Showing 54001 words to 57000 words out of 135756 words

Chapter 19 - Bibiyata Akeyi book Complete 1 to end..txt

25 Nov 2024

7576

takaiga radio's station, "
Tv chennel's,"
Bana k'asarnan zallah ba har na k'asa she da yawa."
Zance gabki d'aya ya karad'e duniya. "
Kowani tasha kika bud'e labaran kenan." MG daya gajine da recieving call, kawai sai ya yanke call saidai massag gashi har yanzu yan wshing basu barshi ya d'an samu tym yakira *hanna* ba. "
K'anin mai martaba ne zaune a falon mai martaba,"
Magana yake yi, yana cewa, "
Yaya aduba wannan lamari gaskiya baida ce ace ya auri yar gidan talaka ba."
Mahaifin yarinyar fa malamin makaranta ne,"
Kaduba matsayi da dukiya irinna yareema ga mulki, arasa wacce za'a aura masa sai yar gidan malamin makaranta yanzu yaya maiyaci yabawa iyalinsa har za'a gani ayi sha'awar aure? "
Ran mai martaba in yayi dubu yab'aci, dan irin maganganun da k'aninsa yake fad'i ya6ata masa rai,"
Amma dayake dattijo ne mai hakuri yasashi sharewa yabarshi yaci yacigaba da cewa ai wannan yakamata yayi tunda munada 'ya'ya mata sai qhad'ashi da d'aya aciki, "
Mai martaba ne ya nisa sannan yace,"
Mai dukiya dakuma talaka duk Allah ne yayisu, "
Kuma inaso kasani koda yar bukka yareema yakawo yace yanaso toh ita zan aura masa."
Balle mahaifin yarinyar yanada rufiin asirinsa duk abinda ake nema wajen aure to wannan yarinya da mahaifanta suna dashi addu'a yakamata muyi Allah yasanya alkhairii acikinsa. "
Duk da bahaka yasoba amma jikinsa yayi sanyi." Ammah bata tsaya ko inaba sai gidan kawar ta aminiyarta,"
Hajiya lamii tana zuwa tafara mata birgima tana cewa wallhy malam yacuceni duk kud'in da nake she ace baimin aiki mai kyauba, "
Shege dan iska halama boka ne," 😳nikuwa nace kajimin amman nan dama ke atunaniki wajan malami kike zuwa toka kin yaudarii kankii. "
Dan wannan ba malamii bane."
Hajiya lamii ne tayita rarrshinta sannan tace tayi hakuri su k'ara jarrava wani suganii,"
Cikin kuka Ammah tace mai nake dashi dazanje wajan wani kefa kina kallo na tattare duk kada rori na nasayar naba wannan macucin,"
Menake dashi dazan je wani waje,"
Cikin lallashi tace mata kiyi hakurii mutafii wani kauye abincika kinsan irinsu basusan zqfin kud'ii ba sai mu bincika."
Cikin d'an gamsuwa da maganar ta Ammah tayi shiru sannan tace to yanzu yaya zanyi tace kodaiyaya kisan yanda kikayi kika nemo kud'ii koda bbu yawa, "
Gaki da yara ai Had'a musu wuta zakiyi sai sun nemo miki."
Ahaka sukayi sallama Ammah tatafi bayan tagama kitsa mata makircii."


Can wajen su umma kuwa sunanan suna shiri iya dai-dai gwargwado sunyi k'okari sosai wajan tanadarwa da baki abun buk'ata. "
Alokacinne anty maman amal tace ashirya *hanna* dan tasan dangin sarauta yanzu haka da mata za'azo kuma zasu bukqcii ganinta,"


