Showing 54001 words to 57000 words out of 89213 words

Chapter 19 - Anya Baiwa Ce 2 Complete Hausa Novel By Aisha Adam.txt

30 Nov 2024

5341

ya sa nake karaya..."


"Karaya ga gawurtaccen jarumin maza sam bai dace da kai ba. Bana buƙatar saka jin kalmar daga bakinka domin sam bata dace da kai ba. Ta dace da gurbin zama shi ya sa ta samu sukunin zama a cikin zuciyarka. Kada ka taɓa tsammanin bata yi maka adalci ba domin ta ɗora ƙwarya a gurbinta. Ya za a yi ka hukuntata alhalin ta yi abin da ya dace domin duk abin da kake muradi yana tare da kai. Ka daina kewaye-kewaye domin ba zai haifar da Ɗa mai ido ba." Rayzuta ta faɗa tana kashe masa ido ɗaya. Mayar mata da martanin murmushi ya yi ya ruƙu hannunta, wannan ne karo na farko da haka ya fara faruwa a tsakaninsu, wani irin yaar ta ji a jikinta ta ɗago da idanunta karaf suka haɗa ido, rana ta farko kenan da ta gagara jurewa kallonsa a hankali ta sauke kanta ƙasa, tana cikin wannan yanayin ta riski muryarsa na cewa, "A yau zan bayyana miki abin da ya daɗe yana yi mini yawo a cikin zuciyata, Rayzuta!" Ya ambaci sunanta cikin wani irin yanayi mai wuyar fasaltuwa. Ɗagowa ta yi ta kalle shi sannan ta sunkuyar da ka ƙasa ya ci gaba da cewa, "Koda za ki sa a hukunta ni sai na furta domin barin kashi a ciki baya maganin yunwa. Na san ba zan samu matsayin da za ki amshi ta yi na ba domin bambamcin tsakanin ruwa da jini a bayyane yake. Rayzuta ina ƙaunarki tun ranar dana fara tozali da ke! Ina sonki fiye da tunanin mai tunani. Sai dai bana jin zan iya mallakarki a matsayin matar..."


"Wa ya gaya maka?" Rayzuta ta yi maganar tana harɗe hannuwa a ƙirji sai ta ci gaba da cewa, "Na zura maka ido ne dama domin na ga iya gudun ruwanka. Furzaan! Na jima da dakon ƙauna da soyayarka, sai dai na yi kawaici ne domin mace da kunya aka santa. Duk wasu alamu na soyayya ina nuna maka amma kai sai ka nuna kamar baka gane ba shi ya sa na kame baki na." Farinciki ne ya lulluɓe masa zuciya lokaci ɗaya ya rungumota jikinsa ita ma ta kwantar da kanta tana jin wani irin farinciki a zuciyarta. Ɗago da ita ya yi yace, "Faɗa mini mafarkin da kika yi."


Ta ku biyu ta ƙara sannan ta juyo ta kalleshi ta ce, "Na yi mafarkin ana ɗaura mana aure sai wani irin duhu ya mamayr wurin daga baya kuma sai na Takawa ya fara zubar da jini."


Hankali a tashe ya furta, "Jini kuma?" Kanta tsaye Rayzuta ta ce, "Eh mene ne?" Murmushin yaƙe ya yi yace, "A'a babu komai!" Sauya fuska ta yi ta ce, "Amma sai na ga kamar baka yi farinciki ba." Hancin ta ya riƙe yana cewa,"Ke dai bakinki baya shiru." Ita da shi suka saki dariya lokaci ɗaya.


Suna cikin wannan yanayin Zulik ya faɗa wurin hannunsa riƙe da kwari da baka, yana ganinsu a wannan yanayin ransa ba ƙaramin ɓaci ya yi ba. Haɗiye yawu mai ɗaci ya yi ya ƙirƙiro murmushin yaƙe ya ɗora a fuskarsa ya ƙarasa yana cewa, "Barkanku da hutawa." Rayzuta na tamke fuska ta yi ta fara haramar wucewa, da sauri Zulik ya sha gabanta yana cewa, "Yau ba za ki bar wurin nan ba har sai kin sanar mini me na yi miki?" Da mamaki ta juyo ta kalleshi fuska a tamke ta ce, "Zan tunasar da kai kada harshenka ya yi gangancin furta abin da zai kaika ga mummunan hukunci, ka tuna wace ce a gabanka." Fuzaan ya tausasa murya yana cewa, "Rayzuta! Ki tsaya don Allah ki saurare shi."


