Showing 75001 words to 78000 words out of 198792 words

Chapter 26 - ZEE-BABY-1-AND-2 COMPLETE HAUSA NOVEL By hausanovels001.txt

27 Nov 2024

9738

dear kibar kukan don Allah karki tayarmun da hankali fadamun me ya faru ta fada itama tana shashekar kuka dan tana mugun son zee batason taga damuwarta da sauri zee ta dago muryata na rawa tace"my dear nayi shiru kema yi shiru dan Allah ki temakeni ki auri Yaya Sardauna na tsani waccen matar tasa wlh batada hali da sauri Nisha ta fizge jikinta"haba my zee ya zaki fadi haka mutumin da ko yaushe idan mun hadu sai ya dokeni taya zan zauna da Wanda nake mugun tsoro kuma ai shima bazai yardaba"idan har kina kaunata da zuciya daya kuma kinason na rayu cikin farin ciki ki amsamun zaki auresa ko da bakya sonsa ta fada tana kuka Nisha har zufa wuyace take keto mata ita ba wai ta tsanesa bane asalima tanajin wani yanayi akansa kuma samun kamar Sardauna ayanzu wuya yakema yan mata saide so dayane mahafus takema amma bazata taba tozarta zee ba rumgumeta tayi tana buga bayanta"to yi shiru naji zan aureshi amma kice karya rika dukana wlh aduniya babu mutumin da nake tsoro sama da Yaya Faisal ajiyar zuciya zee ta sabke jin Nisha bata watsa mata k'asa a idanuba hawayenta Nisha ta goge mata zee tace"to muje ku gaisa idanu Nisha ta zaro "wlh bazan jeba marerecewa zee tayi Dole ta hakura suka fito gabanta na faduwa dan zee na mata kwarjini bata iya mata musu duk da ta bata shekaru biyar zee ta bude motar "Yayana gata? kamar bazai magana ba yace"Ok ta shigo mugaisa da sauri zee ta kallesa shima ita yake kallo murmushi na sakar masa na matasa na kalli Nisha muryata na rawa nace"

my dear ki shiga ku gaisa cikin tsoro ta shiga niko na koma bayan mota na lumshe idanuna duniyar jinake tana juyamin muryar Nisha na tsinto cike da nutsuwa tana cewa"Yayamun ina yini abin mamaki rasa naji ya amsa mata cikin zazagar muryasa yace"lfy lau Aisha ya su umma ya karatu ya kika gani kin amunce da zabin zainab zaki aureni amma ki cire wannan tsoron yayi yawa ji muryaki yada take rawa amsa nakeson ji dan yada aka tsara wancan to ba kari ke nake sauraro?? daurewa tayi ta saita muryarta tace" eh Yayamun bazanki abunda my dear ta baniba na amince" gud kanwata to shiga gida bai sake magana ba itama shiru tayi ta juyo ta kalli zee idanunta alumshe "mai dear zan shiga gida da sauri na tataro nutsuwata na bude motar na fito itama ta fito"Nagode Nisha murmushi tayi "kuje yana jiranki zamuyi waya"ok nagode gida ta shiga nima na shiga motar na rufe ya mata key yaja muka tafi"Yayana nagode da kyautar daka ka amsa ai ta maka ko? saida yasha kamshi ya tab'e baki"ai batada laifi tunda a dan koshe take dama siririyace banaso itako Aisha bata cikin ramamu duk bata da jiki sosai kuma tana da kyau daide nata ga nutsuwa kuma ba yarinya karama bace zatakai 23 year gud tamun tunda zabin kice wani irin bakin cikine ya tokareni amma na dake nayi murmushi "yauwa yayana naji dadi mutika Allah ya tabbatar da Alkhairi bai sake magana yaci GABA da driving dinsa cikin nutsuwa

