Showing 48001 words to 51000 words out of 89213 words
Chapter 17 - Anya Baiwa Ce 2 Complete Hausa Novel By Aisha Adam.txt
domin shafar abin da ke cikinta amma tausayin Safiyya ya hanashi aiwatar da abin da ya yi niyya.
Ba a ɗauki lokaci ba Likitoci suka shi ga bawa Abu agajin gaggawa, sun shafe lokaci akanta sannan suka samu nasara ceto rayuwarta. Ba ƙaramin galabaita ta yi ba fuskarta ta yi fayau ga wani haske bau da ta yi na zubar jinin da ta yi daga jikinta. Maryo ba ƙaramin kuka ta ci ba lokacin da ta yi tozali da halin da ƴar uwarta take ciki, Inna Habi ce ta dinga lallashin Maryo don tana tsoron kar ciwon Maryo ya ta shi su rafke mata gabaɗaya. Ba a barin kowa na shiga wurin Abu saboda Likitoci sun yi mata allurar bacci tana buƙatar hutu ita da abin da yake cikinta. Donma suna tsoron yi mata aiki a halin da take ciki da aiki za su yi mata su ciro abin da yake cikinta. Amma a hakanma idan ta samu lafiya za su yi mata aiki a cire yaron cikinta.
Maryo na zaune a harabar Asibitin Inna Habi na tafi kama ruwa a banɗaki, Saif ne ya ƙarasa wurinta cikin shiga ta alfarma wacce da ka gani babu ko tantama za ka tabbatar da cewa jinin sarauta ne ne a cikinta. Takunsa kaɗai abin kallo ne me ɗauke da ɗaukan hankalin me jin da kallonsa. Yana ƙarasawa wurinta ƙamshinsa ya doki hancinta, gabanta ne ya yi mummunan faɗuwa, a hankali ta lumshe idanu wata irin ƙaunarsa na ƙara fisgarta. A hankali ta fara motsa bakinta tana faɗin, "Ya hayyu ya ƙayyimu!" Saboda ita kaɗai ce kalmar da za ta iya furtawa don samun sauƙin abin da take ji a cikin zuciyarta. Bakinsa ɗauke da sallama ya tsaya a wurinta yana ƙare mata kallo, lokaci ɗaya ya ga ta zabge ta faɗa. Ciki-ciki ta amsa masa tana ƙoƙarin barin wurin, sa sauri ya sha gabanta yana faɗin,
"Ya me jiki!" Haka kawai ta ji haushin tambayar da ya yi mata amma babu yadda ta iya ta furta masa, "Da sauƙi!" Tana ƙoƙarin bi ta gefensa ya sake shan gabanta yana cewa, "Don Allah ki saurare ni Maryo. Wallahi ban auri Abu don wata manufa ba, ke nake so ke nake ƙauna bana jin akwai wata ƴa mace da za ta maye gurbinki. Ki yarda da ni aurena da Ƴar uwarki Ƙaddara ce ta tsananin rabo. Allah ne shaidata sam ban san yadda lamarin ya kasance ba, amma ko a yanzu a shirye nake na aure ki tun da ba ciki ɗaya kuka fito da ita ba..." Da sauri ta ɗaga masa hannu fuskarta a murtuke babu annuri a ƙasan zuciyarta wutar ƙaunarsa na ƙara ruruwa, idanunta ne ya ciko da ƙwallah ta dube shi ido cikin ido ta ce, "Saif!" Yadda ta ambaci sunansa kaɗai sai da ya razana ƴan hanjin cikinsa, kamar me ciwon haƙori haka ya amsa mata sannan ta ɗora da cewar,
"Na rufe babin soyayyarka tun lokacin dana gano Ƴar uwata kake aure, ko kaɗan babu soyayyarka a zuciyata. Wallahi ko mazan duniya sun ƙare ba zan aure ka ba Saif." A haukace ya buga mata tsawa yana faɗin, "Kin san me kike faɗa kuwa?" Ita ma a ɗan tsawace ta ce, "Ka ɗauka hauka nake yi? Ina cikin hankalina Saif na gaya maka bana son ka bana ƙaunarka kuma wallahi ba zan aure ka ba. Muddin ka saki ƴar uwata ko ka wulaƙanta wallahi zan baka mamaki, amma na yi maka alƙawarin ba zan aure ka ba sai dai idan gawata za ka aura ba ni ba..." Bata rufe baki ba Saif ya ɗauke da mari yana faɗin, "Baki da hankali ne kin san me kike faɗa kuwa?"
