Showing 18001 words to 21000 words out of 135756 words
kuma bana tunanin za'akara min wani lokacin, captain ahmad tattaro hankalinsa yayi gabaki daya dan yasan yana wuya furta kalmomi musu yawa abakin oganna shi, Har inde kuwa yafara magana mai tsayi to maganar nada mahimmanci.
" Iska ya furzar, tareda shafa sumar kansa ya lumshe idoh, ya cikaba da cewa, ka tabbatar ka kira captain bala ya tabbatar ba'asamu matsala ba.
================
*Hanna* ce suka fito a lectures, kowa ya gaji likis.
Amira ce ta fara magana " inbanda jaraba irin na wannan malami ace monday za'afara exam Amma haryanzu yaki gama lectures, hmm ni wallahi nagaji nema, Ina gama exam kano zanbi yar uwata Sai Dan fara IT zandawo, bade tafiya zakiyi ki barni ba????? Amira ta amshe zancen, ahap Sai kuma kiyi, hameeda Wanda duk haushin su yacikata, itaba da karatu ba Sai shan wahaala, taama kasa tanka musu,
Harsunzo tsallaka titin wajen school din Wata mota tatsaya agabansu.
To be continued
Ur's
_z33yyb3rw3r_
*BIBIYATA AKEYI*
_
_Bismillahirahmanirrahim_
_
Writting by
© _zaynab_ _bawa_
( _z33yyb3rw3r_ )
Wannan shafin nakune yan uwana, nakaina Allah yabarmunku, *Anty* *rashida* *Anty* *ummi* da kuma *Anty* *sadiya*
Zaynab bawa na matukar kaunar ku
Page 21
*
Har sun "zo dasu tsallaka" titi, wanda ke wajan makarantar su" Wata motace tatsaya, a dai-dai gabansu. Sunyi matukar "tsorata ganin gilashin motar bakine wulik, zuge gilashin motar akayi" yaya jalal suka gani, hakanne yasasu sauke ajiyan zuciya, da mamaki fall aransu, na tambayar yaushe yazo, saurin bude bayan motar *hanna* tayi tashige, sannan amira tabi bayanta, juyowa yayi ya galla musu "harara , shine zaku barmin wannan uwar rawan Kan a gaba??? Kayi hakuri yaya, Allah nagaji ne baxan iya zagayawa ba" juyawa kawai yayi, a dai-dai lokacin" hameeda ta iso" bude motar tayi tashiga.
Amira yafaara kaiwa yasauke". Sannan suka wuce gida.
Agajiye kowa ya shiga gida, wanka suka fara yi, sannan sukaci abinci, Sai Bayan sunyi sallar isha" suna zaune, *hanna* ce" ta tabo hameeda ke ga yaya nan yazo, na tabbata zai amsa mana tambayoyin mu. Tashi sukayi suka nufi d'akin da yaya yake.
Isowa kafar d'akin sukayi, *hanna* ce ta kwankwasa kofar dakin" shigo kawai yabasu amsa shiga sukayi da sallama suka sameshi, azaune yana chartting, zama sukayi akusa dashi, ta gefen katifar da yake zaune, yaya yaushe ka isoh, dazu" yabasu amsa atakaice.
Yaya dan Allah kabar chartting dinnan magana mai mahinmanci zamu, kallonsu yayi sannan ya gyara zamansa, ehem Ina sauraronku!!!!
Yaya Dan Allah akwai wani cin amana da mama da umman kano suka taba yi neh???? Kallonsu yayi cikin mamaki me yasa kukace haka???? Tambaya kuma akan tambaya kabamu amsa mana, hade rai yayi Idan baku futo kun min bayani ba ya ya za'ayi na fahimta???
Ammah na yawan kiranmu da dangin maciya aamana" wani lokacin har ma cewa su adda hafsa da rabi'ah takeyi wai mu maciya amana neh" wai suyi hankali damu, cikin bacin rai yadago ya kallesu, itah ammanneh tafada muku Haka???? Ehh!! *Hanna* tayi saurin daga Kai, furzar da Wata iska yayi.
Sannan yafara cewa "mu asalinmu yan garin bauchi ne, kakaninmu asalin su yan dambam ne, sunan kakanmu Mal Ahmadu da matarsa rabi'atuh, Allah ya azurtasu da yara guda takwas, inda yawancin su tun suna yara suke rasuwa, guda biyu kawai Allah ya zaunar musu Wanda sune baba na bauchi da kuma abba na kano", wato muhammadu shine baban bauchi, da kuma yusuf shine karami wanda ake kiransa da abbah.
