Showing 78001 words to 81000 words out of 198792 words

Chapter 27 - ZEE-BABY-1-AND-2 COMPLETE HAUSA NOVEL By hausanovels001.txt

27 Nov 2024

9751

itace ta zabamun mahabeer ya bushe da dariya "kaide fadi gaskiya dama kanaso sai ayi yar gida kai tsaye yace"eh dama da ita za 'ayi bro ko wata zaka samomun ne? ya fadi yana masa wani Dan iskan kallon raini afakaice murmushi Mahbeer yai "haba wata kuma wlh naji dadin hakan Daddy yace"Faisal da gaske ka yarda zaka auri Aisha ayau insha Allahu zanga mahaifinta"eh Daddyna ya fada yana rumgume ghaisha dariya Daddy,

yayi ummi Raiyan ma dariya tai" kai amma naji dadi Allah ya Sanya Alkhairi sukace Amin Daddy wayarsa ya ciro ya kira Abban Nisha bugo daya ya daga da sallama " wa'alaiki sallam Alhaji Bashir inason ganin ka da yamma zanzo? OK nagode sai anjima ya tsinke kiran yace" Saminu bayan la'asar sai mu tafi yace zai jiramu? " to shikena ba damuwa Allah ya kaimu yasa haka shi yafi Alkhairi Nuhu yace" Ameen Daddy yace kutashi mutafi gun mai ran karfe yaji komai ghaisha tace"wai yau baza kuci abuncin ranaba ne har karfe uku zatayi Raiyan tashi muje Auta tashi muje kaci abunci fuska ya yamutsa ashagwabe yace." Mamana ni banson cin komai? " No tashi muje kamashi tayi suka nufi kan dining su Daddy suna dariya suka Mike ya kama hannun zee baby Dan duk abinan da ake tana jikin Daddy tayi lakwas tarasa meke mata dadi dukansu kan dining suka nufa kowa yaja kujera ya zauna zee gun mahbeer ta koma ghaisha tayi serving d'insu jalof din shinkafa ce taji nikeken naman rago da kayan lambu da soyayar kaza asama sai uban kamshi take zee kore damuwarta tayi sunacin abuncinsu tare ita da mahbeer Wanda hakan ya Kular da Sardauna daket ghaisha ta takura masa yaci mai Dan yawa ya Saki jikinsa saboda ghaisha sai tambarsa take ko bashida lafiyane Daddy yace"abinda abokinsa da matar da zai aura suka masa jinki abun karamine khadija ai Dole zai damu murmushi yay "Daddy wlh basa gabana dama ta ficemun arai Aishar tayimun dari bisa dari Allah ya tabbatar da Alkhairi sukace "Ameen Allah yayima Albarka ya Amsa da "Ameen zee ta kallesa karaf suka hada idanu wani irin mugun yanayi suka shiga atare idanunsu suka lumshe atare zee kanta ta boye jikin mahbeer tana sabke ajiyar zuciya idanunsa ya bude yana kallonta ganin yada ta manna kanta jikin mahbeer yasa ya Mike yanajan tsaki yabar gurin Sam babu Wanda ya lura suna aikin kwasar jalof mahbeer ya kalli zee ya dagota Dan yau tayi mugun taso masa sha'awa daurewa kawai yakeyi yanzu haka sai yayi wanka Kafin yayi la'asar" zee ki zauna kin koshine kallonsa take tana lumshe idanu Wanda suka fara Ja murmushi ya Saki ya Mike ya kama hannuta Dan yagano bacci takeji

