Showing 165001 words to 168000 words out of 198792 words
Chapter 56 - ZEE-BABY-1-AND-2 COMPLETE HAUSA NOVEL By hausanovels001.txt
ta ganta kirjin Sardauna ta kura masa idanu kallon da ya matane yasa ta sada kanta k'asa ta cusa kanta kirjinsa tana zubar da hawaye ga wani irin sanyi da takeji zazzabi ya rufeta.
matseta yayi sosai yanajin hucin zafin zazzabi jikinta na ratsashi, ajiyar zuciya yake ya kankameta sosai yana shafa laulausan gashin kanta da ya zubo ya rufe mata fuskarta yana tatara mata gefe daya,ya janyeta jikinsa makaleshi tayi tana rawar sanyi.
Rankwafa wa yayi bakinsa saman kunnanta yana shafa fuskarta "ki sakeni zan hada miki magani bana son zazzabin jikinki ya kara fadar maganar cikin wani yanayi na shauki.
Sakinsa tayi tana nishi.
Ya mike ya sabka ya hada alluran ya shigar da ita jikinsa cikin mugunta ya tsira mata.
hadiye kukan ta tayi ta shige jikinsa sosai ahankali ta furta"Yayana ina sonka bazan iya rayuwa babu kaiba kamun adalci kar ka rabu dani pls Sardauna."
Makaleta yayi yana wani irin numfashi jiyake kamar ana kara masa sonta da kaunarta sam bazai iya rayuwa babu zainab ba.
k'asan makoshi yayi magana yada bazata jiba ya tura kansa k'asan wuyanta yana jujuya kansa"My Abulena kin gama da rayuwata sonki yamun mugun kamu bazan iya cutar dake ba gashi kin kashe rai amma na,saka miki idanu na kasa fadawa kowa saboda banaso amuzanta mun ke sorry amma dole zan hukun taki.
Zeey kuwa jinta jikin Sardauna ga, Alluran da ya, mata bacci ya dauketa,
sai saukar numfashinta Sardauna yaji.
Janyeta yayi ya sabka ya dauki waya ya kira ghaisha, ya fada mata komai amma baice zeey ba ce ta zubar yace itama bata da lfy zazzabi take ghaisha tazo ta kwana da ita shi jinyar Nisha yake.
Bajimawa kuwa su ghaisha sukazo duk dare yayi har ummi gani zeey ba wani buguwa tayi ba suka koma ghaisha kade ta tsaya gurin zeey sai daddah tace ita zata kula da Nisha amma Sardauna ya tsaya su kwana tare.
Sai can tsakiyar dare Nisha ta farka,Sardauna ya kaita toilet ya mata wanka da ruwan gumi ya canza mata kayan da yaje gida ya kawo, ya bata abunci taci da maguguna ya fada mata gaskiya cikin ya zube haka tayi ta kuka tana cewe zeey ta cuceta amma ta yafe mata dan Allah Sardauna karda ya taba zee ko ya mata wani Abun sai daket ya samu ta koma bacci shima ya kwanta.
Ashe abinda basu saniba Daddah ba bacci take ba idanunta biyu ta jisu tayi mamakin ya akayi zeey ta zubarwa da Aisha cikinta, ahaka har bacci ya dauketa.
Washe gari bayan Sardauna yaje gidansa ya dawo lokacin zeey taji sauki zazzabin Sardauna ya sallamesu amma basu tafi ba ita da ghaisha suna gurin Nisha wacce ta sake da zeey ta nuna babu wani Abu itace ke Jan zeey da hira tana nuna mata karta bari yan gida su sani taji dadin hakan damuwarta daya Sardauna baya kulata.
Da misalin karfe goma shadaya na safe dakin cike yake da yan uwa suna ta zuwa dubiyar Nisha kowa yaji zafin fitar cikin dan sunyi mutikar mamaki cikin wata biyar ya zube kai tsaye batare da tayi doguwar jin yaba ko ya nemi kasheta.
Zeey baby ce zauna kusan Nisha tana rike da hannunta zeey "my dear wlh inajin ciwon wannan zubewar cikin fiye da tunaninki.
Sardauna ne ya shigo da sallama karaf akunnensa idanu suka hada da zeey ya zafga mata harara.
kanta ta kauda zuciyara na mata daci kamar daga sama sukaji murya daddah tace"tsaninku da Allah acikin ku biyu waye ya zuba maganin zubar da ciki alemo da gangan.
Arikice suke kallonta gabaki dayan dakin suka hada baki wajan furta"innalillahi wainnahilahir Rajiun!!