Mal. Ahmadu ne ya yanke shwarar tura babban bauchi, makarantar allo, sunyi yawo garuruwa kala-kala, inda akarshe suka yada dogon zango a bauchi, ganin zaman da yakeyi ne yasa ya nemi sana'a yafarayi, bayan sana'ar tafara karfi ne yasa ya yanke shawar shiga makaranta, alokacin yanada shekara sha daya yasa aka bashi aji hudu, sanda yayi shekara biyu sannan yagama makarantar primary.
Sai alokacin yasamu damar zuwa wahaifinsa, "ya yi iya kokarin sa wajen yin sana'a, yasamu kudin da zaisaya wa iyayensa abubuwa da yawa"
Alokacin yasamu kaninsa Dan kimanin shekaru takwas a duniya,
Bai dade ba yasake koma wa" dan yin karatun secoundry nasa.
Ahaka "yanayi yana zuwa kallon mahaifansa, Ana Haka Allah yayiwa mahaifiyarsu rasuwa, gaskiya sunji zafin wannan rashi Amma Haka sukayi tawakkali.
Bata dad'e da rasuwa ba Allah yakarbi ran Mal. Ahmadu, sunyi kuka na rashin mahaifi, damuwarsu daya" yadda yusuf zai kasance" dama bawani dangi ne garesu ba, Koda sunada su ma babu Wanda zai iya rike yusuf, dan kowa fama yakeyi da kansa.
Haka yatattari kaninsa, sukayi cikin garin bauchi ya rungumi sana'a sosai Dan ganin ya ciyar da kaninsa.
Ahaka yasamu aiki, awani shago nan yaci gaba da karatunsa, ba'a dad'e ba yasa kaninsa shima.
Ahaka Har yagama karatunsa, bedade da gamawa ba" yasamu aikin koyarwa, dan kunsan zamanin da basai kanada wani ba" kake samun aiki, bezaya ba yaci gaba da karatunsa na NCE a lokacin da yagama ne albashinsa yayi kwalri, tara kudin yafarayi Har yasaya fili, Ahaka suka hadu da Ammah, Ya aureta, dafarko sunfara zaman lafiya, inda daga baya suka fara samun matsala,
Sai da yayi da gaske tafuto ta nuna masa ita kaninsa ne bataso, aikuwa anan Wata babbar matsala takara tasaowa, Dan ya nuna mata duk duniya bbu Wanda yakeso kamar sa,
Bakin hali kala-kala tafara nuna masa"
Ganin Haka yasa yayansa turashi garin kano karatu, kodan hakan da yayi ma bawai ya Mata bane, Sai kuma ta tada rikici Kan, duk wani dukiyarsa takare akan karatun kaninsa, dan Haka adole tasa shima yakoma karatu, Amma hakan baisa yafasa turawa kaninsa kudin karatu ba.
Koda yusuf ya ga Haka sayya daina dawowa hutu, "Har Allah yasa yagama karatu, inda dama ya dade yana soyayya da umma (khadija), ba'ad'au lokaci ba baba yaje ya tambaya masa auranta, anyi biki masha Allah alokacin yaran Amma daya, Ahmad Wanda yaci sunan babansu tanada wani tsohon ciki takusa haihuwa.
Abba yasamu lecturing a buk inda yaci gaba da karatunsa na masters" ba'a dade ba umma tahaifi danta santalele " Wanda yaci suna aminu sunan baban umman kanwarta akaturo dan tayata zama, daganan kuma taci gaba da zama awajanta.
Irin halin Ammah ne yasa baba tafiya kasar waje karo karatu, kozai rabu da masifarta.
Amma Haka yaje yadawo, saima abinda yakaru, hakanne yasa abba yanke shawarar, yimasa maganr karin aure" baiyi musu ba Amma yashaida masa baida wacce zai aura, shaida masa yayi ya dad'e yana masa sha'war kanwar matarsa tanada hnkali, da farko " baba yaki ganin cewa abin kunya ne ya auri kanwar matar kaninsa , Amma daga baya ya amince, ba'a samu matsala ba aka fara gudanar da biki, Koda Ammah taji labari ba'ayita da dadi ba" dan cewa tayi tun yana talaka take tare dashi, Sai yanzu da yayi kudi, ganin ba Wanda yadamu da ita yasa ta lafawa, mama da baba suna matukar zaman lpy amma tana fuskantar kalu bale, daga wajan Ammah.
To be continued
_Ur's_
_Z33yyb3rw3r_
*BIBIYATA AKEYI*
_
_Bismillahirahmanirrahim_
_
Writting by
© _zaynab_ _bawa_
( _z33yyb3rw3r_ )
Page 22
*
Mama ta fuskanci kalu bale da yawa" awajan Ammah, kuma Har gobe tana kara fuskantar wani kalu balen.
Farko tafara Mata da makirci da yawa" inda saita ebeh abinci da siyar, sannan kuma tace mama ne ta ebe, lokacin da suke su kadai, hakan bata faruwa Sai bayan ya auri mama, hakanne yasa yafara yarda cewa mama tana eba masa abinci gakuma satar kudi da ake yawan yimasa.