✨✨✨✨✨✨✨✨✨✨✨✨

Wai ina labarin mashakurah da bandar😆lokacin da ta fito da gudu tana kuka ya biyo bayanta yana kiranta bata ko saurare shiba tana bude mota yana shigowa tsoron kar idon sani yagansu ko Ahmed ya fito taja motar da karfi tabar hospial d'in tana rusar kuka tana tafiya mai nisa tayi parking gefen titi "Allah ya isa ban yafemaba bandar fita kaban guri rumgumota yayi ya matseta"my shukurah ina sonki bazan barki ba Dole sai kin kaini gidanku ayanzu na gani daga nan sai na barki jin haka ta buge a hannusa" sakeni to uban jaraba murmushi yayi ya cafko bakinta ya tsotsa iya son ransa lakwas tayi ta narke jikinsa dan abukace take ganin haka ya shiga murzata da tsotsarta kuka ta fara ta fizge kanta ta tashi motar " jarababe kawai "jarababudai tsaki tayi tana tuki bata sake kula shiba har ta ISO gidansu akofar gidansu tayi parking ta bude motar ta fito Dadynta na kofar gida yayi shirin zuwa juma'a yana waya jikin motarsa yaga ta fito tana masifa "bandar fito ka kama gabanka ni ayanzu na sami mai sona aurena saura wata daya kuma yaudara da kamun Allah ya isa yanzu haka cikin ka ajikina wata biyu gobe warhaka anzubar dashi dan ina kaunar Sardauna tsakani da Allah kai baka isa kazo rana tsaka ka kashemun aureba inasoshi kaje na barka da Allah sabkowa yayi ransa amugun b'ace ya wanketa da mari "kinyi karya ki zubarmun da ciki dama jikina yabani akwai ajiyata tare dake saboda nagani a mafarki kuma ke kinyi kadan kirabamu da Sardauna Alhaji Ma'aruf gabaki daya jikinsa rawa yakeyi zufa na keto masa ya ISO garesu mashakurah zatayi magana yace"shukurah ni kikaci amana tarbiyar da nabaki kenan to yanzu komai zai kammala kushiga ciki naje sallah na dawo ya fice yana tangadi ya barsu tsaye Wanda sai yanzu mashakurah ta tuna ba fa a kebe sukeba iya tashin hankali mashakurah ta shiga da gudu ta nufi gida tana wani irin kuka mai firgitarwa bandar jikinsa yayi mugun sanyi amma yanajin akan shukurah saide kome zai faru ya faru masallaci ya nufa da niyar ana tashi zai dawo

***
ba har muka ISO gida Sardauna bai sake mun magana ba sanin dama bayada, surutu yasa nayi shiru nima honr yayi aka bude get ya danno motar cikin gidan parking space ya nufa yay parking nayi nayi na bude na kasa shagwabewa nayi na kallesa"Yayana budemun baice komaiba ya rankwafo jikinmu na gugar juna ya budemun sai naji yace"washhh idona arikice na riko kansa"Yayana sannu menene ya fadamaka ido duk na rikice rumgumosa nayi na tallabo kansa na bude idanunsa ina busawa harshena NASA ina lasar idanunsa kara shigewa jikinta yayi ya rumgumeta gam"My Kanwata wayyo idona kuka ta saka masa ta rumgumesa"Yayana kayi hakuri wlh nayi ta dubawa banga komaiba mukoma hospital adubaka ganin yada hankalinta ya tashi tana kuka wani irin tausayinta ya mamaye zuciyarsa fuskarta ya tallabo"Sorry My Kanwas wlh banida komai dan nasha sweet ya fada yana had'e bakinsu da zafi zafi yake kissing d'inta lallausan harsheta ya kamo yana tsotsa yana zukar yawunta yana hadiyewa kallon junansu