Daddah tace"wlh dole mutum ya zuba maganin tsakanin Aisha da Zainab.
Zeey barkewa tayi da kuka ta, tashi tazo gaban Daddah tana raraba idanu"Sardauna zuface take keto masa hankalinsa amugun tashe idan yana kaunar abin da, zai batawa, zainab suna to yana kaunar mutuwarsa.
Ghaisha tace"nifa bana gane me kuke nufi..kamar daga sama suka tsinto muryar Rabia ta shigo tana cewa"yo dama ta yaya zaku gane ni Nice na keda shedar kumai.
Zeey ta nufi gunta yauwa munafuka yar iska ai dama nasan hakkin rai bazai barki ba dole jini zai tambayeki ki kawo kanki.
Hannu Rabia ta dagawa zeey"dakata malama ke Nisha tsakaninki da Allah ki fadi gaskiya kawai kice Zainab ta zubar miki da ciki dan me zaki boye.
Gabaka dayan dakin ya dauki salati.
Nisha ta fashe da kuka tana girgiza kai" dan Allah Rabia meyasa zaki tonawa yar uwata asiri wlh na yafe mata.
Jikin zeey ko ina rawa yake taji ta tozarta ta kasa koda motsa dan ya tsanta.
Sardauna ya isa gaban Rabia yana karantar wasu yanayi ga me da ita cikin daka tsawa yace"dan ubanki waye shedarki na cewa zeena itace ta zubar mun da cikina.
"Wlh itace amshi waya ka kalla idan baka yarda ba."Wayar Sardauna ya amsa ya kurama idanu zeey tsaye a kitchen tana waige waige ta ciro magani arigarta ta bude fridge ta dauki drinks irin Wanda Nisha ta sha ta ballo maganin ta bude ta zuba ta girgiza sosai ta maida dan hancin ta rufe ta maida fridge tana tsalle da ihu tana juyi da rawa tana cewa"Sardauna na tsaneka ban taba sonka ba sai na dauki fansa bana yafiya bana Afuwa kuma bani manta ranar daukan fansa dole cikin Aisha zai zube zan kasance cikin farin ciki.
gabaki dayan ilahirin jikin Sardauna rawa yake.
yan dakin dikira suke da salalami.
Zeey ta barke da kuka ta fada saman Sardauna"Yayana ka yarda, dani dan Allah karka bari na tozarta wlh ba ni bace saidai idan wani sharri ne za'a dauramun don Allah kayi wani Abu akai.
Sardauna idanu kawai ya kurama zeey idanunsa jajur.
ghaisha tace"Rabia zo nan."Sardauna yace"ghaisha wata shedar kike nema bayan wannan.
Rabia ta juya zata gurin ghaisha Zeey ta saki Sardauna tayi wani irin uban ihu tayi kukan kura ta damki wuyan Rabia ta mata muguwar shaka, amma sai kawai ta yanke jiki ta zube k'asa sumammiya.
Aguje Sardauna yayo kanta yana kiranta gabanta ya zube ya dagota ya rungumeta yana shafa fuskarta"Zainab tashi kallon Rabia yayi yana mata wani mugun kallon tsana yace"kinsan Allah Yau zakici durin Uwaki huncin ki sai yafi na zainab.........................โ๐ป
*8/February/2020*
*๐๐๐ฉ๐ปโ๐ฆฑZEE BABY๐ฉ๐ปโ๐ฆฑ๐๐*
MALLAKAR UMMU FAREESA NE
*DAN ALLAH KARKU FITARMUN DA BOOK WAJE*
*Book 2 ๐๐ป12*
....Ciccibar zeey Sardauna yayi.
Ya Mike tsaye ya kalli ghaisha"momyna ku rike min ita zan dawo gareta ta amsa min tambayoyin da zan mata sam bzn yarda da wannan abun ba wlh akwai Wanda ya saka zeena sam bz halinta bane,ya fada yana ficewa daga dakin.
Nisha ranta yayi mugun baci taya Sardauna yake nuna yafi son zee akan cikinta gashi yaga shaida amma ya kasa daukar mataki akanta saima cewa yake sai yayi binci ke, fashewa tayi da kuka.
Ghaisha ta rungumota"Kiyi hakuri Aisha bari kukan, Rabia ta yaya kina kallo momy tayi haka amma kika kasa fadawa Aisha ko Sardauna ko ki dauke lemon ki canza kika bari tasha saida mai afkuwa ta afku zaki kawo sheda, kin kyauta Kenan.?