"Me kake so?" Ta tambaye shi a gajarce.


Wani shu'umin murmushi Zulik ya yi domin ya san haƙƙansa ya kusa cimma ruwa, saboda duk maganganun da su Furzaan suka yi tun daga farko har ƙarshe yana laɓe yana jin su. Juyawa ya yi wurin Furzaan yace, "Duk cikin gidan nan ka fi kowa kusanci da Gimbiya kai ne babban abokinta don Allah ka roƙar mini alfarma a wurinta, ta taimaka ta amshi soyayyata duk duniya babu wacce nake so nake ƙauna sama da ita." Jin maganganunsa yake kamar saukar aradu, ido ya zura masa yana jin maganganunsa na yi masa yawo a tsakiyar ka. Yana shirin yin magaga Rayzuta ta ce, "Karka wahalar da yawun bakinka domin wannan buƙatar taka daidai take ta ɓillar ƙaho a tsakiyar kan ɗan tsako. Na riga da na samu masoyi na haƙiƙa domin na gwada shi ta hanyoyi mabambamta. Don Allah ina roƙonka ka bar wahalar fa kanka domin wannan ba abu bane mai faruwa. Tana gama faɗa ta yi gaba kafin ta fita ya sha gabanta da sauri ya sha gabanta ya saki murmushi yana cewa, "Wallahi sai na aureki kin ji na gaya miki bar ganin ina lallaɓaki amma sai na nuna miki idan na nemi abu dole sai na same shi babu ruwana da matsayinki abin da na sani..." Bai rufe baki ba ta ɗauke shi da mari. Ta nuna shi da ɗan yatsa tana cewa, "Ina ganin mutumcinka ne saboda kai abokin Masoyina ne, amma kana neman ka kaini magaryar tuƙewa idan ka sake yi mini makaman..." Bata yi aune ga ta ji ya rumgomata da sauri Furzaan ya janyota jikinsa ya ture Zulik cikin fushi yana cewa, "Ya isa haka karka fara ƙoƙarin wuce gona da iri. Tun da ta ce bata ƙaunarka ana dole ne?" Zulik ya saki murmushi sannan ya nuna su yana cewa, "Allah ko? To mu zuba mu gani ni da ku shege ka fasa. Wallahi sai na cimma ƙuɗurina a kanki." Yana gama maganar ya fice daga lambun.


Wannan shi ne mafarin rashin jituwar Zulik da Furzaan...


Kafin wani lokaci tuni labarin haihuwar Abu ta karaɗe ciki da wajen masarautar Kano, wannan labari ba ƙaramin faranta ran su Inna Habi ya yi ba. Saɓanij Fulani Maryama da wannan saƙo ya zame mata mummunan albishir, wannan saƙo ba ƙaramin ɗaga mata hankali ya yi ba dukda ta san wutsiyar raƙumi ta yi nesa da ƙasa. Amma sam bata ji daɗin haka ba, amma a wannan karon tana shakar ziyarta ɗaya daga cikin Bokayenta saboda hannun da take fama da shi har gobe babu wani ci gaba da a ke samu. Masu magungunan gargajiya kala-kala sun zo kowa ya gwada basirarsa amma babu wani sauƙi ko canji. Canji ɗaya take lura da shi wato ta lura hannun nata ya fara tsotsewa yana ƙanƙancewa.


Jakadiya maruru ya yi mata sauƙi har ya fara saɓa, da safiyar ranar da Abu ta haihu ta leƙa wurin Fualani Maryama bayan sun gaisa Jakadiya ta yi ƙasa da murya ta ce, "Fulani ashe mummunan mafarkin da na yi a daren jiya ba banza ba? Wacce yarinyar ashe haihiwa za ta yi? Ya a ka yi muka yi sake har wannan lamarin ya auku? Maryama kina me har ta haife cikin nan ba tare da an ɓarar da shi ba." Fulani Maryama fuska ɗauke da damuwa ta janyo shanyayen hannunta tana nunawa Jakadiya, da sauri Jakadiya ta yi baya tana zaro ido waje ta ce, "Na taɓa ki da alheri Maryama meye wannan nake gani ido biyu da farar safiyar nan?"