suke batasan lokacin da ta kamo harshensa tana tsotsaba wani irin kissing sukewa juna kowa neman yawun dan uwansa yake yana sha sun manne juna suna rike da fuskokin junansu idanunsu suka lumshe sukaci gaba da tsotsar bakinsu sunajin wani irin gadin dadi na ratsasu 5minute zee ta zare bakinta anashi ta janye jikinta ta koma gun zamanta tana lashe yawunsa da ya b'ata mata saman bakinta ta kallesa tayi narai narai da idanu " My Yayana kamun wayo shagwab'e mata yayi "please my sweet baby kibani sweet na sha yanzune fa na fara shan yawun ya fada zai rumgumota da sauri ta fice daga motar tana dariya da gudu ta nufi part d'insu ghaisha tanajin wani irin farin ciki sai lashe bakinta takeyi tanajin zakin bakin nata da kamshin Sardauna ya baibayeta shiko Sardauna daket ya saita nutsuwarsa ya fito yana tangadi ya rufe motarsa direct part d'insu ya nufa bashida nutsuwar da zai shiga gidansu zee parlo ta shigo da gudu tana dariya parlon cike yake da jama'a kallonta suke gun ummi ta nufa ghaisha ta tareta ta fado jikinta"momy menene ina yayanki "ummina gashi can "masha Allah sannu Jan hannuta tayi suka nufi kujera ta rumgumeta zee tace" ummina ina farin ciki Daddy yace "zo momy gayamun me yasaki farin ciki ummi Raiyan kallon yarta take itama ranta fari tas yada yarta ta fita ba lfy kuma ta dawo da lfy tana farin ciki gashi kowa na sonta kawo saminu yace"momy kizo kibamu labarin me kika samu na farin ciki Nuhu yace"kanwata ni zo ki fadamu dariya tayi "to bari na fadawa ummina sai ta fada muku ta janye jikinta daga ghaisha ta Mike ta nufi gun umminta ta fada jikinta ta rumgumeta tana mata kiss"habibty ummina nayi missing d'inki ta fada da harshan larabci itama kiss ta mata tana mata bayanin Nisha da Sardauna da harshan larabci dariya ummi tayi takai mata dukan wasa Daddy yace"Raiyan meye momy tace wai? " wai ta hada Aiyusher Aure da Faisal ido ghaisha ta zaro tana dariya"kunji shirme mahabeer ne ya shigo da sallama zee najin muryasa ta Mike da gudu tayi gunsa sanin zata sakashi kunya yaja baya ya kama hannuta yana dariya"my zeena imiss u"i miss u too my heart Allah nayi missing dinka sosai my heart kasan me?? " sai kin fada rabin raina dariya tayi iyayan nasu suka bisu da kallo cike da sha'awarsu"my heart bari naje nayi wanka da sallah nazo na baka labari "ok amma na miki fadan kibar bari lokacin sallah na wucewa"ni my heart banason fada zanyi fushi Allah kara matse hannusa yayi anashi "yi hakuri my rayuwata muje na rakaki kiyi maza ina jiranki dariya tayi tana makale da hannusa har kofar d'aki ya rakata ya saki hannuta ta shige ya nufo gun Daddy yana zama Daddy ya kallesa "mahabeer Allah yama albarka kaci gaba da kula da momy kalli yada mahaifiyarta take farin ciki dariya mahbeer yayi ya rumgume Daddy ghaisha tace "mahabeer ina Autana Sardauna Najib fushi yayi zaiyi magana a kayi sallama gabaki dayansu suka amsa Daddy ya Mike cikin girmamawa ya tarbesu "Alhaji Ma'aruf barka da zuwa ghaisha ta Mike ta tarbi Hajiyar mashakurah hafeeza da gudu tace ta rumgume mashakurah taga tana kuka Ahmed da bandar suka nufi gun mahabeer duk zama sukayi cikin girmamawa ana gaigaisawa cikin girmamawa ghaisha ta kirawo maimu mai aiki ta cika musu gabansu da kayan motsa baki dasu ruwa da lemo Ma'aruf yayi gyaran murya yace "Alhaji Abdulmutallab kuyi hakuri da bayanin da ya kawomu ba mai dadi bane duk da kasan cewarta 'yata bazan rufa mata asiriba tunda bata rufama kantaba saboda batayi aiki da tarbiyar da na bata ayau ina nadamar turata k'asar turawa domun yin karatu ina Faisal akirawoshi dan inaso yaji komai daga bakina gabaki dayan parlon kallon mamaki da Al'ajabi sukema Alhaji Ma'aruf me suke shirin gani uba nacewa zai fallasa yarsa ta cikinsa lalla abun babbane Daddy ya kira number Sardauna tanata ringing bai daga ba ya kira kusan sau biyar ya kalli Najib"Najib tashi maza dubo Faisal yanzu ya maido momy maybe bacci yake jeka tasoshi mik'ewa, Najib yayi ya tafi Kiran Sardauna dan sun matsu suji meke faruwa.............✍🏻