"Dan Allah kuyi hakuri wlh ban zata ba zata iya kisan kan."daddah tace"Karya kikeyi kece babbar munafuka zainab bazata iya wannan abun ba dole da Wanda ya sakata ko sharri jinnunta ne ba.
Ghaisha tace"Tabbas akwai lauje cikin nadi.
Idanu Rabia ta fara cicirawa"kuyi hakuri wlh bani na saka taba.
Umma hauwa wacce tunda ake abun batayi magana da idanu take binsu. Salma tace"Koma miye ai gashi dai zainab aka gani amma nasan tanada hujjar yin hakan kekuma ki jira Dr Sardauna zaki masa, bayani tsaf munafukan yan aiki kawai.
Nisha cikin kuka tace"Allah ka sakamun da gagawa."Umma ta buge mata baki"yar uwar taki kike bari da Allah yarinya da Aljanu ke damunta ai wlh zasu iya hada komai domin su kuntata mata."ghaisha tace"Hakane kiyi hakuri Aisha Allah ya baki Wanda ya fishi.
Sardauna yana shiga dakin da ya kamata ya duba zeey ya fara bata temakon gagawa yakai minti talatin kafin ya samu ta farfado.
Amma bata haiyacinta sai fizge fizge take,rungumeta yayi gam jikinsa"zainab bazan iya cutar dakeba duk da idanuna sun gwadamun gaskiya.
Bin kicen lafiyarta jininta ya hau sosai drip ya saka mata ya fice yaje yaci uwar Rabia.
Da sallama Sardauna ya shigo yana raba idanu"Ghaisha ina Rabia.? "wace Rabia bayan kazo ka fita da ita kace zaka kaita gurin yan sanda.?" ni kuma wlh ban shigo ba kinga abinda nake zargi ko wlh mutanan zeey ne wlh ni dama nasan zainab bazata, aikata haka ba sam jikina bai ba ni wannan Rabiar mutum bace saboda zeey tana tabata ta zube asume shiyasa nace ku rikemun ita na duba zeey na dawo gareta kunga sunyi sufata sun zo sun tafi da ita wlh Allah duk ranar da suka sake kusantar zeena sai na kunar dasu kome zai faru ya faru nima shegen kai nane inama ace mutum ne yayi ma zainab haka wlh Allah da yayi. nadamar zuwansa duniya amma suma ina Addu'ar Allah ya hadamu su sake zuwa hammmm.
Daddah tace"Wlh abinda na gama fadi kenan yanzu cewar anya ba sharrin Aljanun zainaba bane.
Nisha kuresu tayi da idanu takai ci da bakin ciki sun mata yawa. Sardauna yace"gud zasuci ubansu wlh zasu fice ta karfin tsiya abin ya dawo kaina inaji ina gani an zubar mun da ciki ya fada yana wucewa ransa amugun bace.
Duk jama'ar dakin mamaki ne ya kamasu da Al'ajabi dan tabbas matar ba mutum bace.
Sardauna yana fita gurin zee ya koma ya zauna bakin gado ya dago da kanta ya kai bakinsa kunnenta ya fara karatu da karfin gaske.
Motsi zee ta fara ta fashe da kuka ta rungume Sardauna da shiko ya dage yana zuba mata karatu.
"Yayana me yasa ka kasa, yarda dani ka tsaneni ko.? Ta fada tana fizge fizge Dafeta yayi sosai yana cigaba da karatun, kukan ta fasa ta lafe cikin jikinsa ta lumshe idanunta dan tanajin dadin karatun bacci ya sake dauketa babu irin karatun da Sardauna baima zeey ba amma babu alamar Aljani ayanzu dole ya barta dan baccinta ma take, idanu ya kura mata yana kara rungumeta yana shafa laulausan gashinta.
*************
to fa haka aka yini aka sake kwana babu labarin Aljanin zee babu irin rukiyya da ba'a yi mata ba a hospital su daddy har babban malamin rukiyya suka dauko amma zee babu labarin aljani Sardauna yace gudawa sukayi yana jiran dawowarsu zasuci ubansu daidai yake dasu.
Sosai Sardauna yake kula da zee saboda Rabiar asalin tana gidan Sardauna har hospital tazo Sardauna babu irin abinda bai ba tabbas ya gano wacan Aljanace yaji dadin samun hanyar kare zee dinsa kuma yan uwansu duk sun yarda zeey bazata zubar da cikin Nisha ba.