Kuka ne ya kwacewa Maryo ta tsugunna tana fashewa da wani irin kuka me tsuma zuciya, jikin Saif ne ya yi sanyi wata irin nadama ta kamashi, kwantar da murya ya yi ya tsugunna a wurinta yana miƙa mata farin hankicif ɗin hannunsa. Kallonsa ta yi zuciyarta na fisgarta akan ta amshi ƙyallen amma bata jin za ta iya karɓa saboda yadda zuciyarta take jin raɗaɗi akansa, kallonsa ta yi cikin kuka ta ce, "Me ya sa mafi yawancin lokuta Maza kun fiye san kanku ne, me ye laifina don na ce zan nemi zaɓin raina na aura. Me ya sa za ka hanani farincikina bayan kai ka auri zaɓin ranka, ko me za ka yi mini wallahi ba zan aure ka ba Saif. Babu yadda za a yi na auri mijin Ƴar uwar da nake jin ta har cikin jinin jikina, wane irin kallo mutane za su yi mini, ita kanta wane irin kallo za ta yi mini." Hannuwanta biyu ta haɗa alamu roƙo ta ci gaba da cewa, "Don Allah ka fita daga rayuwata, ka tsaya a matsayin Mijin Ƴar uwa zan ci gaba da baka girmanka na mijin Yayata amma muddin ka nemi wuce gona da iri za ka sha mamakina."
🥺 ANA WATA GA WATA😢
_LITTAFIN NAN NA KUƊI NE DA NAIRA 200 ZAKI KARANTA SHI CIKIN KWANCIYAR HANKALI, ZAKU BIYA TA WANNAN ACCOUNT ƊIN, FIRST BANK 3090957579 AISHA ADAM, ZA'A TURO DA SHAIDAR BIYA TA WANNAN LAMBAR,0706 206 2624, DAN GIRMAN ALLAH IDAN KINSAN ZAKI FITARMUN DA LITTAFI NA YAFE CINIKINKI._
[08/01, 19:21] Ameera Adam🌚: 59...
Idanu kawai ya zurawa Maryo yana jin kowacce kalma daga cikin bakinta na sauka a dodon kunnensa, duk kalma ɗaya ji yake tamkar ana buga masa guduma a tsakar ka. Samun kansa ya yi da kasa furta mata koda da kalma ɗaya ne domin zantukanta sun gama kashe gaɓɓan jikinsa ta yadda ƙafafuwansa ma Jansu yake ba tare da yana iya ɗaga su yadda ya kamata ba. Ikon Allah ne ya kai Saif gida yana shiga ɗaki ya faɗa kan gado kamar mace sai haka ya fashe da kuka me tsanani. Tun da yake a rayuwa waɗannan kalaman ne mafi muni da ya taɓa riska a rayuwarsa, tashi ya yi ya zauna ya zuba uban tagumi a fili a fara surutai kamar zautacce, "Me ya sa za ki guje ni a lokacin da nake da buƙatarki? Me ya sa ba za ki fahimci tasirin ƙaddara da faruwarta ba? Ke kaɗai nake so ke kaɗai nake ƙauna ba zan taɓa iya haɗa soyayyarki da wata ba. Don Allah ki ceci rayuwata kar ki bari magauta su yi mana dariya." Daga bakin ƙofa ya ji an ƙyaƙyace da dariya Salman ne ya ɗaga labulen ƙofar yana ci gaba da dariyar rainin hankali sannan yace, "Dariya kuma sai dai kar a kuma. Na gaya maka na raba ka da ita har abada ba za ta dawo gare ka ba, me zai hana ka nemi wasu ƴan matan ka aura kake wahalar da kanka a banza? Wannan shawara ce nake baka ka taimaki kanka ka sanawa kanka salama amma ina tunanin kafi kowa sanin irin kafiya da tsayawa akan magana ɗayanta." Saif murmushi ya saki yana tafa hannuwa sannan ya tsagaita ya kalli Salman da kallon ƙiyayya sannan yace, "Idan har baka manta da Kafiya da tsayawa akan magana ɗayanta ba, be kyauta ace ka amanta da tsantsar kiyayyar da take yi maka ba, kada ka manta kaine ka kashe mata mahaifi, ka kashe mace mafi muhimmanci a rayuwarta kana tunanin duk wanda aka yi wa wannan ɗanyan aikin akwi wata ƙauna ko soyayya da zai nunawa wanda ya aika masa haka?"