💃🏻Yar ilu ce yar gaban goshin Kainuwa🤪

*💖💖👩🏻‍🦱ZEE BABY👩🏻‍🦱💖💖*

MALAKIN UMMU FAREESA

*DAN ALLAH KARKU FITARMUN DA BOOK WAJE*


*👉🏻28*


....Sardauna kwance yake saman makeken gadonsa ya nade cikin blanket sai juyi yake ya kama lips d'insa na k'asa yana tsotsa sai juyi yake Najib ne yayi knocking d'in kofar yanaji yaki tashi yaci gaba da juye juye yana lumshe idanunsa saida ya buga kusan so shida ya bude lumsassun idanunsa da suka kada sukayi jajur suka k'ank'ance dan jaraba tsaki yaja ya janye blanket d'in jikinsa ya sabko daga saman gadon ya nufi kofar ya bude kofar fuskarsa tam babu walwala ya zabgama Najib harara "uban me zan maka mutum baza'a barshi ya hutaba" bro Daddy yake kiranka bai jiraba ya juya dan karya zazageji duba yada idanunsa yayi Ja kofar ya rufe ya shiga bathroom fanfo ya kunna ya sakarma kanshi shower idanunsa lumshe ruwan na zubowa tsakiyar kansa sai ajiyar zuciya yake sabkewa yajima sosai kafin yayi wanka ya fito daure da towel jikinsa ya goge agaguce ya murza maiyukansa masu dadi da kamshi gashinsa ya taje baki sudik sai sheki yake wardrobe ya bude ya ciro 3qourter ya saka da Riga shart ya fesa turare wow nace Sardauna yayi mugun kyau ba kadan ba ko inda wayoyinsa suke bai kallaba ya nufi kofar ya bude ya fice ko key bai murza ba yana takunsa na kasaitattun maza niko nace wlh kayi Dr Sardauna dan ka kai kuma ka hadu ta ko ina yana fitowa direct part d'insu ghaisha ya nufa da sallama ya shigo parlon zee baby ya hango tana sanye da wata doguwar Riga yar kanti ruwan toka tayi Mata mugun kyau amma ta kamata kuma batada hannu tasaki gashinta har gadon bayanta tana kusan Mahabeer azaune tana rike da hannusa sai shagwaba take zuba masa yana dariya da aikin lallashi wani irin Abu yaji aransa kansa ya kauda karaf suka hada idanu mashakurah jitake kamar ta kamosa saboda mugun kyawun da Dr Sardauna yayi face ya hade ya kauda kansa sai lokacin ya lura da iyayanta cikin girmamawa ya nufi gun

iyayanta ya gaishesu sai lokacin yaga bandar da Ahmed cike da mamaki yake kallonsu gun Daddy ya nufa ya zauna kusansa hankalinsa gun zee sai lokacin zee taji kamshin Sardauna da zazakar muryasa yana cewa" Daddy gani yade lafiya kuwa kallonsa zee tayi karaf idanunsu ya sark'e da juna face ya had'e ya zabga mata harara ya kauda kansa fuska ta yamutsa ta turo baki"Yaya Sardauna ina ta nemanka fah banza ya mata ko kallonta bai sakeba mahbeer ya juyo da fuskarta gareshi "my zeena kin fiye tsokana me zai baki dariya tayi ta maida hankalinta kan mahbeer Daddy yayi gyaran murya "to Alhaji ma'aruf muna saurarenka kallon mashakura yayi "sai kuzo ku basu bayani tsuru tsuru tayi tana cicira idanu Sardauna cike da mamaki yake kallonsu Dan bai gane komaiba bandar ne ya taso yazo gabansu ya zauna mashakurah sai kif kif take da idanu"Dan Allah Dady ina neman gafaraku wlh nine na batama shukurah rayuwa amma kaddarace bada son ranmuba abinda ya faru kuwa shine wata rana Landon na dawo daga makaranta ina shigowa gida kasancewar mu biyarne agidan kowa da part d'insa nide ina ganin maza uku agidan mu saba Ashe cikon ta biyar macace lokacin da na shigo ba kowa kuka narikaji kasa-kasa kofar na duba naga shukurah aduke tana kuka na isa gareta cike da mamaki Dan ni bansan da maceba na na tambayeta daga ina tazo tace agidan take

