Showing 18001 words to 21000 words out of 89213 words

Chapter 7 - Anya Baiwa Ce 2 Complete Hausa Novel By Aisha Adam.txt

30 Nov 2024

5352

numfashi a tattare da ita, Fulani Fahima da sauran mutanen da ke wurin jikinsu ba ƙaramin sanyi ya yi ba, ban da hawaye babu abin da suke yi. Fulani Fahima zani ta janyo ta janye Maleek da ƙyar ta rufa mata, sannan ta aika aka sanarwa da Sarki Abdallah rasuwarta.


R I P MARYO😭


A lokacin da zanen ƙaddarar wasu take ƙarewa a lokacin wasu suke farawa, ita ƙaddara kamar inuwa ce baka taɓa guje mata. Wani ƙaddararsa haɗe take da kasada ƙarshenma kasa, haka wani yake rayuwa ba tare da cimma burinsa na duniya ba. Bakowanne buri ne ake iya cika shi ba, wani duk yadda ya kai ga cimma burinsa zanen ƙaddararsa na katange burukansa.


ALLAH SA KANKU BE KULLE DA YAWA BA😂😂😂😂😂😂 TO GAMU A WANI YANAYI ME DAƊI NE KO MARAR DAƊI CI GABAN LABARIN SHI ZAI IDAR DA HAKA, AMMA FA SAI DAI KU YI HAƘURI DA YADDA TSARIN LABARIN YAKE SABODA TAFE YAKE DA BAN TAUSAYI NA RASHIN CIKAR MURADI.


_LITTAFIN NAN NA KUƊI NE DA NAIRA 200 ZAKI KARANTA SHI CIKIN KWANCIYAR HANKALI, ZAKU BIYA TA WANNAN ACCOUNT ƊIN, FIRST BANK 3090957579 AISHA ADAM, ZA'A TURO DA SHAIDAR BIYA TA WANNAN LAMBAR,0706 206 2624, DAN GIRMAN ALLAH IDAN KINSAN ZAKI FITARMUN DA LITTAFI NA YAFE CINIKINKI._
[11/12/2021, 19:14] Ameera Adam🌚: 46...




Inna Habi zuciyarta sai harbawa take jikinta ya yi wani irin sanyi, zantukan Jakadiya ne suke yi mata yawo a zuciya. Duk lokacin da ta kai aya a mamaita maganar Jakadiya sai ta ji ƙirjinta ya buga, janye masakin lallen ta yi gefe jiki a mace don yadda take ji da ace bata gama saka lallen ba babu yadda za a yi ta ci gaba da zama a wurin.


Abu na cikin ɗaki haka kawai ta ji gabanta na faɗuwa musamman da ta tuna da Mahaifiyarta, zaro ido waje ta yi tana dafe ƙirji a fili ta ce, "Na shiga uku na! Wallahi Idan Inna ta sani na san kashe ni za ta yi. Na shiga uku." Nan take jikinta ya hau karkarwa tsoro na ci gaba da mamaye zuciyarta, ilahirin jikinta gumi yake tana fargabar haɗuwarsu da Mahaifiyarta don ta san ta aikata babban laifi domin ko da wasa bata taɓa yi mata hirar Saif ba. Ta ina ma za ta fara tun da bata manta yadda aka ƙarke da Maryo ba. Wani irin bugu ƙirjinta ya ƙara yi wanda har sai da ta yi saurin dafe zuciyarta tana jingina da bango, tunowa ta yi da cikin da ke jikin Maryo wanda take ta iƙirarin na Saif ne. Wani ƙulun baƙin ciki ne ya kamata ta a zuciyarta ta ayyana, " Kenan Saif ya taɓa sanin Maryo?" Nan take hawaye ya fara gangarowa daga idanunta, a gefe ɗaya tana jin haushin Saif da Maryo amma Maryo ta fi mugun bata haushi.


