Showing 6001 words to 9000 words out of 89213 words
Chapter 3 - Anya Baiwa Ce 2 Complete Hausa Novel By Aisha Adam.txt
duniya akan nemo sahihiyar yalwatacciyar soyayyarka. Kada ka manta daraja ɗaya kake ci na ɓoyayyar alaƙarmu da tuni zancen wani ake ba kai ba. Karka ƙara dakatar da ni akan hukuncin da nake zartarwa dai dai da laifin masu aikata shi idan ba haka ba kaima ina iya bi ta kanka." Tana gama faɗa ta kuma yanke jiki ta koma bacci tare ta sauke ajiyar zuciyar kamar wacce tayi tseren gudu, wanda haka ya yi dai-dai da hankaɗe katangar ɗakin da Dokin ya yi ya kutso cikin ɗakin yana ɗaga ƙafafuwa sama tare da ci gaba da haniniya mara daɗin sauraro.
Ga mu a wannan yanayin lamari dai ya ɗauki hazo, Masarautar Adamawa na cikin yanayi, ina fatana kalaman wannan shafin bai rikitar da ku ba🤣🤣
_LITTAFIN ANYA BAIWA CE? NA KUƊI NE DA NAIRA 200 ZAKI KARANTA SHI CIKIN KWANCIYAR HANKALI, ZAKU BIYA TA WANNAN ACCOUNT ƊIN, FIRST BANK 3090957579 AISHA ADAM, ZA'A TURO DA SHAIDAR BIYA TA WANNAN LAMBAR,0706 206 2624, DAN GIRMAN ALLAH IDAN KINSAN ZAKI FITARMUN DA LITTAFI NA YAFE CINIKINKI._
[02/12/2021, 18:01] Ameera Adam🌚: 39....
Maleek kusan mutuwar tsaye ya yi ban da karkarwa babu abin da jikinsa yake yi, runtse idonsa ya yi ya miƙa wuya ya saddaƙar da sai dai wani ya ƙara numfashi ba shi ba. Dokin bai saurara ba ya buga wata haniniya tare da buga ƙafafuwansa na gaba a ƙasa da ƙarfi, nan take komai da ke cikin ɗakin ya tsalle kamar waɗanda ake yi wa girgizar ƙasa. A cikin abubuwan da suka yi tsalle sama har da Maleek wanda tuni ya sarewa rayuwa, yana gabda faɗowa sama dokin ya cafe shi da bakinsa ya ci gaba da wata irin haniniya. Maleek jikinsa ne ya saki wanda yake nufi da ɗaukewar numfashinsa a take ya sume bai ƙara sanin abin da yake faruwa ba. Dokin na ganin haka ya yi wurgi da shi cen gefe sannan ya juya a haukace ya ci gaba da banke masu ƙararrarun kwana, waɗanda suke da rabon shan wahala kuma suna kwance kamar gawarwarki cikin jini, wasu ko numfashin kirki basa iya yi. A haukaci ya nufi sashen Mai martaba bugu ɗaya ya kaiwa katangar ɗakin ta rushe, sai ga haske rana ta dallare cikin turakarsa wace take a kusan cike ta maɓoye daga ƴaƴansa bayinsa harda dogarawansa da sauran mutanen cikin gida. Suna ganin dokin gabaɗaya jikinsu ya fara tsuma shiru suka yi kamar waɗanda ruwa ya cinye su, masu sakin fitsari na yi masu zawo a wando suna yi. Kafe su ya yi da idanuwa yana zaro harshe kamar zalamamman maye da ke gabda haɗiyar bil'adama, waige-waige ya dinga kamar me neman abu sai kuma ya fara takawa a hankali har gaban su Sarki Abdallah, miƙa kai ya dinga yi yana shinshimasu ɗaya bayan ɗaya. Duk wanda dokin ya kai kansa sai ya yi kamar zai mutu saboda tashin hankali. Sarki Abdallah tuni ya janyo rawanin har saman fuskarsa ya mayar da shi kamar hijabi. Dokin na zuwa kan wani Dogarin Sarki ya gatsawa kansa haƙora yana fisgoshi, ya fyaɗa shi da bango nan take ya faɗi ko shurawa bai ƙara yi ba, nan take ɗakin ya hautsine da hayaniya ban da ihun yara da manya babu abin da yake tashi a ɗakin, dan gabaɗaya sun saddaƙar da ƙara samun zuƙar iskar duniya. Suna tsaka da ihun ya sake fisgo wata baiwa dake rakuɓe acen gefe har ya