Showing 63001 words to 66000 words out of 198792 words
Chapter 22 - ZEE-BABY-1-AND-2 COMPLETE HAUSA NOVEL By hausanovels001.txt
saida ya biya shopping mall yayi tsince tsince abubuwa ya kashe kudi ba kadanba kan kayan ciye ciye da turaruka masu uban tsada, yana zuwa gida part d'insu ya shige ya nufi bangaransa ya bude hadaddan d'akinsa sai uban kamshi ke tashi carpet malale ko ina ga manyan kujeru tamkar d'akin Amarya bed d'insa kadai abun kallone ledojin hannusa ya ajiye harda su ghaisha yama sayaya amma bashida niyar komawa part d'insu ayau yayi niya sai gobe kayan jikinsa ya cire ya daura towel ya nufi bathroom shower ya kunna yasakarwa kansa
ruwa yajima sosai kafin yayi wanka ya dauro Alwalla ya fito dan bacci yakeji sosai yau ga gajiya jikinsa ya goge ya murza maiyukansa masu kamshi da dadi yasaka jallabiya ya shimfida darduma ya tayar da sallah wayoyinsa har biyu sai ringing suke atare, raka'a hudu yayi ya dauki Alqura'ani ya fara karatu yajima sosai dan yafi awa guda yana karatu akinrasa yafi so goma sujada yayi nanma yajima yana tasbihi ga ubangijinsa yana nema gafara Allah yana kara neman kusanci ga Allah subahanahu wata'alah yanama Annabinmu Muhammad s,w,a kirari Yajima sosai ya dago ya daga hannuwansa sama yashiga kwararo Addu'a ya shafa ya Mike ya nufi gun wayarsa yana dubawa Wanda suka kirasa yaga bandar yamasa kira uku mashakurah kira hudu Daddy kira biyu Ahmed kira uku sai number da babu suna kansa ya dafe"oh sweet baby ko miyene kiranta yayi wayar akashe kin Kiran Ahmed yayi yana murmushi ya kira bandar shima akashe wayar kiran Daddy yayi bugo daya ya daga"Faisal ina ka shiga bakaci komai ba"Daddy gidansu Ahmed naje da nazo bacci ya daukeni" to maza fito ko tea kasha ko coffee maza mu har mun kwanta dare yayi" to Daddy ganinan"yauwa Dr dariya Sardauna yai ya kashe wayar ya nufo parlo Mahabeer na zaune da casbi ahannusa Dr ya kallesa "bro bakayi bacci ba har shabiyu? " wlh tunanin halin da zeena take ciki ya hanani bacci baki ya tab'e "ni na tafi cikin gida nasha coffee nazo na kwanta wlh bacci nakeji mik'ewa Mahabeer yayi"muje naga ko ta tashi ko tea na hada mata baiwar Allah bataci komaiba Dr Sardauna baice komaiba suka fito can ko lokacin da Sardauna yakira Daddy d'akin Aunty Amarya yake tanajin yana maganar Sardauna yazo yaci wani abu kar ya kwanta haka zuwat ta Mike ta saci kallon Daddy taga baya kallon gefenta cikin rawar jiki ta nufi idan ta boye maganin ta dauko ta shiga toilet ta ciro Wanda Sardauna zai tsallaka ta fice daga dakin direct dakin su khalisat ta nufa cikin sa'a taci Karo da khalisat ta fito shan ruwa ta kirata suka lab'e ta sinto ledar ta maganin "amshi babu lokaci da safe namiki bayani kiyi maza kije kofar parlo ki Barbada maganin wannan Sardauna zai shigo yanzu kinga darene babu Wanda zai shigo yanzu ki badeshi baki daya "momy na menene?? " kece zaki San ko nameye nan gaba badai sonsa kikeba? " eh momy"to maza jeki ba lokaci ta fada tana komawa