"Jakadiya babu wanda zai yarda da abin da zan faɗa idan bake ba. Yarinyar nan Maryo ita ta tsotse mini hannuna."


"Kamar ya Fulani kina nufin ture ta yi miki?" Jakadiya ta tambaya hankali a tashe. Fulani Maryama ta rausayar da kai ta ce, "Turen Ƙadangare na yi wa Sirikar Zaliha shi ne ta diro mini yadda na ganta ido biyu in ga Annabi, amma yaran nan kowacce sai cewa ta yi bata ganta ba. Wallahi yarinyar ba mutum ba aljana ce, idan ba aljan ba waye zai aikata haka matsa hannuna fa ta yi amma ji na yi kamar ta tura shi cikin wuta. Tun daga lokacin shi kenan bana jin komai." Jakadiya jikinta ba ƙaramin sanyi ya yi ba ta ce, "Maganar gaskiya Maryama ya kamata mu samawa ranmu salama akan yarinyar nan, ni fa ba tun yau lamarinta yake bani tsoro ba. Mu kawo ido mu zuba wanda muka yi a baya ma Allah ya yafe mana." Wani murmushi Fulani Maryama ta yi ta ce, "Jakadiya kina matuƙar ba ni mamaki, me ya sa kike saurun karaya ne?" Tsoro ƙarara ya bayyana fuskar Jakadiya a take ta miƙe tana cewa, "Maryama kin daina ba ni mamaki yanzu lamarinki tsoro yake bani, ni bari ki ga wucewata Allah ya baki lafiya amma duk yanda hannunki yake tsotsewa kamar an tsotse rake baki daddara ba." Wannan karan ko kyakkyawar sallama ba su ba Jakadiya ta fice ta faɗa sashen Fulani Zaliha. A cen ma bata daɗe ba saboda bata samu fuska ba, tana fita dagan sashen ta wuce sashen sauran Matan Sarki sannan ta koma sashensu.


Inna Habi lokacin da aka sanar da ita ba ƙaramin farin ciki ta yi amma fir ta ƙi zuwa ganin Abu da Jaririnta (Saboda tsananin kunya irin ta mutanen da) Maryo ko bari a gama sanar da saƙon ba ta yi ba ta fice da gudu ko takalmi babu. Tana zuwa ko a gurguje ta gaishe da Fulani Zaliha, murmushi ɗauke a fuskar Fulani Zaliha ta ce, "Ai fa ba zama an ɗaurawa karya aure. Su Maryo an yi ɗa da alama ko takalma baki taho da su ba." Maryo na shirin bata amsa ta ji kukan Jaririn Abu da gudu ta faɗa ɗakin tana zuwa ta haye kan gadon ƙarfen ta karɓe Jaririn da ke ta mutsu-mutsi yana saka hannu a baki." Cak Maryo ta tsaya tana zuba masa ido sakamakon tsananin kamar da ta ga yana yi da Saif, wani irin farinciki ne ya kamata a zuciyarta take ayyana,


"Tabbas ko ban auri Saif ba wannan ya zame mini abin farinciki. Yau Ɗan Saif ne a hannuna jininsa ne mallakinsa. Wannan shi ne murna biyu ga shi Ɗan 'yar uwata mahaifinsa kuma masoyi na." Ba ta san lokacin da ta rungume shi tsam a jikinta ba sai kuma ta faraa yi masa kissis cikin so da ƙauna.