ɗaga zai fyaɗa da ƙasa kamar daga sama suka jiyo muryar Maryo tana cewa. "Dakata! Ba mutuwa zai yi ba. A bashi wahala." Tun bata rufe baki ba dokin ya fara tumurmusar baiwar ban da ihu da ƙaraji babu abin da take yi, gabaɗaya hankulan mutanen wurin a tashe yake a lokacin da za a tsaga jikinsu wataƙila ba za a samu jini a jiki ba. Yana gama tumurmusa ta ya ƙarasa wurin Maryo da ke tsaye kyam tana ƙare musu kallo, russunar da kai ya yi a gaban ta cikin girmamawa yana jirana umarninta. Hannu ta sa ta fara shafa kansa tana murmushi sannan ta ɗago da kai ta kalli wurin ayarin mutanen, ta fara takawa a hankali cikin ƙasaita. Tana ƙarasawa ta fara kurɗawa cikin mutanen ban da zare idanu babu abin da suke yi.Hannu biyu ta sa ta riƙo Jakadiyar Sarki Abdallah ta ɗago ta, jikin Jakadiya sai rawa yake kamar mazari haka ta tsayar da ita tana ƙoƙarin faɗuwa saboda ƙafafuwanta sun ga za ɗaukarta. Kallon ta ta yi tana murmushi ta ce, "Alƙawarin da na ɗauka miki na cika miko shi tabbas wannan hukun da na yi musu bai kai azabtarwar da suka yi mana ba, amma ko babu komai sun ɗanɗana kuɗarsu." Ita dai Jakadiya tana tsaye kamar gunki sai raba ido take kamar shege a rabon gado. Hawaye ne ya ɗan zubo mata ta sa gefen hannunta ta goge sannan ta ci gaba da cewa, "Amma har gobe zuciyata ta gagara yafe musu bana tunanin zan iya manta abin da aka aiwatar gare mu." Jakadiya kamar fitar tusa haka ta tsinci bakinta yana faɗin, "Ita yafiya alama ce ta tsarkakkakiyar zuciya. Yafewa macuci ba aibu bane duba da muma muna yiwa Ubangijin da ya hallice mu laifi, kuma idan muka roƙe shi yana yafe mana, ki tausasa zuciyarki laifin wani baya shafar wani." Gyaɗa kai Maryo ta yi ta ce, "Saboda ke zan yi, saboda darajar bakinki amma ina neman yafiyar ki, amma tabbas sai ha hukunta Fulani Halimatu. Ta cutar da baiwar Allah na tsawon shekaru, ta yi tsammanin asirinta ba zai tonu ba wanda hakan ba ƙaramin kuskure bane. Ita ta killace Mai babban ɗaki a kogon bokanta sai ni na ɗauko ta, a shekarun baya kun wayi gari da gawar Mai babban ɗaki wanda sam ba ita bace rufa ido suka yi muku ita da bokanta, kuma billahillazi sai ta girbi abin da ta shuka. Kinsan darajarwa tasa na taimake Mai babban ɗaki?" Jakadiya kasa magana ta yi Maryo ta ci gaba da cewa, "Saboda Maleek ne! Akwai ɓoyayyar alaƙar da ke tsakaninmu. Ba za ku taɓa fahimta ba sai nan gaba. Na taimaka mata ne saboda duk cikin jikokinta ta fi ƙaunarsa, ta bashi kulawar da babu wani jika da ya samu haka." ɗaga kai ta yi ta kalli Sarki Abdallah ta ce, "Ka gaggauta mayar da ita ɗakinta domin Mai babban ɗaki ta fi ƙarfin zama a ɗakin baya, Uwa uwa ce babu na biyunta idan har kana san gamawa da mulkinka lafiya, kuma ka fara hukunta matarka kafin ta aminshi nawa hukuncin." Tana gama faɗa ta kalli Jakadiya cikin tausasa murya ta ce, "Ya Mahaifiyata zaman ki a nan ba dace ba ko za ki biyo ni mu tafi?" Da sauru Jakadiya ta fara girgiza kai ta ce, "A'a zan zauna a nan Allah ya yi miki albarka." Murmushi Maryo ta yi mata ta ce, "Ba zan takura miki ba. Amma idan akwai abin da kike buƙata ki sanar da ni." Jakadiya ta gaɗa kai, Maryo ta juya ta kama dokin ta kamar tsuntsuwa haka ta ɗafe kansa suka fice daga ɗakin.
