuwar gwamin jaki. Macece mafita akan lamarin ta ina zan fara?"Marduska ya zura hannunsa cikin wutar da ke zaɓalɓalawa kamar wacce ake watsa mata makamashi, waɗansu gwarwashi ya ɗebo guda biyu ya murje su a tafin hannunsa ya ƙura musu idanu sannan ya ɗago da kai yana sauke ajiyar zuciya kamar wanda ya yi tseren gudu yace, "Karki ki ji zafina ko kaɗan domin ba za ki fahimci amfanin zuwanki wurin nan ba sai gaba, idan har kin ɗauki shawarwarin da na baki na baya da wanda zan kuma baki a yanzu. Ni haska miki fitila nake wacce zata nusar da ke hanya me ɓillewa, shawara zan baki bansan yadda zaki ɗauke ta saboda kowacce ba lallai tayi miki daɗi ba, dan kowacce tana tafe da ƙalubale. Za ki iya fassara hakan da gaba kura baya damisa, ko kuma ki kira ta da gaba kura baya siyaƙi. Amma mafi muhimmanci a wurinki ki baje kunnuwanki domin ki ɗauki maganganun da zan sanar dake ɗaya bayan ɗaya. Nima fa bincike na yi sai kuma harsashe na bansani ba zai tabbata ko ba zai tabbata ba amma yana da kyau ki riƙe su, wataƙila Rayzuta ta dawo masarautarku wataƙila kuma ta tafi kenan dan ban ga yaƙinin juyowa masarauta a tattare da ita ba. Idan har ta dawo kiyi ƙoƙarin janta a jikinki, dukda nasan tsananin ƙiyayyar da ke tsakaninku. Ki kasance me ɓoye ƙiyayyarki a fili dangane da ita, idan ba haka Salman da kika haifa kina ji kina gani zai murɗe wuyanki har lahira. A haukace yake ya zauce akanta ta yadda baya ji bare gani akanta, duk wani abu da yake ƙoƙarin yi masa iyaka da ita yana iya hallakashi." Da sauri Fulani Maryama ta ce, "Ai tuni Maleek ya tafi da ita kuma lafiya ƙalau suke zaune.'Marduska ya ɗago jajayen idanunsa masu kama da gauta yace, "Wa yace miki suna zaune lafiya, Masarautar Adamawa na cikin ƙadamin da bil'adam bai isa ya dakatar da abin da yake faruwa ba a halin yanzu." Ya ƙarasa maganar yana nuna mata ƙwaryar dake gabansa nan take sai ga hargitsin masarautar Adamawa ya sauka aciki, shafe ganinsu ya yi sannan ya ɗago yace, "Idan kina tantama bayan ki koma ki kira ɗaya daga cikin masarautar zai sanar da ke halin da ake ciki." Fulani Maryama jiki a sanyaye kamar wacce aka zarewa laka ta ce, "Wai ba garin nake nufi ba. Na ji kace Zulik na iya hallaka kowa bayan kuma Maleek ya tafi da ita babu wani abu da ya biyo baya." murmushi Marduska ya yi har sai da ƙaton wawulon bakinsa ya bayyana sannan yace, "Ai ya san ba matarsa bace. Hasalima ya san duk tsanani babu wani abu da zai taɓa haɗata da Maleek, sai dai akwai wata ɓoyayyar alaƙa a tsakaninsu da ba kowa ne ya san da ita ba, wannan alaƙa ya sa Rayzuta ba za ta bari a cutar da shi ba abu na biyu da ya sa ba zai cutar da shi ba yaron na da riƙon ibada sosai, dan haka zai yi wuya jinnu su iya cutar da shi amma ban tabbatar ba. Abu na gaba da zan shaida miki idan har Zulik ya ƙara kawo miki ƙudurin aurenta ki goya masa ba har a samu ya mallake ta, ita kuma sai ki samu ki lallashe ta da yaudara har ta amince ta aure shi. Amma kinsan duk wannan ba zai yuwau ba har sai abu ɗaya ya tabbata." Da sauri Fulani Marayama ta ce meye shi." Marduska ya ce, "Maryama kenan. Ai duk gaggawar unguwar zoma ta bari a haihuwa kuma duk gaggawar asara ta jira samu. Kawai daga ganin hadari sai ki fara wanka da kashi?" Fulani Maryama a ɗan kunyace take faɗin, "Marduska na ƙagu ne na ji, amma ai naƙuda ga me tsohon ciki ba laifi bane?" Ya mayar mata da amsa da cewar, "Idan har cikin ya isa haihuwa ba idan kuma bakwaini ne kinga wataƙila asararsa za'ayi." Shiru ta yi tana kallon sa bata tanka masa ba dan ta san idan ta biye masa sun dinga yi kenan. Marduska ganin haka yasa ya ci gaba da cewa, "Ba za ki taɓa karya ƙadarin Rayzuta ba har Furzan wato Saif ya yi aure, idan ma bakya jan sa a jiki yanzu ki fara domin ki fahimci halin da yake ciki, na ga soyayya a ƙarƙashin zuciyarsa idan har kike cire dannaniyyar soyayyar da Zulik ya binne masa ya faɗa tarkon soyyaya, ki hanzarta goya masa baya ya yi aure muddin be yi aure ba bana tunanin zaki iya tanƙwara zuciyar Rayzuta hakan ma zai iya jawo miki allura ta tono garma. Idan kika samu zulik ya aureta wataƙila ki ci gaba da cin karenki babu babbaka, wata ƙila kuma ƙaiƙayi kan iya koma kan masheƙiya. Ku ta tashi ku tafi na yi iya yi na" Fulani Maryama zata ƙara magana ya katse ta da cewar, "Babu abin da zan kuma furtawa dangane da halin da masarautarku zata iya shiga, abu ɗaya na sani zan baku magani wannan garin ya daina zuba, dama ba komai bane kashin aljanin da yake latsar kanku ne idan kuka wanke kanku da maganin har abada bazai dawo ba, na gama magana bana buƙatar tambaya ko ƙarin bayani ku ta shi ku fice." Yana gama magana ya wurga musu wani garin magni, Jakadiya sai raba ido take Fualni Maryama na gaba tana biye da ita zugwai-zugwai kamar jela har suka fice daga kogon dutsen.