Governor na garin bauchi kuwa yasha mamakin ganin cewa MG yasauka agarinsa batare da yasani ba, "
Amma yanzu ankirashi akan cewa jirgin mai martaba yakusa sauka,"
Hakama yakira abokinsa sarkin bauchi yasanar dashi. "
Aikuwa nan ma aka fara shirin tar6an sa."
Duk ilahiran masu tarban sarkii sun hallara a airpot na Abubakar tafawa balewa."
Kafin su taso daga kano kuwa sanda zance yakai kunnen fulani kakar MG bakaramin farin ciki tayiba, "
Tunda tajii zancen zuwa tace ai atafar sai anje da ita zataje taga jikanta."
Dake tana samun kulawa sosai kuma ga kud'ii yasa tsufanta baiyi yawa sosai ba. "
Aikuwa hakanne tafaru aka shirya hadda gwaggonsu khadija k'anwarsu mai martaba da sauran 'yan uwah zuwa garin bauchin yakubu."
K'arfe 12 :00 dai-dai jirginsu yasauka a airpot, "
Kai tsaye fada suka wuce,"
Basu d'auki lokacii ba akayi gidan su *hanna*, "
Alokacin angama shirye komai dan, har Abokan baba samada biyar sun zo tar6an baki da kuma wasu dattijai,"
Yan anguwarsu duk aka had'u, "
Isowarsu ba jama'ar anguwar ba kad'ai har makwabtan anguwar fitowa sukayi dan ganin wa'yannan mutane ak'ofar gidan da suka sauka ne yasa mutane shan mamaki basu k'ara sarewa ba sanda sukaga har Governor awannna tafiyar."
Da fara'a su Abba da sauran dajjijan nan suka fito suka tar6e su Cikin amince, "
Suka wuce falon Abba dasu,"
Su kuma matan Cikin gida suka wuce aka wuce shashin mama dasu,"
Ammah ta window take leqe yayinda wani irin bakin ciki yacika ta har wani dushu dushu take kallo. "
Data sani takeyi marar adadi dabata rabata da najeeb ba da tabarta dashi akan ace ta auri wannan dan banzan mai kud'in." abin bakin ciki ma yanda algaitu ya ciki anguwar tako ina algaita ansan dangin sarauta sun shigo, "gaba ki d'aya anguwar sai ta d'auki kamshii dan duk yanda suka wuce akwai masu bin wajan da turaren wuta na gaushi. haka al'adinsu yake har indai za'aje neman aure a gidan sarauta to anguwar sai tasan da zuwansu."
Jiri ne yafara ebanta Aikuwa awajan ta sulale ak'asa Batasan yanda takeba. "
Gashi hafsat tatafii makarnat rabi'ah kuma tana gidan anty maryam jiya da tazo tare suka tafii."
D'aki aka shiga nan akafara gaigaisawa Cikin mutumta juna."
Nan da nan bada 6ata lokacii ba suka fara abinda yakawosu lokacin an kawo musu kayan motsa baki, "
Alokacin Momy kadija kanwar Abba tatashi tafita sai gata tashigo da dogarawa har guda goma sha biyu kowa da akwatii ahannunsa yashigo dashi ajiyewa sukayi sunayi suna kirari a matar yareema ahaka suka gama suka fice da baya-baya,"
Kallon kayan suka tsyayi nan aka musu bayanin kan cewa kayan naganii inaso ne. "
Nan mama tace ai atafar kayan sunyi yawa saidai arage,"
Fulanii ce tace ai matar yareema ta cancanchi fiyeda haka dan haka k'arna k'ara jin wannan abun ai muma yar muce. "
Ahaka sukayi ta hira kamar da ansaba da juna."
Fulani ce tace aishin zaku kawomin kishyata naganta ne kosai nabi duk dakunan ina bincikawa, "
Dariya dukansu sukasa Momy khadija ne tace wa Fulanii,"
Umma wannan kishiyarde ta tsorataki tun daga jinta kika rikice gabaki d'aya saikin ganta. "
Dariya duka d'akin ak'asa sannan Fulanii tace to ba dolena naji kishi ba,"
Tanason kwacemun wannan had'adden miji wanda ni kad'ai keda irinsa. "
Nanma dariya akayi sosai, sannan anty mmn amal tatashi tashiga d'aya daga Cikin d'akunan,"
Can jimawa tafito hannunta riqeda *hanna* kanta rufe da qyale amma fuskanta abud'e yake kanta yana k'asa, "
Tundaga nesa suke kallonta suna masha Allah,"
Dan *hanna* tayi kyau sosai."
Zuwa tayi ta zauna acan d'an nesa dasu tafara gidansu ahankali Cikin fara'a suka amshe yayinda Momy khadija taja hannunta zuwa gabanta, "
Tsugunawa tayi ta rungumeta sannan tace welcome to our family dear,"
Hakan kuwa ba karamin dad'ii yayiwa su mama da umma ba sunsan sunakai 'yarsu yanda ake sonta Ahaka kowacce mata tayita rungumeta Cikin farin ciki. "
Daga k' arshe fulani tariqeta gam kamar za'a kwaceta tana cewa aikwa bari mu gaisa ko,"
Aikuwa *hanna* taji dad'ii janta datayi yisukeyi kamar zasu cinyeta dan kowanne acikinsu murna sukeyi sunga matar yareema pics kam alokacin tasha bbu adadii. "
Fulani kam riqeta tayi gam tana cewa Allah yamiki albarka,"
Allah yamiki albarka, abunda take nana tawa kenan hannunta na riqe dana *hanna* duka biyun wanda hakan sanda yayi sanadiyar da yasa *hanna* zubda hawaye. "
Data tuna lokacin da ko mashinshini bata da shi har abin gorii yazama sai gashi waiyau itane Cikin dangin mujinda zata aura suna sonta kamar su halaka."
Fulani ne talura da hawayen ahankali tasa gefen gyalenta ta share mata bata bari kowa yaganii ba ta Girgiza mata kai ko ba'a fad'a ba tasan kukan farin ciki takeyi. "
Dan duk wani labarinta moddibbo yasanr da fulani shi yasa takejin son yarinyarda tausayinta." Maza kuwa suma awajensu sungama yanke shawarar za'ayi aure nan da wata d'aya da satii biyu. "
Ahaka Cikin farin ciki aka gama komai kowa sai yaba halin kowa yakeyi dan daga wajen kowa anga halin karamcii," Daga mata aka futo da huhun goro da caton na mint da dabino, kowane gida abinda ake kaimusu kenan, "
Duk anguwar bbu gidanda baisamu huhun goro da caton d'in mint dana dabino ba kuma,"
Kuma ko ina idan aka shiga sai an shaida musu cewa na neman auren *hanna* ne, "
Duk gidanda aka shiga sai anyi mamaki dan tunda suke sunsan ba'at6a sallama ta cewa anzo wajen *hanna* ba sai gashi yau dogarawa ne ke raba goronta kuma wai hakanma goronda za'akai na neman auren wata shine ake rabashi kowane gida,"
Bayan angama komai suka fito sukasa akira musu matan su tafii. "
Nan wani bafade yashiga yasanar dasu da suka taso tafiyane fulani ta bud'e gyalen *hanna*ta cusa mata wani d'an karamin akwai sannan aka fita rakasu."