Idanu ya zuba mata har sai da ta fara tsarguwa ta sunkuyar da idonta ƙada tana murnushi, daga cen nesa Uwar bayi ce tafe tana kallonsu cikin takaici. Ji take kamar ta ƙarasa wurin da suke zaune ta damƙi wuyan yarinyar ta shaƙe kowa ya huta, hannunta na dama ta kalla wanda yake ɗauke da ƙwaryar fura da nono wanda yaji garin magani, amma idan ba a gabanka aka saka ba, ba za ka san da wani magani a ciki ba. Tana ƙarasawa wurinsu ta faɗaɗa fara'arta cikin girmamawa ta yi sallama tana faɗin, "Barkanku da hutawa ranka shi daɗe." Saif ya ɗago idanu ya kalleta yana cewa, "Barka dai Baba." Miƙa masa ƙwaryar furar hanunta ta ta yi ta ce, "Ga fura Bintu ta damo maka ta ce a kawo maka jikin nata ya ƙara warwarewa." Faɗaɗa fara'arsa ya yi yace, "Na gode Babah ita kuma Allah ya ƙara mata lafiya." Mayar da kallon sa ya yi wurin Abuh yace, "Kema za ki sha ko?" Gyaɗa masa kai ta yi sannan ya tura mata ƙwaryar yace, "Ga shi sha ki rage mini." Hankali a tashe Uwar bayi ta karaf ta ce, "Amma ai kai na kawowa." Kallon ta ya yi yace, "Ni da Abuh kusan ɗaya ne." Uwar bayi haɗiye mugun yawu ta yi dan bata so asirinta ya tonu yasa ta ce, "To shi ke nan amma ka tabbatar da ka sha fa." Kallonta ya yi yana nazartar maganar ganin haka yasa ta wayance da cewar, "Na ga idan baka sha ba Bintu ba za ta ji daɗi ba." Gyaɗa mata kai kawai ya yi bai kalleta ba yace, "Uwar bayi a bamu wuri." Sumi sumi ta tashi tana faɗin, "Na barku lafiya." Kallon Abuh ya yi yace, "Ba ni furar nan!" Abuh ta ɗan kwaɓe fuska ta ce, "Sha fa zan yi." Ya ɗan tsuke fuska yace, "Na ce ki bani." Miƙa masa ta yi ta wurga masa tambaya, "Dama Bintu har abinci take aiko maka?" ta tambaya tana kafeshi da idonta. Ɗagowa ya yi da manyan idanuwansa ya kalleta sai kuma ta ji ba za ta iya ci gaba da jurewa kallonsa ba, sunkuyar da kai ta yi ƙasa ta ce, "Amma kawai na yi mamaki ne." murmushi ya yi yace, "To me ya sa kika tambaya? Ko bakya son haka?" Bata san lokacin da ta gyaɗa masa kai ba, ya saki lallausan murmushi yace, "Saboda me?" Ta yi karaf ta ce, "Idan kana so ka bani na dinga yi maka." Kallonta ya yi yana jin wani irin farinciki cikin zuciyarsa yake tunanin, "Shin ko itama ta farajin abin da nake ji a zuciya ta?" kallonta ya yi yace, "Shi ke nan! Kin san Bintu ta yi wani irin ciwo me ban tausayi shi yasa nake tausayin yarinyar, amma yanzu ta warware. Ina tunanin sabon da muka yi yasa lokaci-lokaci take aiko mini da fura." Kallonsa ta yi sai dai a ƙasan zuciyarta bata ji daɗin abin ba. Gabanta ne ya yu mummunan faɗuwa da ta ayyana meye na ta na jin babu daɗi dangane da haka, tunowa ta yi da Maryo sai ta ji tausayin ƴar uwarta ya kamata. Ina ma yadda Saif yake sakar mata fuska haka zai yi wa Maryo. Tafa hannunsa ya yi a saitin fuskarsa yace, "Tunanin me kike yi?" Idonta ne ya kawo ƙwallah ta ce, "Ƴar Uwata Maryo." Tsuke fuska ya yi yana jan guntun tsaki, Abuh ta fara girgiza kai tana faɗin, "Me ya sa baka ƙaunar ƴar uwata alhalin ta fini kyawawan halaye." Fuska ɗaure ya kalle ta yace, "Na ce miki bata da kyawawan halaye ne? Ba na san damuwa fa." Daga haka bai ƙara tanka mata ba ya fara ƙoƙarin ta shi, da sauri ita ma ta miƙe tana faɗin, "Dan Allah ka yi haƙuri." Gyaɗa mata kai ya yi ya wuce kamar za ta yi kuka haka ta bi bayansa kamar jela.