Inna Habi jikinta har rawa yake tana gama wanke lallen ta fice daga gidan ko neman izinin Fulani Maryama bata yi bi, tana shiga sashen Fulani Zaliha ta nemi iso wurin Fulani Zaliha, ba a ɗauki lokaci ba suka yi mata iso tana shiga ta same ta a zaune cikin shiga ta alfarma. Russunawa ta yi ta gaida Fulani Zaliha, ta mayar mata da murmushi tana faɗin, "Barkanki da zuwa Inna Habiba ya aiki, ya bayan saduwa?" Inna Habi da kwarjinin baiwar Allahr ya mamaye zuciyarta ta tattaro jarumta ta ce, "Ranki shi daɗe sai alheri." Fulani Zaliha ta yi mata murmushi don lokaci ɗaya ta ji matar ta kwanta mata a rai. Ɗan jim Inna Habi ta yi Fulani Zaliha ta lura da yanayin da Inna Habi take ciki kamar tana cikin damuwa, gyara zaman ta tayi ta ce, "Inna Habiba ga dai abin alheri ya haɗamu." Inna Habi gabanta ya faɗi tana addu'ar Allah a samu saɓanin magana akan abin da Jakadiya ta sanar mata da shi. Jiki a sanyaye ta ce, "Ki gafarce ni ranki shi daɗe na yi jinkirin yi miki Allah sanya alheri." Fulani Zaliha murmushi ta yi mata ta ce, "Karki damu Inna wannan ba wani abu bane, na yi matuƙar farinciki da Abu za ta kasance matar Ɗana, Allah ya biya ki da gidan Aljanna sakamakon tarbiyyar da kika bata." Idanun Inna Habi ne ya ciko da ƙwalla gabanta na ci gaba da faɗuwa ta ce, "Amin Ranki shi daɗe." Abu da ke ɗaki jin muryar Innarta ba ƙaramin ɗaga hankalinta ya yi ba, tana ta zarya a ɗaki ta ji Fulani Zaliha ta aika da akira ta.


Kamar mara gaskiya tun kafin baiwar ta shiga kiranta ta yi zaraf ta fito, ɗakin ta shiga tana sunne kai ƙasa tana zura ƙafarta ta ji ƙirjinta na bugawa. Murmushin yaƙe ta yi ta ƙarasa gefen Inna Habi tana raba ido ta ce, "Barka da zuwa Inna ran...amm... dama..." Haka ta fara inda-inda Inna ta yi murmushi ta ce, "Ba komai kawai dama na ce zan zo na yi wa Fulani Allah sanya alheri ne."


Inna Habi ta miƙe ta kuma rassunawa ta ce, "A huta lafiya ranki shi daɗe." Fulani Zaliha ta amsa mata sannan ta ce, "Abu ki tashi ki yi mata rakiya mana." Kamar wacce aka zarewa laka a jiki Abu ta miƙe ta bi bayan Inna Habi tana raba idanu, tana zuwa soro Inna Habi ta juyo ta kife ta mari kafin ta ɗago ta kuma kife ta da mari sai kuma ta rufe ta da duka tana fashewa da wani irin kuka me tsuma zuciya.


Sarki Abdallah wata tsawa ya bugawa Dogarin da ya same shi da mutuwar Maryo ya yi yana faɗin, "Yarinyar da ta bar waurin nan yanzu ita za ka ce mini ta mutu kana hauka ne?" Dogarin sunkuyar da kai ƙasa ya yi ya fara motsa baki don be san da wane yanayi zai gamsar da Sarki Abdallah ba. Ɗagowa ya yi zai yi magana Maleek ya shiga a haukace kamar mahaukaci sabon kamu, yana zuwa ya durƙushe gaban Sarki Aminullah yana kuka yana faɗin, "Wai shukra ta mutu yanzu nan fa ta fita daga wurin nan. Don Allah Ranka shi daɗe muje ka tashe ta, wallahi ba zan iya rayuwa babu ita ba." Jikin Sarki Abdallah ne ya yi sanyi don yadda ya ga Maleek tabbas babu ko tantama maganar da Dogari ya faɗa haka ne. Dafa kafaɗar Maleek ya yi yace, "Ka yi haƙuri Maleek amma duk wanda ka ga ya mutu kwanansa ne ya ƙare." Maleek ya ɗago da hawaye shaɓe-shaɓe yace, "Kwananta be ƙare ba wallahi idan muka je da kai za ka iya tashin ta." Da sauri Sarki Abdallah ya kife Maleek da mari, sai lokacin ya saita nutsuwarsa ya fasa wani irin kuka me tsuma zuciya, dan duk wanda yake cikin gidan ya san irin zallar soyayyar da yake yi wa Shukransa. Me babban ɗaki da tun shigowar Dogari tana jin saƙonsa ta fashe da kuka hankalinta na daɗa tashi. Sarki Abdallah tattaro jarunmta ya yi yana jin zuciyarsa na rauni ya kalli Dogarin yace, "A je a sanarwa da Jakadiya ta je su yi mata sutura."