Bqyan sun tafii ne ya auwal yayi waya ya shaida musu tun jiya adda hindu ta haihu, ta haifa d'anta namiji wanda tun jiya yaki fada ne dan bayaso yaraba musu hankali. "








To be continued




Ur's
*Z33yyb3rw3r*
[9/24, 8:45 AM] ‪+234 810 367 2210‬: *BIBIYATA AKEYI*
_
_Bismillahirahmanirrahim_




_
Writting by



© _zaynab_ _bawa_
( _z33yyb3rw3r_ )


*Alhamdulillahi am feelling much better,"*
*Thank u all for d du'a, care.* *Massages, luv."*
*Luv u all* ❤. "




Page 48




*
Murnane ya 6arke agidan, ga murnar auran *hanna* ga kuma na haihuwar adda hindu."
Basu tsaya jan lokacii ba aka shaida masa akan ana sallamarsu su wuce bauchi. "
Dan ga baki d'aya yanzu zaman su zaifii yawa a bauchi tunda shirye shiryen biki za'a fara duk da da d'an sauran lokacii amma kuma yakamata komai afara tanadinsa da wuri."
Awashe gari kuma abba zai wuce kano," domin aikinsa. "
Umma kuma sai anyi suna zata koma."
Da yamma su adda hindu suka kamo hanya itada yaya auwal, "
Alokacin da su abba sukaji bakaramin fad'a sukayiwa su umma ba."
Abba ne yana fad'a yana cewa inbanda shashanci yarinya da d'anyan jego zaku d'aukota kuma jegon farko ko wanka bata samu ba. "
Fad'a sosai abba da baba sukayi,"
Hakuri kawai suke bayarwa dan suma yanzu sun fara danasanin cewa suzo da sukayi ga gari da nisa tsakani tafiyar samada 3hour. "