bangaranta da gudu khalisat ta nufi kofar parlo cikin rawar jiki ta barbade kofar parlon zuciyarta fari tas tana murna kuma daidai lokacin tajiyo murya Sardauna na tafe yana waya da gudu ta nufi hanyar bedroom tana cikin farin ciki Karo sukayi da Nisha"ke lfy me ya fito dake kuma kike irin wannan dariyar yawa zarara batace komai ba ta rab'e ta shige ciki Nisha kuwa ta nufi kitchen don hadama zee tea ta tashi ta shiga bathroom tayi wanka ko da khalisat ta shigo zee tana bathroom Dan haka ta haye bed ta shige cikin blanket hafeeza ma bacci takeyi Dr Sardauna ko suna fitowa suna dab da shiga bandar ya kira Sardauna ya daga rike hannu Mahabeer yai "bro ka jirani mana murmushi yai ya jirasa suna ta hirasu da bandar Akan yana tafe insha Allah nan da kwana biyar mahabeer ganin hirasu ba mai karewa baceba ya janyo hannu Sardauna "muje mana ciki wai kuyi wayar kiyawa Sardauna yai mahabeer ko ya fizge hannusa"to Nima kabarni naje naga Rabin raina ya fada yana murmushi ya nufi parlon yana sanyo kafarsa kansa ya Sara gabansa ya fadi da Sauri ya furta" Auzubillahi minal shaidaninr Rajim bismillahir Rahamanir la'ilaha innah anta subahanaka inni kutum minal zalumin ya fada yana shiga tsakiyar parlon kamar cira qaya yaji bayajin faduwar gaban sai kasala kadan kadan parlon shiru alamun kowa yayi bacci motsi yaji a kitchen ya nufin kitchen din Nisha na kokarin hadama zee tea ganin irin kayan dake jikinta yayi maza ya juyo ya fito ya lab'e"Nisha zee ta tashi ne?? dariya tayi "bro yo meye na labewa eh ta tashi tea ne zan kaimata ka ajiye hankalinka tana lfy dariya yayi"yauwa kanwata nagode ki gaishemun ita sai da safe na koma ya fada yana tafiya lokacin Dr Sardauna ya shigo akofar parlo suka hadu Mahabeer yace da ka hakura da coffeen mun koma? " haba wlh sai na hada nasha Daddyna fah yace nazo nasha kafada mahabeer ya daga yana dariya ya fice Dan yasan Nisha najin motsinsa zata Ari ta kare ficewa yayi Sardauna ya shigo direct kitchen ya nufa Nisha ma ta hada tea ta dauko ta nufo kofa ita zata fito shi zai shiga Karo sukayi saida tea din ya Dan zubar masa akirji saboda tsabar tsorata da kaduwa kasa motsi tayi tsawar da ya buga matane yasa ta Saki cup d'in ya tarwatse ak'asa jikinta ya dauki rawa ta rumtse idanunta"Dan ubanki me kike nema awanan Daren idanu ta bude jikinta na rawa"yaya kayi hakuri wlh ban San kana hanyaba ta fada fitsari na kwararo mata daga k'asan cinyoyinta idanu yazo ganin tana tsiyayar da fitsari dama rigar yar guntuwace cinyoyinta duk awaje saboda tsabar bakin ciki da haushinta wai fitsari take atsaye yasa ya Kara marinta ya harbata da Kafarsa ta fadi k'asa ya taketa ya wuce yabar kitchen din ya fasa shan coffeen ya fice daga parlon fashewa tayi da kuka ta Mike tana jamasa Allah ya isa toilet din parlor taje ta wanko jikinta ta dawo ta sake hadama zee wani tea tana hawaye. ta kawo mata zee zaune take ta kunna wakar larabci Tasha sirot da kwaya ba kadanba Nisha ta shigo tana matsar kwalla zee tace "ke dawa? " wlh yaya Dr ya dokeni zee cikin masifa tace"Allah ya isarmiki shege Dan iska halan matsarki yajeyi kika kiya ya manmareki ta fada azafafe tanama Nisha wani mugun kallo idanunta sunyi jajir? Idanu Nisha ta zaro" wlh A,A Dan na zuba masa tea ban ganiba ne wlh Allah bai tabani ba shi ba Dan iska bane ajiyar zuciya zee ta sabke ta rumgume nisha ta amshi tea din Tasha suna hira Nisha taje ta sake wanka ta canza rigar bacci suka kwanta suna hirasu har zee ta fara maye tana sambati tana kiran Sardauna Nisha ta Rumgumeta tana mata Addu'a jinta ko Aljanunta ne zasu motsa ahaka har bacci ya dauketa itama Nisha baccine ya dauketa suna rumgume da juna Asuba ta gari, Dr Sardauna na komawa ya saka kayan bacci yasha lemo guda ya haye saman bed ya shige blanket bai jimaba bacci ya daukesa mahabeer ma yana zuwa yayi alwalla ya fara sallahr nafila sai kusan karfe biyu ya gama yanama zee dinsa Addu'a Allah ya rabata da jinnu yajima kafin ya Mike yai shirin kwanciya bai jimaba da kwanciya barci ya daukesa asubah ta gari,