cikinta yake ciwo kamata nayi muka tafi hospital Ana likitan yake cewa ya kamata takiyaye cin kayan da suke Kara mata ni'ima saboda tanada karfin sha'awa ya kamata akiyaye aka bamu maguguna muka dawo gida na rakata har part dinta na bata magani Tasha na mata sallama na tafi to daga ranar ne muka saba kullum muna tare idan bama zuwa makaranta har soyayya ta kullu tsakaninmu mai karfi Muke Dan tsotse tsotse har shaidan yayi rinjaye akanmu amma nine na lalata amma wlh ban taba aikata zina ba sai akanta tunda mukayi so daya muka kasa hakuri kullum sai muyi haka muka dauki tsawon lokaci hutunta na karshene da tazo ta koma ta sauyamun daket nake samu nayi har ta karasa wataninta ta dawo wlh narasa nutsuwa ina mugun mafarkai akanta kullum cikin nadama nake da neman gafara gun Allah gashi duk zaman da mukayi bansan yar wani gari bace Dan taki fadamun nashiga damuwa ga yawon mafarkai da nake akanta wlh natsani kaina na tsani zina sai gashi yau Allah ya hadamu harda

cikina wata biyu ajikinta gabaki daya kallamar shahada suka dauka suna tafa hannuwa Sardauna cike da mamaki yake kallon mashakurah da bandar Alhaji Ma'aruf yace" to kunji Dan haka abinda zance Abdulmutallab kuyi hakuri kunji yada Al'amarin yazo wlh nayi nadamar turata kasar turawa karatu ni tarbiya da naba 'yata ban taba zaton zata tazama karuwa ba awata k'asa wlh da ko a Nigeria bazatayi ba karatu balle kasar waje Dan haka Alhji kuyi hakuri ga kudinku anema masa yarinya mai nutsuwa tsarkakarka ya aura sukuma mazinatan sai su auri junansu bayan sun haifi shegen naso ace inada wata yar da nabashi "haba wlh abarsu munbar muku bayada ma'aruf baiba su amshi kudin sukaki Dole ya hakura ya Mike ransa ab'ace hajiyar mashakurah ma ta Mike sukayi musu sallama mashakurah sai kuka take tana nadama haka suka fito har harabar gida suka rakosu parlon ya rage daga Sardauna sai Ahmed da mahabeer da zee Sardauna ya zubama bandar idanu tashi bandar yayi ya nufo gun Sardauna zaiyi magana Sardauna ya Mike ya Saki murmushi" karkaban hakuri wlh ni bata zuciyata ko da haka bata faruba inada niyar fasa auranta Dan yau naje gun wacce zan aura kuma insha Allah ayau dinan za'a samun ranar aure da ita ya fada yana murmushi rumgumesh bandar yayi" nagode Dr bayansa Sardauna ya buga Dan shi Sam ko ajikinsa Ahmed ya taso "to bandar mutafi ko sakinsa Sardauna yayi ya kaima Ahmed dukan wasa"bazai tafi ba Dan rainin hankali jerawa sukayi zasu fita Mahabeer ya kira Sardauna juyowayayi fuskarsa babu walwala yace"bro nazone" jeka ka dawo baice komaiba suka fice yana wani shegen tako cike da jarumta da kuzari zee ta shagala da kallon Sardauna tanajin wani iri gashin jikinta sai mik'ewa yake har ya bacewa ganinta kanta ta kwantar kafadar Mahbeer "my heart" my zeena ya dai?

"Wlh Yaya Sardauna ya hadu dayawa komai nashi abin sha'awane My dear Nisha tayi sa'a ko my heart" kina nufin yafini kyau ne? " no my heart ni banceba ta fada tana saka mishi kuka" OK yi shiru my zeena wlh kukanki nasani adamuwa amma karki sake yabon wani agabana wlh inada kishi akanki duk da nasan bada wani Abu kika fadiba nagane nufinki kece kika zabo masa Nisha tun kafin haka ta faru ya fada yana goge mata fuska ya sakar mata kiss a goshi fushi tayi sai cika take tana batsewa sai daket ya shawo kanta ta hakura yana sata dariya ummi Raiyan ce ta fito kallonsu tayi tana murmushi su Daddy suka dawo daga rakiya har ghaisha Sardauna na rike da hannun Daddy zama sukayi Sardauna kusan ghaisha yaje ya Dora kansa kafadarta Daddy yace" Sardauna yanzu ya kenan nifa ku uku nayi niyar aurawa Dan haka babu fashi sai ka bazama nemo mata rada yay wa ghaisha zee ce tayi caraf ta Mike ta dawo gun Daddy "Daddy ai sunyi magana da Nisha a aura mishi ita har hira na rakashi d'azu kallonta Sardauna yayi ghaisha tace" Autana hakane? " eh

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login