Jakadiya na shiga gidan gabanta ya faɗi, fuskarta ɗauke da hawaye ya ɗaga labulen ɗakin da Maryo take kwance. A hankali ta zame zanin bayan an kawo mata ruwan da za ta wanke Maryo da shi, idanunta na sauka kan Maryo ta zaro ido cikin tashin hankali. Waɗansu irin manyan tururuwai ne suka zagaye ta masu yawan gaske, daga cikin kunnenta jini ne yake ɗiga kaɗan. A hankali tururuwar ta fara zaizaiyar ƙasar wurin da maryo take a kwance, A hankali Jakadiya ta ɗora hannunta akan hannun Maryo ta ji shi sanyi ƙalau, wata tururuwa ce ta hau saman hannun Jakadiya cikin azaba ta fasa ƙalla ta fice daga ɗakin tana kururuwan neman taimako.


A tsorace mutanen wurin kowa ya ɗiba da gudu don a tunaninsu Gawa ce ta riƙe ta, Jakadiya ban da juyi babu abin da take a tsakar gidan da ƙyar ta samu ta fisge Tururuwar da ƙarfin tsiya, sai ga shi ta haɗa da fatar wurin da ta ciza, jini ne ya fara gangarowa daga hannun Jakadiya yana ɗiga. Duk inda Jinin ya ɗiga da sauri Tururuwar za ta bi ta fara zuƙa.


BARKA DA HUTUN ƘARSHEN MAKO🥰




_LITTAFIN NAN NA KUƊI NE DA NAIRA 200 ZAKI KARANTA SHI CIKIN KWANCIYAR HANKALI, ZAKU BIYA TA WANNAN ACCOUNT ƊIN, FIRST BANK 3090957579 AISHA ADAM, ZA'A TURO DA SHAIDAR BIYA TA WANNAN LAMBAR,0706 206 2624, DAN GIRMAN ALLAH IDAN KINSAN ZAKI FITARMUN DA LITTAFI NA YAFE CINIKINKI._
[12/12/2021, 19:34] Ameera Adam🌚: 47....




Jakadiya tsaye ta yi cikin tsoro tana kallon ikon Allah saboda abu ne da bata taɓa ganin irinsa ba. Ganin Jakadiya a tsaitsaye yasa Sauran matan Sarki Abdallah leƙowa suna ganin abin da yake faruwa, ɗaya bayan ɗaya haka suka fara fitowa suna kalon hannunta da yake ɗigar da Jini, sannu suka fara yi mata suna tambayar ba a sin abin da yake faruwa. Nuna musu turuwar ta yi cikin haki ta ce, "Turuwa ce ta zagaye gawar, kinga wannan ita ta maƙale mini a hannu dubbi yadda hannun ya yi." Dafe ƙirji suka yi cikin ta'ajibi kowa tsoro ya kama shi. Fulani Fahima ce ta yi namijin ƙoƙarin cewa, "Jakadiya mu shiga mu gani mu biyu ko zamu iya sai a sauyawa gawar wurin kwanciya." Jakadiya ta yi tsalle gefe ta ce, "Allah ya taimakeki ni dai tun da muke da ke ban taɓa yi miki musu ba amma maganar gaskiya ba zan iya tunkarar gawar nan ba, don ni kaɗai na san halin da na shiga lokacin da Tururuwar nan ta hau kan hannuna." Fulani Fahima bata tankawa Jakadiya ta kalli wasu Bayinta mata biyu ta buga musu tsawa tana nuna musu ɗakin, jikinsu banda rawa babu abin da yake yi, haka suka ɗafa labulen ɗakin suka fara tozali da wannan tururuwar don ta yanzu har ta fi ta lokacin da Jakadiya ta shi ga rawa. Fulani Fahima dakatar da su sannan ta umarci da ɗauko fiya-fiya. Tana nan tsaye suka dawo da fiya-fiyan ta karɓa ta fara yarfawa, Maryo ce ta ɗago da hannunta wanda Furzaan ya taɓa saka mata zobe ta fara girgizawa alamar a'a. Da sauri duk suka ja ba Fulani Faliha saki kwalbar kalanzir ɗin ta faɗi ƙasa, a zabure Maryo ta ɗago da kai idanunta a rufe hanci da bakinta na ɗigar da Jini cikin ƙaraji ta ce, "Na gaya muku ku bari." Kalanzir ɗin na fara taɓa Tururuwar ta fara tashi sama kamar fari tana yo wa kan su Fulani Fahima."