dariya suka musu suna binsu da kallo yana rike da hannuta har bedroom can ya dauketa ya kwantar da ita ya lulubeta da blanket ya rankwafo ya mata kiss"my zee babyna maza bacci rikoshi tayi ta fashe da kuka" Ya Allah don Allah ki sakeni my zeena kinaso ki kaini bango ganin ba sakinsa zatayi ba ga kukan da take yasa ya tsaya yaga ita gudunta bata masa komaiba rumgumeshi tayi gam tana kuka bayanta ya fara bubbugawa ya gyara mata gashinta yakai bakinsa kunneta yana mata waka yana shafa gashinta da lalami da kalamai masu dadi shiru tayi ta Kara makaleshi sai sukurtu take tamkardai bataji yada take so ba da ta rumgumeshin cikin wayo da dubara yasamu tayi bacci yaji tana fitar da numfashi tare da sabke ajiyar zuciya murmushi yai ya janye jikinsa ya gyara mata kwanciyata ya sakar mata kiss saman lips d'inta yana shafa kyakywar fuskarta" I love u my zeena wlh ina tsananin sonki da kaunarki na matsu a daura mana aure hakurina ya fara gazawa akanki dauriyata ta kare wlh duk lokacin da zaki rabenni sai nayi wanka gashi ke baki dauki komai ahakaba juyi yaga ta fara tana lalube ta kwabe fuska tana kiran "Sardauna tana nishi sai mimmk'ewa take dariya yayi "kai rashin jituwa batayi ba kijifa fitina me Dr yayi kuma jin ta riko hannusa tana cewa"Yaya Sardauna please kark.. Da Sauri ya janye hannusa yana dariya ya Mike ya rufeta yana cewa " karya mike Allura ko ya fice yana dariya lokacin da ya fito su Daddy sun tafi part din Daddah sai ghaisha da ummi Raiyan nanah na zaune saman cinyarta suna hira kunya tasa ya nufi hanyar fita yana Sosa kai dariya ummi Raiyan tayi ghaisha tace"wlh mahbeer akan momy bashida kunya dariya kawai yayi ya fice yana zuwa part d'insu bedroom dinsa ya nufa yayi wankan tsarki ya canza kaya ya fito ya nufi part d'insu Daddah Dr Sardauna ko yana zauwa ya kure karfin Ac ya fada saman bed ya shige cikin blanket ya kwanta yana juyi da Jan tsaki har bacci yayi Nasara daukeshi, Daddy ko suna part d'in Daddah mahbeer ya iskosu har sun fada musu abinda ya faru da shawara da suka yanke tunda Sardauna yace Zainab ta zaba mashi Aisha kuma ya amince yana Sonta Daddah da mai ran karfe sunji dadi sosai, Ana sukaci gaba da hira saida aka kira sallah la'asar suka tashi akayi Alwalla suka nufi masallaci daga can zasu gidansu Nisha Kiran sallah la'asar ne ya tashi Dr Sardauna bathroom ya shiga ya dauro alwalla jallabiya ya dora kan kayansa ya tafi masallaci ummi Raiyan ce ta shigo bedroom d'in taga zee sai sharara bacci take tashinta tayi fargigit ta farka ta kalli umminta "tashi maza kiyi sallah "ummina yanzu ne fah na fara baccin? " eh tashi dai sabkowa tayi ta shiga bathroom tana turo baki ta dauro Alwalla ta fito ta yafa mayafi ta hau saman Darduma ta tayar da sallah ummi ma tashiga ta dauro Alwalla ta fito ta shimfida wata darduma ta tayar da, sallah zee tana gamawa hafeeza ta shigo zee ta kalleta" sister ina kika shiga tun d'azu? " ina gidan Daddah fah bari nayi sallah yau wanka zani Swimming pool nayi murmushi zee tayi "zan biki amma bazan wanka ba ta fada tana nufar dressing mirror ta gyara gashinta ta daure da wani ribbon mai shegen kyau ta gyara fuskarta wardrobe ta bude ta ciro wata Riga pink color mai santsi iya gwiwa mai masifar kyau ta cire ta jikinta ta saka Dan ko tayi sha'awar wankama sai tayi wow nace tayi wani mugun kyau amma komai nata ya fito rigar ba karamun karbarta tayiba ummi Raiyan ta kalleta ta Mike"zainaba kinci gidanku bazaki fita ahakaba shagwabewa tayi" ummi Swimming pool zamu fah abaya ta dauko ta sakamata saman kayan "bakiga akwai ma'aikataba agidan kuma ta gabansu zakubi idan kunje sai kicire Dole ta hakura ummi ta janyo hannuta "muje parlo idanu hafeeza ta gama shiryawa sai ta fito ku tafi Dan tasan halin 'yar tata zata iya cirewa shiyasa ta mata wayo suka fito parlor ta jirata