**********************************
*Bayan kwana ukku*
Bayan wannan lokacin abubuwa sun faru kamar su gabar Sardauna da zee baby ta dore Dan ko dawasa baya kallon inda take itama haka saidai ita rashinsa na mugun daga mata hankali har ta Dan rame sha'awarsa tana damunta ta rasa ya zatayi ta gaji da rashin Sardauna tana bukatarsa tanason gumin jikinsa tanason kamshinsa da sauraron zazagar muryasa da sweet d'in lips dinsa amma haka ta daure ta basar yada ya basar da ita suke rayuwa cikin k'unci da takura Nisha ko tun wahegari da sasafe ta gudu gidansu tace bazata iya rayuwa dukaba dama saboda zee ta matsa abarta ta dado tarinka zuwa makaranta daganan Najib ya kaita gida mahabeer dai yananan ras babu abinda ya samesa soyayyarsu da zee sai abunda yaci gaba suna kula da junansu zee said sangarta take maza iri iri zee ko ita da Aunty amarya basa wani shirin duk da ita zee sam batasan abinda ya faruba ranar amma washe gari fur ta hana ta zaman parlo gashi malam yace karta kuma nemansa sai wa'adi ya cika ita da khalisat farin ciki sukeyi Sardauna ya tsallaka magani jiran lokaci kawai sukeyi na wajan Daddy kuwa tun washe gari da zata hada masa babban aminin mairan karfe Alhaji Nuhu ya rasu a daura daga zuwa ganin dangi dama jikin tsofa ba lfy bace dashi gabaki dayansu mazan suka dunguma daura har Dr amma shi da mahabeer basu kwana ba su Nuhune suka kwana Daddy ko na can shine ya saka bata bashi maganin ba sai yaune zata bashi khalisat yaune zata wanke fuskarta da magani,
✨✨✨✨✨✨✨✨✨✨✨✨
da misalin karfe shida na Yamma Dr Sardauna ya bari asibiti ya nufo gida yana zuwa yayi parking ya fito ya rufe motar cikin takunsa na isa da kasaita ya yake tafiya cike da kuzari waya manne akunnesa sanye yake cikin suit bakake sunyi masifar yi masa kyau gashinsa ya Dan sabko wuyansa said zuba uban kamshi yake ya nufi part d'insu ghaisha a parlo kuwa baby kowa said zee baby zaune tana game awayarta su Aunty amarya ko tana kitchen Ana k'ulla mugun Abu sai nanah da nawwara na kallon Tv da sallama ya shigo parlon yana waya sai murmushi yake aciki na amsa sanin darajar sallama ko kallo bata ishesaba ya wuce ta gabanta ya nufi kujerun can nesa da ita Wanda ko kallon juna basayi ya zauna tunda na kallesa na dauke kaina zuciyata na bugawa da karfi saboda irin kalaman da na tsinto yana fadama mashakurah ga muryasa ta kashe mun jiki ga kamshinsa kasala naji ta kamani daurewa nayi naci gaba da sha'anina cikin dauriya kiran ya katse dama hira irin kayan da take sone sukeyi dan asatinan zai hado akwatina ganin ita dayace a parlon yasa ya Mike yana kiran ghaisha shiru bata amsaba ya nufi d'akinta zee tashi tayi jikinta amce tabar parlon bedroom ta shige Nawwara tace"yayamu mama tana gidan Daddah sai Aunty amarya a kitchen juyowa yayi ya nufi kitchen d'in har ya shiga kuma ya fito ya juya zai fita kenan khalisat ta fito daga d'akin Aunty Amarya fuskarta sharf da ruwa cikin farin ciki ta karasa"Yayamun Dr.............✍🏻
Idan nasamu dama zan k'aro muku zuwa yamma
💃🏻Year ilu ce🤪
*💖💖👩🏻🦱ZEE BABY👩🏻🦱💖💖*
*DAN ALLAH KARKU FITARMUN DA BOOK WAJE*
*👉🏻23*