Saif ya karka kai gefe yana murmushin ƙeta yace, "Tabbas na san ka fi kowa sanin wane ne ni, bana cin alwashi a banza don haka ka yi taka tsantsan." Yana gama faɗin haka ya fice daga gidan, bakin ciki ne ya turniƙe Salman ya shiga kaiwa da kawowa domin neman mafita. Kamar wanda aka ɗanawa wuta haka ya zabura ya fice, zuwa ya samu Bafade Sama'ila a gaggauce ya same shi ya bashi saƙo wurin Maryo don yadda yake jin jiri na ɗibansa zau iya faɗuwa kafin ya koma asibitin.
"Sama'ila ka saurare da kyau bana san ka yi mini jinkiri a yanzu nake son kaje ka samu..." Ganin saƙon duk bata lokaci ne ya sa ya katse maganar da yake yi wa Bafade Sama'ila yana cewa, "Jeka kawai na fasa aiken." Kallonsa suka yi da tausayi lokacin da ya juya zai koma don duk wanda ya kalli Saif ya san yana cikin matsananciyar damuwa. A taunaninsu ciwon da Matarsa ne ya sa shi birkecewa sai dai abin ne ya haɗe masa goma da ashirin.
Lokacin da Inna Habi ta dawo fuskar Maryo ta yi jawur duk wanda ya ganta sai ya gane taci kuka ta more. Inna Habi na ganinta ta ji babu daɗi zama ta yi a kusa da ita tana faɗin, "Dukda ba za ki gaya mini damuwar zuciyarki ba amma zai fi kyau a kodayaushe ki dinga ambaton Allah a zuciyarki, in sha Allah, Allah zai kawo miki mafita. Idan kuma ciwon ƴat uwarki ne Addu'a ita ce mafita ba kuka ba." Maryo gyaɗa kai ta yi tana goge hawayen idonta. Suna nan zaune guguwar iska ta fara kaɗawa sannu a hankali ta hango wani katon Jangwalagwada ya nufi ɗakin da Abu take kwance, jikinta har rawa yake da sauri ta tashi da gudu ta nufi ɗakin. Tana shiga ta ga ya tunkari wurin da Abu take kwance. Tsawa ta buga masa nan take ya tsaya tsam wuri ɗaya, A daidai lokacin ne Inna Habi ta ƙaraso wurin, Maryo ta so ta ce ya koma wurin da aka turo shi amma ta san muddin ta yi haka kwanciyar hankali ƙaura zai yi daga jikin Innar tasu. Ɗan kwalin kanta ta cire ta fara kaɗa shi tana faɗin, "Idan ka sake dawowa ni da kai ne." Kamar me jin abin da ake faɗa haka Ƙadangaren nan ya nufi har waje ya fice, da sauri Inna Habi ta matsa da mamaki tana faɗin, "Ikon Allah! Maryo me zai shigo da Ƙadangare ɗakin nan." Maryo ta yi yaƙe tana cewa, "Inna wataƙila guguwar nan ce ta gigita shi ya rasa wurin zuwa shi ya sa ya yo nan." Inna Habi zuciyarta ɗaya ta amince da abin da Maryo ta gaya mata bisa suɓutar baki Maryo ta ce, "Lallai kin ki magaryar tuƙewa a wannan karon zab nuna miki ba a taɓa mini ƴar uwa a kwana lafiya." Inna Habi da bata ji kalaman Maryo sosai ba ta ce, "Magana kike Maryo?" Maryo ta wayance da cewar, "A'a Inna muje kar Likitoci su shigo su same mu a ciki."nan take suka fice daga ɗakin.