K'arfe shida dai-dai hafsa ta dawo daga makaranta,"
Ganin mutane cin cirindo acikin gidansu suna fitowa daga shashin mama. "
D'akin ammah tawuce nan tasamu ammah afalo a sume da gudu takarasa tana fad'in ammah, ammah, jijjagata tafarayi ganin bata ko motsi yasa tanufi fridge da gudu ta ebo ruwa ta fara yayyafa mata."
Koda ta yayyafa mata wata nauyayyan ajiyar zuciya tasake, "
Can kuma kamar wanda aka zabureta ta mike tana cewa na shiga uku wallhy boka ka cuceni daka bar yarinyar nan zatayi aure kuma dan gidan sarki Allah ya'isa tsakanina dakai."
Nan tayi shiru tafara dube dube afalon nan idonta yadauka kan hafsat da take binta da kallon tuhuma. "
Mai Mai ta kalmar tayi tace boka," boka fa kikace ammah? tana magana kuka na k'okarin kwace mata, "
Ammah dama kina zuwa wajen boka dan ya cutar min da 'yar uwa?"
Cikin in ina ammah tace um um malami nefa fa, "
Cikin kuka da tsawa hafsa tace ina bambamci ammah har indai zakije wajan wani da sunan ya cutar da d'an uwanka wallhy bokane ba malami ba," Cikin kuka tahad'e hannuwanta biyu👏 ammah na rokeku kudena 6atawa malamai suna idan zaku kirqsu da bokansu yafi, d'an jan numfashi tayi sannan taci gaba da cewa, "
Ammah nifa *hanna* bawai bana sonta bane karkiyi tunanin bazanji zafin cutarda ita da kikayi ba wallhy ammah dole sai naji zafi dan 'yar uwa tace,"
Hasalima abinda yasa nakejin haushinta irin yanda baba yake nuna bambamci atsakanine, bayaga haka bbu komai soyayyarta nanan dan k'are azuciyata."
*(gaskiya iyaye yakamata mu kula duk irin soyayya dake tsakanin yara har indai zaka nuna kafison d'aya ko kuma kafi kula da d'aya to jin haushin 'yan uwa zaishiga tsakani dan Allah iyayenmu akiyaye." nuna bambamci d mahaifin *hanna* *yakeyi tsakani shiyakawo jin haushi tsakaninsu amma bawai dan' d'aya baison d'aya ba dan Allah zank'ara roqon iyayenmu akan mukiyaye hakan idan yayi tsananin har gaba yake haifarwa tsakanin 'yan Uwa)*
Jikin ammah ne yayi sanyi, wani irin nauyin d'iyarta ne ya rufe ta, "
Yarda tahaifa itace ke gaya mata gaskiya."
Duk ilahirin gidan na tsaye abakin k'ofar ammah duk jikinsu yayi sanyi jin abinda yafaru,"
Shiga ciki sukayi nan idanuwan ammah yafara zuru-zuru kamar wanda tayi k'arya kodayake ai abinda tayi yafii k'arya. "
Kowanne yasamu wajen yazauna abinda su ammah basu saniba shine tun farkon fara maganar suke tsaye,"
Dan zuwa hafsa ganin mahaifiyarta akwance saita sakee k'ara wanda itakanta batasan lokacinda tayiba hakan yayi sanadiyar janyo hankalin gidan, "
Sun zo shiga sukaji abunda ammah ke fad'a wanda sunada tabbacin idan ta sun shiga bazasuji komai ba yasasu tsayawa."
Kuka sosai ammah takeyi takasa cewa komai."
Babane yayi gyaran murya, sannan ya kalli hafsa da kanta ke sunkuye ga baki d'aya kunyar kowa ya rufe ta yace. " Kiyi hakuri d'iyata nasan nayi kuskurenda mafi akasarin iyaye suke aikatawa, "
Ki yafeni bawai dan nafison *hanna* bane yasa haka,"
Dukanku ina sonku kuma 'ya' ya nane kuma inasonku dan haka Kiyi hakuri kicire komai aranki hakan bazata sake faruwa ba da ikon Allah. "
Cikin muryar kuka tace babana na yafe maka, dukda nima nasan irin biyayyar da *hanna* take maka nima bana maka amma in sha Allah daga yanzu zakazaka sameni me yimaka biyayya."
Allah yamuku albarka baki d'aya aka amsa da amin. "
Sannan yajuya da kallonsa wajen Ammah yace kin kyautawa rayuwarki,"
Kin cutarda 'yarki Wallhy nayi danasanin aurenki Allah ya wadai irin halinki hak'ika wannan magana tayiwa hafasat zafii amma kuma, Ammah ita tajawa kanta. "
Sunkuyarda kai tayi Sannan tace dan Allah kuyafeni wallhy son zuciyane yajamin haka,"
Nayi danasani wannan rayuwa da nad'aukarwa kaina, "
Wai yau yar cikane takemun nasiha ita take gwadamun abunda nakeyi ba dai-dai bane,"
Wayyo Allah na kaicona. "
Dan Allah kutaimaka ku naima mun gafarar *hanna* bansan dawani ido zan kalleta ba na cutarda ita tuntana jaririya,"
Wallhy har kunyar kallonta nakeyi. "
Jikin mama ne yayi sanyi tabbas tasan care Ammah ta shiryu dan ita tazauna da ita na kimainin shekaru ashirin da biyar 25 kuma tasan halinta tasan tunda tafara neman gafara to tabbas ta shiryu."
Dan tunda suke ko yi hakuri bata ta6a ji dai-dai da baba ta ta6a cewa ba. "
Babane yace gafarar *hanna* zaki nema dan ita kika cutar,"
Juyawa tayi gun *hanna* gwuiwo winta azube ak'asa tana neman gafarar ta, tana cewa *hanna* nasan na cutar da ke iyakacin cutarwa kiyafeni *hanna* hatta saurayinki da kuka rabu kwanakii ma nice silar rabuwarku ni nasayarda komai na mallaka na rabaku kinga Allah ya nunamin ikon sa kinga irin mijin daya baki. "
Kukane ya kufcewa *hanna* jin cewa rabata da najeeb akayi har yanzu sonsa bai ragu kokad'an azuciyar taba kuma haryanzu ko d'igon son MG bata fara jiba."