Bayan sallah la'asar su Daddy suka tafi gidansu Nisha Daddy ya kira babban amininsa Alhaji shazali harda mai ran karfe aka tafi Alhji bashir ya tarbesu da hannu bibbiyu bayan sun gama gaisawa ne Daddy yayi gyaran murya yace"Bashir abinda ya kawomu Akan maganar Aisha ne da Faisal yace ita yakeso kaddara ta rabashi da wacce zai aura to da nace yasamo wata yace Aisha ya zaba wai harma yazo sunyi magana shine nace to bari muzo kar muyi k'asa agwiwa Abu na gidane mairan karfe yace "idan babu damuwa Bashir munaso atsayar da magana munzo neman aure Bashir k'asa yayi da Kansa cikin jin kunyar surikin NASA yace" to madallah ai duk Abu na gidane tunda har sun daideta banida ja bari na kira Alhaji yanzu mik'ewa yayi ya fito yana farin cikin abun dama shi yaron da Nisha take so bai bawani kwanta masaba parlon ya shigo da sallama umma Hauwa na zaune Nisha na jikinta akwance ta Mike hayatu na zaune yana waya zama Bashir yayi yana kiran waya Babban Wansa ya kira yake sheda masa komai cikin farin cikin yace gashinan zai zo ya bada auran Aisha cikin jin dadi ya kashe wayar Hauwa ta kallesa" Alhaji bangane ba fah ta kalli Nisha wace tayi tsuru tsuru da idanu sai kif kif take da idanu Bashir yayi dariya ya kalli Nisha"Aisha kinason Dan uwanki zaki aureshi ko? kunya taji ta rumgume Hauwa ta boye kanta tana daga kai Hauwa tace"ikon Allah Bashir ya warware mata duk yanda akayi har zauwar Sardauna gun Nisha zauwar Dan uwansane yasa ya Mike ya koma gunsu Daddy suka nemi auren Aisha Mamuda ya basu har sadaki Saminu ya bayar nera dubu dari nan take mamuda ya amsa aka tsayar da ranar aure daide da na mahbeer kwana ashirin da bakwai yau daide yayi saura kowa agurin farin cikin yake da wanan Abu mahbeer ana gamawa ya Mike ya shigo ya gaishe da hauwa wacce itama tayi farin cikin sosai sai waya take da kawaye da abokan zama suna tayata murna irin wannan Abun Alheri kai tsaye da Allah ya kawo hayatune yasa nisha gaba yana zagi "Dan ubanki kika yarda aka hadaki da wannan mugun Dr Mara imani zakici ubanki shegiya karaf akunne mahbeer hayatu na zagin Dr Sardauna kuma yasan dalilin zagin da sallama ya shigo Nisha na ganinsa ta Mike ta taresa ta rike hannusa "Oyoyo bro dariya yayi "Amaryar mu aban goro sakin hannusa tayi cikin kunya ta ruga daki da gudu ta boye kai ya girgiza ya zauna kusan umma dariya umma tayi " mahbeer kasa kanwarka jin kunya kaga masifafan da ya takurata tun dazu mik'ewa hayatu yayi yabar parlon ko kallo bai ishi mahbeer ba Dan yaji zafin zagin da yama Sardauna dama yanada haushinsa murmushi mahbeer ya saki" umma ina yini " lafiya lau ina momy kai ya Sosa na barota tana bacci yau rigima takeji dariya umma tayi zatayi magana wasu mata uku suka shigo da sallama mahabeer ya Mike "umma suna jirana na tafi "to zanzo gidan zuwa dare dariya yayi ya fice a bakin get ya samu su Daddy sun fito suna shiga motar Nuhu da sauri ya karasa mairan karfe zai shiga mota ya rikeshi yana tsokanarsa sandar hannusa ya kwada masa dariya mahabeer yayi ya sakeshi ya gewaya mazaunin direba ya tashi motar ya mata key yabi banyan motar su Nuhu get aka bude musu suka fice................... ✍🏻