Cikin tashin hankali suka fice daga ɗakin a fice, kafin futarsu Wata turuwa ta maƙalewa Fulani Fahima a ƙafa, fara kuka ta yi saboda azaba Bayinta tuni suka fice a guje Jakadiya ta faɗa Turakar Sarki Abdallah ba tare da ta sani ba. Da ƙyar Fulani Fahima ta fisge Turuwar ta ɗauki kujera ƴar tsugunno ta makawa Tururuwar amma wani abun mamaki sai ji ta yi kamar ta makawa Dutse, Kamar mutum haka Tururuwar ta juya tana kallonta sannan ta koma ɗakin ta Maryo take.


Fulani Fahima ɗingisawa ta yi ta fice daga sashen tana fita harabar gidan babu kowa sai wani Dogari, aikensa ta yi wurin Sarki Abdallah ta sanar da shi ya gaya masa duk abin da yake faruwa. Lokacin da saƙon ya isa kunnen Sarki Abdallah da sauri ya fito ya nufo sashen yana tafe Me babban ɗaki da Maleek na biye da shi, ganin Sarki Abdallah kamar baya saurin da ya kamata ya sa yasa Maleek zubawa a guje ya shige ciki.


Maleek na shiga be tsaya tambaya ba ya faɗa ɗakin, kwance ya samu Maryo kamar gawa babu alamar numfashi a jikinta, zubewa ya yi a wurin yana wani irin kuka me tsuma zuciya yana faɗin, "Shukra don Allah karki tafi ki barni, meye wannan nake gani baibaye da jikinki..." Be ƙarasa faɗa ba Fulani Fahima ta leƙa ta ce, "Kai Maleek maza ka fito kar turuwarnan ta illata ka. Wannan ba Tururuwar gaske ba ce wallahi sai dai da wata a ƙasa." Wata Baiwa da ke gefe ƙasa-ƙasa cikin gulma ta ce, "Wa ya sani ko zalinci da ta yi wa wasu ne yaje bibiyarta tun kafin kabarinta." Tana rufe baki suka ji ta fasa ihu tana birgima a wurin. Maleek Kallon Mahaifiyarsa cikin Kuka yace, "Ummi da na yi rayuwa babu Shukra gara nima na bita ko me Tururuwar nan za ta yi mini zan jure." Kamar waɗanda ya faɗa akan kunnensa haka Tururuwar ta fara zagaye shi suka fara hawa jikinsa, tun yana runtsa ido saboda azaba har ya fara zubda ƙwalla, sannu a hankali Jikinsa ya fara ɗigar da jini a duk wuraren da Tururuwar ta cije shi.




_LITTAFIN NAN NA KUƊI NE DA NAIRA 200 ZAKI KARANTA SHI CIKIN KWANCIYAR HANKALI, ZAKU BIYA TA WANNAN ACCOUNT ƊIN, FIRST BANK 3090957579 AISHA ADAM, ZA'A TURO DA SHAIDAR BIYA TA WANNAN LAMBAR,0706 206 2624, DAN GIRMAN ALLAH IDAN KINSAN ZAKI FITARMUN DA LITTAFI NA YAFE CINIKINKI._
[13/12/2021, 19:22] Ameera Adam🌚: 48...