"Maryama lafiya na ga kwana biyu kina ɗari-ɗari da ni ko wani abu yana damun ki ne?" Sarki Aminullah ya faɗa yana ƙare mata kallo dan ba haka ta saba zuwa turakarsa ba ko da babu wani abu da yake haɗa su amma tana nuna masa kulawa. Murmushi ta yi tana kallonsa amma a ƙasa zuciyarta, ji take ƙirjinta na dukan uku-uku. Tattaro jarumta ta yi dukda a lokacin jikinta ya kusa jiƙewa da gumi ta ce, "Babu komai Ranka shi daɗe kaine dai ka ga haka." Sarki Aminullah yace, "Na sai wani sha mini ƙamshi ake ina jin sai na ƙara ƙwarƙwara." Fulani Maryama dukda ta san a yanzu Sarki Aminulla babu amfani da zai ƙara yi wa wata mace sai da ta ji babu daɗi a ƙasan ranta, amma da yake ta ƙwarai a kissa sai ta ce, "Allah ya baka yawan rai, wannan ai ba komai bane ka ga masu kula da kai za su ƙara yawa. Allah dai ya ƙara haɗa kanmu." Sarki Aminullah yace, "Allah ya yi miki albarka Maryama ke kam ta daban ce, shi yasa nake ƙaunarki saboda kyawawan ɗabi'unki." Murmushin jin daɗi ta yi ta ci gaba ta fari cikin kissa. Bayan sa ya kalla yace, "Maryama zo ki miƙe mini Jakar cen dan ina tunanin gobe ne tafiya ta ƙasar Gaya, miƙo mini ki zuba waɗannan kayan a ciki." Zuciya ɗaya Fulani Maryama ta miƙe ta je ta ɗauko jaka ta zauna daga ɗan nesa da shi tana ƙoƙarin buɗe jakar, shammatarta ya yi ya janyota jikinsa yana cewa, "Bahaushe yace duk wanda ya riga kwana zai riga ka..." sauran maganarsa ce ta maƙale ganin ɗan kwalin Fulani Maryama a ƙasa lokacin da ya janyo ne ya zame, a razane ya ja da baya cikin tsoro yace, "Maryama! Anya kece ko wata aka sauya mini?"
😂😂😂😂Takawa ya ga bayan silva😂😂😂😂
Kuyi manage pls
_LITTAFIN NAN NA KUƊI NE DA NAIRA 200 ZAKI KARANTA SHI CIKIN KWANCIYAR HANKALI, ZAKU BIYA TA WANNAN ACCOUNT ƊIN, FIRST BANK 3090957579 AISHA ADAM, ZA'A TURO DA SHAIDAR BIYA TA WANNAN LAMBAR,0706 206 2624, DAN GIRMAN ALLAH IDAN KINSAN ZAKI FITARMUN DA LITTAFI NA YAFE CINIKINKI._
[04/12/2021, 18:13] Ameera Adam🌚: 40...