*💖💖👩🏻‍🦱ZEE BABY👩🏻‍🦱💖💖*



*DAN ALLAH KARKU FITARMUN DA BOOK WAJE*


*👉🏻29*


....saman titi Mahbeer ya harba motar cikin nutsuwa yake tukinsa hankalinsa kwance yake sharara gudu yana tunanin zee dinsa ko ta tasho tayi sallah kawu saminu na masa hira dariya kawai yake hankalinsa kwance yake driving dinsa ya dauki hanyar kofar Marusa lowcos,
Nisha ko tunda ta shige bedroom ta fada saman bed ta lumshe idanunta tanajin wani irin dadi tamkar dama tanaso haka ta tsinci kanta afarin ciki sai juyi take tana sakin murmushi ko me ta tuna ta zabura ta bude idanunta ta dafe kirjinta"wayyo nashiga uku Yaya Sardauna tsama fah gareshi gashi inajin tsoronsa ya zanyi zama dashi mahafus zaice naci amanarsa murmushi tasaki "to ai Dr yacemun nasaki jikina dashi nabar tsoronsa bazai dokeni ba Sorry mahafus ni Dan uwana zan aura ta fada tana kwanciya rigingine ta shiga duniyar tunani batasan lokaci yajaba saida taji hassan na kiranta"Aunty kizo Abba na kira mik'ewa tayi tana turo baki"wlh idan karyace zaka sani tare suka fito Bashir yace"Aisha zo mana kusansa ta zauna cike da kunya tana sunne kai "Abba gani? " yauwa Aishatul humairah ga kudin sadakinki nakine halak malak kiyi yanda kikeso ya kamo hannuta ya Dora mata "kai Abba Allah ni ba ruwana ku rike na Baku kai da umma bari na dauki dubu biyar nasha ice cream ta zagi dubu biyar ta ajiye sauran cinyar Abba ta Mike da gudu tayi d'aki dariya abin ya basu shida Hauwa da kallo suka bita har ta shige hayatu ko sai zabga Mata harara yake

bangaran su mashakurah bayan sun koma gida iyayan babu Wanda ya shiga sabgarta bedroom ta shiga ta fada saman bed ta fashe da kuka tana nadama da danasani ga son Dr Sardauna kamar ya kasheta jitayi ta tsani bandar arayuwarta da bai shigo rayuwartaba da hakan bata faruba da babu mai rabata da Sardauna Miji na kerema sa'a yayarta takira tana fadamata duk abinda ya fara tsabar rikita da takaici da mamakin abinda mashakurah ta aikata yasa ta tsinke kiran kukan mashakurah ya karu rana zafi inuwa k'una lalai ta kira tazo su yanke shawara mai fitar dasu amma tana zuwa iyayan mashakurah suka hanata shiga gunta shiyasa yau ta wuni cikin kunci da ta kura sai kuka take tana nadamar
aikata zina arayuwarta,

✨✨✨✨✨✨✨✨

khalisat ce zaune ta rabka uban tagumi ta rame tayi baki sai abkin kuka tana kiran Sardauna Aunty amarya na hango itama tayi baki ta rame sai wasu kuraje da suka fara fito mata ta nufo gun khalisat "wai keba zakiyi tawakali ba kiyi hakuri ki amshi kaddara ki cireshi aranki tunda duk inda mukaje sai ace babu aure tsakaninku amma ai nace miki kiyi hakuri har wa'adin da boka kafi madubi ya daukarmun idan yacika mukoma mugani zai sake mana sabon shiri kallon uwar tayi ta fashe da kuka"wlh momy duk kece kika jawo mana muna zaman zamanmu da mutane masu mutumci son zuciya yasa kika aikata abundan muka aikata gashi munyi biyu babu ke babu ni babu Aunty amarya kanta da tasani takeyi Mara anfani. kukan itama ta fara ta rumgume yar tata tana bata baki akan zasu koma insha Allah tayi hakuri ita inna kallansu take ta rabka ta gumi Dan tasan duk laifintane itace bata Dora mariya atarbiya ba ta koya mata son abin duniya da da mugunta da makirci har itama ta Dora yarta a turba Mara kyau Allah ya kyauta yasa mufi karfin zuciyarmu Amin ya Allah