Sosai suka fara samun matsala" inda ita mama batasan meye laifin ta ba amma baba ya canja kwarai da gaske, Dan ko maganar ta ba sosai yake amsawa ba.
Alokacin tanada cikin anty hajja, dake mama macece mai "sirri" yasa bawanda ta taba fadawa, duk yataru wani abinda take gani bata magana, kuma iya kyauta tawa tana kokari wajan yiwa baba biyayya" dan tabbas mama tafi umma hakuri.
Ana Haka Har Allah yasa *Wata* *rana* yadawo lokacin dawowarsa baiyiba, yadawo Dan yayi mantuwa ne, daga bakin kofa yahadu da Ahmad da kayan abinci niki niki, yana futa dasu,
Ga mai abin hawa yana jiransa Ana loda masa kaya, zai dashi yayi ya tambayeshi Ina zaikai kayan??? Cewa yayi zai Kai gidansu goggo ne (gidansu kakaninsa), baba yayi matukar mamaki cikin hikima ya tambayeshi ko yaune farko, aikuwa kunsan yaro" kuma bawai yasan meyake faruwa bane. Atake ya shaida masa ai yadade yana kaiwa.
Betsare yaron ba, Amma cikin zafin zuciya ya nufi dakin Ammah, abinda yaji ne ya matukar birkita zuciyarsa. Wato Ammah yaji suna tadi tadi da kawarta irin makircin da suke shukawa, Anan yaji shirin satar da take shirin yi masa na makudan kudi, kuma su daurawa mama Alokacin tace ta tabbata dole Sai ya saketa.
Wani irin tausayin mama ne yakamshi, da tuno irin abubuwan da yayi ta Mata, Har zai juya yaga Idan be tabbatar wa da Ammah yajita ba" toh wannan sace sacen da takeyi bazata daina ba, bude dakin yayi ya shiga da Sallama, amsawa sukayi, cikin kid'ima Dan basuyi tsammanin ganinsa yanzu ba.
Neman waje yayi ya zauna, tareda fuskantar su.
Kiji tsoron Allah halima duk wannan abunda kikeyi dan kikori Aisha Wanda ita ta daukeki amtsayin yar uwa.
Wannan abinda kikeyi bashi zaisani rabuwa da "itaba" mai yasa bazaki riki kaddara ki dauketa amtsayin yar uwarki ba' shiru tayi yayi ta mata magana mai sanyaya jiki hadeda wa'azi.
Alokacin jikin Ammah yayi sanyi, amma cikin zuciyarata, haryanzu son ta kori mama yana nan.
Sai bayan yafita kawarta ta kara zugata, Kan yacimata mutumci akan kishiya, Ana tadaura Mata aniyar zuwa gun boka, dan takori mama.
Mama taga sauyi sosai awajan baba, Dan wancen lokacin ma tabari akan sauyin yanayi, yasashi canja Mata.
Sosai baba yake nuna Mata kulawa, dan mama cikin ta bai hana Mata kula dashi ba yanda mama takasan ce, mace mai tsafta.
Wannan kulawa ba karamin cin ran Ammah yakeyi ba, ko lokacin suna su kadai bata samu wannan kulawa bah.
Bayan Wata biyu, ta haifi yarta mace, akasa Mata sunan umma, wato khadija Ana kiranta da (hajja), sosai baba ke nuna Mata soyayya, ma yarinyar dayake duk yaran Ammah maza neh, guda uku.
Haka rayuwa taci gaba da tafiya, lokacin inda yaran Ammah shida" uku maza uku Mata, yaya Ahmad shine babba yana aiki a lagos yanzu da matansa biyu da yara hudu. Sai yaya jabir da yaya unais da anty Maryam duk rana daya akayi auransu, Sai rabi ' ah da hafsat.
Yaran mama uku tanada cikin na hudu, Anty hajja itace babba tanada yara uku, Muhammad shine babba Sai Aisha (mamii) karamin shine aslam, Sai maman amal itama yaranta biyu, Anty hundatu ne Wanda bata dade dayin aure ba, ta auri babban dan umma.
Alokacin da aka haifi *hanna* ne kuma Ammah tadauki tsana ta daura Mata.
Alokacin ne tamata asiri, aka tura Mata aljanu Wanda bbu tabbacin akwai su ajikinta.
Sai saleem da abba.
Nisa wa yayi sannan yace kutashi kuje ku kwanta, dare yayi, tashi sukayi duk jikinsu yayi sanyi, danjin hali irinna Ammah.