Suna gabda fitowa Uwar Bayi ta ƙaraso tana tambayarsu, "Na dawo daga bakin Asibiti aka ce mini kun shigo ko sun bari a shiga wurinta ne?" Inna Habi ce ta yi mata bayanin abin da ya kai su ɗakin sai ta yi jim kamar me nazari sannan ta ce, "Allah ya kyauta." Suna yin gaba Maryo ta waiga ta kalli bakin ƙofar nan take wasu Maguna guda biyu suka ratso daga jikin bango suka shiga ɗakin da Abu take kwance. Maryo sallama ta yi wa Inna Habi akan za ta je gida ta canja kaya, haka kawai Inna Habi ta ƙi aminta da abin da Maryo ta gaya mata, don ta san wace ce Maryo da maƙo babu yadda za ayi Abu na cikin wannan halin har ta iya komawa gida canja kaya, ta barwa zuciyarta akwai abin da Maryo za ta koma yi gida ba dai canza kaya ba. Amma bata tanka mata komai ba har ta isa ƙofar asibitin Idon Inna Habi na kanta har ta fice daga harabar asibtin. Maryo na gabda fita suka yi kaciɓus da Saif tsayawa ya yi a gabanta, za ta bi ta gefensa yace, "Ina za ki?" bata kalle shi ba ta furta, "Gida!"
"Kin san akwia hatsari dangane da barinki asibitin nan." Saif ya faɗa yana zuba mata idanu. "Shi ya sa nake son zuwa na yi wa tufkar hanci." Maryo ta faɗa tana yin gaba. Juyawa ya yi yace, "Wannan me sauƙi ce zan ji da ita." Sai da ta waigo ta yi masa kallon tsaf sannan ta ce, "Alƙawari na ɗauka ba zan lamuncewa duk wanda yake ƙoƙarin cutar da ƴar wata kowaye." Saif ya saki murmushi da be yo niyya ba don maganarta ta ƙarshe kamar da biyu take faɗa masa wai, "Kowaye " Taku biyu ya yi zuwa gare ta yace, "Bana son ya cutar da ita ina tausayin halin da take ciki tun da bata ji bata gani ba, bana son haƙƙinta ya kamani." Maryo rasa wanne za ta yi farincikin Ƴar uwarta ta samu miji me kulawa da ita ko kuma kishin wanda take ƙauna yana faɗin kulawar da zai yake bawa wata. Dannewa kishinta ta yi don bata jin za ta nunawa Saif tana jin zafin ƴar uwarta, ta gyara tsayuwarta ta ce, "Ka yi aiki tuƙuri domin ganin ka kare martaba, haƙƙi, rai da lafiyar Matarka, ka zame mata mijinta da za ta yi alfahari da jarumtarsa. Ni na tsaya mata ne a matsayim ƴar uwarta Kaima ya kamata ka tsaya mata a matsayinka na mijinta."
"Jarumta jinina ce juriya numfashina ce sadaukarwa rayuwata ce bana tunanin Ƴar uwarki za ta yi tsammanin ta yi zaɓen tumun dare. Ina son ki tsaya a gare ta saboda ke kaɗai na aminta da ke..." Tun be ƙarasa magana Maryo ta ɗaga masa hannu tana katse shi, "Kana nufin Mahaifiyarmu za ta cutar da ita?" Girgiza kai ya yi yace, "Ban taɓa kawo haka a kaina ba. Kin san waye shi yaci alwashin sai ya cutar da ita, kin san kuwa tun da ya furta Allah ne kaɗai ya san ta yadda zai ɓullowa lamarin." Maryo ta kalle shi a tsorace Saif ya gyaɗa mata kai, idanunta ne suka ciko da ƙwalla ta ce, "Na barta a hannun Allah na yi imani ba zai iya yi mata komai ba, zan je ga Maryama domin ta taɓo tsuliyar Dodo. Idan har ya yi kuskuren taɓa ta ko abin da yake cikinta na yi rantsuwa da girman Allah abin da ya faru na ambaliyar da aka yi a shekarun baya sai an maimaita ta." Tana gama faɗa ta yi gaba Saif ya wuce cikin asibitin zuciyarsa cike da tausayin halin da Abu take ciki.