Mahbeer suna zuwa gida su kawu saminu suka shiga motcinsu suka nufi gidajamsu mahbeer ko part d'in Daddah ya nufa yana tsokaransu, Sardauna bayan ya dawo daga sallah ya cire jallabiyar jikinsa ya kwashi wayoyinsa ya dauki kwalin sigari da lemo gudu biyu ya fito ya nufi swimming pool can nesa da ruwan ya zauna gun wash gugayan kujeru ya zauna yana shan sigarinsa yana kallon ruwa zee suna zaune a parlor tana jikin umminta ghaisha na tambayarta"momy fushin me kikene? baki ta turo "ummina yo ba ummi bace tace wai na tafi Swimming pool da abaya dariya ghaisha tayi "yi hakuri kinsan fah akwai ma'aikata yan aiki da masu gadi zasu ganki kibari da kun karya kwanar sai kicire murmushi ummi Raiyan tayi tana shafa kan zee da take turo baki hafeeza ce ta fito da katon hijab cikin ko yar mitsitsiyar rigace ta wanka ta Iso "sister tashi mutafi mik'ewa zee baby tayi tana kallon hafeeza "sister ahaka zaki? murmushi tayi ta janye hijabin dariya zee tayi ta ce"ummina yanzu na gano dariya suka musu hafeeza ta kama hannu zee zasu tafi ummi tace"baby kawo wayarki karki sakata ruwa "ummina pic zamu dauka ta fada suna ficewa daga parlon anutse suke tafiya aikuwa inda sukabi suka hadu hashim me wanki da isah mai ba shifkoki ruwa suna karya kwana zee ta cire Abayarta da gudu ta nufi gun ta ajiye abayarta saman kujera hafeeza ta iso ta cire hijabinta ta ajiye zee ta zauna hafeeza tace" tashi muyi nutso tare kafada zee ta makale "jeki ba yanzu ba zanyi jeki zanyi pic ne da gudu hafeeza ta nufi gun ruwan ta tsunduma tana nutso zee tayi tsaye tana daukar hoto iri iri wani

tayi murmushi wani ta turo baki wani tayi dariya duk abinda take Sardauna na kwance saman kujera na kallonta kai ya girgiza ya lumshe idanunsa yanajin wani irin feelings yada surah jikinta ta baiyana tsaki yaja ya bude idanunsa ahankali kamar bayason magana yace "zee baby karaf akunneta idanu ta fara rarabawa tana neman Sardauna Dan taji muryasa shagwabewa tayi tana turo baki"Yayana naji muryarka kana ina please ka fito wlh tun d'azu nakejin kamshinka Yaya Sardauna dabas ta zauna tana kallon hafeeza wacce take wankanta cikin kwanciyar hankali lallausan murmushi ya Saki Dan yasan bata ganshiba sake kiranta yayi ta shiga waige waige mik'ewa tayi ta nufi gun kujerun da Sardauna yake kwance Dan tabbas taji ajikinta yana gurin yana ganin ta nufo gun ya lumshe idanunsa "Yayana kana inane ta fada tana isuwa gun ta gansa akwance "Yayana shiru ya mata ahankali ta karasu gunsa ta duka gabansa gwiwowinta ak'asa ta riko hannusa "Yayana gani bude idanunka lfy kuwa shiru taji kuma taga kamar baya motsi girgizashi tana kiran sunsa "Yayana ka tashi mana meyasa meka ko bakada lfy yaufa kai angone Daddy ya kira ummi ghaisha yace anyi Sadakinka da Nisha ansa ranar aure daidai da namu da ya mahbeer kwanaki kadan suka rage Yaya tashi kabani gorona namaka zaben mata wlh kun dace najini ina farin ciki duk da bamu shiri dakai amma na zabama ka mata kayarda zaka aureta Yaya Sardauna naji nabaka daraja mai girma nagode kuma insha Allah ni dakai bazamu sake fadaba ai kaima bazaka dokeniba ko angon Yayata Nisha ta fadi tana dariya tana leken fuskarshi shiru bai bude idanuba sai taga kamar yana kokowa da numfashinsa da karfi karfi arikice take zizigashi tana kiransa "Yayana Sardauna menene bude idanunka kaji tashi tayi ta lallaba ta kwanta saman kujera ta rumgumeshi ta fashe da kuka ta had'e face dinsu"Yayana menene don Allah kabude idanunka ko mutuwa dai kayi sauran Dan kuzarinsa da ya rage ya tataro jarumtarsa ya bude idanunsa ya zuba mata idanu hawayenta na zuba saman bakinsa yana lashewa ahankali naji ankira sunana Wanda na rasa nutsuwa nan take na rude fuskata

na janye na kallesa ina shashekar kuka "Yayana wai meye yasamaeka ina baka labarin matarka kayi banza dani zaune ya Mike yajanyoni jikinsa ya kamo fuskata ya zubamun tsumammun idanunsa masu fitar dani haiyaci"my Kanwas mutikar kinaso mushirya dake maza ki hadiye kukanki kimun shiru idan ba so kike ciwon zuciya ya kamaniba da Sauri na dora hannuna saman bakinsa ina girgiza kaina"Yayana wlh na daina

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login