*****************
Bayan kwana biyar cikin kwana biyar dinan
zeey kullum da zazzabi take kwana ga amai tamkar zata amaye hanjinta bataci bata sha do Sardauna ya maida hankalinsa gareta daddah da umma suke jiyar Nisha Sardauna shida ghaisha kullum sai ya d'aura mata drip shine abincinta saida suka kwana biyar hospital sai yaune
daga zee har Nisha suka dawo gida saidai.
Sardauna yana cikin tashin hankali na cirewa Nisha mahaifarta sakammakon lalacewar da tayi mutikar tana jikinta tofa tamkar tana hanyar mutuwane nan kusa mutikar ta sake daukan ciki dole tasa ya cire aboye yana kukan tausayinta da bazata haifa masa wani danba gashi Allah ya masa son yara saidai yayi alkawalin bazai fadawa family ba zai boye abin azuciyarsa ko ita bazata saniba zai kulata yabata soyayya sosai dan yasan shine sila tunda shi ya mata cikin.
Abinda ya rage masa damuwa ya bin ciki zeey d'insa ciki gareta tsawo sati hudu saidai laulayin da yake damunta.
Sardauna farin ciki haukane kawai bai ba nan take ya manta bakin cikin da yake ciki kudi yayi ta rabawa sadaka ya goyata cikin dakin yana zagayawa da ita yana ihu ghaisha saida ta dokesa tukun ya sauketa ita dai zeey sororo tayi tana kallonsa dan yanzu kunyar kowa takeji gani take ta tozarta. Sardauna ko ko ajikinsa sosai yake bata kulawa shiyasa saida sukayi kwana biyar a hospital kafin ya sako matansa su dawo gida yau da safe.
Kakaf family dinsu babu Wanda baisan zee nada ciki ba murna kowa yake sosai suke farin ciki suna Addu'ar Allah ya tsareta daga sharrin Aljaninta.
โกโกโกโกโกโกโกโกโกโกโก
Da misalin karfe biyar na yamma zaune suke a babban dakin taro na gidansu daddy an tara yan uwa kowa yana nan maza da mata zeey na kusan ghaisha ta rungumeta Nisha kusan ummi Raiyan.
Mairan karfe yace"Alhamdulillah Allah abin godiya da ya kasance duk wannan yawan zuri'a nawane kuma masu kaunar junansu dan haka inaso kuci gaba da hada kanku dan haka wannan taron an hadashine saboda zainab da Aisha da kuma Sardauna
kunji yada Aljanan zainaba suka so hada fitina tsakanin ma'auratan da abokiyar zamanta da wasu kalilin cikin dangi to Alhmdllh idan dai mutum zuciyarsa daya to babu abinda zai samesa na sharri koda yaso samunsa Allah zai kawo sauki cikin lokaci kankane kamar yada ta faru da zainab dan haka mun hada taron nan ne domin ku sake ganewa cewar ba zainaba bace ta zubar ma da Aisha cikinta aikin mutanan boyane dan haka mu dage da tayata da Addu'a Allah ya rabata da wanna bala'in da take ciki dan ciwon Aljanai ba karamin ciwo bane ke kuma Aisha Allah ya baki hakurin jure ciwon rashin da kikayi ya baki Wanda ya fishi.
Ga baki daya suka amsa "Amin.
Maijidda tace"wlh ni dama nasan zainab bazata iya wannan abuba."zainab tace nima haka. Kowa na gurin ya shaidi zee har Nisha tace"wlh dama jikina ya gama bani ba ita bace Allah ya isa da akaso hadani da yar uwata ta fada ta Mike ta nufi gun zee suka rungume juna suna kuka.
Kowa yan dakin saida ya tausaya musu kawu Saminu yace"to kuyi hakuri Allah na tare daku Aisha Allah ya miki albarka ya kauma baki mai anfani.
Nisha ta sake samun matsayi cikin family kowa sai Albarka yake samata da yabon hankalinta.
Nuhu yace"wlh Aljani shedani ne yaso hadasa fitina tsakanin yan uwan juna Allah bai bashi sa'a ba."Sardauna ya zubawa matansa idanu cike da so da akaunar so bama zeey kamar ya kamota ya cinyeta yakeji ya matsu su tafi gida sai wani lumshe idanu yake yana shafa kwantacciyar sumar kansa.