....bai ko juyoba yaci gaba da tafiya hankalinta ne ya tashi da gudu Tasha gabansa "please yayamu ka tsaya don Allah bai ko d'agoba ya kalleta kuma baiyi magana ba y rab'ata ta ya wuce Dan haka kawai yarinyar yaji baya ra'ayinta kuma idan ka bashi haushi baya garajan magana gudun kar yama illah hankalinta atashe ta nufi kitchen gun mamarta jikinta ta fada ta saki kuka"ke lfy kuwa? " momy bai kalleniba kuma bai mun maganaba"innah lillahi wa'innailahir raji'un kiwa Allah da manzo s.a.w kibishi kimasa magana" momy wlh bazai amsaba karfa ya dokeni "to bari ajima zuwa dare kisake shegen yaro uban jarabar taurin kai ai mungodawa Allah tunda anyi mai wuyar ya tsallaka maganin jeki zauna yau sai ya amsa maganarki fitowa khalisat tayi tana murmushin jin dadi ta zauna a parlo zee baby kuwa tana shiga bedroom d'insu ta fada saman bed ta fashe da kuka wi wi da ta rasa ko na menene saida tayi mai isarta ta Mike taje ta wanko fuskarta ta dawo ta kwanta tana rawar sanyi blanket taja ta rufa tana karkarwa, Dr Sardauna yana fita part d'insu ya nufa ransa ab'ace yana shiga ya bude d'akinsa ya fada saman bed ya lumshe idanunsa ya dafe kansa ya rasa meke damunsa sai juyi yakeyi tsikar jikinsa na mimmik'ewa yanajin wani yanayi rasa dalilin hakan ya Addu'a ya shiga karantowa amma yaji feelings bai raguba mamaki yakeyi abunda yasashi yanayin ya rasa ko menene basarwa yayi ya lumshe idanunsa
Tunanin ko menene yaga Aunty amarya na zubawa cikin wata yar tukunya tana Kiran sunan Daddy tsaki yaja ya basar da zancan ya Mike saboda an fara Kiran sallah bathroom yashiga ya dauro alwalla ya k'ara fesa turare ya fito da Mahabeer suka hadu akofar gida suka nufi masallaci zee na rawar sanyi taji ana sallah haka ta Mike ta dauro Alwalla tayi sallah azaune saboda bata iya tsayawa ko fatiha batayi ba ta kwanta saman dardumar. bayan sallah isha ghaisha na zaune aparlo Nuhu ya shigo da sallama yana rike da hannusa meerah ta sakeshi ta ruga gun ghaisha"Oyoyo Meerah dariya tayi Nuhu ya zauna kusan ghaisha yana gaidata"ya su maryama? " suna lfy ina momy tazo muje yau ina gaiyatarta Ashe jibi ummi raiyan take isowa d'azu Daddy yake fadamun agun aiki? " eh jibi take zauwa hafeeza tace"babban yaya nima ina zuwa dariya yayi" to jeki kice ta shirya kema ki shirya ku fito da gudu ta nufi bedroom Daddy ne suka shigo da su Mahabeer atare khalisat ko kunya babu ta kalli Dr tace"yayamun sannu dan Allah maganin ciwon kai zaka bani da kallo suka bita baki dayan parlon har Daddy amma banda Sardauna Wanda ya kwashe mata iska yaje ya zauna kusan nuhu ya rumgumeshi kunya yasa ta Mike tabar gun mahabeer ya bita da kallo"babban yaya ina gaisuwa Nuhu yace"Dr namu wlh maryama na nemanka tace wai amarya ta mata kwace dariya yai"tayi hakuri gobe zan zagaya Daddy ya zauna yana musu dariya mahabeer tace"babban yaya ya gajiyar daura "wlh ai mun huta ai Aunty Amarya tazo ta zauna suka gaisa da nuhu tana tambayarsa gida, hafeeza tana shiga taga zee akwance k'asa tana rawar sanyi gunta ta matsu ta dafata "sister zazzabine kikeyi?bata iya ko bude idanu parlo hafeeza ta dawo da gudu