Kunyar duniya ce ta lulluɓe idanuwan Fulani Maryama dan bata taɓa tsammanin haka daga wurin Sarki Aminullah ba, sunne kai ƙasa ta yi cikin jin nauyi ta fara sharar ƙwallar munafurci tana faɗin, "Wani tsautsayi ne ya afka mini ranka shi daɗe." Cikin mamaki yace, "Tsautsayi? Meye silar fitar gashin na ki dubi fa ki ga yadda kan ya yi taƙwal kamar wacce aka yi wa aski da sabuwar aska." Fulani Maryama ta kuma goge ƙwalla a karo na biyu tana satar kallon Takawa, ta fara laluben ƙasa tana nemo ɗan kwalinta ta ji ya ƙara faɗin, "Wai ba magana nake yi miki ba?" Fulani Maryama cikinta ne ya kaɗa tsoro ya kama ta saboda yadda ta ga Sarki Aminullah ya yi mata magana, tattaro jarumta ta yi ta ce, "Rannan ne ina wayar gari na ga kaina haka gashin sauke a ƙasa na yi kuka kamar raina zai fita, amma ban sanar da kai ba saboda kar na ɗaga maka hankali." Sarki Aminullah ya ƙuri da ido yana ƙarewa hallitar Fulani Maryama kallo, tsarguwa ta yi musamman da ta tuna lokacin da Jakadiya take faɗin kanta kamar na jinjirin jaki. Sunkuyar da kai ƙasa ta yi tana wata sa hannun rigarta ta riski muryar Takawa yana cewa, "Sam wannan ba ma'askin dare bane dole a nemo masu magani." A firgice Fulani Maryama ta ɗago ta kalle shi kamar za ta yi kuka ta ce, "Haba ranka shi daɗe. Yanzu kamar ni a matsayin uwar garkenka sai a yi ta yayata abin da ya faru har da neman masu magani? Wai ba zai zama kamar abin kunya ba kuwa, dan Allah ka rufa mini asiri ka bar maganar nan." Sakin baki ya yi yana kallon Fulani Maryama dan a iya saninsa Maryama macece mai matuƙar ƙaunar gashi, amma wai yau ita take cewa a bar maganar nema mata maganin gashi? Tsare ta ya yi ido yace, "Tun yaushe hakan ya faru?" Sani ta yi idan ta gaya masa gaskiyar lokacin ba makawa sai ya nema mata masu magani, hakan ne yasa ta basar ta ce, "Shekaran jiya ne Ranka shi daɗe." Jinjina kai ya yi har lokacin idonsa na kan Fulani Maryama, a kaikaice ta kalle shi ta ce, "To wannan kallon fa ko munin matarka kake kallowa?" Sarki Aminullah ya kuma sakin baki da hanci yana kallom ɓoɗareren hancinta da sulluwar doguwar ƙeyarta yace, "Kin taɓa jin uwa ta hango munin ɗanta?" Fulani Maryama ta kwaɓe baki ita a dole shagwaɓa za ta yi ta ce, "To amma ai gani na yi kana kallona" Sarki Aminullah ya yi murmushi yace, "Dan na kalli matata aibu ne?" Girgiza masa kai ta yi ta ɗauko wani zancen da cewar, "Allah ya taimake ka ni kuwa me zai hana yaran nan kace su fito da matayen aure, yanzu fa lokaci ya yi da ya kamata ace su ajiye iyali, idan muka duba shekarunsu su tafi talatin-talatin fa." Sarki Aminullah ya numfasa yace, "Tabbas maganarki na kan turba amma kina ganin har Saif? Tun da kinga be daɗe da tashi ba." Wani murmushi ta yi wanda ita kaɗai ta san manufarsa ta mayar da kallon ta gare shi ta ce, "Haba Ranka shi daɗe ya kake faɗin haka kamar ba namiji ba, yanzu idan ƙanwata ta ji za ta ji daɗin abin da ka faɗa? Saif fa namiji ne kuma na tabbata ko kafin ya warke aka aura masa mace tsaf zai zauna da abarsa bare yanzu da ya samu lafiya rass da shi." Daɗi ne ya mamaye zuciyar Sarki Aminullah saboda yadda take bawa gabaɗaya iyalinsa muhimmanci, kallonta ya yi cikin ƙauna yace, "To me ƙanwa ai nima ba gulmar ta na yi ba gani na yi dai kamar a bari ya ƙara samun lafiya amma tun da kince haka shi ke nan, ai Saif da Salman duk ɗaya ne Allah ya yi musu albarka. In sha Allah zan tara su da maganar." Fulani Maryama ta kasa ɓoye farin cikinta a fili har sai da ta bayyana a sarari ta ce, "Allah ya tabbatar mana da alheri ka ga a ce har yanzu Yarima na yawo babu mata ne ai sai a saka masa rauni tun da shi jagoran al'umma ne." Gyaɗa mata kai ya yi ya faɗa duniyar tunani dan Allah ya sani yana faragabar ranar da za a ce Salman na riƙe da ragamar masarautar, dukda irin ƙaunar da yake ji zuciyarsa na yi masa. Amma haka kawai yaji yana fargaba. Ganin ya yi shiru yasa Fulani Maryama ta ce, "Tunanin me kake yi ranka shi daɗe?" Murmushi ya yi yace, "Ina tunanin yadda watarana za ku wayi gari da rashina, amma a kullin ina addu'ar Allah ya haɗa kan zuri'a ta." Duk yadda Fulani Maryama take da burin Salman ya samu nasarar ɗarewa kan karagar mulki, amma wannan kalaman na Sarki Aminullah ba ƙaramin raunata mata zuciya ya