Daddy yace"yanzu sai magana ta gaba shine Raiyan da Saminu kanin mijinta mun yanke zata aureshi taci gaba da zama karkashin inuwar dan uwan mijinta mun gama magana da ita da kuma mahaifiyarta ta kuma amince shima ya amince.
dariya yan dakin suka dauka baki daya zeey kuwa murna tasa tayi dan ihu tana cewa"yauwa daddy inaso ahadasu Allah ya basu zaman lfy da kwanciyar hankali.
Hassan da hussaini ma murna sukeyi Ammi tace"Alhmdllh ai shiyasa tun farko na amince haka Allah ya tsara mata aurqn yan uwa biyu meye ajikin wani jansi da baza'a aura ace sai balarabe dan uwanta kuma ai zubin larabawan gareku wlh naji dadin hakan yayi min dari bisa dari amma Raiyan nawa take da zatace bazata sake aure ba wanna zuri'a mai albarka Ubangiji ya kara hade kanku."suka amsa" Ameen.
Maijidda tace"kanina Allah ya kara tsarzmun kai duk Wanda zai cutar dakai mutum ko Aljan Allah ya shiga tsakanin ku dashi Allah ya baka wani kuma insha Allah cikin jikin zeeanab yafi karfinsu nan gani nan bari."Dariya Sardauna yayi yana kada kai.
Nisha takai ci da bakin ciki yasata ta Mike tabar gurin ta fice tana matsar kwalar bakin ciki rabuwa da cikinta saidai tayi kudirin zubar da cikin zeey idan yaso suma sai ace aljannanta ne suka zubar.
Haka taron ya watse cike da so da kaunar junansu daddah ta kama zee suka tafi part d'inta su ghaisha da su ummi suka koma ciki ummi Raiyan duk kunya ta gama kamata jin zata auri kanan mijinta sai sun ne sun ne take.
Su Sardauna suna gidan har bayan isha'i kafin suyi shirin tafiya zeey na rungume da Ammi ta kurawa Sardauna idanu sai lumshesu take dan wata irin jaraba ce take cinta sotake tajita a jikin Sardauna yana cacakarta da karfin gaske bakinsa ta kurawa idanu suna magana da Daddy kan sanya ranar auran Hafeeza da Ahmed.
Ghaisha tace"Allah ya kaimu goben hankali ya kwanta yanzu ai Autana zo kaji."Sardauna ya mike daga kusan daddy ya zura hannunwansa cikin aljuhu yana takunsa cikin isa da kasaita fuskarsa dauke da murmushi ya nufi gun ghaisha.
Nisha ta kureshi da idanu tanajin mugun sonsa na azalzalar zuciyarta sai lumshe idanu take.
Ya zauna kusan ghaisha ya kwanto jikinta"My momy gani."Autana Allah yama Albarka ya karemun kai ta fada tana shafa kansa.
"Ameen momana mu zamu tafi gida bacci nakeji kwana biyu banida nutsuwa.
"Bakomai ai gashi Allah ya warware komai cikin sauki tashi muje na hada maka coffee kasha ta fada tana janyeshi jikinta ta Mike ta mikar dashi suka nufi kan dining.
Hassan da hussaini mamakin shagwabar Sardauna suke sukayi ta musu dariya.
Daddy yace!"ai zaku gaji idan dai khadija da Faisal ne."Najibi yace"ni wlh kishi nakeyi.
Hafeeza tace" wlh nima."ummi tayi dariya"Aikuwa zakuyi tayi.
Nisha fa haushin kowa takeji kawai dai ta daurene ana raha dan kar agano ta.
Ghaisha kuwa saidai tama Sardauna wayo yaci abunci sosai ta tsiyaya masa fruit yasha tukun ta hado masa coffee da kanta ta kawo masa suka dawo parlo yana sha suna hira da daddy har ya gama ya kalli Nisha"Aisha ku tashi mu tafi gida.
Zuwat ta mike zee ta kura mata idanu tayi Saurin dauke kanta tanawa Ammi magana.
Sardauna ya mike ya nufi gurinsu ummi ya musu sallama suna musabaha dasu Hassan ya kalli zeey"baby tashi mutafi.
Buris tayi da shi saida Ammi ta mikar da ita tsaye bata kallesa ba ta nufi gun ummi ta rungumeta ta mata kiss ta rungume su hussaini suka yi sallama taje tama su daddy sallama da ghaisha Nisha ma ta musu suka tafi.
A cikin mota zeey tana baya Nisha na GABA ita da Sardauna tana rungume jikinsa yana shafa cikinta yana jin haushin rashin cikin sai ciza lips dinsa yake gefe tausayin Nisha yake.
Narke masa tayi ajiki"my Dr kayi