Har bayan shigar Maleek ɗaki wurin Maryo bai daina jin iface-ifacen mata da ƙananan yara ba. Wata irin haniniya dokin yake me tsoratarwa wacce iskar da ke ta shi a wurin kaɗai abar tsoro ce, har lokacin jikinsa ban da rawa babu abin da yake yi musamman idan ya tuno halin da ya riski wani mutumi a ciki wanda har lokacin bai gane fuskarsa ba sakamakon yadda jini ya wanke ta. Daga bayan ɗakinsu ya ji kukan dokin kafin ya yi wani motsi yaji ya bigi katangar ɗakinsu har sai da wani sashe na daga jikin katangar ya zube. Kamar mace haka kuka ya ƙwace masa tare da furta, "Innalillahiwa'inna'ilaihirraji'un." da sauri ya faɗa kan gadon yana dukan Maryo yana kiran sunanta musamman daya tuna abin da dokin yake yi a waje yana gudun kar ya fashe ɗakin suma ya same su ya illata su. Abin da ya faru lokacin da su Maleek suka fita suna zuwa suka samu wani baƙin doki yana hauka, bakinsa ɗauke da wani mutum ya kafa masa haƙoransa ya riƙe masa gadon bayansa yana fyaɗa shi da ƙasa ban da jini babu abin da yake zuba a fuskar mutumin, wani babban tashin hankali da ban tsoro haɗe da ban ta'ajibi duk wurin da Dokin ya taka sai ƙasar wurin ta dagargaje ta tsage tana ƙoƙarin ruftawa ciki, duk waɗanda suke tafe a hanya haka ya dinga bangaje mutane suna faɗuwa a sume wasu kuma nan take kansu yake fashewa su mutu. Haka ya ci gaba da fyaɗa mutumin bakinsa da bango, ba shiri suna ganin haka kowa ya fara yi takai-takai domin neman ɓuya. Maleek cikin tashin hankali ya fara dukan Maryo yana cewa, "Shukra! Shukra wai me yake damunki wannan wanne irin bacci ne kike yi haka ki tashi mu tafi sashen Mai martaba zai fi nan saboda da alama dokin nan yana ƙoƙarin shigowa nan." Kamar gawa haka ya janyo Maryo ta yi yaraf ban da yana jin numfashinta zai iya rantsewa da Allah gawa ce a wurin, hannu ya sa da ƙarfi ya ɗan mari gefen fuskarta yana kiranta sunanta. Tun bai ɗauke hannunsa daga kan fuskarta ba jini ya fara ɗiga daga hancinta, buɗe dararan idanuwanta tayi suna haɗa ido da sauri ya wurgar da ita tare da ja baya, sakamakon ganin fuskar baƙin dokin da ya yi ƙuru-ƙuru ciki yana buɗe baki, gefen wajen da ya mareta da wajen da ya riƙeta tuni ya fara tsattsafo da jini, haka shima daga hannuwansa da gefen wajen da jikinta ya taɓa shi nan da nan ya yi burɗinɗin tare da yin taruwar jini. Yana daga gefe yana ƙoƙarin guduwa yaji ta fara magana cikin wata irin murya me amsa amo mara daɗin saurare, "Kana yawan shiga hurumin da ba naka ba, amma ina ƙara jan kunnenka da ka tsaya matsayinka. Ina ɗaga maka ƙafa ne saboda ɓoyayyar alaƙarmu banasan taɓa rayuwarka saboda gaba nima rashinka zai sani a matsala, jini na kai komo yana wucewa ta sassan jijiyoyin cikin jiki, baka kamaci zaka masoyi na gari ba idan aka duba zunzurutun soyayya da matsayinta, ka gaggauta shiga duniya wataƙila ka iya nemarwa kanka mafita amma ba wannan ba, domin mazaunin gida baya taɓa cimma nasara da muradin zuciyarsa. Ita soyyaya a duk inda take bata ɓuya karka kasance me raunatacciyar zuciyar da wata zata nuna mata jajircewa, kayi ta gudu kamar me laluben ƙarshen