Abu bata yi wani yunƙurin hana Inna Habi dukan da take mata ba, kuka take tun ƙarfinta tana durƙshe a wurin. Inna Habi sai da ta daketa har ta gaji sannan ta rabu da ita, jin shiru Inna Habi ta daina dukanta yasa ta ɗago ta kalli Inna Habi idanunta sun yi jawur, Inna Habi ta share hawayen fuskarta cikin takaici ta fara magana, "Abu tir da halinki ace wai kina soyayya da wani ni a matsayina na mahaifiyarki har ban sani ba, wani abun takaici wai har a saka miki ranar aure ina Mahaifiyarki ban samu wannan matsayin ba. Na gode da kike watsar da mutumci na, kwaɗayi dai mabuɗin wahala ne na tabbata kwaɗayin mulki da ƙyale-ƙyalen duniya ne ya kwashe ki, amma ke da kanki kin san kwaɗayi mabuɗin wahala ne. Amma tun da rayuwar da kika zaɓawa kanki kenan, ki je kiyi amma ban taɓa tsammanin za ki iya auren mutumin da ƴar uwarki take mutuwar sonsa ba, kin bani kunya Abu kin ci amanar ƴar uwarki sam ban taɓa tsammamin haka daga gare ki ba, na ɗauka za ki taya Maryo kishin abin da take so ashe ba haka bane? Na gode wa Allah da Allah ya sa ke ma be yi miko irin na ƴar uwarki ba." Inna Habi ta share ƙwallah cikin takaici ta ci gaba da cewa, "Ban san ta ina na gazawa tarbiyyarku ba, ban san ta ɓangaren da na samu naƙasu a harkar tarbiyyarku ba. Allah ya gani na baku tarbiyya daidai gwargwado, amma daga ƙarshe gabaɗaya ke da ƴar uwarki kuka watsa mini ƙasa a ido." Inna Habi na gama faɗa ta juya za ta fita da sauri Abu ta riƙo zaninta cikin kuka ta fara faɗin, "Inna don Allah ki yi haƙuri tabbas ban kyauta ba amma wallahi nima ban san da sanya ranar ba sai jiya, kuma an hanani shiga sashen Fulani Maryama. Amma Inna ni kaina ina ji a zuciyata ban kyautawa Maryo ba, sai dai ni kaina ban san lokacin da na faɗa soyayyarsa ba. Ina yi masa soyayyar da ni kaina ban san ya aka yi na afka ba, don Allah ki taya ni da Addu'a Inna Allah ya cire mini shi a zuciyata amma..." Bata ƙarasa faɗa ba Inna Habi ta fisge haɗe da hankaɗeta gefe ta ce, "Lokacin da kika fahimci haka kin yi shawara da ni, kije Abu tun da haka kika zaɓarwa kanki ni nawa ido ne Allah sanya alheri." Tana gama faɗa ta fice daga soron gidan, Abu durƙushewa ta yi tana wani irin kuka me tsuma zuciya don har ga Allah bata jin za ta iya rabuwa da Saif a wannan lokacin da take jin ba za ta iya rabuwa da wani Namijin ba bayan shi. A gefe ɗaya tana jin maganganun Inna na ci gaba da tururi a zuciyarta saboda zafin da suka yi mata, wannan shi ake kira da gaba kura baya siyaƙi tabbas ta lura da Inna Habi ta kai ƙololuwar ɓacin rai amma don ta san Inna ba macece me saurin fushi ba, amma idan ta yi fushi da abu kafin ta huce aiki ne.


Ganin yadda jikin Maleek yake yi ba ƙaramin ɗagawa Fulani Fahima ya yi ba, kuka take ta shiga ɗakin tana janshi amma yana zaune kamar wanda aka ɗaure a wurin. Ana cikin wannan yanayin Sarki Abdallah ya shiga saboda labarin lamarin ya ishi kunnensa tun lokacin da Maleek ya shiga ɗakin da Maryo take, Me babban ɗaki ban da kuka babu abin da take yi donma an hanata shiga amma sau uku tana dumfarar ɗakin suna janyeta, Sarki Abdallah ba ƙaramin tashin hankali ya shiga ba ganin halin da su Maleek suke ciki, da sauri ya juyo ya bada umarnin kiran masu magani daga sassan wurare dake cikin garin Adamawa cikin gaggawa, tun da ya samu labarin Maryo bata mutu ba amma kuma tana cikin wani irin yanayi. Ba a ɗauki lokaci ba masu magani suka dinga zuwa suna gwada fikirarsu amma kowanne da Tururuwa ɗaya ta maƙale masa zai fice da gudu yana kuruwa ko waige baya yi. Maleek tun yana cikin hayyacinsa har ya daina gane abin da yake faruwa saboda galabaita. Haka masu magunguna suka dinga yi wasu ko ɗakin basa shiga suna ji ƴan uwansu masu magani sun fasa ihu za su fita suma a guje. Sarki Abdallah da Fulani Fahima haka suka fara cire tsammani da Maleek don Tururuwar gabaɗaya ta yanyame jikinsa, ko motsin kirki baya yi. Suna nan tsaye wani sarkin Maharba Me magani ya shigo, ɗan Dattijo ne hannunsa ɗauke da Jakar fatar Damisa, Sarkin Maharba ne shine shugabansu a wannan nahiyar.


Yana ɗaga labulen ɗakin ya yi tozali da abin da yake faruwa, ƙurawa tururuwar Ido ya yi ya taka a hankali ya shiga ɗakin ya ɗauki Tururuwa ɗaya ya ɗora akan tafin hannunsa, duk tsananin zafin da yake ji a saman hannunsa be hanashi ƙurawa Tururuwar idanu ba, da

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login