Dakin mama suka nufa, da Sallama suka shiga ganin momy sukayi zaune akan kujera, harara ta watsa musu daga Ina kuke??? Mama daga dakin yaya jalal muke, sauke ajiyan zuciya tasauke, shine zaku Kai dare Haka??? , kallon agogo sukayi, shadaya nadare 11:00, mama wallahy bamusan dare yayi Haka ba, kuwuce ku kwanta,
Bamusu sum-sum suka wuce daki.
Bayan sun shiga ne" *hanna* tadauki wayarta ganin misscalls din najeeb tayi kusan 10, ganin dare yayi ne kawai yahana ta kiransa dan rabonta da muryarsa tun safe,
Kwanciya tayi cikeda kewarsa aranta.
Jarabawa suka fara sosai, kanta yayi zafi, kokadan bata da lokaci duk tarame.
Gashi ansa ranar auran Anty samha yarinyar umma.
A ranar yaune MG yake shirin dirowa kasar sa ta haihuwa.
Jirgi guda kasar Dubai ta bashi Dan tafiya da duk sojojinsa. Sai dai sukansu sunsan dasuyi rashin masu tsaro sosai, tareda Ummii da intisar da affan.
================
*Masarautar* *kano*
Shirye Shirye akeyi sosai na tarban *yareema* abdallah, kota Ina gyara masarautar akeyi, hatta garin kano sanda tasan da sunada bako inda, Har shugaban kasane yazo" dan taryansa,
Karfe uku 30:00 dai-dai jirginsu ya dira a Nigeria, garin kano.
Dumbin taron jama'a ne suka zo taryansa, inda daga masarautarsu ma gayya gudane. Sannan ga governor da sauran Manya, hadda shugaban sojoji wato chief wanda afuska Sai farin ciki yakeyi sosai, azuciyar sa kuma da dadama daya kasheshi a wajan.
Gabaki daya suka dugun zuma sukayi, masarauta.
To be continued
_Ur's_
_z33yyb3rw3r_
*BIBIYATA AKEYI*
_
_Bismillahirahmanirrahim_
_
Writting by
© _zaynab_ _bawa_
( _z33yyb3rw3r_ )
Page 23
*
Masarauta duka suka nufa" nan da nan kowani sako da lungu, na cikin masarautar ya dauka " *yareemah* ya isoh, dan ko ba'a fada ba yanda masarautar tadauki kidan algaitu da ko ina hakan ya'isa yasanar da isowar *Yareeema*".
Cikin fada suka nufa kai tsaye" inda mai martaba da mukarrabansa suke jiran isowarsu".
Sanda suka gama kwaasan gaisuwa, sannan suka nufi dakin da mai martaba da iyalansa suke cin abinci ".
Aranan idan kaga fuskan MG koda bai kasance mai fara'a ba" amma fuskansa ya nuna yana cikin farinciki".
Sosai aka tanadar musu kalolin abinci", duk daman sababban abu ne agidan sarauta, amma nayau daban yake".
Duk iyalan mai martaba suna tare awajan".
Abinci sukeci cikin kwanciyar hankali da farinciki, irin wanda suka dade basuji ba.
Dan sundau tsawon lokaci basu hadu haka ba.
Bayan angama cin Abinci ne " duk suka tare a falon mai martaba, tadi sukeyi Sosai irin na yan uwan da suka dade basu zanta ba".
Kana kallon wannan zuri'a sai sun burgeka" sun baka sha'awa irin yadda suke tadi kai ahade, dan awajan baza ka taba banbance cewa wannan dan wannan bane.
Affan ne ya kalli MG yace" ya yareemah wai Yaushe wannan antynmu mai sa'ar tadazo ne???? Kallon sa MG yayi" cikin tsolaya ya kashe masa idoh daya, eh ai ya kamata musanta yanzu gaskiya, nan da nan kamar wanda suke jira ayi magana suka hau kansa kowa so yake koda hotonta a nuna masa, dan sun tabbata tacika mai sa'a, samun miji irin yareemah yana wuya"
Gaban intisar sai faduwa yakeyi, Cikin zuciyarta tana addu'a Allah yasa itace wannan mai sa'ar",
Wacce naji sun kirata da anty surayya ne da karbi zancen, itace first born a yaran mai martaba.
Yareemah yakamata ka duba wannan zancen, tajuya ta kalli duk mutanen falon, sannan tace " ka kalli irin farincikin da muke ciki yanzu, kuma inada tabbaci da'akwai matarka a ciki, farincikin mu saiya fi haka, bakunan mu sayya fi haka budewa.
Duk danginna bamuda burin da yawuce" muga iyalinka kai kanka kasani duk zuri'ar mu babu mutumin da ya kaika soyuwa cikin rayukanmu.
Kokasan iyayaenmu basuda burin daya wuce ace" yau sunga 'ya' yanka, kokasan shiru kawai suka maka dan basasan abinda zai takura ka, amma bawai dan sun hakura da zancen auranka ba" shekarunka fa talatin da biyar 35 'yan mata sun