"Babban yaya wlh batada lfy jikinta zafi sai karkarwa takeyi ko idanu bata iya budewa da sauri mahabeer ya Mike "muje na ganta bedroom suka nufa nuhu ma yabi bayansu Daddy ya kalli Sardauna da yawani kwanta jikin ghaisha "Dr maza tashi ka kaita hospital dan Allah ka dubata da kyau momyna bansan meke damunta ba kwana biyu duk ta rame shiru yayi dan bayaso yayi musu ran Daddy ya baci kamar yada yaga yanzu hankalinsa a tashe ghaisha ta dagoshi ta masa nuni ya tashi badan yasoba ya Mike"Daddy idan sun fito ina mota ya fice yana fita suka fito Mahabeer ya daukota ahannu nuhu yace "Daddy ina Dr ne? " kuje yana mota shida nuhu suka fice Aunty amrya ranta fari Tas har Addu'a take Allah yasa ta mutu ghaisha ranta duk babu dadi ganin haka yace ta sanyo hijabi su bisu abaya Aunty amarya dan kar aga gazawarta itama tace zata Daddy ya ce ta zauna su Mahabeer suna fitowa Dr Sardauna na mota yana jiransu baya mahabeer ya zauna da zee nuhu na gaba Sardauna yaja motar honr yayi bakin get mai dagi ya wamgame masa get ya fizgi motar da karfi ya harbata saman titi Nuhu na Lure dashi bayason tafiyar kai ya girgiza ya dafa kafadarsa "Dr namu baidai ce komaiba har suka Iso hospital d'in ko gama parking baiba mahabeer ya bude motar ya fito da zee baki Sardauna ya tab'e ya bishi da harara yanajan tsaki Nuhu ya kallesa "Faisal meye wai? " ni babu komai ya fada yana fitowa ko kallonsu baiba ya kama hanyar tafiya da karfi karfi yake takunsa cikin isa da jarumta Nuhu kai ya girgiza wannan miskilin k'anan NASA na bashi dariya tsama ba masa komaiba yana gaba suna binsa abaya har suka shigo wani room da ke kusa da kofar shiga ya nunawa Mahabeer ya shiga yana biye dashi kwantar da ita yayi zai fita Sardauna yace"ka tsaya mana idan za'a mata allura sai ka riketa? " wlh Dr bazan iyaba sauran kukantaba kamata nasan idan kaine bata ganina bazatayi kukaba ya fada yana ficewa Dr baice komaiba ya dauko kayan gwaji ya fara gwadata ya shiga bata temakon gagawa saboda numfashinta dab yake da tsayawa ga wani irin zafi jikinta baya yasamu lumfashinta ya dawo normal ya dauko wani towel mai dan girma yaje toilet ya hado ruwan gumi ya zauna bakin gado daukarta yayi cak ya rumgumeta Riga da siket ne jikinta ko aka bai damuba domin cetoto dan jikinta zafin yayi yawa ya d'agota Riga ya cire mata sai breziya ya bar mata ya tsomo towel d'in aruwa ya matse yana danna mata ajikinta da cikinta gashinta ya rufe mata fuska ya ajiye towel d'in ya tatare mata gashinta ya daure mata ya birkitata yana danna mata abayanta sosai takejin dadin hakan dan zazzabin ya fara sauka tare da gumin jikinta ya juyota ya janye siket din yana danna mata acinyarta motsi ta fara ya kara rumgumeta gam yana danna mata saboda har yanzu jikinta kawai zafi bude idanu tayi karaf suka had'a idanu fuskarsa babu annuri itama had'e fuska tayi dan ta fara jin dadin ruwan zafin amma ta basar buge masa hannu tayi" dallah malam meye haka banaso bai sake dannawa ba ya fasa ya ajiye towel ya janyeta daga jikinsa ya kwantar da ita ya Mike bai ko kalleta ba mik'ewa tayi tana tasaka rigarta"wannan ai iskancine taya za'a ciremun Riga ta fada tana Jan tsaki shikam sanin duk abinda zatayi masa ya fita sabgarta yasa bai tanka mataba itama jin bai kulataba ta tuno da basu magana nutsuwart ta dawo tayi kwance tana turo baki allurai ya hado ya dawo gunta idanu ta zaro ganin alluran yasa gabana faduwa amma na dauki niyar hakuri yamun bazan bari yaga gazawata ba bai mun magana ba ya ajiye alluran yasa tattausan hannusa ya juyar dani ya kwantar ya janye siket dina inaji ina gani ya surkunamun allurai har biyu amma na dake ban ko motsaba har ya gama yabar gurin saida naji tafiyarsa