Salman da ke cikin siffar Likitan da ke kula da Abu yana ganin wucewarwa Maryo ya shiga ɗakin da Abu take kwance, Magunan da Maryo ta wakilta na ganinsa suka taso masa da gudu suka fara kai masa cizo da fiƙoƙinsu, nan take suka shiga artabu ganin za su ɓata masa lokaci ya shiga hura musu baƙar iska nan take suka ƙone ƙurmus. Tsaye ya yi a bakin gadon Abu da ke sauke numfashi sama-sama, duk wanda ya kalle ta zai tabbatar da baccin daɗi take yi ba, wata uwar dariya ya bushe da ita nan take ya rikiɗa zuwa suffar Maryo. Tashinta ya fara yana dukan kafaɗarta, buɗe ido Abu ta yi idanunta suka yi tozali akan fuskar ƴar uwarta. Da murnarta Abu ta yunƙura da ƙyar taba ƙoƙarin ta shi, cike da ɗoki ta furta, "Maryo ke ce nake gani yaushe kuka zo.?" Saif ya fara ɓaɓɓaka dariya yana faɗin, "Bana ƙaunarki tun da kika aure mini masoyina kuma sai na wahalar da ke." Yana rufe baki ya dunƙule hannu ya daki cikin Abu, nan take ta ƙwalla uwar ƙara har sai da su Inna Habi suka jiyo ihunta.
BILLAHI HAR KUSAN KUKA NA YI WA ABU😢
AMUN AFUWA BAN YI EDITING BA
_LITTAFIN NAN NA KUƊI NE DA NAIRA 200 ZAKI KARANTA SHI CIKIN KWANCIYAR HANKALI, ZAKU BIYA TA WANNAN ACCOUNT ƊIN, FIRST BANK 3090957579 AISHA ADAM, ZA'A TURO DA SHAIDAR BIYA TA WANNAN LAMBAR,0706 206 2624, DAN GIRMAN ALLAH IDAN KINSAN ZAKI FITARMUN DA LITTAFI NA YAFE CINIKINKI._
[11/01, 14:23] Ameera Adam🌚: 60...
Wani irin azababben duka ta ji cikin baccinta a firgice ta miƙe zaune tana waige haɗe da soshe-soshe, a razane ta sauke idanunta kan Maryo da ke tsaye a gefe ta zuba mata manyan idanuwanta fuskarta murtuk kamar ta fusataccen bujimin Sa. Da sauri Fulani Maryama ta ja da baya tana watso mata tambaya wacce ga dukkan alamu bata cikin hayyacinta, "Lafiya me kika zo yi mini waye ya baki izinin shigowa?"
"Ki sani ina ragawa wanda ya nemi cutar da ni haka duk wata ɗan adam da zai cutar da ni bana ɗaukan wani mataki a kansa amma in wani ya yi yunƙurin cutar da wani nawa tabbas zan nuna masa iyakarsa. Ba na son ki fusatani ta yadda zan azabtar da ke da hukunci me tsanani. Na zo na yi miki jan kunne domin bakin rijiya ba wurin wasan makaho bane." Maryo ta faɗa tana ƙara haɗe fuska. Fulani Maryama ta saki murmushi domin ga duk wanda ya yi wa Fulani Maryama farin sani zai tabbatar ƙarfin hali irin nata, zai yi wuya farat ɗaya ka fahimci tashin hankalin da take ciki, tana dabƙwarin gwiwa fiye da tunanin mai tunani. Gyara zamanta ta yi ta kalli Maryo fuskarta kwance da murmushi tana cewa, "Yaro man kaza. 'Yan mata me kike faɗa haka ne?" Haushi ne ya ƙara kama Maryo ta furzar da iska me zafi nan take idanunta suka rine jawur, da sauri ta ƙarasa ta kama hannun Fulani Maryama ta damƙe shi da ƙarfin tsiya, wani irin zafi zumm! Ya ratsa cikin hannunta zafin har tsakiyar kanta. Wata uwar ƙara ta saki sannan Maryo ta saki hannunta ta ce, "Wannan gargaɗi ne na yi miki amma wallahi duk ranar da kika sake turowa 'Yar uwata wani mugun abin na rantse da zatin Ubangiji sai kin komai abar tausayi a gidan nan, na ƙata jadadda miki 'Yar uwata ba sa'ar yinki bace muddin kika nemi cutar da ita sai na kashe ki da rayuwarki, sai kin wulaƙanta kina ji kina gani babi uwar da bokayenki za su iya yi miki." Maryo na gama faɗar haka ta fice daga ɗakin, Fulani Maryama bata samu sukunin iya furta komai ba saboda tsananin azabar da take ciki.
Jin ihunta ya sa