Wata irin kunyarta Abu take ji, kamar ta san abin da yake zuciyar Maryo. Ta ɗora hannunta a kan Maryo tana sunkuyar da kai ƙasa ta ce, "Bawa baya taɓa gujewa ƙaddaras sai dai wannan ƙaddarar ba ta zo mini ta sigar da nake buƙata ba. Ta yi mini yankan ƙauna domin tana neman yin katanga ga a tsakanin masoya. Maryo!" Abu ta kira sunanta cikin wata irin murya ta ci gaba da cewa, "Wannan yaron da yake hannunki Ɗanki ne halak malak ina raye da bana raye na mallaka miki shi koda mahaifinsa bai amince ba ni na mallaka miki tun da ni na san zafin naƙudar shi." Idon Maryo ne ya ciko da ƙwallah ta kalli Abu ta ce, "Tun da na zo duniya babu kyautar da na taɓa farinciki da ita irin wannan haƙiƙa ke ƴar uwace ta daban." Abu ta yi murmushi tana cewa, "Abu na gaba ina son ki janye maganar aurenki da Maleek idan har ina da matsayi a wurinki. Karki damu da ni na sha gaya miki zamana da Saif yanzo ƙarshe amma kina ɗaukar lamarin kamar wasa, wallahi ba zan koma gidansa ba..." Da sauri Maryo dakatar da ita tana cewa, "Don Allah ina tsaka da farinciki kada ki ruje mini shi. Na gaya miki ina ƙaunarsa ne da za ki tursasani aurensa. Me ya sa bakwason farincikina ne? Na samu mijin da zai bani kulawa miji mai ƙaunata ya kike so ki sa ni auren wanda bana so." Maryo na maganar hawaye na zuba.


"Ƙarya kike!" Da sauri Maryo ta ɗago ta kalleta Avu ta ci gaba da cewa,


"Kalmanki sun furta akasin abin da yake zuciyarki, kin manta cece Abu kin san na fi kowa karantarki da halin da kike ciki me ya sa za ki cuci kanki? Babu komai idan kun san wata ba ku san wata ba." Da sauri Maryo ta kalli Abu ta ce, "Me za ki yi?" Kai tsaye Abu ta ce, "Abin da ta dace!"


"Don Allah..." Da sauri Abu ta katse ta, "Mu bar maganar tun da dai ba za ki aure shi ba shi kenan" Jikin Maryo ne ya yi sanyi don ta san Abu sarai ta san akwai abin da ta ƙulla. Kukan da Jaririn yake tsalawa ne ya sa Fulani Zaliha ta yi musu magana, a kunyace Abu ta karɓe shi ta fara bashi Mama. Maryo ta guntse dariyarta suna haɗa ido Abu ta ɗaɗa mata duka ta ce, "Munafuka faɗi abin da yake bakinki!" Maryo ta fashe da dariya don dama a cike take da ita, sai da ta yi mai isarta sannan ta ce, "Oh! Ni 'Ya su Abu wai kunya ta kike ji." Abu ta basar don ta san halin Maryo sarai idan ta gano lagonka ka shiga uku ta ce, "Kunyar uwar mai sai ka ce wata sirikita ke ni ko Fulani ba na jin kunyarta bare ke." Maryo ta riƙe baki ta ce, "Allah ya shiryeki na san za ki aikata abin fa ya fi haka." Abu daɗi ta ji har ciki ranta yanda ta ga ƴar uwarta ta saki jiki suna wasa da dariya a gefe ɗaya kuma ta ji haushin kanta domin da bata auru Saif ba babu wani abu da zai shiga tsakaninsu yanzu da tuni Ɗan Maryo ne a hannunta.


Suna na zaune suna hira Jaririn ya tsanyare da wani irin matsanancin kuka jikinsa na wani karkarwa, a zabure Maryo ta miƙe tsaye ta karɓi Jaririn ta zuba masa ido sai kawai ta sake shi a ƙasa ya faɗi, bata bi ta kansa ba ta fice daga ɗakin.


Sorry 4 the errors ban yi editing ba


_LITTAFIN NAN NA KUƊI NE DA NAIRA 200 ZAKI KARANTA SHI CIKIN KWANCIYAR HANKALI, ZAKU BIYA TA WANNAN ACCOUNT ƊIN, FIRST BANK 3090957579 AISHA ADAM, ZA'A TURO DA SHAIDAR BIYA TA WANNAN LAMBAR,0706 206 2624, DAN GIRMAN ALLAH IDAN KINSAN ZAKI FITARMUN DA LITTAFI NA YAFE CINIKINKI._
[13/01, 16:13] Ameera Adam🌚: 62...