Tashi tayi aguje tabar dakin, wani irin tausayin kanta da najeeb ne yarufeta. "
Kuka tayi iyakar iyawarta dan yanzu abin yadawo mata sabo fill."
Dakyar umma ta lallasheta tayi sallah, Sannan tashiga tad'aurawa su adda hindu abinda zata samu sucii irin wanda akeso masu jego su sha. "
Tana zaune ita kad'ai ad'aki hafsat ta shigo, zama tasamu waje tayi Sannan tace *hanna* wato bazaki yafewa mahaifiyata bako,"
Nasan tayi laipy amma yakamata ki yafe mata. "
Ta nemi gafarki fa."
Ce miki akayi ban yafe mata ba."
Kin yafe mata ne amma baki gaya mata ba kinsan haryanzu kuka takeyi taki sauraron kowa gani takeyi in baki yafe mata ba, zata shiga wani hali,"
Nisawa tayi Sannan tak'ara cewa *hanna* kinsan yanda d'iya da mahaifiya suke duk laipynda ta aikata bazanso ganinta Cikin tashin hankali ba,"
*Hanna* plz kiyafe mata, "
Hameeda Ce tace *hanna* plz let d bygone be bygone."
No family is perfect we argue and fight, sometimes we stop talking to each other but *hanna* family is family, luv will alway's be there. "
Ganin sunason damunta kawai tafuce tabar masu d'akin basu bitava suka zauna ad'akin itada Hameeda."
Tana futa taga bbu kowa zuruf tashige d'akin Ammah kamar mai tsoron karwani yaganta, "
Azaune tasamu Ammah nata rusar kuka kamar ranta zai fita har wani dushi dushi take kallo,"
Zuwa *hanna* tayi tazauna agabanta Sannan tasa hannu tashare mata hawaye, "
D'agowa tayi tace *hanna* sa hannu tayi ala66anta tace shiiiishshsh Ammah kidena kuka na yafe miki Allah yayafe mana baki d''aya."
Cikin kuka tace *hanna* nagode, nagode Allah yamiki albarka, "
Amin *hanna* ta amsa Sannan tace Ammah dan Allah kimin alk'awarin bazaki sake cutarda niba,"
Kar sai na saki jiki dake ki k'ara cutarda ni. "
Ammah bama niba ko wani dan Allah karki k' ara cutarda wani,"
Girgiza kai Ammah tafayi kuka nak'ara k'ok'arin kwace mata tace *hanna* ki yarda dani na gyara halina wallhy yanzu ko kwaro bana iyajii zan cutar balle kuma d'an adam."
Jijjiga kai *hanna* tayi Sannan tace Ammah ciki abinci dan nasan rabonki da abinci tun da safe, "
Murmushi Ammah tayi tanajin son *hanna* nashiga zuciyarta,"
To 'yata jeki kawo mana abincin sai muci tare nasan kema bawai kinci bane dariya *hanna* tayi Sannan tace nikam Ammah complex zansha wollah bazanci tuwo ba. "
Ammah ne tamiqe tace mukam ai saida tuwo, bari kiga nashiga ne eba inyaso sai kishiga ciki akwai complex d'in ." K'arfe tara dai-dai su adda hindu suka isoh gabaki d'aya ta shigata, "
Jin tsayuwar mota yasa *hanna* dake d'akin Ammah mikewa tace su adda hindu sun iso,"
Ammah ne takalleta tace dama tana hanya ne, "
Eh Ammah yau ta haihu tafad'a ta zumud'i,"
Haihuwa shine dan rashin hankali zasu kamo hanya. "
Fita duka sukayi daga bakin hanya Ammah taga duk sunyi

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login