Da sauri Fulani Zaliha ta faɗo ɗakin domim kukan da Jaririn yake sam bana lafiya bane, Abu tana tsaye jikinta na karkarwa da sauri Fulani Zaliha ta ɗauke shi tana buga mata tsawa, "Wannan wanne irin sakarci ne kuke yi haka za ku yarda yaro kuna kuna tsaye kina kallonsa me yake damunki ne?" Abu kasa furta komai ta yi sai kawai ta fashe da kuka don yanayin da ta ga 'yar uwarta a ciki ya tabbatar mata da tabbas akwai abin da yake faruwa. Fulani Zaliha ce ta miƙa mata Jaririn a faɗace tana cewa, "Maza kaɓe shi ki ba shi ya sha." Shiru Abu ta yi kamar kurma sai da Fulani Zaliha ta maimata mata maganar sannan Abu ta sunkuyar da kai ƙasa ta amshi Jariri da ya ƙura mata ido ƙir (Waɗanda suka karanta littafina na Jariri ne kaɗai za su fahimci yanayin🤣) har sai da Abu ta tsargu tsoro ya ɗan kamata. Fulani Zaliha ta ce, "Abu wai ko wani abu na daminki ina yi magana kina ji na?" Abu ta sunkuyar da kai ƙasa cikin sanyim murya ta ce, "Ki gafarceni Ranki ya daɗe amma bana jin Maryo ta yi kuskure domin ba za ta yarda shi a banza ba, na tabbata tana da dalilin yin haka. Ina ji a jiki a kwai wani ɓoyayan al'amari a dangen da jariri..." Da sauri Fulani Zaliha ta katse ta a fusace, "Ba na son sakarci kina hauka ne? Karki sake ki furta kalma mara daɗi a kan jikana."


A kan dole Fulani Zaliha ta tursasa Abu ta bawa Jaririn Mama, tana zama rai a ɓace ta fara bashi ya fara sha kawai sai gani ta yi Abu ta fara sanƙame wa idanunta suna niyyar kafewa. Wani babban tashin hankali sai ga jini ya ɓalle mata ya zuba kamar an buɗe famfo. Tuni Fulani Zaliha ta cire Jaririn da yake ta zuƙarta ta ajiye shi a gefe ta fita kururwar neman taimakon mutane. A daidai lokacin Saif ya shiga ya samu Mahaifiyarsa cikin tashin hankali, ba ƙaramin tsorata ya yi da ganin jinin da yake zuba daga jikinta ba. Dunƙule hannunsa ya yi yana ɗan girgiza kansa sai ya ɗora a saman kanta nan take ta sandare numfashi ya yi ƙaura daga gangar jikinta. Wata gauruwar ajiyar zuciya ya sauke yana dafe kansa, sai ya mayar da kallonsa ga Jaririn da yake kwance ya saki wani irin murmushi domin shi lamarin Salman ya fara ba shi dariya. A zuciyarsa yake ayyana, "Tabbas yaƙin ba iya a kan Maryo bane, saboda da a kanta ne ba zai yi mini haka ba. Tun da ya kwana da sanin ba da ni a ka saka mata rana ba. Amma wannan karon shi ne na farko kuma na ƙarshe." A gaggauce ya tashi ya je fita Mahaifiyarsa ta shiga ita da Jakadiya da Unguwar zoma. Bai saurare su ba ya yi gaba har ya kusa fita ya juyo ya ce, "Ammi Maryo ta shigo wurin nan ne?" Fulani Zaliha ta ce, "Eh yanzun nan ta fita."


"Tana ɗakin abin nan ya faruwa?"


"A'a ita ta yarda Jaririn dai a ƙasa sannan ta fice." Fulani Zaliha ta ba shi amsa.

"Kar ku taɓa Abu ba za ta tashi yanzu ba Ammi." Yana gama maganar ya fice a gaggauce. Sororo suka yi suna mamakin furucinsa, Fulani Zaliha ta ce, "Unguwar zoma maza mu je ki duba ta ko wani abin za ki jiƙa mata idan kuma turare ne a samo garwashi." Unguwar zoma ta zurawa Abu ido ba don tana tsoron furta abin da ta gani ba da ta gaya musu gaskiya amma babu yanda ta iya haka ta yi gaba suna biye da ita a baya.


Maryo tana fita babu in da ta tsaya sai fadar Sarki Aminullah ta shiga ko kyakkyawar sallama ba ta

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login